Free chapter · Read without an account

Page-21

by Aisha G Umar · “SANADIN ƘADDARATA”

*FASAHA WRITER'S ASSOCIATION*
     (*F.W.A)*©✍️
     ⭐⭐⭐

Ƙungiya masu aiki cikin salon hikima da fasaha gurin juya tunanin al-umma, kaifin alƙalumansu ya zarta takobi ©✍
___________________________________________________



بسم الله الرحمن الرحيم.
اللهم صلي وسلم على نبينا محمد. 




❁ 𝐒𝐀𝐍𝐀𝐃𝐈𝐍 Ƙ𝐀𝐃𝐃𝐀𝐑𝐀𝐓𝐀 ❁ 




Free book📓



By


*Aisha G Umar*
_*🌹𝑍𝑎ℎ𝑟𝑎-𝑡𝑢𝑙-𝑄𝑎𝑙𝑎𝑚🖋️*_




Page2️⃣1️⃣






Jin an durƙusa akaina ne yasa ni ɗago kaina a hankali, tare da ɗaura idanuna cikin na sa, kamar yadda shima na sa idanuwan ke cikin na wa. Take zuciyata ta fara wani irin harbawa wanda ba lallai na taɓa jin irin wannan yanayin ba.

Shima à ɓangaren Abba kallon Nuriyyah ya ke yi yayin da zuciyarsa ke motsawa a hankali, bai yi magana ba kuma bai ɗaga da durƙushen da ya yi yana kallon fiskarta ba, bayan wasu sakwanni. Zafi na fara ji à gurin gwuiwar hannuna ashe lokacin da na faɗi na ƙurje a wurin ban sani ba, zafin da na ji ne yasa ni saurin kai hannuna a wurin tare da fitar da sauti "ahhh" sai a lokacin Abba ya fita daga duniyar da ya ke ya yi saurin cewa, "oh sorry, yana miki zafi sosai?".

Ban yi masa magana ba sai ƙoƙarin tashi da na ke yi, miƙewa ya yi tare da miƙo min hannu alamar zai taimaka min in tashi, kallonsa na yi na rashin fahimtar abun da ya ke son yi, hakan yasa ya lura da hannun da ya miƙa min, ya yi saurin janye hannunsa ni kuma na miƙe ina kaɗe jikina ko da ba wai ƙasa ba ne a wurin. "Kina lafiya?" Abba ya faɗi yana kallona, ɗaga masa kai na yi alamar eh.

"Amma ke bakya gani ne?" Na tsinkayi muryarsa ya faɗi hakan, da mamaki na bar karkaɗe jikina da na ke yi na dawo da dubana garesa. Kafin na yi magana ya ɗaura da cewa, "ba kya gani ne lokacin da ki ka iso ƙofar? Ki rinƙa lura nan gaba kada ki sa ke yin hakan, ba ki san a inda zaki faɗi ba kuma" ya faɗi tare da kawar da kansa kamar ba shi ya yi maganar ba yasa ƙafarsa zai wuce.

Abun da ya faɗa mamaki yasa ni da sauri na dakatar da shi tare da haɗe fiska, na sha gabansa ina kallonsa haɗi da ɗan haɗe girana alamar ya fa raina min wayo, shi fa ya turo ya sa ni na fa ɗi, amma kuma ya yi min wannan maganar? Ɗaga min gira ya yi alamar ya dai? Saboda na tsaida shi amma ban yi magana ba.

Duk da ina jin sautin da zuciyata ke min amma bai hanani cewa ba, "me ma ka ce?" Bai amsa min ba sai ni na ƙara faɗin, "ni ya kamata na ce maka ba ka gani ne? Saboda kai ka turo ƙofar da ƙarfi kamar wanda aka sa gasar ƙarfi, ba ka yi tunanin ko akwai wani ba, kawai ka turo abunka kamar kafi kowa hanzari" bai ce komai ba sai da ya kalleni daga ƙasa har sama, hannunsa ya ɗaga yana yin sama da shi wai yana auna tsawona da na sa.

Tsaida maganar da na ke na yi ina bin hannunsa da kallo, "me ka ke yi ne?" Na yi masa tambayar fiskana na bayyanar da ɓacin rai kaɗan, murmushi ya saki sannan ya ce, "ina son gasgata wani magana ne", gyara tsayuwata na yi na sake tambayarsa, "wani magana?" "An ce gajerun mata akwaisu da surutu sannan da masifa, gashi kuma na ga hakan daga gareki".

Buɗe baki na yi jin abun da ya faɗa, "ni ni ce gajera?" Na faɗi kamar mai ei'ina ina kallonsa tare da sake haɗe fiskata sosai, girgiza min kai ya yi alamar tabbatarwa sannan ya sake sa ƙafa yana wucewa, taku biyu ya yi na sake shan gabansa, ban ga wasa a idonsa ba, hakan kuma bai hanani cewa ba, "akan me zaka ce min gajera?". Girgiza min kai kawai ya yi ya wuce abunsa. Na juya ina bin bayansa da kallo a fili na ce, "dube shi fa, sai ka ce shi tsawon ya ke da shi, amma wai ni ce gajera!".

Ƙasa da kaina na yi saboda maganar ta sa ta ɗan min tsaye a ƙirji, "to kuma wai ni gajerar ce?" Sai na giɗa kaina da sauri na sake cewa, "a ah ba haka ba ne" na faɗi ina sake kallon sashin da ya yi na Hajiya Kaka, "to ko ma waye shi? Ƙila shima bikin ya kawo shi" na faɗi sannan nima na wuce aiken da Momy ta yi min da sauri.

Abba kuwa ko da isansa falon Hajiya Kaka ya tarar da Asma'u har da wasilla, da gudu su ka iso garesa cike da farin ciki sosai, shima faɗaɗa murmushin fiskansa ya yi da murna, "oyoyo yaya Abba your welcome!" Su ka haɗa baki gurin faɗi cike da murna, shima ya amsa da, "Sisters ya ku ke? Kai amma kun canza fa sosai, ashe da ko na haɗu da ku a waje ma ba zan gane ku ba".

"Haba dai yaya Abba, in ba ka ganemu ba ai ba ka yi mana adalci ba" cewar Asma'u tana dariya, ta sake ɗaurawa da cewa, "to ina tsarabata" "dama wannan kalmar na ke jira, na san dole sai kin faɗeta, amma haka ake yi ne? Ba a tambayeni ya hanya ba, sai kawai ace ina tsaraba?" "Yaya Abba ai na san ba ka gaji ba, tun da har fita ka yi ba ka huta ba". Faɗin Asma'u.

Itama Wasila ta ce, "gaskiyanta ne yaya Abba, to dama ɗazu ba ka ba ni na wa ba, sai ka haɗa ka ba mu tare", sai da Abba ya gyara sannan ya ce, "to kar ku damu na zo muku da tsaraba dukkanku" da murna su ka haɗa baki gurin faɗin yauwa, nan su ka zauna a falo suna hira gwanin sha'awa.

Bayan na dawo ban je inda Asma'u ta ke ba, saboda ance tana sashin Hajiya Kaka, don haka na shige ɗakinmu na zauna abuna. Lokacin Sadiya ta shigo, zuwa kusa da ni ta yi ta zauna a gefena tare da saƙale hannunta a kafaɗana tana cewa, "'yan mata faɗa min me matsalar? Ya aka yi na ganki ke kaɗai haka cikin kaɗaici? Ina su ƙawayen na ki su ke?" Ta ƙarashe tana kallona haɗi da ɗaga min gira.

Nima da ya ke kallonta na ke sai na ce, "suna can sashen Hajiya Kaka" Sadiya ta san me yasa ban je sashin ba, don haka fiskarta ya bayyanar da wani iri na rashin daɗi, ni kuwa ganin hakan yasa na ɗago ɗayar hannuna na ɗaura akan na ta ina cewa, "amma ni dai ba gani tare da Antyna ba? Tom Anty Sadiya, faɗa min shin idan ki ka tafi zaki yi kewarmu?" Cire hannunta ta yi da ta sa a kafaɗana.

Ta riƙo hannuna, wani tunani ne ya faɗa ranta akan auren da za ta yi ɗin, amma sai ta share ta ce da ni, "zan yi kewarku sosai fiye da tunani, yanzu wani abu na ke ji, ina kamar..." sai kuma ta dakata, "kamar me Anty Sadiya?" Na faɗi ina kallonta. "Kamar a fasa aurena da Faruq, duk da cewa ina sonshi kuwa, saboda ina tsoron kada matsalar danginsa ya zamar min matsala a rayuwarmu, sai dai na san babu yadda za ayi hakan ya faru yanzu".

Girgiza hannun Anty Sadiya na yi cikin damuwa na ce, "me ki ka ce Anty Sadiya, ya kamar idonki na kawo ƙwallah?", ijjiyar zuciya cikin sauri Sadiya ta yi ta sa hannunta ta goge ƙwallan tana kallona, saboda ta gane maganar da ta yi a zuciyarta ta yi ba a fili ta faɗi ba. Sake tambayarta da na yi ne yasa ta miƙewa tare da sakar min murmushin yaƙe ta ce, "ba komai ƙanwata, amma ki yi min addu'a kin ji?" Girgiza mata kai na yi sai ta sake cewa.

"To bari na je sabida akwai program ɗin da mu ke haɗawa akan bikin" tana faɗi ta fice, ko abun da ya kawo ta ma ba ta yi ba. Sauke kaina ƙasa na yi saboda kamar akwai abun da ya ke damun Anty Sadiya, to amma ta yu ko tunanin dangi ne yasa ta hakan, don na ji ana cewa idan amarya zata yi aure tana sa tunani a ranta na rabuwa da 'yan uwa. 

Tashi na yi na ɗauko alqur'ani don in rage lokaci da shi. Ina cikin rerashi cikin nutsuwa Asma'u da Wasila su ka shigo ɗakin, "a haf malamar tana nan" cewar Asma'u suna murmushi, samun aya ba yi na tsaya ina jefa musu kallon tuhuma, "oh calm malama, irin wannan kallo haka?" Wasila ta yi maganar tana dariya, ni kuwa na ce, "ku dai ku ke min kallon da ban gane masa ba, ji na yi Asmee har da cewa malamar ta na nan".

Dariya su ka yi Wasila ta ce, "eh mana to duba ki mu ke yi, tun ɗazu yaya Abba ya dawo amma ke ba mu ganki ba bare ku gaisa ki yi masa magana" murmushin ya kubuce min na ce, "da gaske?" Wasila ta amshi Alqur'anin da ke hannuna ta maida shi mazauninsa, sannan ita da Asma'u kowa ya kama hannuna su ka ɗaga ni na tashi, Wasila tana cewa, "mu je ki ga da gaske ɗin" saurin giɗa kai na yi ina cewa, "a ah ku bari ba yanzu ba".

Ko saurarona ba su yi ba mu ka kama hanyar zuwa side ɗin Hajiya Kaka, jin kiran da Mama ke yi mata ne yasa da sauri ta dubeni ni da Asma'u ta ce, "na ji Mama na kirana, bari na yi sauri na je kada a samu matsala, da toh Asma'u ta amsa ni kuma ina mamakin yadda Wasilar ta ke tsanasnin tsoron mahaifiyarta ta, saboda da zararar ta ji muryarta to tashi ta ke da hanzari sosai, duk da abu ne mai kyau ɗa ya ji tsoron mahaifansa, amma na ta ya yi yawa, kuma sauran 'yan uwan na ta ba na ganin suna haka. 

"Ke Asmee ban faɗa miki ba" Nan na zayyanewa Asma'u abun da ya faru, dariya ta kwashe da shi tana cewa, "kai amma koma waye wannan ya burgeni, ko ba komai ya haɗu da ɗan masifar Nuriyyah". Ta faɗi tana dariya har mu ka isa sashin Hajiya Kaka, Hajiya Kaka da wasu 'yan uwa da yawa suna falon, gaishesu na yi, wa'yan da su ka iya amsawa sun amsa, wa'yan da bakinsu ya yi nauyi kuma sun yi shiru, ba tare da Asma'u ta tsaya jira ba ta cigaba da jana, ni kam gaba ɗaya na rasa me ke min daɗi, saboda mutanen falon da ke min gani-gani ne? Ko kuwa saboda zan haɗu da Abba ne? Nima ban sani ba.

Ɗakin Abba mu ka nufa yayin da zuciyata ke bani wani sauti na daban, sai kuma wani tunani ya zo min, kar dai shine wanda mu ka haɗu ɗazu?. Bayan Asma'u ta yi sallama ya bada izinin shiga, sa kai mu ka yi ciki tare da sake yin sallama, ko da mu ka shiga yana zaune a kujera kansa kuma akan laptop ɗinsa, ya ɗan ba mu baya hakan yasa banga fiskarsa ba.

A ƙofar na tsaya Asma'u ta ƙarasa ciki, tana yi masa magana akan aiki ya ke yi ne? Sai ya ce da ita eh wani abu mai mahimmanci ya ke yi, "yayana ga Nuriyyah na kawo maka ita ku gaisa" cewar Asma'u, ba tare da ya yi magana ba ya ce, "Nuriyyah kuma?" "Eh wacche na ke maka maganarta in muna waya, ga ta nan" ta faɗi tare da juyawa ta ganni à ƙofa tsaye, ta ce, "taho mana".

A hankali na ke takowa zuwa inda Asma'u ta ke, lokacin Abba ya ɗago kai murmushi ya bayyana a fiskarsa, kafin na iso gun Asma'u ya ɗago kansa, nima dama idona na kansa don ganin fiskarsa, duk da ina jin shi ne wannan mutumin da ya bugeni kuma ya faɗa min magana ɗazu. Zaro ido na yi ko da ganin tabbas shi ɗin ne. "Asmee dama wannan shi ne yaya Abban?" Na tambayi Asma'u.

"Wannan gajerar yarinyar masifaffiyar ita ce Nuriyyah?" Faɗin Abba shima yana nuna ni da yatsa, haɗe fiskata na yi jin ya sake faɗa min wani maganar. Da mamaki Asma'u ta ke binmu da kallo kafin ta yi magana Abba ya sake cewa, "my Si ya aka yi ki ka iya zama da wannan mai tsiwan haka?".

"Kin gani ko Asmee? Ɗazu ya ce min gajera, ga shi yanzu ya sake faɗa min haka, har da cewa mai tsiwa, yanzu ke Asmee kin yar da ina da tsiwa?" Asma'u da ta ke kallonmu kawai ta giɗa min kai alamar a ah, "yauwa kin faɗi gaskiya" na faɗi ina juyawa gun Abba na ce, "ka gani, kai ne mai tsiwa da neman tsokana, kuma ai ɗazu kai ne ka min mugunta, da a ce ka yi tambaya akwai mutum a kusa? Da ni zan ce maka eh, sai ka bari na wuce kai kuma ka wuce, amma sai ka turo da ƙarfi, shine ni ban...".

Katseni ya yi da faɗin, "kin fi kama da 'yar gidan radio, saboda akwai ki da surutu sosai" haɗe fiskata na yi na dubi Asma'u na ce, "ni na koma sashin Momy" kafin na fice na juyo na dubeshi na ce, "yaya Abban nan ka tsokaneni, kuma saboda kai kamar yaya ka ke awurina, da ba don haka ba Abba zan kiraka" "bayan kin riga da kin faɗa gajera?" ya faɗi yana murmushi, ni kuma juya kai na yi na fice a ɗakin, ina jin haushinsa.

Shi da Asma'u su ka haɗa ido sai kuma su ka kwashe da dariya, "wannan Nuriyyar akwaita da ban dariya" ya faɗi yana cigaba da danna laptop ɗinsa, Asma'u ta ce, "nima ban san da hakan ba sai yanzu".

WASHE GARI.

Sarƙoƙi da yawa aka kawo don mutane kowa ya ɗauki na shi. Ina cikin ɗaki ban fita ba, sabida idan ba aike ba ne ko wani abun na dole ba na son fita saboda mutane, Asma'u ta yi ta yi da ni inzo mu je in zaɓi nawa wanda zamu sa na aure, amma na ƙi na ce ita ta zaɓar min, ba don ta so ba ta wuce ta barni. Kiran da Momy ta yi min ne yasa ni saurin fitowa ina amsawa, na ga ta fito riƙe da wani waya a hannunta yana ringing, ko da na isa inda ta ke ta ce min.

"Na kira Asma'u tana ina? Ko ma amshi wannan wayar ki kaiwa Abba, tun ɗazu da ya zo ya bar shi sai kira ake ta yi" Momy ta faɗi tana miƙa min wayar, amsa na yi kamar mai tunani sai kuma na juya ina neman wanda zan ba ya taimakeni ya kai masa, saboda ba na son haɗuwa da yaya Abba, na san in na je wata tsokanar zai min, kuma ma zuciyata ba ta sukuni idan na ganshi gaba ɗaya.

Kasancewar ban ga wanda zan ba ba sannan ga waya ta sake ring yasa na yanke shawar zan kai masa kawai, a yau ma kamar jiya mutane cike a falon Hajiya Kaka, bayan na gaishesu ban tsaya wani jira ba bare a samu wata da za ta jefa min magana. Ɗakin jiya na nufa inda Abban ya ke don Momy ta ce min yana ɗakinsa. Ƙwanƙwasa ƙofar na yi amma na ji shiru ba a amsa sallamar ba, kuma ga kiran da ya ke jikin wayar bai bar ringing ba, don ma dai na latsa gurin kashe hasken wayar ne da harda ƙara zai yi.

Tura ƙofar na yi na shiga don in ajje wayar kawai na fito tun da alamu babu mutum a ciki, ina tura ƙofar shi kuma ya fito daga toilet ɗaure da tawel a ƙugu, saura kaɗan wayarsa da ke hannuna ta faɗi ƙasa saboda razanar da na yi bayan na kalleshi, sannan na yi saurin riƙeta haɗi da juyawa na bashi baya, numfashina ya fara up and dawn. Shi kam Abba da kallo ya bi Nuriyyah haɗi da mamakin me ya kawota?....


Last page
___________________________________________________

Hmm kun ji dai abun da ya wakana a cikin page ɗin nan. Me yasa Sadiya ta yi tunanin fasa auren Faruq? Shin akwai wani abu da ba mu sani ba? Ga Nur and Abba, wai wannan faɗa ne ko kuwa?😁

Mu kasance a next page don jin me zai faru?




_*🌹𝑍𝑎ℎ𝑟𝑎-𝑡𝑢𝑙-𝑄𝑎𝑙𝑎𝑚🖋️*_

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.