Free chapter · Read without an account
Chapter 5
by Amanarcool · AKWAI SILA
đź’¦ AKWAI SILA đź’¦
BY AMANARCOOL
YOTA ID/021
PAGE 9-10
Gurin ya yi shiru na ɗan lokaci, Jiniyo da Joriyya sai huci suke. Jiniyo ya fara ƙoƙarin ƙwace jikinsa ya daki Joriyya direban ya ƙara riƙe shi yana faɗin,
"Jiniyo kayi haƙuri, kada ka fara wannan ganganci ka sa ƙaramin abu ya koma babba, duk da tana ƴar uwarka taɓa ta ba zai haifar da ɗa mai ido a tsakaninku ba".
Jiniyo ba ya gane abin da ake faɗa saboda zuciyarsa ta rufe, idanunsa sun yi jajir tsabar ɓacin rai. Ya nuna Joriyya da yatsa cikin rawar murya ya ce "Ke Joriyya ke ni kika yi wa haka a matsayina na ɗan uwanki? Ni kika zubar wa da mutunci a gaban wannan dabba? Kika mari ne saboda shi Joriyya?".
Matsowa ta yi gabansa kamar wata cikakkiyar budurwar da take jin ta isa daidai take da kowa, cike da raunin murya ta ce "Na mare ka ne saboda ka taɓa shi. Na mare ka ne saboda ka zubar da abincin da na kawo masa. Na mare ka ne saboda na fahimci kana son ganin kukana fiye da farin ciki" Ta ƙarasa maganar cikin hargagi da ɗaga murya kamar wata babbar mace.
Jiniyo ya zaro ido "Ni? Ni ke son ganin kina kuka? Joriyya anya baki samu shafuwar aljanu ba kuwa? Anya ke ce? Kalamanki sun girmi shekarunki".
Joriyya ta girgiza kai, hawaye suna sauka
"Eh kai ɗin, akan me za ka takurawa rayuwata? Kar ka manta ni ba mallakinka bace, ni ba abin da ka ƙirƙiro bane, kana iƙirarin cewar kana son farin cikina, sai gashi yau ka yi mini abin da bazan taɓa mantawa da shi ba, ka bani mamakin da ban taɓa tunani ba". Ta juya tana kallon mahaukacin da ke tsaye gefe yana ɗan karkarwa.Yana kallonta tamkar yaron da aka ɗauke wa abincinsa.
Idanuwansa sun cika da ƙura, sai dai duk da haka akwai haske a ciki, haske mai kama da fargaba da wani guntun farin ciki.
Jiniyo ya kalle shi da idon ƙiyayya ya ce
"Wallahi ka sake matsowa inda take zan…"
Kafin ya ƙare maganar, mahaukacin ya yi gaba kamar zai faɗi a gabansu, hannunsa na rawa, babu kalma, babu magana, amma idonsa ya tsaya a kan Joriyya kamar yana son faɗin abu, kamar yana tuna wani abu mai zurfi. Sai kawai ya miƙa mata hannu a hankali tamkar jariri.
Jiniyo ya yi tsalle ya ce "Kada ki kuskura ki taɓa hannun sa, Joriyya kada ki taɓa hannun wannan mutumen yana ƙoƙarin shiga tsakaninsu".
Kafin ya ƙaraso Joriyya ta riƙe hannun mahaukacin, ji ta yi kamar an jona mata wutar lantarki, shi kuma ya sauke wata ajiyar zuciya mai tsayi, mai zafi, mai kama da kuka da murmushi a lokaci ɗaya, zame hannun shi ya yi a nata ya zube ƙasa, dafe zuciyarsa ya yi yana jin wani nauyi na raguwa a zuciyarsa na tsawon shekaru.
Joriyya ta rusuna tana girgiza shi
"Ka tashi mana, kayi min magana, kayi min magana"Ta faÉ—a cikin kuka.
Jiniyo ya ƙaraso cikin sauri yana faɗin
"Ki matsa gefe, ki matsa ki bar shi".
Miƙewa mahaukacin ya yi da ƙyar, ya ja numfashi, ya kalle Jiniyo da idonsa da suka canza launi, muryarsa na fita ƙasa-ƙasa kamar sabuwar murya ya ce "Ka bar ta".
Dukkan su suka tsaya. Jiniyo ya É—an ja da baya, Joriyya ta rufe baki cikin tsoro, karensa kuwa ya soma ihu yana zagaye su tamkar yana kare wani sirri da ba su sani ba. Mahaukacin ya É—an É—aga yatsarsa yana kallon Joriyya, idonsa sun rikice, muryarsa ta fara fitowa da wahala yana faÉ—in
"Kar ki tafi…"
Kafin ya ƙarasa ya faɗi gurin a some
Ihu Joriyya ta kurma "Ku taimaka mana, ku taimaka mana".
Direba ya zo da sauri da robar ruwa a hannunsa, ya yayyafa masa a fuska nan take ya sauke a jiyar zuciya yana buɗe idonsa a hankali. Joriyya ta ce wa direban "Ɗaga shi zaune" zaro ido ya yi ya ce "Shalele duka fa yake yi, naje garin ɗaga shi ya shaƙe ni? Shalele ki tashi mu koma gida tunda dai ya tashi".
Baƙin ciki da zafin kishi ne suka sa Jiniyo ya tsaya cak babu baki, babu ƙarfi sai kalmar da mahaukacin ya faɗa take dawo masa a kunne "Kar ki tafi…" Ji yake ƙirjinsa ya yi masa wani irin nauyi, mai fushi da tsoro da wata sabuwar fargabar da bai taɓa jin irinta ba suka yi masa dirar mikiya a zuciyarsa.
A hankali mahaukacin ya tashi zaune kamar babu abin da ya faru, ya fara wasa da kayan dake baje a gurin da yake tarawa, nan hankalin Joriyya ya kwanta, ganin Jiniyo ya ɓarar da abincin da ta zo masa da shi ne, tasa direba ya tsallaka bakin titi ya karɓo masa biredi. Jiniyo ji ya yi idan ya ce gaba da tsayi a gurin komai zai iya faruwa cikin ƙunar zuciya ya bar wajan, sai dai ya ƙullaci wannan mahaukacin a ransa, mugunta ce take zuwar masa kala-kala da zai yi masa domin huce haushin abin da Joriyya ta yi masa akansa. Direba ya karɓo masa biredin ta miƙa masa ya karɓa cikin rawar jiki ya fara turawa bakinsa kamar wanda ya shekara bai saka komai a cikinsa ba, sai yanzu ta ji natsuwarta ta dawo, ta miƙe a hankali ta ɗauki flask ɗinta ta bar gurin, buɗe mata mota direba ya yi ta shiga, sannan ya shiga ya ja motar suka nufi hanyar komawa gida.
A hanya direba sai sauke ajiye zuciya yake yi yana kallon Joriyya a madubi bai ce uffan ba, sai dai yana tunanin kamar yarinyar tana buƙatar addu'a domin abin da take yi ya wuce haddi. Ita kuwa kanta a jingine yake da kujera, idonta a rufe, zuciyarta ɗauke da nauyin abubuwa uku, mahaukacin, Jiniyo, da marin da ta yi masa. Da isar su gida kafin ma direba ya tsaya, aka buɗe ƙofar falon da zai sada ka da cikin gidan da ƙarfi, Daddy ne idanunsa sun rine, ya fito da sauri kamar wanda ya ji labarin an yi masa kisan kai.
"Shalele zo nan yanzu".
Ta fito daga mota a hankali, jiki a sanyaye kamar wadda ƙwai ya fashewa a ciki.
Momy ta biyo bayan Daddy fuskarta a ɗaure ta ce "Na faɗa maka tun farko Auta yarinya ce mai zafin zuciya, ba kowa ne lokaci ya kamata a riƙa yi mata wasa da dariya ba, damar da aka bata ne ya sa take yin abin da taga dama. Ka ga abin da muke tsoro yana shirin faruwa yanzu, tunda har ta san ta fita da kanta zuwa gurin wancan mahaukacin".
Daddy ya tsare Joriyya da idanuwansa masu kaifi "Ina kika je? Waye ya baki izinin fita? Gurin wancan mahaukaci kika je ko? Kin san abin da kika aikata kuwa?".
Ta buɗe baki za ta yi magana sai hawayen da ta maƙale suka fara sauka.Ta durƙusa da sauri. "Daddy kayi haƙuri, ban je gurin sharri ba, ban yi abu da nufin cuta ba".
Momy ta ɗagota tana jijjigarta kamar za ta ɓallata "Ke kin haukace ne? Gurin mahaukacin ne ba gurin sharri ba? Muna tunanin ke yarinya ce mai hankali sai ga shi…"
Sai ta kasa ƙarasa maganar ta juya ga Daddy cikin ƙunar rai ta ce "Abubuwan nan sun yi yawa. Tunda ta kamu da sha’awar tausayin wannan yaron gabaɗaya ta sauya, kamar ba Joriyyata ba, tana yin abubuwan da bai kamata ace mai ƙananun shekaru kamar ta na yi ba".
Daddy ya shaƙi iska ya fitar da ƙarfi. "Ba zan bari ta lalace a idona ba, ba zan zuba ido na ga tarbiyyar da muka fara yi na zubewa ba." Ya juya ya kalli Joriyya.
"Ki yi ƙoƙari ki dawo kan hanyar da ta dace. Ina son ganin hankalinki ya kwanta, zuciyarki ta samu nutsuwa. Dole ne na tashi tsaye akan wannan lamarin, dole ne in yi ƙoƙari wajan ganin na raba ki da zuwa gurin mahaukacin nan".
Zuciyarta ta tsinke kamar an yanka ta ce
"Daddy ni É—in?".
"Ke É—in" ya ce cikin tsawa
"Ba zan barki ki lalata rayuwarki ba, ba zan bari ki sake kusantar wancan yaron ba, ba za ki zubar mini da mutunci ba".
Ta lumshe ido, zuciyarta na buɗewa, kalmar wancan yaron ta dake ta fiye da komai. Raɓa su ta yi ta shige ciki tana jin zafi sosai a ranta
Jiniyo ya shiga falon gidansu ran shi a matuƙar ɓace. Mahaifiyarsa na zaune kallo ɗaya ta yi masa ta san cewa ran shi a ɓace yake. "Lafiya kuwa Jiniyo? Naga ranka a ɓace haka?". Ya tsaya ya kalleta da idon da suka haɗa zafi da ciwo ya ce
"Mama Joriyya ta yi mini wulaƙanci, ta tozarta ni saboda wani tangaran da ban san ko ɗan uban waye ba, mahaukacin banza".
Hajiya Munira ta ce "Wani kuma? Shi ne ya sa kake ɓacin rai haka kamar wanda ubansa ya mutu?" Jiniyo ya zaro ido zuciyarsa na bugawa kamar ana kaɗa gangar salla "Joriyya ce ta mare ni a kan wani mahaukacin, ta kai masa abinci, ta tsaya masa, ta riƙe hannunsa!".
Hajiya Munira ta dafe ƙirjinta tare da jinjina kai a hankali, zuciyarta cike da mamaki da tashin hankali "Subhanallah! Yarinyar nan akwai abin mamaki" ta ce cikin rawar muryar da takaici. Ta kalli ɗan nata gabaɗaya fuska a kumbure ta yi ja saboda marin da ya sha."Jiniyo mari fa? Kana mi ƙaramar yarinyar za ta mare ka? Me ya haɗa ku da har za ta iya ɗaga hannu ta kwaɗa maka mari haka?".
Jiniyo ya yi shiru, idanuwansa sun gama bayyana ɓacin ran da yake ciki, zafin marin ba wai a fuska yake ba a zuciya yake, a mutunci "Na rantse Mama" ya ce cikin muryar da ta shaƙu da zafi da fushi,
"kamar zuciyata ta fashe lokacin da ta taɓa shi gaba, ta riƙe hannunsa, ta dube ni kamar ban da wani ƙima a idonta rangaɗa mini mari kamar wani ɗanta".
Hajiya Munira ta ɗaga kai ta dubi shi cikin murya mai ɗauke da ɓacin rai ta ce "To gaskiya dole a je a tattauna wannan abin Joriyya ta fara shiga wata hanya da ba ta dace da ita ba. Wannan abu bai kamata ba, tun yanzu ne ya kamata a hana ta yin wannan kasadar, yarinya sai ka ce mai shafuwar aljanu?" Ta miƙe tsaye cikin zafin rai, ta ɗauki mayafinta "Mu tafi gidan nasu, ai ni ban san da haka ba sai yanzu, Anty ba ta faɗa mini ba, yarinya ƙarama tana neman tsokanowa mutane rigima". Ta yi maganar tana fita daga falon Jiniyo ya rufa mata baya.
Momy na zaune idanunta sun kumbura saboda rashin bacci da tashin hankali. Sallamar ƙanwarta ta ji Hajiya Munira sai Jiniyo dake bayanta fuska a ɗaure kamar matashi da ya sha ƙunci a kasuwa.
Momy ta ce "Munira ke ce da safiyar nan? Allah ya sa dai lafiya? Sannu da zuwa".
Munira ta zauna fuskarta É—auke da damuwa suka gaisa kafin ta ce "Na zo ne saboda Joriyya. Akwai abin da ya faru yau tsakaninta da É—an uwanta kuma abin ya yi girma da yawa". Momy ta lumshe ido, kamar ta san me za a ce.
Munira ta kalli Momy kai tsaye ta ce
"An samu rashin fahimta tsakanin Joriyya da ɗan uwanta, inda ta kai ga har ta ɗaga hannu ta mare shi, abin bai yi mini daɗi ba sam, a matsayin su na ƴan uwa ban so suka fara samun saɓa ni har haka ba, da na tambaye shi me ya haɗa su? Shi ne yake gaya mini akan wani mahaukaci ne ta mare shi".
Momy ta sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi ta ce "Innalillahi wa'inna ilaihim raji'un wallahi abin nan ya isheni Munira, yanzu Joriyya ce ta mare Jiniyo?" Ta maida duban ta ga Jiniyon ta ce "Kana zaman me da har za ka bari ta mare ka?" Shiru ya yi ya kasa magana, ta kuma cewa "Ka yi haƙuri Jiniyo, in sha Allah komai zai daidai, ku yi ta addu'a Allah ya raba ta da wannan masifar".
"Amma na yi mamaki da jin wannan zance, kuma shi ne baki sanar da ni ba?". Momy ta ce "Ki yi haƙuri a ruɗe nake shi ya sa, tana yin abubuwan da ba ta taɓa yi ba ne, kamar wata mai shafar aljanu. Tausayin wannan mahaukacin ya rikita ta, Na'ima ta ce idan da yiyuwar ta koma gurin ta da zama sai a tura can ɗin, ko Allah zai sa rashin ganinsa ya sa ta daina jin abin da take ji". Jiniyo ya runtse ido yana ɓoye zafin da yake ji, kenan rabuwa zai yi da Joriyya? Nan take ya ji zuciyarsa kamar an ɗaure ta da sarƙa. Bai so ya nuna ba, amma fuskarsa ta riga ta tona asiri halin da yake ciki, nan ya ji ya ƙara tsanar mahaukacin nan tare da alwashin sai ya azabtar da shi tunda shi ne ya yi sanadiyar da Joriyya za ta iya barin ƙasar nan.
A mugun hasale Jiniyo ya fita zuciyarsa na zafi kamar wutar da aka kunna ana zuba mata fetur. Matsala ɗaya ce ke damunsa mahaukacin nan da ya ƙwace masa Joriyya, kai tsaye ya nufi gurin mahaukacin da wani irin duhun fushi da muguntar da yake jin sun shige shi lokaci ɗaya, bai tarar da shi a cikin bolar ba, ya tsaya yana waige-waige sai can ya hange shi cikin wani kango dake kusa da bolar. Ya ƙarasa da sauri cikin kangon idonsa sun yi duhu sosai, tsayawa ya yi akansa ya ce "Wai kai ne kake son ɓata mini farin cikina ko?".
Mahaukacin ya É—ago kai a hankali, idonsa sunyi haske, muryarsa na fita da wahala ya ce "Kar ki tafi...."
Jiniyo ya ji kalmar ta ƙara masa zafin zuciya. Ya yi wani irin tsalle ya ture shi da ƙarfin da bai taɓa zatar yana da shi ba, Mahaukacin ya faɗi hannun sa ya bugu da dutse.Ya saki ƙara kamar ƙaramin yaro.
"Idan ka sake ko da kallonta ne sai na ƙwaƙule maka ido, wawan banza daƙiƙi kawai". Ya ƙarasa maganar cikin ihu da hargagi.
A hankali mahaukacin ya ɗago da idonsa yana kallon Jiniyo, da ƙyar ya ɗaga hannunsa da ya bugu wanda alamu ke nuna kamar ya yi targaɗe a hannun, ya dafe kansa ya fara ihu, Jiniyo ya tsaya, tsoro ya daki zuciyarsa na ɗan lokaci, cikin mugunta da rashin imani ya kuma sa ƙafarsa ya harbi mahaukacin tare da taka masa hannun da ya bugu, mahaukacin ya saki ƙara mai ƙarfin gaske. Karensa ne ya shigo gurin da gudu ya nufi Jiniyo, cikin zafin nama Jiniyo ya bar gurin, karen ya rufa masa baya, bai yi nasar cimma sa ba ya faɗa motsarsa ya ja ta da gudu ya bar gurin.
Amanarcool ✍️
***