Free chapter · Read without an account
Chapter 7
NA MUKA DOSIq
S-Reza ✍️
Chapter 7️⃣
Ɓangaren Sara kuwa farin ciki take yi sosai burinta kawai gari ya waye a bar mata gida ita kaɗai tayi wanka sannan ta dafa abinci taci, kuma taje gurin Ziyach ta sanar masa da wannan abun farin cikin. A haka barci yayi gaba da ita cike da mafarkai masu daɗi. Da safe kuwa Mommy ta sayo mata sabon buroshi da makilin da sabulun wanka da soso. Sannan ta haɗa musu abun kari kamar dai ba ita ba. Tana yi tana sauri domin tana da gurin zuwa mai muhimmanci. Ko lokacin da Sara ta tashi har ta gama komai. Idan da ada ne da duka zata tashe ta, sannan ta ɗiba mata abincin kaɗan tana ci ta turata waje ta rufe gidan nata, ko kuma shi Daddy ɗin ya korata waje. Amma yau sai gani tayi Mommy ta kama hannunta ta kaita har gurin da zata wanke baki, bayan ta gama wanda har jini sai da bakin yayi. Ta zaunar da ita a ƙasa ta kawo mata abinci tace idan taci ta kwanta kar ta fita ko ina yanzu zata dawo. Ita dai Sara sai gyaɗa kai take kamar ƙadangaruwa. Bayan Mommy ta fita ne tayi wanka ta saka kayan da ta nuna mata sannan ta zauna a ɗakin tana ta murmushi ita ɗaya. Lokaci ɗaya kuma tunanin taje gidan su Ziyach ya faɗo mata domin da shi ne kaɗai zata raba wannan farin cikin da take ciki. Ai kuwa tayi wuff ta bar gidan da gudun ta, tayi hanyar gidan su Ziyach.
*ZIYACH*
Ko tsoro baiji ba ya nufi gidan su Sadiq abokinsa domin karɓar jakarsa. Da yake ɗakin sadiq ɗin yana ƙofar gida yasa yana zuwa ya tura ƙofa ya shiga babu ko sallama. Yana shiga yaga babu kowa, amma kafin ya zauna Sadiq ɗin ya turo ƙofar shima ya shigo yana kallonsa. Ziyach ya fara cewa "Idan zaka je kallon wasa kazo mu tafi lokacin farawa ya kusa. Yana faɗa ya jawo jakarsa da ya gani kusa da jakar Sadiq ɗin. Ya buɗe yaga komai nasa na ciki ya ɗauki wayarsa yana dubawa. Sadiq kuwa da tsabar takaici ya rasa ma me zai ce masa sai cewa yayi. "Ba zan je ba" Ziyach ya ce "To ni dai na tafi sai ka jini. Yana faɗa yayi hanyar waje ko a jikinsa. Ganin dai da gaske fita zaiyi yasa Sadiq faɗin "Wato kai ko a jikinka ko Ziyach? Kayi abu amma kamar ma baka san kayi ba ko? Kasan kuwa irin abun da ƴan team suke faɗa a kanka, shi kansa koce Wallahi kaɗan ya rage baiyi kuka ba, wai ma ina kaje ne lokacin? Sadiq ya ƙarasa da Muryar da kana ji kasan shima ransa a ɓace yake da abun da abokin nasa yayi domin shima yana cikin ƴan wasan, kuma tare da shi suka ci buri a kan wannan kofin, shi dai ban san wani abu da Ziyach ya bawa muhimmanci da har zai bar wannan wasan ya je ga wannan abun ba. Ziyach ya dawo da baya ya ce "Okay kenan dole sai dani zaku iya cin wasa ko? Idan babu ni ba zaku iya ba ko? To dan uwar mutum ya sameni ya min maganar Allah da sai na ci abu ta kazar uwar yaro. Sadiq ya ce "Matsala ta da kai kenan zuciya da saurin zagi, yanzu da kai ne a kayi wa haka da ka dinga masifa kenan harma sai kayi faɗa da mutum. Yanzu dai ina ne kaje, na bi bayanka ban same ka ba, lafiya dai ko? Ziyach ya ce "Lokacin wasa nayi kawai kazo mu tafi babu lokaci ka bar wannan shirmen please. Haka suka kama hanyar gidan kallon kwallon ba tare da Sadiq ya sake cewa komai ba. Kafin a tashi daga kallon Ziyach yayi faɗa da mutum biyu ƴan team ɗin su da suka fara masa korafi akan abun da ya faru ɗin. A faɗa na biyun nema har abun ya kai ga Ziyach yayiwa yaron ƙofi ƙafarsa ta riƙe ya kasa ta ƙawa. Hakan yasa yaron ya dinga kuka babu yadda ba'ayi da Ziyach ba yaki sakar masa ƙafar, Sadiq kaman yayi kuka yana ta roƙon sa amma yayi masa banza. Har ƙofar gidan su Ziyach ɗin aka zo Alpha ya fito jin ana ta ihu ana bawa Ziyach hakuri. Koda Alpah yayi magana Ziyach ya ce "Ba dai shi shege bane ina daidai da uwarsa ma kuma ƙafa ce ba za'a sake ba ya je yayi duk yadda za'ayi. Haka dai Ziyach ya shige gida ba tare da sakar masa da ƙafar ba. Alpha ya ce da mutanen suje gida zai sa ya sake shi yanzu. Ko da ya samu Ziyach da lallashi da ban baki yasa ya sakar wa da yaron ƙafa, ai kuwa sai gashi yana tafiyarsa lafiya lau.
Washegari da safe Nadiya take sanar masa da abun da Abbu yace akan su Katii. Ziyach ya ce "Meye Hakim ya ce lokacin da Abbu yayi maganar "Nadiya ta ce "Taɓ ai cewa yayi ba zasu zauna a wannan gidan ba kuma shi ai su Abbu sun riga da sun ce mana iyayensu sun mutu to kuma yanzu zasu ce wai suna raye, to basu isa su zo nan ba domin bamu san su ba. Shiru yayi yana mamakin kenan da gaske ne Abbu yana da iyaye basu mutu ba, idan kuwa haka ne to shima yana bayan Abbu akan gara su dawo kusa dasu suma su dinga ganin ƴan uwansu bayan su uncle Abdul. Tun daga sama ya fara magana ganin Abbu da Hakim suna zaune a Palo. "Dama ashe Abbu kuna da ƴan uwa amma kukayi mana ƙarya cewar sun mutu, gaskiya kun cutar damu wallhi, ashe muna da yan uwa amma kuka barmu haka kaida Ummu?. Ya ƙarasa maganar yana samun guri ya zauna yana cigaba da nuna mamaki. Abbu ya ɗogo yana kallon sa. Yaci gaba da faɗin "Idan zaka tafi ɗaukosu Abbu zan bika domin ina son ganin ƴan uwana kusa da ni, kuma dama nace maka wannan karan zanje Saudiyya ko? To kawai sai mu tafi. Kafin ya rufe baki Hakim ya ce "Babu wasu mutane da zasu shigo mana gida wallhi, idan kai baka da hankali kamar su ɗin to sai ka kwashi kayanka ka bisu amma ba dai suzo nan gidan ba. Hakim ya faɗa yana jin dama yasan sai sun samu banbancin ra'ayi da shi hakan yasa ya shirya. Ziyach bai bi ta kansa ba ya zauna yana kallon Abbu da yake ta murmushi abun sa. Shi dai yana son yaga ranar da ra'ayin Hakim da Ziyach zai zo ɗaya. Abbu ya ce "Nima ba zuwa zanyi ba Ziyach zan sa ne azo da su. Ziyach ya ce "Allahumma tufi kum ya abi love you so much. Yana faɗa ya zagaya ya rungume Alpah duk domin yaga ya ƙunsawa ɗan uwan nasa haushi. Daidai lokacin Ummu take sauƙowa da shirin fita. Hakim ya ce "Abbu ka daina biyewa wannan yaron wallhi fa da gaske babu ƴar iskar da zata shigo mana gida da har kuke ƙara mur" Da wani irin sauri Abbu ya sharara masa mari hannu bibbiyu yana sakin huci. Ya ce "La anta Hakim! Katii mahaifiyatace, akan ta zan iya cin mutuncin kowa, kuma daga yau ka iya bakinka akan tun ma kafin tazo gidan, kuma kamar yadda na faɗa a wannan satin zata zo kuma zasu zo har wannan gidan. Ummu ta ce "Maganar banza kenan, kasan kana son ita tsohuwar taka amma ka iya guduwa ka barta, sai yanzu zaka zo da wani borin kunya kana cewa wai zaka iya cin mutuncin kowa, ai kaman yadda yaron naka ya faɗa ne ba dai a wannan gidan ba sai dai wani gidan Wallhi, kuma ina nan akan bakana na tona asirin komai idan har suka shigo wannan gidan. Ta faɗa tana jin wani irin tsanar Alpha ɗin a ranta, tana jin Alpah ya gama cutar da ita, ya raboto da danginta ya kawo ta nan, gashi ita bata yi dacen yara ba bare tace ta samu masu share mata kuka. Hakim dai ya riƙe kumatu yana bin Abbu da wani irin kallo zuciyarsa na basa cewar kawai ya rama wannan marin kar ya bari. Abbu da yake mata wani irin kallon raini ya ce "Ki sani cewar ana iya rabuwa da kowa da komai amma banda uwa da uba da ƴaƴa, dan haka ki iya bakinki duk rawar kanki kisan inda zakiyi banda bangaren mahaifiyata. Ummu ta ce "Ƙarya kake yi Alpah har iyayen ana iya rabuwa da su tunda gashi ni ka raboni da nawa iyayen, kuma ba zan taɓa yafe maka ba, mugu azzalumi macuci tsinanne wanda Allah ya kwashewa albarka. Ta fashe da wani irin kuka wanda kana ji kasan ta tuno da iyayenta ne, har wani ƙara take yi kamar zata shiɗe tsabar kuka. Tsaki yaja yayi sama ba tare da yace komai ba yana jin ya gaji da wannan rayuwar gidan nasa, Gara ma su Katii ɗin suzo ko komai zai dawo daidai. Ziyach kuwa abincin sa kawai yake ci kamar baya Falon, kukan da Ummu ke yi kuwa ko a jikinsa. Shi kuwa Hakim waje ya fita ya tsaya yana ta tunanin abun yi, sosai yaso ya rama marin da Abbu yayi masa amma wata zuciyar ta sanar dashi abun da zai yi. Ɗakinsa ya shiga ya ɗauko wuƙa ya fito ya samu duk tayoyin motar gidan wanda ake hawa da wanda ba'a hawa guda takwas duk yabi ya yanka su, mai gadi na kallonsa amma ya kasa magana. Sai da ya gama kafin ya fito ƙofar gida ya tsaya yana ta huci, sosai ransa yake a ɓace ji yake kamar ya shiga gidan ya rama dukan akan Ziyach. Bai fi minti biyu da tsayuwa ba yaji murya mace a kusa dashi tana dariya, kafin ya ankara sai ji yayi ta rungume shi ta baya tana dariya. A zuciye ya riƙo hannunta ya dawo da ita gaban sa ya ɗaga hannu zai sauke mata mari sai kuma ya tsaya yana kallon ta. Har lokacin tana dariya cikin turancinta mai daɗi ta ce "Kalli jikina kaga nayi kyau ko? Ta faɗa tana nuna masa sabuwar rigarta, sannan ta wake masa baki alamar yau ta wanke baki. Hakim da yaji ransa ya ƙara ɓaci ganin tazo tana masa shirme gata yarinya, shi bai ma taɓa ganinta ba. Ya ce "Ke zanci uwarki idan baki bar nan ba, ina wasa dake ne ko ni sa'an ki ne?. Sara ta sake yin dariya domin tasan shi da saurin zagi. Hakan yasa ta ƙara faɗawa jikinsa tana cewa "Daddy ya tafi jiya, Mommy kuma ta ce daga yau ba zata ƙar" Ai kafin ta ƙarasa ya falla mata lafiyayyun marika guda biyu masu lafiya wanda yasa bata san lokacin da ta saki wani irin ƙara ba, dama gata da murya kuka kamar tsanya.
Cikin gida kuwa ganin ya fita waje ne mai gadi ya shiga gida da sauri ya sanar da abun da Hakim ɗin yayi. Lokacin iya Ziyach da Nadiya ne a Palo amma ko a jikinsa, sai Nadiya ce ta haura sama ta sanarwa da Daddy. Ai kuwa da sauri Daddy ya fito harda gudu. Hakan yasa Ziyach bin bayansa domin yaba idonsa abinci. Sosai ran Abbu yayi mugu mugun ɓaci ganin irin abun da yayi. Suna cikin dubawa ne kuma suka ji kukan yarinya a waje da ƙarfi hakan yasa Ziyach fita wajen domin ya duba, suma su Abbu suka rufa masa baya tare da mai gadi. Yana fita yaga Hakim ya riƙe Sara sai sarfa mata zagi yake ita kuma tana kuka duk ta fita a haiyacinta domin marukan farkon nan sun shigeta sosai. Da wani irin sauri ya ƙarasa gurin yana shiga tsakaninsu. Ita dai tsabar shigar Mari bata ma kula da Ziyach ɗin ne yazo gurin ba, ita duk a tunaninta shine ya mareta haka. Babu wani magana ko neman ba'asi ya ware hannu ya saukewa yayan nasa mari yana kuma zagin sa akan me wannan ƙaramar yarinyar tayi masa da zai kamata da duka, shi ko kunya baya ji. Yanda Ziyach ɗin yake faɗa kamar wanda aka taɓa uwarsa, har wani kumfar baki yake yana jin wani zafin kai a zuwar masa. Daidai lokacin Nadiya da Abbu suka ƙaraso. Abbu na ganin haka ya shiga kiran uncle Abdul. Hakim da marin da Abbu yayi masa har lokacin yake nan danyen a kumatunsa kuma sai ga wannan marin da Ziyach yazo yayi masa, hakan yasa gaba ɗaya yazo wuya. Wuƙa ce a hannunsa wacce yake tunanin kamar Ziyach ɗin bai ganta bane da har zai maresa, tayar mota ya yanka da ita yanzu, kuma yasan sun gani shine bai ji tsoron abun da zafaru ns. Wata jijiya ce ta fito masa a wuya mai ƙarfi yana kallon yanda ƙanin nasa ke ƙara cigaba da zagin sa kamar ya samu yara. Cikin second ɗaya tsinin wuƙar ta sauƙa a gefen wuyan Ziyach wanda yasa Sara da Nadiya sakin kuka a lokaci ɗaya. Yana soka masa wuƙar ya zare sannan shima ya shiga zaginsa yana faɗin abun da ya tsaya masa a rai, yana haɗawa da Abbu duk yana zagi. Daidai lokacin kuma Sara ta dawo hankalinta, idan ta kalli Hakim sai ta kalli Ziyach ta kasa gane waye Ziyach a ciki, sosai ta diririce agurin. Haka take ta kallonsu ita tsabar rudewa ma ta kasa gane waye ya mareta a cikin su. Da sauri Abbu ya kamo Ziyach da har ya zube a ƙasa ya sa hannu a gurin da jini yake zuba. Uncle Abdul na zuwa suka kama Ziyech da jini ke zuba sosai suka saka shi a mota, Abbu ya shiga suka nufi asibiti. Shi kuwa Hakim gida ya shiga yana jin yadda Nadiya ke ihu ta shege ɗakin Ummu. Sara kuwa kuka take tayi har ta koma gida ta kasa gane abun da ta gani, to Ziyach ne ya mareta ko dai shi aka sokawa wuƙa. Haka take ta kuka har Mommy ta dawo ta sameta, kenan dai su ɗin ƴan biyu ne, to waye Ziyach dinta a ciki. Mommy ta tambayeta me saka ta kuka tace babu komai. Mommy ta ce "Oho dai koma meye ke ya shafa. Yanzu dai tashi kizo. Toilet suka shiga tasa ta cire kayan ta komai da komai. Ta ɗauko wani farin abu mai maiƙo mai kama da man shanu. Ta ce "Idan kika min ihu sai na fasa miki baki, shegiya shekara sha biyu harda wani abu amma nono sun ƙi fara fitowa to ba zamu jirasu ba. Ita dai Sara sai kwallon ta kawai take yi. Haka ta dinga ɗiban wannan man tana shafawa akan ƙirjin da babu komai sai gurbinsu, tana shafawa tana jan su wanda har sai Sara ɗin ta runtse ido tsabar zafi. Haka ta dinga mata wasa dasu har dai ta ce taje ta zauna. Ita kuwa tunanin Ziyach da halin da yake ciki take ta yi.