Free chapter · Read without an account

Page-16

by Aisha G Umar · “SANADIN ƘADDARATA”

*FASAHA WRITER'S ASSOCIATION*
     (*F.W.A)*©✍️
     ⭐⭐⭐

Ƙungiya masu aiki cikin salon hikima da fasaha gurin juya tunanin al-umma, kaifin alƙalumansu ya zarta takobi ©✍
___________________________________________________



بسم الله الرحمن الرحيم.
اللهم صلي وسلم على نبينا محمد. 




❁ 𝐒𝐀𝐍𝐀𝐃𝐈𝐍 Ƙ𝐀𝐃𝐃𝐀𝐑𝐀𝐓𝐀 ❁ 




Free book📓



By


*Aisha G Umar*
_*🌹𝑍𝑎ℎ𝑟𝑎-𝑡𝑢𝑙-𝑄𝑎𝑙𝑎𝑚🖋️*_




Page1️⃣6️⃣





Momy na kitchen Sadiya ta zo ta sameta, ganin damuwa a fiskar 'yarta yasa Momy dawo da gabaki ɗaya hankalinta kan Sadiyar haɗi da dafa kafaɗunta tana cewa, "masoyiyata me ke damunki haka?" Sai da Sadiya ta ɗago ta kalli Momyn fiskarta cikin damuwa ta ce, "Momy wai da gaske ni munafuka ce?"....

"Subhanallah 'yata wa ya faɗa miki haka?" Faɗin Momy, Sadiya ta kuma cewa, "wata ce Ina zaune a class bayan an tashi break, na hangota tana buɗe jakan wata, daga baya kuma mai jakar ta zo tana cewa ba ta ga calculatornta ba, shine ni kuma na ce, na gan wata ta buɗe jakan, na nuna musu ita, shine fah ta zazzageni tana cewa wai ni munafuka ce, kuma sharri na yi mata. Har da zan yi kokuwa da ita amma sai na tuna alƙawarin da ki ka ce in yi miki rannan, kin ce duk abun da aka min kar na tanka na rabu da mutum, amma Momy na ji haushi da na ƙyaleta".

Sai da Momy ta sauke ƙaramar ajiyar zuciya haɗi da murmushi ta ce, "ke ba munafuka ba ce 'yata, kuma na ji daɗi da ki ka ƙyale yarinyar ba ki rama ba, dama haka wasu yaran su ke akwai tsokana, suna ƙoƙarin yin komai don su nemeki da faɗa, amma abun da na ke so da ke yanzu, ki daina shiga abin da bai shafeki ba, sannan ki san da wa za ki zauna, ba ma makaranta kawai ba ako ina, saboda mutane sun kasance iri daban daban Sadiya, na yi farin ciki da ki ka riƙe min alƙawari duk da zuciyarki na son ramuwa, kamar yadda na saba faɗa miki, aduk lokacin da aka zalumceki kar ki ce don an yi miki ke ma zaki rama, ko kuma ki zo ki faɗawa wani abun da ya faru, a ah kiyi haƙuri ki bar komai a ranki, duk daran daɗewa za ki ga ribarshi, kinji?".

Amsa mata Sadiya ta yi da cewa, "Momy ko da ke ce kada na faɗawa?" Kafin Momy ta ba ta amsa wayarta da ke ijje a gefe ya yi ƙara, hakan yasa ta maida hankalinta a kan wayar, ta ɗauka tana shirin fita daga kitchen ɗin saboda ba ta picking call a kitchen, Sadiya ta yi saurin riƙo hannun Momy ta kuma cewa, "Momy ba ki ce komai ba, ko da ke ce kada na faɗawa?".

Juyowa Momy ta yi ta dubi Sadiya sannan ta sakar mata da murmushi ta ce, "ƙwarai kuwa 'yata, ko da ni ce kuwa, saboda akwai abubuwa da yawa wanda za ki iya jurewa ba tare da kin sanar min ba" Momy ta faɗi sannan ta juya ta wuce haɗi da amsa wayar, tasa a kunnenta.

Amma da ta kai ƙofar fita, sai zuciyarta ta buga, "me ya sa na ce ko da ni ce" ta faɗi a ranta, wani abu ya motsa a ƙirjinta na ɗan lokaci, sai dai ta girgiza kai kamar tana korar wannan tunanin, ta wuce tana magana a wayar.

Numfashi Sadiya ta sauke tana cewa, "to Momy insha allah zan cigaba da yin yadda ki ka ce, duk abun da za a yi min zan yi haƙuri, zan daure sannan kuma ba zan taɓa tada murya a kai ba, kuma ba zan faɗawa kowa ba, ko da ace ke ce, zan barshi cikin raina" ta faɗi kamar Momy na gabanta.

Kamar dai Momy ta yi gaskiya da ta yi tunanin me yasa ta cewa Sadiya haka?. Domin kuwa wannan amsar da ta ba Sadiyar ta riga da ta adana shi a wani ɓangare na memoryn kanta ba, wanda kuma hakan zai iya zama abun tauyi ga wani rayuwar Sadiyar da ke zuwa nan gaba.

BAYAN SHEKARU BAKWAI 7.

Babu abun da zan ce da ahalin Hajiya Rahama Momy, sai addu'a da fatan alkhairi, saboda sun ɗauke min nayin ɗawainiyata ta ko wace fanni, a wa'yan nan shekarun da na zauna da su, zama ne mu ka yi na daɗi, kamar dangi ɗaya.

A yanzu na zama budurwa 'yar shekara goma sha tara a duniya, ni da Asma'u sa'ata, yayin da anty Sadiya kuma ta ke da ashirin da ɗaya. A wannan lokacin aka sa ranar auren Sadiya, yanzu haka saura wata ɗaya kacal ya rage musha biki. 

Yayin da Dady kuma ya shirya komar da aikinsa gaba ɗaya zuwa garin Abuja, yana so yayi kusa da danginsa ya daɗe baya tare da su, ko ziyara yawan aiki ya hanashi, sannan yana son ayi auren 'yarsa Sadiya cikin dangi sosai. 

Hatta muma transfer ɗin makarantarmu ya kammala ni da Asma'u, burina shine ace yau I'm a Doctor, amma a wurin Asma'u kuwa lawyer shine fatanta, Anty Sadiya kuwa sai dai mu ce ABU Mai labule zata shiga, duk da ta sanar da mu cewa Faruq mijin da zata aura ya ce zata cigaba da karatunta ko da ya aureta. A ɓangaren addini kuwa, alhamdulillahi mun daɗe da sauke alqur'ani da wasu littafai.

DARE .

Mun kammala haɗe kayanmu gaba ɗaya, domin komawarmu garin Abuja gobe ne. Muna zaune a falo bayan mun kammala cin abincin dare, Momy ta dubemu ta ce, "my daughters maza ku tashi ku je ku kwanta, saboda gobe idan Allah ya kaimu da sassafe zamu kama hanya" cikin murna Sadiya ta ce, "aikuwa Momy, don na san ba zan iya barcin mota ba", Dady ya yi dariya ya ce, "to wani barci ma tafiyar da ba wani nisa gareta ba?"

Asma'u ta ce, "ni kam Dady ko na kwanta yanzu ma ba zan yi barci mai kyau ba, saboda murnan zan je inga Hajiya Kaka mai mitan tsiya" Dady ya ce, "ke Asma'u ki kiyayeni, Mahaifiyata ce zaki ce mai mita?" Dariya su ka sa Momy ta kuma cewa, "rabu da ita, zata je ta sameta ai, gashi dama Hajiya Kaka na cewa sun daɗe ba ta gansu ba".

Ni dai shiru na yi kawai ina kallonsu, saboda tun da tafiyar nan ya taso jikina a mace ya ke, i don't know what's the reason. Dubana Dady ya yi ya ce, "Nuriyyah ya ki ka yi shiru ba ki cewa komai?" Murmushin nan dai na yi masa ba tare da amsa ba, "to oyah, ku je ku kwanta maza" cewar Momy. Da to muka amsa sannan mu ka tashi zuwa ɗakinmu muna yi musu sai da safe.

"Asmee ya family house ɗinku ya ke?" na yi tambayar wa Asma'u bayan mun kwanta, sai da ta yi shiru kamar mai tunanin wani abu sannan ta ce, "family house ɗinmu babba ne sosai! Sashi uku ne, babban sashi shine na Hajiya Kaka wato mahaifiyar Dady, kankanmu ya rasu kusan shekara takwas yanzu, sai ɗayan sashin kuma na uncle Usman, ɗayan kuma na Dady ne". "Akwai mutane da yawa a cikin gidan?" Na kuma yiwa Asma'u tambaya.

Ta amsa da cewa, "eh toh akwai duk da wasu da yawa sun yi aure kuma ba a gidan su ka zauna ba, sashin Hajiya Kaka ita ce kawai sai yaya Abba da dama kin san a wurinta ya girma". Abba shine yaron Momy na farko, asalin sunansa Muhammad, ana kiranshi da Abba ne saboda ya ci sunan kakansu wanda ya rasu, ana yaye shi Hajiya Kaka ta amshesa, duk da cewa gida ɗaya su ke da zama da su Momyn a lokacin, kafin su zo Jos. Bayan an haife shi Momy ta haifi yara biyu amma ba su zauna ba, sun rasu, sannan Sadiya daga baya kuma Asma'u. Duk na san wannan labarin ne daga bakinsu Sadiya.

Asma'u ta ɗaura da faɗin, "sai sashin uncle Usman kuma, yana da matarsa mai suna Mama, suna da yara shida, amma yanzu uku ne a gida, sauran sun yi aure, to kin ga kuwa babu wani yawa a ciki, amma muna da 'yan uwa na kusa wa'yan da ba su yi nisa da gidan ba".

"har yanzu ba ku yi barci ba?" Cewar Sadiya da ta shigo yanzu, domin ba da ita muka shigo ɗakin ba, murmushi mu ka yi mata ina cewa, "Anty Sadiya kin san ba ma iya barci ba tare da ke ba", "haka ne ƙanwata" cewar Sadiya tana kwantawa a nata gadon. Na kuma cewa, "gashi kuma kin kusa yin nisa da mu", sai da ta yi ɗan dariya ta ce, "kafin kuma ku tafi ba?".

"Aaah anty ko da Asmee ki ke ne?" Na faɗi ina nuna Asma'u da ke gefena, harara Asma'u ta yi min tana dariya. Ƙarshe dai Sadiya da Asma'u sun yi barci amma ni ban yi ba, tunani na ta kewayawa cikin kai na, shin ya zamana zai koma a family house ɗinsu Dady? Za su karɓeni mu zauna tare? Ko zasu ƙi amincewa da ni? Ya zamana zai kasance a inda ban sani ba? Akwai wani abu da nake jin ba zai dace ba idan muka koma Abuja, duk da ban san farin ciki ne ko akasinsa ba. Bana son wannan tunanin amma ko yaushe sai ya dawo min kwatsam....



Last page.
___________________________________________________

Hmm ya komawa family house zata kaya? Kuna ganin zasu yarda da Nuriyyah kuwa? Kun dai ji abun da Nuriyyah ta ke ji a ranta.

Mu kasance a next page don jin me zai faru gaba?





_*🌹𝑍𝑎ℎ𝑟𝑎-𝑡𝑢𝑙-𝑄𝑎𝑙𝑎𝑚🖋️*_

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.