Free chapter · Read without an account
21
BABBAN GIDA….
NAZEEFAH SABO NASHE✍🏽
***.
21.
Ya dinga yak’i da zuciyarsa wajen ganin bai furta abinda zuciyarsa take so ya furta Kai tsaye ba. Had’iye maganar ya yi a zuciyarsa yana Jin zafin yarda bai furta abinda yake so ya ce d’in ba. Mommy ta bishi da kallon mamaki. Kafin ta yi k’wafa ta ce “Saboda na hanaka kula y’ar banzar yarinyar can shine kake tsuke min fuska?” Girgiza Kai ya yi kafin ya damk’i takardar cikin hannunsa. Ya mik’e jiki a salub’e da nufin barın parlorn. “Idan kaso ka k’i bin umarnina Zayyad, ka ga ko zaka ga daidai a rayuwarka….” Sosai ya danne wani abu da ya ji yana yunk’uro masa a zuciya. Anya kuwa Mommy ce ta haifeshi. Shine tambayar da har yau ya Gaza samun amsarta. Bai sani ba ko ta sa Uwar duniyarta daban data sauran iyaye da ya saba gani. Iyaye masu son y’ay’ansu, masu sadaukar da dükkan farin cikinsu don na yaransu, masu ganin yaransu cikin walwala. Ba irin tasa Uwar ba, da bara buri irin taga b’acin ransa bata damu da son ransa ba, matuk’ar ita zata çıka nata burin. “Ba abinda zai Hana shi ganin alheri Hajara.” Ya tsinkayi muryar mahaifinsa da ta fita cikin alamun fushi. Hakan yasa k’afafunsa suka tsaya çak suka kasa d’aukarsa ya jingina da k’arfen step yana fatan kada abin ya zama babban issue, don bai tab’a Jin muryar mahaifinsa ta fita Amon sauti irin wannan ba. “Hajara duk abinda kike ina sane, na saka miki ido ne na ga iya gudun ruwanki, amma na lura ke baki san zuru ba don haka magana ta k’arshe da zan gaya miki ki cire idanunki daga kan yaran nan….” “Idan ba haka ba fa?” Itama ta furta cikin nata sautin mai bayyana fusata da nuna alamun ta shirya aksar duk wani hukuncinsa koda kuwa zata yi nadama daga baya… “Zan hukunci Akan ki, irin hukuncin da zai Yanke duk wata alak’a da ke tsakaninmu, wallahi a wannan karan ba zan yarda ki sake samun damar raba kaina da y’an uwana ba, wancan karan ma da kika ci galaba ki sani ba wayonki ko dabararki bane, umarnin Baba Alhaji na bi na k’i sakinki, a yanzu kuwa ba Baba Alhaji zan iya sakin ki wallahi kuma ba nadamar da zan yi don na rabu da Annoba…..” wannan karan Zayyad ji ya yi ba zai iya cigaba da saurara ba ya şaka hannu ya toshe kunnensa, zuciyarsa rawa kawai take, ya dinga rok’on Ubangiji kada Allah ya bawa mahaifinsa damar rabuwa da mahaifyarsa….. Ji ya yi an ja hannunsa. Ya bud’e ido kawai yana kallon Mahaifinsa da ya ja hannunsa suka fice daga sasan da sauri. Duk da haka yana cigaba da jiyo sautin Amon Mommyn da take cigaba da duk maganganun data ga dama. Mahaifinsa bai tsaya ko ina ba sai şaşsan Jadda. Jadda da take zaune Tana lazimi Kiyya a gefenta ta bisu da kallo. Sam Daddy bai kula da Kiyya ba, amma Zayyad ya ganta don a jikinsa ya ji Tana parlorn Sai kuwa yana juyawa ya ganta a kwance saman three seater ta lumshe Idanunta. “Jadda, na gaji da halin Hajara wallahi zan datse igiyar auren dake tsakaninmu….” Jadda ta waro ido. Kiyya kuwa zuciyarta ta ji tana bugawa da sauri. Bata son rabuwar aure ko na yara balle nasu Mommy da ya tasamma shekaru arba’in. “Allahumma La sahla…. “Jadda ta yi addu’ar tana kallon Daddy Sai kuma ta umarceshi da ya zauna. Sannan ta kalli Zayyad Tana furta “Ja k’anwarka ku fita.” Kiyya da sauri ta mik’e shi kuma Zayyad ya bi bayanta jikinsa a sanyaye. Ganin Kiyyan ta nufi hanyar waje yasa ya bi bayanta. “Kiyya.” Ta ja ta tsaya ya k’arasa har gabanta ya mik’a mata Hijab d’in hannunsa. Kiyya ta dubi rigar jikinta da wandon da suka matseta sosai Hakan yasa Ammi ta bata Hijab ta ce ta saka sannan ta ja kunnenta da dole ma ta koyi saka kayan hausawa. Ji ta yi ta takura don haka tana shiga sashen Jadda ta cire Hijab d’in ganin ba Mazan a wajen. Ta mik’a hannu don amsar Hijab d’in… Zayyad ya zuba masa idonta da ya sata Jin wani yanayi da ba zata iya fassara menene shi ba. “First and Last warning kada na sake ganinki da wannan shigar pls!” Ya fad’a yana narkar da idanunsa cikin nata. Abinda yasa yanayin jikinta ya sauya gaba d’aya. Bai damu ba ya juya don tafiya kamar bai san abinda ya aikata ba, ba zai iya ba, bai zai iya danne soyayyar Kiyya a zuciyarsa ba. Abu ne da ya tashi da Shi tun yarinta sai dai ya zama dole ya bi umarnin Mommy, umarnin da yake Jin zafinsa a cikin ransa…. Shiru ta yi ta bi bayansa da kallo kafin ta lumshe ido ta kuma sauke ajiyar zuciya tana tab’e baki ta zura hijab d’in. A ranta ta ce “Ko ina ruwansa da jikina?”
Jadda ta gama sauraran Daddy ranta idan ya yi dubu ya b’aci, amma sai ta danne nata b’acin ran kafin ta furta “Ba kalmar saki a tsakaninku Yayansu, ka yi hak’uri amma a sannu watarana za’a mata abinda zai fi sakin ciwo a ranta, ka daina kulata shine kawai shawarar da zan baka.” Auwal ya danne b’acin ran da ke dake taso masa ya girgiza kai. “Tashi ka je, Allah ya maka albarka da Kai da sauran y’anuwanka, In sha Allah zumuncinku zai zama har Aljanna ne, küllüm addu’ar da nake yi kenan.” “Ameen” ya amsa a hankali kafin ya mik’e ya bar wajen.
A parlor Kiyya ta samu su Ammi da Mami şuna hira. “Daga ina ke kuma?” Yasmin ta jefa mata tambaya. Zama kawai ta yi ba tare da ta amsa tambayar da Yasmin take mata ba. Ta juya tana kallon Ammi kafin ta ce “Ammi me yasa Mommy bata sona ne?” Ammi ta yi shiru saboda ita bata son na Çin tambaya, Zakiyya tun jiya take mata wannan tambayar. Mami Sharifat ta ce “Saboda bata son d’anta ya aureki, Hakan ne ma yasa take ta azalzalar a yi bikinsa da Zainab, ai kowa ya gama ganeta.” Zakiyya tab’e baki ta yi kafin ta ce “Nima ta kwantar da hankalinta ba sonsa nake ba, bai min kalar Mijin da nake son aure ba.” Mami Sharifat ta ce “Yauwa y’ar albarka, duk da cancanta shi ya kamata ya aureki don ya k’arasa abinda ya fara, sai dai ko ni ba zan so ki aure shin ba, don a nuna mata ita d’anta yake gabanta yanzu ji take ai duk duniya ba ya ita, saboda ta haifi Breadwinner na jikokin gidan nan, abu guda data manta da shi duk wata nasara da ya samu sanadiyyar Abbi ne, idan Banda haka ba abinda zai yi achieving a rayuwarsa….” “Sharifat ki daina fad’ar haka, shin kun yi da Allah ne?” Ammi ta furta ta mata alamun a bar maganar ko saboda yara. Sharifa cikin hassala ta ce “İta ta yi da Allah ne, duk sauran yaran da muka Haifa ba Za su yi arzikin ba, ki ji fa abinda matar nan ke fad’a, wai saboda an ga Zayyad ya yi kud’i aka dawo da Kiyya don a mak’ala masa, kamar an ce mata ana neman kai da Kiyyan, yarinya ma tsaleliya irin Kiyya har Sai an yi neman kai da ita, ta jira dai taga irin mijin Zakiyya.” Wani irin huci Kiyya kawai take, abin ya b’ata mata rai sosai bata san sanda ta mik’e a hassale ta shiga bedroom d’inta ba. Wasu hawaye na son zubo mata, ita da maza ke bi kamar me itace za’a ce Ana so a mak’alawa wani, wanin ma irin Zayyad da ya wahalar da rayuwarta, tabbas kuwa zata bawa Mommy mamaki zata sha alwashin cusa soyayyarta a zuciyar Zayyad ta yarda ko me za’a yi ba zai hak’ura da ita ba, sai ta gumawa Mommy Takaicin da Sai ya kusa ajalinta. Alk’awari ne ta d’auka…. A haka ta kwana da wannan kudiirin a ranta, a da bata tab’a sawa a zuciyarta zata so Zayyad ba amma a yanzu ko don Mommy zata ja shi a jiki idan yaso zuciyarta ta buga a duk sanda ta ji labarin za’a d’aura aurenta da Breadwinner. Ta saki wani smiling kafin ta furta “Auren Ammi da Abbi, ya bar miki wani tabo da har yau ya kasa rabuwa da zuciyarki, saboda Abbi bai auri k’anwarki ba, a yanzu kuwa aurena da Zayyad na tabbata bugar miki da zuciya zai yi muguwar mata, daga kaina sai kin daina mugunta a rayuwarki.” Ta fad’a Tana sakin wani murmushi. Kafin ta mik’e ta shige toilet wanka ta yi sosai ta fito ta sanya wani shegen sport wear baby pink color da ya fito da duk wata sura ta jikinta. Rigar armless ce sai ta saka head band a gashinta. Hakan ya sake bayyana tsagwaron kyawunta. Turare ta saka sosai a jikinta. Ta zura Camvas shoe a k’afarta, ta tabbata yanzu Zayyad yana field yana training shima. Yasmin ta d’akawa duka don idan bata tasheta ba ta san yanzu zata fara mata mita. “Zan wuce training,idan kin shirya ki biyo ni can.” Yasmin kallonta kawai take. Kafin ta ce “Kan Uba, kin ga wani Uban kyau da kika yi kamar Za ki gasar kyau….” Kiyya ta lumshe idonta ta bud’e tana murmushi kafin a ranta ta ce “zan je gasar rushe gwamantin wata da kafa tawa gwamnatin dai.” A fili kuwa sai tace “Sai kin zo.” Ta fice da sauri Tana zura AirPod a kunnenta. Yasmin ta ce “Fatabarakallahu Ahsanul Khaleek’in.”
Kamar yarda ta yi tsammani kuwa a field d’in ta same shi. Cikin wata irin rausaya da bata san Şam ta iyaba ta nufi wajensa. Numfashinsa ne ya so d’aukewa ganin yarda take tafiya zuciyarsa ta dinga wani irin bugu a fili ya furta “Ya Allah zan iya jurewa rasaki kuwa.” Tana cigaba da taku zuciyarsa na cıgaba da bugu har ta iso inda yake. Wani irin murmushin da ya kusa şaka shi suman tsaye ta sakar masa kafin ta furta “Big Bro… morning?” Ta fad’a Tana zama daf da Shi. Sosai Zayyad ya dinga kokawa da numfashinsa. Kallo kawai yake binta da shi Kiyya kuwa Sai murmushi take sakar masa kafin ta busa masa iska a fuska ta furta “Kallon fa?” Ya sauke ajiyar zuciya a hankali ya ce “Kin yafe min kenan ko Barbie.” Ta lumshe ido Tana d’aga masa gıra kafin ta furta “For ever Ya Zayyad d’ina.” Ya İlahi ya furta a hankali yana cigaba da kallon cute lips d’inta. “Thanks….” Ya ce cikin wata irin murya. “Nima ina so ka yafe min….” “For?” Ya furta idonsa cikin nata yana jinsa a wata duniya daban. Ta d’an sunkuyar da kanta tana wasa da zoben hannunta. Abinda ya ja hankalinsa ya dinga kallon sortable fingers d’inta, masu matuk’ar kyau kamar na jarirai. “Talk mana Barbie.” Ajiyar zuciya ta yi kafin ta furta “Rashin kunyar da na dinga maka….” K’wallar da ta k’ikireta ta kwanta a k’asan idonta ta k’arawa idon kyau “Pls ka yafe min, you don’t deserve…….” “Shsshhh..” ya furta a saitin kunnenta a hankali “I never forgive you…..” wani irin waro idonta ta yi, duk da ta san tsokanarta yake. Ya yi murmushi yana d’aga mata gira. “Unless you obeyed my rules……” ta sauke ajiyar zuciya kamar gaske kafin ta furta “Your wish is my command Yaya Zayyad I do as you said……” wani irin farin ciki ya dinga Jin yana bin zuciyarsa. “Closeness d’inmu zai fi da Bonding….. Za ki zama best friend d’ina da zan dinga baki advice kema ki ba ni. Za ki dinga min abinci ina ci. Ina son in San komai na rayuwarki, ko saurayi Za ki yi sai da yarda ta kin yarda?” Wani irin murmushi ta saki don dama burinta kenan “Na yarda, amma Mommy fa….” Ya lumshe idonsa ya bud’e “Keep it as a secret… what I mean, a gaban Mommy don’t show any sign da zai nuna mata muna tare.” Kiyya ta saki wani murmushi kafin ta d’aga masa kai. “Starting from today….” Ya ce yana mik’a mata hannu alamar su yi alk’awari, ta mik’a masa yatsanta suka k’ulla kafin ta furta “Yes Sir!” Ya saki ajiyar zuciya yana sakin hannunta Yasmin ta iso wajen. Kallonsu kawai take Tana Jin wani dad’i a ranta, sai dai gefe guda na zuciyarta na Jin wani irin tsoro dafatan Allah yasa ba warning d’insu Ammi Zakiyya ta zubar ba. Zayyad ya mik’awa Yasmin hannu suka yi shaking, mamaki yana kama Yasmin d’in, Sanin cewa ba ma’aboncin yi musu wasa bane, kullum cikin b’ata rai yake. Suka gaisa kafin ya mik’e ya bar wajen. Yasmin ta bishi da kallo tana mamakin sauyawartasa. Zakiyya murmushi take Tana kallonta ta ce “Ya dai?” Yasmin ta d’an harareta “Kawai yanayin da na ganku ne bai yi min ba, kada dai ki manta warning d’insu Mammy a kansa.” Zakiyya ta d’aga mata gira tana mik’ewa ta ce “We will talk later….” Ta fara judging, dole Yasmin ta ajiye nata tunanin suka fara yi tare.
Da sassafe Zakiyya ta tashi kashegari, bayan Jin vibrating d’in wayarta na alarm d’in da ta saka sai kuma ga sak’on msg d’insa ya shigo. “Break fast, zan fita office da wuri Barbie….” Ta kalli msg d’in tana murmushi sannan ta mik’e da sauri ta yi wanka ta fito ta shirya cikin wata doguwar Riga mai kyan gaske. Ta nufi kitchen. Ba Wanda ya tashi a gidan tun bayan da suka yi sallah duk suka koma. A bakın freezer ta tsaya Tana duban abinda suke da shi. Ta ji dad’in ganin duk abinda take buk’ata Akwai. Scotch egg ta masa sai ta yi friending samosa da springrolls da already dama Akwai su freeze. Ta yanka fruits ta yi masa smoothie na strawberries da grapes. Ta had’a komai a basket kafin ta sake komawa bedroom ta gyara fuskarta ta fesa turare ta dawo kitchen d’aukan kayan wayarta a kunne tana kiran layinsa. “Ya za’ayi ka karb’a?” Ta furta bayan ya d’aga. A hankali “Morning Barbie….” Da sauri ta yi dariya kafin “Oooop, am sowie, morning Ya Zayyad….” Ya saki ajiyar zuciya yana furta “Ki sameni a car port.” Ya katse wayar yana Jin wani abu na masa yawo a ransa…. “Abincin waye wannan?” Ammi da ta shigo cikin kitchen d’in ta fad’a Tana zuba mata wani kallo. K’iris ya rage Kiyya ta saki basket d’in… “Na ce abincin waye?” Ta sake furtawa cikin daka tsawa….
JIKAR NASHE✍🏽