Free chapter · Read without an account
22
BABBAN GIDA…..
NAZEEFAH SABO NASHE✍🏽
***.
22.
Cikin daburcewa Kiyya ta ce “Na Ya Zayya….” Ta kasa k’arasawa saboda kallon da Ammin ta yi mata. Jijjiga Kai Ammin ta yi kafin ta kalli wayar Kiyya da Zayyad yake ta kira. Sai kawai ta juya tana furta “Ki je ki kai masa ki zo ki same ni ina jiranki.” Da azama kuwa ta suri basket d’in ta fice zuwa inda ya ce ta same shi. Ajiyar zuciya kawai take saukewa ta san yau me rabata da Ammin Sai Allah. Tunda ta nufo wajen motar ya zuba mata idanunsa. Zuciyarsa idan banda bugu ba abinda take yi ta tafi da dükkan tunaninsa, Anya zai iya son wata mace kuwa irin wannan son da yake Jin yana bin kowane Sako da lungu na zuciya da gangar jikinsa. Har ta iso bai sani ba Kiyya ta tab’e bakinta da alama abinda ta shirya d’in ba zai yi wani wahala ba, don a idanunsa take hango mayataccen kallon da yake mata Wanda ta fassarashi da abubuwa kala-kala. Tapping hannunta ta yi a saman fuskarsa Hakan ya dawo da shi daga tunanin da ya yi zurfi. Ta zaga ta bud’e bayan motar ta saka masa Basket d’in. “Ina sauri Ya Zayyad, a dawo lafiya Allah ya tsare min my brother…. Ammi na jira na.” Kafin ya ce komai ta juya ta fara tafiyar da ita kanta bata san ta iya ba. Zayyad Cak numfashinsa ya tsaya ya daina gudu yarda ya kamata sai ma
Da ya dinga fisgoshi “Ya Allah!” Ya furta idanunsa na Tara kwallar da shi kansa bai san dalilin zubarta ba. Zainab ce ta iso wajen fuskarta ta sha makeup sai zabga murmushi take ta tsaya a gefensa Tana furta “Morning My Lovy.” Kallo guda ya mata ya janye idonsa, Şam Zainab bata da muni sai dai bata cikin irin matan da yake mafarkin aure. “Morning” ya furta muryarsa a gintse. Tana wasa da hannunta ta mik’a masa Wata takarda. “Ta mecece?” Ya furta yana sake tsuke girarsa. “Sizes ne Mommy ta ce a baka.” Har zai amsa Sai kuma ya ce “Ki kaiwa Ammi…” Baki sake take kallonsa ta ce “Ammi kuma?” Kallon da ya mata ne yasa ta yi shirun da bata yi niyya ba. Bai sake mata magana ba ya ja motarsa da sauri ya bar wajen. Zuciyarsa azalzalarsa take kawai ya je ya samu Abba Jabeer da suke Kira da Abba J ya gaya masa shifa ga wacce yake so, ba mamaki ya yi supporting d’insa… “Sai kuma ka shirya karb’ar tsinuwar Mommy…..” ya ji kamar an gaya masa a zuciyarsa. A hankali ya cije leb’ensa yana hango yanayin fuskar Zainab data nuna damuwa k’arara. Tab’e bakinsa yana sake Jin haushinta yarda ta mak’ale lallai shi take so abin yana bashi haushi. “Baki ga komai ba.” Ya furta a hankali.
“Ina Jin ki, na ce Uban me ke tsakaninku da shi?” Nanna ta fad’a Idanunta a cikin na Kiyya da take ta dibi dibi ta kasa gamsashshen bayani. “Ba zaki gaya min ba?” “Ammi, wallahi bakomai, kawai dai nasiharku na bi ke da Abbi, da kuka ce na yafe masa, shine shima da ya rok’eni na ce na yafe masa, ya ce idan har na yafe masa yana son küllüm nake bashi breakfast….” Nanna ta yi shiru Şam zuciyarta bata amince da wannan alak’ar ba, amma da ta Tuna remain few days zai tattara ya tafi gidansa sai ta ji ta samu relief. Tana kallon Kiyya ta ce “Ba zan hanaki zumunci da shi ba, sai dai zan yi warning d’inki kada ki k’etare iyaka, sannan ban amince da keb’ewarku ku biyu ba ko da wasa….” Zakiyya ta d’aga Kai. Daidai lokacin Zainab ta shigo da sallama a hankali. Gaishe da Ammi ta yi kafin ta amsa gaisuwar Kiyya da ta mata tana murmushi. “Matar Yayanmu, ya shirin biki?” Zainab d’in ta d’an mayar mata da murmushinta kafin ta ce “Alhamdulilah.” Ammi ta amshi takardar Tana furta “Ta mecece?” “Yaya Zayyad ne ya ce na kawo miki.” Ammi na murmushi ta sake duban Zainab takardar ta ce “Okay sizes ne? Ai kuwa Zakiyya fita ta kamaku ke da Yasmin Akwai shagon da zan aike ku anjima…” Zakiyya Jin fita farinciki ya kamata Tana kallon Zainab ta ce “Sai mu je tare ko?” Zainab ta d’aga Kai kafin ta mik’e ta nufi sashensu zuciyarta na zuba wani turiri me yasa Zayyad zai ce ta kawowa Ammi takardar? İta ba wannan bama, itafa gaba d’aya bata son Kiyya bata san kuma dalili ba? Haka kawai take Jin Tana Jin haushinta, bata san ko Hakan yana da nasaba da abubuwan da suka faru baya ba.
A zaune ta samu Mahmah da Mommy a parlorn Mahmahn. Zainab ta shiga Tana kumburo fuska. Da mamaki Mahmah ke kallonta ta ce “Ke kuma lafiya?” Ta zauna saman kujera ko gaishe da Mommy bata yi ba ta ce “Mahmah wallahi Raina ne a b’ace, wai Ammi ce zata had’a lefe na?” Mommy Hajara da sauri ta ce “Wai in ji Uban wa?” Tab’e baki Zainab ta yi kafin ta ce “Zayyad ne ya fad’a, don kuwa shi ya ce na Kai mata takardar list d’in abubuwan da nake so da kuma sizes d’ina, ina Kai mata ta mik’awa waccan kod’addiyar y’artata ta ce Sai şu je da Yasmin su siyo….” Mommy ta ce “Kan Uba, to wallahi ba’a isa ba, tashi maza muje wajen matar can Aisha ai Hakan ba zai yiyu ba, wannan karan dole ta barni na nunawa duniya nice Uwar Zayyad.” Mahmah ta bita tana Jin haushi itama ita data so Zayyad ya basu kud’i su yi abinda suke so, shine zai wani bawa Nanna, ai kuwa itama da sake, don ita so take yarinyarta idan ta auri Zayyad ya zama sai abinda take so zai yi, ya zama tana juyashi fiye da mahaifiyarsa….
Ba sallama suka tura k’ofar parlorn Ammin suka shiga. Ammi da take zaune Tana saurarar tafsir a tashar sunna Tv ta d’ago kafin cikin gatse ta ce “Wa’alaikumussalam.” Duk da ta san ba su yi sallamar ba. Cikin hassada suke kallon parlorn da yake ta baza sassanyan k’amshi gashi k’al k’al kamar Sabo don Nanna macece y’ar gayu da bata son hayaniya. Tsaye suka yi don basu yi niyyar zama ba. Nanna Tana murmushin cusa musu takaici ta ce “Ku zauna mana Mommy….” Mommy ta mata wani kallo shek’ek’e ta ce “Ba zama nazo yi ba Nanna, na zo ne ki gaya min ko sanda na yi cikin Zayyad tare da ke Auwal ya mana cikin muka haifeshi tare?” Nanna na zaro ido ta jijjiga kai kafin ta ce “A’a, Yaushe kuwa? Ai kowa ya san Zayyad d’anki ne ba nawa ba….” “Idan kuwa haka ne, ya kamata ki k’yale min yaro haka, na taka rawar matsayin uwa a wajensa, don masifa lefen auren nasa ma ke Za ki had’a? To ba zai yiwu ba, ki bani takardar da ya ce a baki sannan ko nawa ya turo miki maza maza ki dawo min da su ga account number, ni ce Uwarsa ni zan had’a lefensa….” Nanna ta dinga kallon takardar da take mik’o mata ta account number d’in Tana murmushi kafin ta ce “Sai dai bai Kai ga turo min kud’in ba, amma abinda za’a yi ki yi masa waya maza ki ce masa kada ya şaka a nawa ya şaka a naki. Ki yi hak’uri ga takardar…” waftar takardar ta yi ta juya da sauri Mahmah Aisha na bin bayanta şuna tafe şuna k’ananan mita. Aisha Sai sake zugata take. “Wallahi kada ki yarda, ta ga Allah ya bashi nasibi shine shima take son ta janyeshi, ta fara tunanin nan gaba shima zai zame mata mamora tunda daf yake da ya fi Mijinta kud’i. Kai shima dai Zayyad Sam bai San darajarki ba wallahi.” Hajara ta sake hawa ta ce “Bar ni da shi don Ubansa, ai wallahi Zayyad Sai na Kai Sinansa wajen Malamai ina ji sun mallake min shi, idan ba haka ba ba zan tab’a gane kansa ba….” Ta gefen ido Aisha ta mata wani banzan kallo kafin ta tab’e baki tana furta “Aa, abin ai bai Kai haka ba, ki dai bud’e masa wuta sosai ya san darajarki ina dalili kura da Shan bugu gardi da k’wace kaya….” Mommy ta yi shiru zuciyarta na sake zafi gefe guda kuma sai sake Danna kiran Zayyad take. A kıra na goma ya samu ya fice daga meeting d’in da suke ya yi excusing mutane saboda kiran ya yi yawa, duk da baya Jin kiran wani mai mahimmanci ne… “Don Ubanka har k’ask’ancin nawa ya Kai na Kira sai ka ga dama zaka d’aga min waya?” Runtse idonsa ya yi kafin ya hau murza goshinsa, murya a ciki sosai ya ce “Afuwa Mommy, ina important meeting da y’an china ne shi yasa.” Ta saki ajiyar zuciya kafin ta ce “Amma Ka san mahimmancin amsa kiran Uwa ko? Ai kamata ya yi ko da Uban wa kake idan na Kira ka, ka ajiye uzirinka ka amsa min.” Ya datse leb’ensa a ransa yana istigfari saboda tunanin da ya bijiro masa Anya Mommy ta cancanci ta amsa matsayin uwa kuwa? A zahiri kuwa sai ya ce “Ki yi hak’uri ba za’a sake ba.” “Allah ya Baka ikon sakewa ma, ba wannan ba dalilin kiranka dama so nake kud’in da zaka turawa Nanna na had’a lefe ka turo min su nan…” Da mamaki ya ce “Wani kud’i kuma? Abbi ne fa ya ce na bada list zai bata ta siyo min komai as contribution d’insa…..” Mommy ta ji wani irin sanyi ya ratsa ta Hakan yasa ta yi shiru. Har Zayyad ya gaji ya ce “Hello Mommy kina ji….” Da hannu Aisha ta dinga mata magana ai kuwa sai ta samu courage ta ce “Wani zancen banza ne wannan? A kan me za’a wani had’a maka lefe alhali kai ma Allah ya hore maka, to ban yarda ba wallahi da kud’inka za’a yi, ka gaya musu su bari ba’a so, salon nan gaba a dinga maka gori…” “Gori kuma Mommy?” Sai ya yi murmushi had’e da cigaba da cewa “In dai gori Abba M zai yi min, ai ina da abinda zai goranta min da yawa, kada ki manta since from day one till today bai fasa wahalta min ba, and ni ba zan iya gaya musu bana son abinda za su min ba gaskiya….” Daga haka ya kashe wayar zuciyarsa na wani irin huci, me Mommy take son zama ne? Ya lumshe ido hawaye na son zubo masa da ya ji amsar da zuciyarsa ta bashi kai tsaye. Mommy kuwa wayar ta dinga kallo kafin ta kalli Aisha ta ce “Kashe min waya fa ya yi?” Aisha ta yi Wata ırin dariya tana tafiya ta ce “Ai ke kuma Hajara, sai dai Allah ya kwatoki, don jinin Fulani ta gama aikinta Akan Zayyad, kan Uba! Wallahi Sai kin tashi tsaye….” Mommy ta dinga cije leb’e ai kuwa duk bala’i Zayyad ba zai yi amfani da lefensuba, a wannan karan Nima zan gwada k’wanjina.
Ammi bata fasa Aiken şu Kiyya ba, don kamar ta San za’a yi haka ta şaka Zakiyya ta yi snapping papern a wayarta. Don haka ko don ta cusa wa Mommy haushi Sai ta had’a lefen nan, ita matarma dariya take bata….
A gajiye su Kiyya suka dawo, suka zubewa Ammi abubuwan da suka samu siyowa. Tana fitowa daga wanka taga missed calls d’insa, kafin ya turo text. “Peppe soup pls, bana Jin dad’i, ki kawo min wajen Jadda.” Ta dinga kallon message d’in, kafin ta fita zuwa parlor. Ta ci sa’a Ammi na zaune sai ta zauna kusa da ita ta nuna mata msg d’in. Ammi ta d’an tab’e Baki ta ce “Ki yi masa mana.” Daga haka ta wuce part d’in Abbansu ta bar Kiyya a tsaye. Murmushi Kiyya ta yi ta shiga kitchen d’in. Allah ya taimaketa şuna ajiye tafasashshen Nama a fridge don haka grating scotch bonnet da onion kawai ta yi ta d’ora peppe mai masifar ya ji. Sannan ta d’ora Arabian tea.
Sallama ta yi a parlorn Jaddan. Jadda da take lazimi ta d’ago Tana kallonta kafin taga ta nufi wajen Zayyad. Duk da idonsa a rufe yake sai da zuciyarsa ta dinga bugawa da ya ji shigowarta. Kansa ne yake ciwo sosai ta zauna tana tafa hannunta ta furta “Ya Zayyad, ga Soup d’in. Ya bud’e idonsa da suka yi nauyi sosai ya zuba mata. Da sauri ta ce “Yaya Zayyad, ka ga idonka kuwa? Fever kake?” Ya d’aga mata kai. “Zuba min, amma kad’an.” Ta kuwa zuba masa, yana fara d’iba hannunsa ya fara rawa Hakan ne yasa ta d’au spoon d’in ta fara bashi a baki. 2 spoon ya yi ya lumshe idonsa. Sallamar Zainab ce tasa cokalin hannun Zakiyya sub’ucewa………
JIKAR NASHE✍🏽