Free chapter · Read without an account

Kamar da wasa pg 17

by Fatima Isah · KAMAR DA WASA

KAMAR DA WASA 💘

          



             Fatima Isa

              


              Page 17




Da kallo ya bisu har sai da motarsu ta tsaya a parking space, sannan a hankali ya lumshe idanunsa. Wani irin abu, wanda shi ma bai san ko na meye ba, yana tokare masa kirji.
Sai da Khalid ya buɗe masa ƙofa kafin ya buɗe idanunsa, ya kuma ƙara sauke su kan yaran nasa da suka nufo shi, ita kuma tana tsaye tana kallonsu.

"Oyoyo Abienmu! Ka taho mana da ice cream ɗin? Uncle Khalid, ina yake?"
Dariya Khalid ya yi, yana shafa kan Iman da ke maganar, sannan ya ce:
"Sorry dear, Abie ya manta. Ayyuka yau sun yi masa yawa. Amma ni yanzu zan je in kawo muku."

Baki suka washe cike da farin ciki.
Sai da ya fito daga mota kafin ya kama hannayensu, ya jawo su jikinsa cike da ƙaunar da yake musu. Sai da suka iso dab da Naana, kafin cikin sanyin murya ta ce:

"Sannu da zuwa, ya aiki?"

Cike da salon nan nashi mai rikita mata zuciya, ya ɗago idanunsa ya sauke a kanta. Tun ba yau ba, ya san Naana yar gayu ce mai son ado. Fuskar nan tata taci kwalliya, dan ko baka tsoron Allah, ta yi kyau bakin gwargwado.

Ya ɗauke idanunsa daga kanta nan take, can ƙasa  leɓe ya ce.
"Alhamdulillah."

Ko da yake maganarsa bata fito sosai ba, amma haka ta yi mata daɗi. Yana gaba tana binsa a baya, Khalid kuma na ɗauke da tarkacen da suka dawo da su.

Sai da suka shiga babban falon farko kafin ya tsaya tare da yaran. Kamar wanda baya son magana, ya ce:
"Ki shirya su. Yanzu zamu fita. Kada ku bata mana lokaci."

"Oh to, amma Hamma, abinci fa? Yanzu suka dawo."

Sai da ya fara tafiya kafin ya juyo ya ce
"Idan muka je can ma yi dinner. Ki shirya kema."

Daga haka bai ƙara cewa komai ba, ya ci gaba da tafiya abinshi.
 Abinda bai haura minti 30 ba suka kammala suka fito parlor suna jiran ya fito basu fi minti 5 ba ya fito cikin kananun kaya da suka zame mashi jiki ko da yaushe sun amshi jikinshi. Top ɗin ta fitar da faɗaɗɗan kirjin shi mai ɗauke ɗa murɗaɗɗen ɗamtse.
Baiyi masu magana ba kawai ya nufi hanyar fita haka ya nuna masu tafiya zasu yi.
Suna fita daga falon  suka samu an jera motocin su a gaban gida, Khalid ya kama kujerar gaba kusa da direba, yara a baya ita kuma Naana ta zauna gefe. Shi kam ya jingina da kujerar yana satar kallon yaran, duk da ba yawan magana,amma  kaunar da yake musu na bayyana a kan fuskarsa.

Hanyar tafiyar ta kasance shiru, sai karar motoci da hasken fitilun birnin Lagos da suka ƙawata daren. Iman ta dora kanta a kafaɗar Abie tana cewa

“Abie, ni fa yunwa nake ji sosai.”

Sai da ya ɗan juyo ya dubeta, sannan a hankali ya ce
“Yanzu zamu je inda za mu ci abinci. Ki yi haƙuri, princess.”

Ƙarshe suka isa gaban wani wuri mai ɗauke da haske da tsari Freedom park (Lagos Island) Koda suka shiga ciki, kamshin turaren iska da sanyin AC suka tarbe su. Ginin ya sha ƙyalli, fitilu na haske kamar taurari, mutane cikin yan gayu masu ji da kansu suna ta zirga-zirga.

Yaran suka yi ta tsallen farin ciki suna cewa
“Wow! Uncle Khalid, this place is beautiful!”

Naana ta yi 
murmushi tana duban Shattima, zuciyarta na bugawa da wani yanayi da ta kasa fassara shi. Ko da ya ɗago idanunsa suka haɗu da nata, ta ƙasa daurewa ta sauke nata ƙasa.

A nutse ya ce mata
“Ki zaɓa musu abinda kike so, sai ki ɗora naki a kai.”

Daga haka ya zauna yana kallon yadda suke ta farin ciki da walwala. Khalid ya riƙa yi musu hotuna da wayarsa, shi kuma ya jingina, hannunsa ɗaya riƙe da wayar shi. A cikin zuciyarsa kuwa, wani irin sanyi ya keji kamar an cire masa wani nauyi da ke daskarar da shi tun dawowar shi daga Abuja.
Ma’aikatan wajan ne suka dinga girmamasu kowanne cikin uniform ɗin su mai tsabta. Kallon farko suka yi masa, kowa ya gane ba ƙaramin mutum bane. Ba wai saboda kayan da ya sanya ba, amma irin natsuwar da ke tattare da shi, kamewar fuska da girman hali.

“Good evening, sir. You are welcome.”
Ɗaya daga cikin waiters ya durƙusa da girmamawa, yana mika menu.

Shattima bai ce komai ba, sai kawai ya ɗaga hannu a hankali, Khalid ya karɓi menu ɗin. Izzar nan tasa ta isa ta sa su nutsuwa. Naana ta ɗan yi murmushi tana jin yadda ma’aikatan ke ta kallon su, musamman shi, kamar wani babban mutum da suka saba gani a talabijin.

Su Minal kuwa suna ta faɗin sunan abincin da suke so. Iman ta riƙa cewa.
“Abie, I want pizza! And ice cream please.”

Juyo da idanunsa ya yi, ba tare da ya motsa fuska ba, ya ce:
“Khalid, order it for them.”

A haka ya jingina, hannunsa ya haɗe a kirjinshi, yana duban sararin ɗakin. Mutane suna ta kallonsa a gefe, wasu ma suna ta magana a hankali:

“Commander Shattima ne wannan fa… na ji labarinsa.”
“Wallahi kai, sai yanzu na tabbatar yana da wani irin kamewa.”

Naana ta ji wata irin izza da alfahari ta lullubeta kasancewar ta kusa da shi, ganin yadda kowa ke daraja shi.

Da aka kawo abinci, ya ɗan ɗaga kai ya dubeta
“Ki kula da su. Ba na so su yi hayaniya a wajen nan.”

Ba tare da ya ɗaga murya ba, amma maganar tasa ta isa ta sa yaran suka nutsu, suka fara ci a hankali.

Naana kuwa, duk da cewa zuciyarta ke harbawa da son tattaunawa da shi, ta kasa buɗe baki. Wannan kamewa da izzarsa sun yi mata nauyi har sai da zuciyarta ta ce.
“Lallai wannan mutumin, idanunsa kaɗai sun isa su hanaka maganarka.”

 Khalid yana tsaye ɗaga gefenshi kamar yadda inda ya matsa za'a sace ogan nashi, cikin sanyi murya ya ce.

"Sir, what should we place for you and Madam as your order?"
  Sai daya ɗan ja ajin daya saba kafin ya saci kallonta ba tare daya ɗago ba ya ce.

"Give her everything that is done for us."
 Duk da bai faɗi suna ba amma yasan da ita yake dan haka kafin ma ya tambayeta ta nuna mashi abinda zai kawo dan tasan waye Hamma bai cika son tarkacen abinci ba. Fried Rice and Chicken with Chicken Salad sai gasashen kifi.
Babu ɓata lokaci akazo aka jera masu shi gwanin sha'awa.
Naana ta ɗauki spoon a hankali, zuciyarta na ɗan rawa saboda kasancewarta kusa da shi.

Shi kuwa Shattima ya ɗauki fork, yana kallon farantin da aka ajiye masa. Bai yi magana ba sai da ya ɗan ɗaga kai ya ce:
“Ki zuba min salad ɗin ko?.”

Kalmar tasa mai sauƙi ta ratsa kunnuwanta kamar wani umarni da ya wajaba a bi. A sanyaye ta ɗauki spoon ta zuba masa, hannunta na ɗan rawa saboda yadda yake kallonta cikin natsuwa.

Bai ce komi ba sai kawai ya ɗauki spoon ya ɗan ɗiba, ya ɗanɗana a hankali. Kafin ya ci gaba daci hankali kwance.
Ganin bata ci ya juyo gare ta cikin murya mai nutsuwa ya ce
“Ki ci naki mana. Kada ki zauna kina kallona.”

Naana ta ɗan sunkuyar da kai, ta ɗiba a hankali ta kai baki. Duk da cewa abincin ya yi mata daɗi, zuciyarta na harbawa kamar ana bugun ganguna a cikinta.

S Y Shattima ya ɗan ɗaga kai ya dubeta, ba tare da murmushi ba, sai idanunsa masu sanyi da zurfi. Ya ci gaba da cin nasa cikin nutsuwa, har sai da ya gama rabin farantin kafin ya ɗan tura shi gaba ya ɗauki gilashin ruwa.

Yaran suna ta surutu a gefe, amma su biyu, kallonsu da ya yi yasa suka yi shiru ba wanda ya ƙara magana. Sai  jin karar spoon da fork suna bugun faranti a hankali.

A ranta kuwa, Naana ta ce
 'Shi kuwa, duk da ya ɗan ci, zuciyarsa ta kasa yin sanyi gaba ɗaya. Akwai wani abu da yake tunkudawa a zuciyarshi, amma izza da kamewarsa sun hana shi bayyana'


#Son zuciya

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.