Free chapter · Read without an account

14

by Nazeefah Sabo Nashe · BABBAN GIDA

BABBAN GIDA…..


NAZEEFAH SABO NASHE✍🏽


***.

14.



Hannunsa ta dinga bi da kallo, ganin yana mik’o mata Ice-cream ‘din. Ta turo baki fuskarta da kwantaccen musrmushin da ya Riga ya gama zama mata a jiki ta ce “Do you forget Ya Zayyad, bana Shan chocolate Ice cream.” Wani irin waro ido ya yi kafin ya ce “Ai kuwa ko ba kya sha yau dole ne ki sha wannan wallahi……” “Me yasa dole sai ta sha Zayyad?” Ammey ta yi masa tambayar daidai lokacin Tana kawo kanta cikin kitchen d’in. Saboda she was surprised Jin abinda ya ce, ta fi kowa sanin Zayyad baya son takurawa Kiyya amma Tana Lura kwanannan kamar alak’ar tasu Tana son rushewa shiru kawai take, ba don komai ba sai don bata son ta had’a husuma kuma ko bakomai bahaushe ya ce akwai Alheri a cikin yin shiru baka ce ba ma Balle ka d’au zunubi… ta saka hannu ta karb’i İçe cream Din da ko a tunani bata zata akwai wani Abu a ciki ba, balle ta zata Zayyad zai iya cutar da Kiyyansa. “Bari ni na sha Ya Zayyad, tunda dai yau ka manta Barbien taka bata Shan Chocolate Ice cream….” Ta kai Spoon d’in bakinta, da sauri Zayyad ya tankwab’e Cup Din ya zube a k’asa. Ammey ta bi Shi da kallo cikin mamaki. Bai bari ta kalli cikin idonsa ba ya yi saurin juyawa ya samu packer da Mop ya kwashe b’arin da ya yi na dole. Ko hauka yake ba zai so Ammey ta sha ta ji Ice cream Din ya canja taste ba, me zai ce mata da me zai kare kansa. A shekarunsa da ya fara hankali ya san abinda ya aikata Sam ba kyau sai yanzu yake Jin wata irin kunya. Ya saka kai zai fice daga kitchen d’in Nanna ta bi shi da kallo wannna Karan jikinta har rawa yake tunaninta guda what does that mean? Me Zayyad yake nufi ne? Dük da zuciyarta na son kawar mata da zargi sai dai sashe guda daga cikin zuciyar tata na tabbatar mata da gaske something went wrong. Ya zama lallai kuma ta gano ko me ye, a yanzu dai ba zata tuhumi Zayyad ba don ta hango tsoro k’arara a idanunsa, sai nan gaba idan zata same shi shi kad’ai ta ji ko me ya faru. Bata fatan a ce Zayyad ya bi layin mahaifiyarsa wajen k’inta ita da tilon y’arta ba zata ji dad’in haka ba daga yaron da take Jin son sa kamar ya tsaga jikinta ya fito. Tana jinsa kamar jininta. Ta lumshe ido kawai bayan ta janye Kiyya da ta sake komawa Barci a tsaye a jikinta don barcin ne sosai a idonta muryar Zayyad da a yanzu ba abinda take tsoro sama da shi ne ya tasheta. Sai ta d’au y’arta ta sab’ata a kafad’a suka shige cikin Bedroom ta dinga tofeta da duk addu’ar da ta zo bakinta, haka kawai idan ta kalleta sai ta ji wani irin tsoro da fad’uwar gaba. Tsoron cutarwa daga wasu sashe na mutanen gidan a yau sai tsoron ya k’aru daga yaron  da take da hope da akansa.


A tsorace Zayyad ya bar part d’in Nanna ya nufi part d’insu, zuciyarsa sai bugawa take. Mommy da take zaune da faccalolinta şuna ta hirar Nanna da ba Wanda suka sakawa ido sai ita da Sharifat. Ta bi shi da kallo yarda ta Ga fuskarsa ta tabbatar akwai matsala. Shima kallo guda ya yi musu ya shige can cikin d’ayan parlorn. Sai Mommy ta ji dad’i da bai zauna ba don kuwa ta tabbata su kansu zasu fuskanci akwai matsala. Idanunsu ta kalla bayan mintuna da shiga d’akin da ya yi, sai ta mik’e tana furta “Ina zuwa, bari na duba babban Yayansu naga kamar ya shigo da damuwa.” Suka kalli juna sai Safiyya ta furta “Zai wuce shegiyar ta fara nuna masa halinta ne….” da sauri Antyn yara ta ce “Gaskiya dai fad’i wani halin Mahmah Banda cutarwa daga wajen Nanna na San ba zata tab’a cutar da shi ba ai kowa ya shaida son da take masa.” Wani kallon banza Mommy da Mahmahn suka zuba mata kafin Mahmah ta yi k’wafa tana furta Anya kuwa ba fuska biyu gareki ba…” Mommy dai bata yi magana ba ta yi saurin shigewa don jikinta idan Banda rawa ba abinda yake. Tana shiga ta ganshi zube a k’asa ya had’e hannayenta ya yi pillow da su idanunsa a lumshe suke sosai. Daga inda take tsaye tana hango yarda k’irjinsa yake d’agawa alamar zuciyarsa ce take bugawa, irin bugün da tsoro ko razana yake haifar dashi. Şam ba zata ce ga sanda ta isa gabansa ba ta zube Tana kiran sunansa. “Zayyad, bud’e idonka ka gaya min abinda ya faru.” Ya ware lumsassun idanun nasa a kanta. Mommy sai ta sake razana “Gaya min komai na ce maka.” A hankali cikin cool voice ya ce “She Caught Me….” Mommy ta waro ido Tana furta “What? Ta kama ka kana me? Na ce ta Kamaka kana aikata me?” Sai da ya Mik’e zaune ya cusa hannayensa cikin tarin sumarsa yana birkitawa a hankali sannan ya sake bud’e birkitattun idanunsa ya ce “Abinda kika şaka ni na aikata, shi yasa Mommy bana son irin wannan abin…..” Mommy ta d’aura hannu a ka tana kallonsa ta ce “Sai ka ce mata me? Ka ce mata ni na saka ka?” Ya zuba mata ido yana Jin wani irin zafi a zuciyarsa da ya rasa na menene shi dai ya san baya son abinda Mommynsa ke aikatawa me yasa yau ya biye mata ya kasa yi mata musu. Mommy da ta gama rud’ewa ta sake Jan hannunsa tana jijjiga shi hankali tashe ta furta “Zayyad, talk to me, sai ka ce mata me?” “Nothing.” Ya furta yana cusa kansa tsakanin cinyoyinsa shi bai san ma da wani ido zai kalli Ammey ba. Ajiyar zuciya Mommy ta sauke kafin ta furta “Ka yi kyan kai da baka yi magana ba, Yauwa kana ji na ka daina nuna alamun rashin gaskiya, na San nan gaba dole zata tambayeka sai ka ce Kiyya ce ta maka laifi ta maka gwalo don an ce ta fika k’ok’ari, kai kuma shine ka ji haushi sai ka zuba mata yawu ka yi diluting a cikin Ice cream d’in, shikkenan case closed…..” wani sanyi Zayyad ya ji ya ratsa shi, abinda Mommy ta fad’a ya kwantar masa da hankali kad’an, amma idan haka ne ya zama mak’aryaci kenan kuma ya san k’arya ba kyau, amma bai manta ba sanda suka ne tafsir da Uncle d’insa an gaya musu Akwai k’aryar da ta halatta bai sani ba ko wannan tana daga ciki…. “Ka ji na gaya maka, kada ka bada k’ofar da za’a gane ka.” Ya d’ago a hankali yana jijjiga mata kai. “Amma Mommy this should be the last pls….ba kyau abinda ki ke yi fa.” Harara ta zuba masa kafin ta yi tsaki ta ce “Saboda wa nake yi idan ba don kai ba, kada ka sake min irin wannan maganar, buri na naga ka fi kowa a grand children d’in gidan nan idan kuma ka fi so na barka shikkenan. Bayan yau Ina ji Ana ta hayya hayya a cikin gida wai ka zama dak’ik’i, Ashe yanzu ne aka haifi gifted.” Daga haka ta mik’e ta fice daga d’akin ta bar Zayyad cikin tafasar zuciya. Ya k’udirce a ransa sai ya san yarda ya yi yaga bayan wannan k’ok’arin nata.




Ammey bata yi masa maganar ba, don haka ya saki jiki abinsa. Sai wata Alhamis yana zaune yana Shan pototo soup da Ammey ta had’a masa da kunun gyad’a don dama bai fiye cin abincin kowa a gidan ba, sai ya tabbatar Ammey ce Ko Mommy Ko Jadda suka yi da hannunsu, don kuwa mutum ne shi mai tsantsamin masifa. Sha yake sosai şuna hira da Ammeyn har yana murmushi hirar da yake so ce hirar yana gama secondary school za’a tura shi Abroad karatun pilot, mafarkinsa kenan kuma shine burin da kowa ya san Zayyad da shi. Uncle Mk kuma ya yi masa alk’awarin ko duka dukiyarsa zata k’are sai ya çıka masa wannan burin nasa. “Ya Zayyad, in tambayeka pls, amma don’t hide anything for me.” Ya ma manta da wancan maganar don haka ransa fes ya ce “I promised you Ammey, ba zan hiding komai ba.” “Ka tabbata? Ka san fa dole ne musulmi ya zama mai çıka alk’awari.” Ya d’age girarsa guda d’aya daga cikin abinda yake k’ara masa kyau ya furta “Yes, Ammey I promised you…” Nanna ta saki murmushi ta ce “Me ka zubawa Kiyya a Ice cream ranar? Just tell me the truth wallahi ba zan maka komai ba….” K’irjinsa ne ya dinga bugawa ya rasa yarda zai yi tabbas Nanna ta saka shi a cikin tsaka mai wuya, ta yaya zai kalli idonta ya ce magani Mommy ta bashi ya zuba mata, ta yaya zai b’ata mahaifiyarsa? Gefe guda kuma yana tunanin ta yaya zai yiwa Nanna k’arya bayan alk’awarin da ya yi mata, me yake so ya zama ne? Daga k’arya sai rashin çıka alk’awari, sai ya ji ya zab’i ya gaya mata gaskiya koda kuwa me zai faru? Ya San dai May be daga ranar Nanna zata dinga masa wani kallo ne. “Ka gaya min Zayyad.” Ya d’ago idanunsa şuna zubar da guntuwar k’walla abinda Nanna bata tab’a gani ba. “Pls Ammey don’t  take it personal, wallahi I regretted pls.” Nanna ta ji zuciyarta ta daka wani tsalle koma me Zayyad zai gaya mata ta tabbatar ba alheri ba ne, sai ta ji Tana tsoron ji ma, amma kuma dole ta ji don gaba a ke ji, kada a saka shi ya zuba mata güba ma bata sani ba. “Tell me, ba zan yi komai ba.” Ya runtse idonsa ya cije leb’ensa kafin ya furta “Maga…ni…ne” Ammey ta waro ido hankali tashe ta dinga kallon Zayyad kafin murayrta na rawa ta ce “Maganin me? Kuma who gave you?” Zayyad wannan karan ji yayı duniyar na juya masa. Nanna ta kamo hannunsa ta matsa ta ce “Ka gaya min, ba abinda zan yi fa.” Cikin kasalalliyar murya ya ce “Mommy ce, amma pls ki yi hak’uri ba zata sake ba…..” Jikinta ya yi salaf bata san sanda ta saki hannun Zayyad ba saboda ji ta yi kamar lakar jikinta ta tsitstsinke….. shin wa ce irin rayuwa muke cike ne? Wace irin Uwa ce Mommy mai d’ora yaranta a turbar da bata dace ba, sai ta ji wani irin tausayin Zayyad da sauran yaran Mommy tausayinsa da take ji sai ya rinajyi laifinsa. Hawaye ya zubo daga idonta hawayen da ya ji saukarsu tamkar zubar darma  a zuciyarsa bai san sanda ya kamo hannunta ba cikin muryar kuka ya furta “Pls Ammey am sorry, wallahi na yi regretting pls and I promised you ba zan sake ba…” “Allah yasa.” Ammey ta furta hankalinta tashe ba zata gayawa kowa ba amma ya zama dole ta ceci Zayyad daga irin tarbiyyar Mommynsa. “Ba kyau Zayyad, ba kyau cutar da musulmi Balle Kiyya da take matsayin y’ar uwarka. Pls kada ka sake.” Ta furta tana murza hannunta cikin nasa, Sam yarda hankalinta ya tashi sai ta manta bata tambayeshi dalilin da yasa ya aikata Hakan ba, may be da a lokacin zata san dabarar da ta yi ta cire zuciyar Zayyad daga tunanin wai Kiyya ta fi shi komai, tabbas da an samu sauk’in wasu lamarin.


Nanna kamar yarda ta yi alk’awari bata gayawa kowa ba ta ja bakinta ta tsuke, sai dai a kullum tana sake Jan Zayyad a jikinta ta kuma dage da yi masa addu’a. Sosai aka samu kan Zayyad a lokacin ya koma suka sake jonewa da Kiyya lamarin da ya sake tayar da hankalin Mommy, ta rasa yarda zata yi Zayyad ya guji Yarinyar ya k’i ta da zuciyarta har dai da ta amince da zuciyar da take bata shawara ta kai sunan yaro Zayyad da yarinya Kiyya wajen Malami a musu mugun farrak’un da Ko ganinta ba zai so ya yi ba. Ta haka ne ta tabbata zata cutar da Kiyya ta kuma tabbatar ta dasawa iyayenta mummunan b’acin rai kwatankwacin Wanda suka haddasa mata…….






Wash yau fa na rubutu… sai dai baa fara komai a labarin Babban gida ba. Labarin yana gaba wannan duk sharar fage ne. 


Ga Comment Section ku yi joining.


Follow this link to join my WhatsApp group: ***



JIKAR NASHE✍🏽

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.