Free chapter · Read without an account
Part 21-22
بسم الله الرحمن الرحيم.
اللهم صلي وسلم على نبينا محمد.
*🖤AMNA DA SAFNA🖤*
Part 2️⃣1️⃣▶️2️⃣2️⃣
📱Writing✍🏼
Aisha G Umar
_*🌹𝑍𝑎ℎ𝑟𝑎-𝑡𝑢𝑙-𝑄𝑎𝑙𝑎𝑚🖋️*_
Shafa kan ta Ammu take yi a hankali, yayin da zuciyar ta ke tinanin wani abu daban, katse mata tinani Safna tayi sanadiyyar ɗagowa da kan ta da tayi, tana faɗin, "Ammu na ina zuwa kinji, ba daɗewa zan yi ba" da ido lawai Ammu ta bita.
Ba ta ɗau lokaci ba ta dawo da ƙaton paranti à hannun ta, ɗauke da kula da kuma plate mai zurfi da cokali a ciki, ijje sa tayi haɗi da buɗe kulan, ashe ferfesun hanta ne a ciki yaji romo sai tashin daddaɗan ƙamshi yake wayyooo😋.
Diba tayi tasa a mazubin sannan ta rufe, ta mayar gefe, zama mai kyau tayi a inda ta zauna ɗazu tana facing ɗin Ammu, "musamman dan ke nayi wannan ferfesun Ammu nasan zaki so shi sosai, yana ɗaya daga cikin abincin da Doctor ya umurta da ki dinga ci" murmushin jin daɗi Ammu tayi da yadda 'yar ta ke kulawa da ita yadda ya kamata, da itane kawai take iya magana mai tsawo.
ɗibawa tayi à spoon ta fara ba ta tana ci, sosai ya yiwa Ammu daɗi, Safna kuwa tana ba Ummee tana yi mata hira.
Fitowa daga falon yayi yana waya, sai dai ganin su da yayi yasa shi tsayawa yana kallon su, musamman Safna da take bawa Ammu abinci tana ta bata labari, sakin baki yayi yana kallon yadda take magana tana ta murmushi wani gurin kam har dariya take, "Ashe dama tana magana haka? har dariya take yi" ya faɗi a zuciyar sa.
"Yazeed kana jina kuwa?, Yazeed" daga can ɓangaren ake cewa jin yayi shiru, "Aliyu zan kira ka" kawai ya furta tare da sauke wayar a kunnen sa, ci gaba da kallon ta yayi, ya fara takawa a hankali kamar wanda ake kira, har ya isa kusa dasu idon sa na kanta, yana jin yadda muryar ta ke ratsa kunnuwan sa.
Tana gama bata, ta ijje kwanon gefe, Ammu kuwa sai murmushi take yi, ganin yadda Mahaifiyar ta ke murmushi, yasa ta cikin farin cikin da ta daɗe bata tsinci kan ta ciki ba, ɗauke da murmushi a fiskar ta tace, "kin ji daɗin labarin da na baki Ammu?" Tayi mata tambayar kamar tana jiran Ammu ta bata amsa, "eh yayi daɗi sosai" taji maganar sa gefen su, ba tare da ko jin motsin zuwan sa ba.
Da sauri ta juya duk da tasan muryar waye amma tayi mamakin furucin na sa, fiskar sa ta gani da murmushi abin da itama za tace bata taɓa ganin hakan daga fiskar sa ba, sai dai ɗaure fiskar da yake yi a duk sanda suka haɗu.
Ganin kallon mamakin da take masa yasa shi fahimtar ya saki layi fa, ɗauke idon sa daga kan ta yayi ya fiske, ya taho gurin Ammu ya durƙusa haɗi da dafa Keken yana cewa, "Aunty Maryam kina lafiya? Na daɗe ban gan ki ba" amsa masa Ammu tayi ta ido, wanda ba fahimtar hakan zaiyi ba, ɗauke ido Safna tayi daga kansa saboda takaicin maganar ta sa, ta ɗauki parantin dan kaiwa kitchen.
Shi kuwa Yazeed juyawa yayi ya bita da kallo, "kada fa ta raina ni dan ta ga na kalle ta?" Ya tambayi kan sa, sai kuma ya miƙe ya koma inda Safna ta tashi ya zauna, yana ƙure Ammu da ido, yana tuna lokacin da take da lafiya, tana da kirki sosai, shima yafi zama a wurin ta wancan lokacin.
"Aunty Maryam kin tuna lokacin da ki ka mana wani irin abunci, mema sunan shi?" Ya faɗi yana tuna sunan abincin, "yauwa Dambu" ya faɗi yana murmushi, yana ci gaba da cewa, "kin iya abinci sosai, haryanzu ban taɓa cin abinci mai daɗin na ki ba, ina fatan ki samu lafiya wata rana ki dafa mana abinci fiye da na da" kulle ido Ammu tayi da a lama itama ta tina wani abun.
Buɗe ido tayi tare da ɗago hannun ta a hankali ta ɗora kan fiskar sa, tana mai sanya masa albarka a zuciyar ta, ranar Asabar da lahadi ne kawai baya zuwa gaishe ta, amma duk ranar da Safna take zuwa makaranta sai ya shigo ya gaishe ta, indai har Safna tana nan kam baya zuwa, tana jin daɗin zuwan da yake yi gaishe ta.
Tsayawa tayi tana kallon su, da mamakin Tsayawar sa har yanzu a wurin Ammu, sannan ga Ammu ta ɗaura masa hannu a fiska, me hakan yake nufi? dan ita ta ma ji tsoro dan ta ɗauka faɗa zai yi saboda fitar da Ammu da tayi, amma sai taga saɓanin haka.
Bata ƙarasa wurin ba sai da taga barin sa wurin sannan, "Ammu lafiyan yaya Yazeed kuwa?" Ta faɗi tana zama a kujerar, sai dai murmushi kawai Ammu tayi mata ba tare da bata amsa ba.
AMNA.
Sallama suka fara ji ana ƙwalawa a ƙofar Gida tare da Ƙonƙosa wa, daga jin sallamar kasan ba lafiya ba, "waye yake mana irin wannan sallamar ko ƙaƙƙautawa babu haka?" Cewar Mamma da ta fito daga ɗaki, daidai fitowar Ummee ita ma daga ɗaki, a tsorace Ummee tace "Mamma jiya kwana nayi ina tinanin abun da Amna suka yi jiya, anya ba Folisawa bane kuwa?".
Zaro ido Mamma tayi a tsorace ita ma tace "zai iya yuwwa, amma dai yanzu muje muga su waye" "Mamma wai maganar me kuke yi ne?" Cewar Amna da ta tashi daga barci jin maganar da suke, hararar ta Ummee tayi tace "Tun da kin tashi sai kije kiga su waye ai" bata yi magana ba ta ɗau ƙaramin mayafi ta yafa ta nufi gate.
Tana buɗewa taga mutane, malaman makarantar su maza biyu da mata biyu, sai wasu da bata san su ba, maza uku mata biyu sai kuma police biyu maza, ƙure ta da ido su kayi ganin me kama da Baturiya ta fito, wannan kam ai bama kama ba Baturiyar ce.
Su kansu Malaman na su basu gane ta ba, saboda kasancewar ta mai hazaƙa da kuma rigima da wanda ya taɓo ta yasa kowani Malami ya san ta, amma rashin ganin ta da glass yasa su rashin gane ta.
Risina wa kaɗan tayi alamar girmamawa ganin Malaman ta tana gaishe su, amsawa su kayi police Kofur Habu yace, "Baturiya nan ne gidan su Amna Hussaini Baba da kuma Mubarak Hussaini Baba?" Cike da mamaki take kallon su, kamar bata san meya faru jiya ba, tace "eh nanne" "ok yi mana sallama da Baban ku" faɗin ɗayan police ɗin Kofur Ali, cike da mamakin hausar da tayi, "Baya...." "ya kika daɗe ne Amna daga ki duba suwaye?" Mamma ta katse ta da son faɗin baya nan.
Malamar su Amina tace, "wai dama Amna ce nan?" Ta faɗi cike da mamakin dama haka idon ta yake, wato shiya sa taji wasu ɗalibai na gulma jiya, sauran ma da mamaki suka bita, iyayen yaran sai magana a zuciyar su suke, wai wannan abar da ko jikin kirki babu, amma ita ce ta logwada musu 'ya'ya haka? kan tayi magana Mamma ta fito, zaro ido tayi tana sallallami, tace "Lafiya kuwa 'Ƴan-sanda abokan wasu?" Ta faɗi cikin rawar murya.
"Abokan kowa dai ko Kaka?" Cewar Kofur Ali, Mamma tace "ina Abokan wasu dai, ai in an ganku to da matsala" dariya kaɗan su kayi sannan su kace "Kaka zamu iya shiga daga ciki?" Jin maganar da sukayi yasa hankalin ta ɗan konciya kaɗan, domin inda da matsala suka zo sai dai ace a wuce station.
"Eh ah mezai hana? Bismillah" shiga sukayi dukkan su, after 5 minutes, Gaba ɗaya mutanen zaune suke kan shimfiɗar da Ummee tayi musu, gefe ma Ummee, Mamma, Mubarak da Amna ne, sai police ɗin da suke tsaye, gaishe da Mubarak da jiki sukayi, sannan suka tambayi Mahaifin su Amna? Mamma ta basu amsa, "Mahaifin su baya nan yayi tafiya".
Cikin Malaman na miji ne ya fara magana, "kamar yadda yaran ku suka sani mu Malaman su ne, mun zone sabida abin da ya faru jiya a School, ba a gaban mu ya faru ba, amma mun samu bayani daga sauran ɗaliban, wa'ennan su ne iyayen yaran" ya faɗi haɗi da nuna musu sauran mutanen.
Mahaifin Zanga ne yace, "Muna masu baku haƙuri akan abin da ya faru, tabbas yaran mu basu kyauta ba da suka tarunma yaro ɗaya sukai masa rauni" kallon-kallo Ummee da Mamma sukayi da mamakin jin maganar, mahaifin Jalo da shi yaron sa yafi raunana acikin su shima yace "duk da cewa muma an raunana mana namu 'ya'yan amma mungane su ke da laifi, amma dan Allah intambaye ku mana? dan Allah 'yar nan ta ku Mutum ce kuwa?".
Juyowa Amna tayi inda yake, tace "bawan Allah me kake nufi?" "Meyasa za kayi mana irin tambayar nan? Yanzu a gaban ka mutum ce ke zaune ko aljan?" Mamma ta katse Amna da faɗan haka, dan tasan Aminatun na ta, Mahaifin Jalo ya ƙara cewa, "gani nayi yadda tayi ma yaran mu luguden nama, kamar ba mutum yayi musu ba, wallahi kai ka ce wata shirgegiyar mota ce tabi ta kansu, numfashi ma da ƙyar ke fita, ai dole nayi tambayar".
"Koma dai Me Ɗan-iskan ɗan ka ya jawa na mu 'ya'yan, duk abinda ɗana yake shi ke sashi" cewar Uban Usy, cikin ɓacin rai Mahaifin Jalo yace "haba Malam taya zaka ce Ɗana ne sila kuma harda ɓatacciyar kalma a kan sa?" ai nan mahaifiyar Salman ta amshe "yaro na duk yafi naku yaran jin jiki, kuma duk 'ya'yan ku suka jamai, kunganni nan kullum sai nayi wa Salmanu faɗa akan ya daina biyewa sheɗanun 'ya'yan ku amma baya ji, gashi ambar ni da jinya".
Ai nan iyayen su Jalo suka hau cacan baki wannan yace wannan, wannan yace wancan, "kai ya'isa" kofur Ali ya daka musu tsawa, dakatawa sukayi kowa ransa ɓace, "Kaka shugaban mu ne yace mu kawo su, su baku haƙuri, saboda yaran su da kansu suka faɗi gaskiya da bakin su, duk da abinda 'yar ku tayi itama ba daidai bane ɗaukar Doka a hannu, itama muna gargaɗin ta da ta kiyaye ɗaukar Doka a hannu nan gaba, shine abunda ya kawo mu, dan haka zamu tafi, tunda komai ya kammala".
Godiya su Mamma sukayi musu, sannan suka ba iyayen yaran haƙuri, sukai sallama suka wuce, Kofur Habu ne ya juyo ya kalli Amna yace, "gaskiya Amna soja ne ya dace dake, wannan ƙarfi haka" ya faɗi yana murmushi, binsa da kallo kawai tayi ta wuce ɗaki ta barsu Mamma.
Mubarak ne yace "Ummee kin ga abinda nace miki ɗazu ko? Ai nasan da ƙyar su Jalo su yarda aiwa Amna wani abu, saboda sunji jiki wallahi" dariya Mamma tayi tace "kai Aminatu na da ƙarfi take sai kace wanda ta fito daga tsatson ILYA ɗan mai ƙarfi?" Cewar Mamma, "hmm" kawai Ummee tayi ta fara naɗe, shimfiɗun. Dariya Mubarak yayi Yace "Mamma tsoron Police ɗin ya tafi ne? ɗazu fa maganar ki Har rawa take yi" "kadai ji da jikin ka rago kawai" Mamma ta bashi amsa, suka sa dariya.
--------------------------------------------
Hmm ashe dai Yazeed na kaiwa Ammu ziyara a ɓoye, ko me yasa baya son Safna ta gan shi? Kuma Me yasa Mamma ƙin sanar da Safna hakan duk da tana iya yi mata magana ta ido?.
Ga dai yadda ta kasance ba'a kai ƙarar Amna police ba, sai ma haƙuri da aka basu, kuma kuna goyon bayan Amna?.
_*🌹𝑍𝑎ℎ𝑟𝑎-𝑡𝑢𝑙-𝑄𝑎𝑙𝑎𝑚🖋️*_