Free chapter · Read without an account

11

by Nazeefah Sabo Nashe · BABBAN GIDA

*BABBAN GIDA….*

New…..



**NAZEEFAH SABO NASHE✍🏽*

BRIGHT PENS.


**I DEDICATED THIS BOOK TO NA’IMA SULAIMAN SARAUTA.**

0803374837.


11.

GODIYA MARA IYAKA DA JIKAR NASHE REAL FANS GROUP… hope wannan karan ma za ku karb’i Babban gida kamar yarda kuka saba karb’ar kowane irin book nawa. Na gode sosai sakamakon Aljanna gareku In sha Allah.🥰



**YOTA004**


***



Zayyad ya jira ya ji ko Uncle din nasa zai yi magana amma ya ji shiru ga shi yana ji ana za’a shigo da amarya. Da sauri ya shiga kitchen ‘din inda Aunty nasa k’awar Mamansa ke had’a garwashin zata zuba maganin, ya nufi Fridge kamar bai ganta ba ya ‘dau bottle water d’in yana sane sanda ya zo daf da ita ya yi kamar zai fa’di ya fa’da a gefen hannunta garwashin da maganin suka watse ruwan kuma da yake ya bu’de bakin bottle Din ya zube a cikin wutar….. da sauri ya zunduma ihu alamar garwashin kamar ya tab’a shi. Hakan ya ja hankalin Mommyn ta shigo kitchen d’in a guje don ba k’aramin so takewa Zayyad ba. Turus ta yi tana kallon aminiyarta kafin ta ce “Ba dai maganin da muka sha Uban wahalar samunsa ba ne zube anan wajen?” Da sauri Sakina ta d’aga Kai kafin ta furta wallahi tsautsayi Zayyad ya fa’di a kan….” “Inna lillahi, Sakina kin cuce ni yanzu shikkenan na yi asarar kud’ina da lokaci na….” Mommy hannuna.” Zayyad ya fa’da yana nuna mata hannunsa da garwashi ya tab’a. Tsaki ta yi tana jan hannun nasa idanunta kuwa banda aikawa Sakina harara ba abinda suke, gashi daga parlor tana ji ana furta “Ina Mommyn yaran ga amaryar an shigo da ita….” Ganin ba wani k’onewa Zayyad din ya yi da yawa ba sai kawai ta saki hannunsa ta fice parlorn tana jin kamar ta jawo Sakina ta yi ta jibga tana murna komai ya zo k’arshe amma ta ja mata wannan asarar idan banda şakacı me yasa zata bari har Zayyad ya fa’di kan abinda ta san ba zata sake Samun damarsa ba, haka nan ta fita parlorn tana k’ok’arin daidaita nutsuwarta don kada a gane halin da take ciki.



Idanun Hajara a saman yatsun Nenne don sune kawai abinda take iya gani a jikinta, amma ko iya k’afar kawai aka mallakawa mutum matsayin abu mai kyau kawai a jikinsa sai ya ce Alhamdulillah kawai. Don wani irin softness skin Allah ya mallakawa Nennen irin fatar da ake kira rainon Madara. 

Ta zauna tana sake k’ok’arin janye damuwarta ta maye shi da farin cikin dole. Aka gaggaisa cikin wasa da barkwanci kafin su yi godiya su mik’e don tafiya. A sannan ta janyo wata leda mai d’auke da turaren Humra da wasu turarukan wanda suka sha zallan aşırı ta mik’a tana furta “Ga shi ba yawa a bawa amarya.” A ranta take jin ko da wannan kad’ai Nenne ta yi amfani zata iya wargaza musu farin cikinsu kuma Mk zai ji ya tsaneta har ya saketa.


Gida dai ya amsa gida don ya yi kyau sosai, iyayenta sun yi k’ok’ari ga mota ga gara da aka cika store guda a gidan banda akwatina da aka narkowa shaddodi da atamfofi y’an gaske.

Aure da ya k’ullu dole kowa kuma ya sarara masa. Tunanin da Mahmud yake yi kenan daidai sanda ya İsa part d’in Jadda da take zaune tana tsimayin jiransa dama so take ta masa nasiha. Ya zauna a gefenta idanunsa a kanta yana sake jin wata irin k’aunarta musamman ganin yarda ta jajirce ta tsaya tsayin daka a harkar aurensa kamar ita ta kawo shi duniya. Har abada yana jinta kamar mahaifiyarsa. “Ango ka sha k’amshi, Alhamdulillah da wannan rana, yau Allah ya nuna min auren Mahmud….” Murmushi kawai yake saki. “Ba zan ce komai ba Mahmud sai Allah ya baku zaman lafiya da zuri’a d’ayyiba fon dükkan wata tarbiyya Alhamdulillah na baku ita, a yanzu ne kuma zan ga tana aiki ko bata yi, Allah ya baku zaman lafiya, duk abinda zaka yi a rayuwar aurenka ka yi koyi da sunnar Manzon Allah, sai ka ga Allah ya shiga dükkan lamarinka.” Tasa hannu ya share hawayen da suke sauko mata wanda ba na komai bane sai na zallar farin ciki. MK ma kukan yake Zayyad ya dinga bin su da ido shima yana jin kamar ya yi kuka. “Kai kuma ya naga kana bin sa baka tafi gida ka kwanta ba?” Jadda ta yiwa Zayyad tambayar da ya gintse fuskarsa ya tsuke gira alamar ba zai yi magana ba, Mk ya yi murmushi ya ce “Ai tare za mu tafi da shi a can zai kwana?” Jadda ta kalleshi shek’ek’e kafin ta furta “Can Ina? Wai part d’inka? Wani irin zance ne mara da’din ji haka? Shikkenan daga kawo yarinya sai a ce wani wai an kai mata yaro, to kada ma ka fara wannan Zancen wannan ai ya zama shiririta bar min shi anan na saka a mayar wa Uwarsa shi….” Zayyad ya mik’e fuskarsa a tsuke kafin ya furta “Na san hanya ai, ba sai kin saka an mayar da ni ba. Uncle Good Night.” Jadda ido ta zuba masa kafin ta yi kwafa ta ce za ka zo ka same ni ne, kunnuwa kamar na Ubanka, d’an k’wal Uba…” Mk dariya kawai yake kafin ya mik’e shi kansa ya ji dad’in hana Zayyad da Jadda ta yi don daren yau kam so yake ya sarara sosai da amaryarsa…. 



Yana shiga cikin part ‘din, ya ji wani sanyin farin ciki yana sake shiga zuciyarsa burinsa na mallakar Nanna ya cika. Har ya saka k’afa zai shiga bedroom d’inta ya dinga ji ana wani nocking da d’an k’arfi. Hakan yasa ya juya ya bud’e k’ofar idanunsa a cikin na Zayyad da ya d’an sakar masa murmushi. Mk Din ma murmushin ya sakar masa ya saka hannu yana lakace masa kumatu ya aka yi Kiddo?” “Mommy ta bawa Anty wata leda, pls make sure bata yi Using nasa ba, yanzu na ji tana fad’awa Aunt Nafeesa matuk’ar Anty Amarya ta yi Using to zata ruguza muku farin ciki as she said…..” Mk kallon yaron kawai yake tausayinsa na sake ratsa shi na rashin Uwa ta gari. Ya yi zurfi cikin tunaninsa har Zayyad ya gaji ya ja hannunsa ya yi pecking kafin ya ce Good Night ya juya da gudu… ya saki ajiyar zuciya k’aunar yaron da tausayinsa na sake shigarsa, dole ne ma ya dawo k’ark’ashin kulawarsa da tarbiyyarsa don idan an bi ta mahaifinsa mutum ne mai sanyin gaske da bai zama lallai ya tsaya ya lura da wacece matarsa ba.


Haka yana shiga ya kuwa ga ledar da Zayyad ya gaya masa bai mata magana ba ya d’au ledar ya fice.



Bayan wata biyu da bikin, abubuwa da dama sun faru, wasu masu da’di wasu akasin hakan. Nenne sam bata san kudirinsu a kanta ba, zaune take da su da zuciya d’aya, kuma Allah yana kareta daga makircinsu Zayyad yana kawowa Mk duk wani rahoto na Uwarsa, wanda Hakan yasa duk asirin da suka yi baya kamata dalili bata amfani da shi, bata san Zayyad ke ruguza mata duk wani shiri ba…



Jikin Nenne ya murje ya yi wani irin kyau na masifa, wanda kallo guda zaka mata ka san tana da shigar ciki a jikinta, abinka da skin mai kyau sai ya sake khan fatar nan ta zama kamar k’wai.



Ganin duk abinda suka yi baya aiki, Hakan yasa suka fara bayyana mata halinsu, tsanarta suke nunawa sosai, suka janye jikinsu daga gareta suka kuma hana y’ay’ansu shiga sabgarta, hakan sam baya damunta don ita dama ba wani damuwa ta yi da jama’a ba balle hakan ya dameta. Yara kuwa tsoratar da su suka yi akan wai tana yanka mutane, kuma tana da Aljannu, don haka Şam basa shiga sashenta idan ka d’auke Zayyad da ya k’i yarda yake shiga abinsa. Uwarsa ba yarda bata yi da shi ba amma haka ta gaji ta kyaleshi ganin Hakan da take yana son ya janyo hankalin Jadda ta fuskanci akwai matsala, abinda basa so, don kuwa sun san Jadda Sarai bata d’aukar Wargi. Idan kuwa Mk yana nan basu isa su hana su ba, don da kansa yake jan yaran zuwa sashensa. 



Lokacin da ta yi wata uku ne aka yi meeting da aka saba na Family. Anan ne Mk ya samu dama ya kalli Baba Alhaji ya nemi izinin yin magana aka ba shi.  Murya a sanyaye ya furta abinda ke ransa wanda ya girgiza zuciyar Mommy ta yi saurin kallonsa zuciyarta na mata wani irin fusga kamar zata zazzageshi don dai kawai a gaban su Baba Alhaji su ke. “Yaro na Zayyad nake son ya dawo k’ark’ashin kulawata Baba Alhaji saboda k’arafafa zumuncin da ke tsakaninmu. Ina neman wannan alfarmar a wajen Babban Yaya don Allah.”


Cikin matuk’ar farin cikin da ya kasa b’uya a idanun Baba Alhaji ya ce “Ma sha Allah, Alhamdulillah hakan ya yi Mahmud, kowa a yasan Zayyad na ka ne, musamman zan iya cewa don kai aka haifeshi bayan kamanni na kwabo da kwabo haka nan kaf halayenka ne da Zayyad, zan iya cewa kurwarka ce a jikinsa, na ari bakin Auwal Babban Yaya na ci masa albasa na baka Zayyad halak malak….na san ba zai hana ba” Auwal da ya dinga jin farin ciki fiye da na Baba Alhaji ya ce “Ba zan hana ba Baba Alhaji, ko da bai karb’i Zayyad ba ai na san ni kawai haihuwarsa na yi, duk wahalar Zayyad Auta ne yake yi, School fees da duk wani sutura da responsibilities Mk ne yake yi, ni kuwa idan ba so nake na zama butulu ba me yasa zan hana shi?” Mk farin cikinsa ya kasa b’oyuwa bai san sanda ya mik’e a guje ba ya rungume Yaya Babba ba yana jaddada godiyarsa. Kowa ya taya shi murna banda Mommy Hajara da take yak’en dole, ta ina zata yarda Nanna ta rik’e mata yaro? Matar da duk duniya ba wanda ta tsana sama da ita… Amma haka ta dinga yak’e kamar zautacciya, ta san dai ko Karen hauka ya cijeta bata isa ta ce bata amince da wannan lamari ba. Amma wallahi da sake.


Haka tana ji tana gani Mk ya d’auke Zayyad, wanda hakan ya faranta ran Nanna don dama bata son zaman shirun da take yi. Soyayya sosai take nunawa yaron kamar ita ta haifeshi.


Da wani irin zazzafan zazzab’i  ta farka a wata rana, hakan yasa ta kwanta ta kasa fita. Ga shi Mk baya k’asar. Zayyad ya rasa yarda zai yi kuma har a lokacin Nanna bata da mai aiki, ta ce ina aikin yake da za’a d’auko mata mai aiki, ko bayi bata yarda aka kawo mata daga gidansu ba, simple rayuwa take abinta ba girman kai bakomai kamar ba yar sarki ba. Da sauri Zayyad ya fita zuwa sashen Jadda sai dai yana zuwa yaga part Din a kulle sai ya koma sashen Mommy, duk da k’irjinsa sai bugawa yake, sosai yake tsoron gayawa Mommyn amma haka ya shiga parlorn ya tarar da Mommyn şuna zaune da k’awarta Sakina da ta mayar da gidan kamar gidan Ubanta. Mommyn ta kalleshi shek’ek’e don yanzu haushinsa take ji musamman ganin yarda sam baya yarda da duk abinda take ce masa. “Menene ka zo ka tsaya  min anan?” Shiru ya yi yana wasa da hannunsa kadın ya ce “Mommy, Anty Is sick….” “Sai aka yi yaya? Ni na d’ora mata ciwon?” Wani kallo Sakina ta mata da yasa ta yi shiru tana kallon Zayyad kafin ta furta “Sai ka wuce ka je d’akin ka na nan gidan kuma kada ka sake ka fito sai mun dawo….” Ya tsaya a sanyaye yana kallonta ta daka masa Tsawar da yasa ya tafi cikin room d’insa a guje jikinsa sai rawa yake, ga shi ya bar handset d’insa a gidan Uncle d’insa. Mommy bata yarda ba sai da ta kulloshi da key ta waje, sannan suka kalli Juna da Sakina suka tafa, Sakina ta ce “Kin ga yanzu hankali kwance sai mu aiwatar da k’udirinmu…..


Jikr Nshe


JIKAR NASHE✍🏽

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.