Free chapter · Read without an account

Chapter 35

by Narrnarhh Bukar · BAHAGON TUNANI BOOK 1,2&3

The Amazing Pen ✍️.......

BAHAGON TUNANI

بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم

035

''And so what idan ya tsine mini! A tunaninki ko tsinuwa sau dubu zai mini za ta kamani ne! Hhhhh! Kin yi sake marayan zaki ya girma! Karan bana shi ke maganin zoman bana! Ba Yasir ba ne da kika mallake yake bin umarninki jikinshi na rawa ko Hamida ba! Na san komai! Duk abin da kike ƙullawa ke da uwarki ina sane da su! Babu abin da kika isa ki yi da yardar Allah wallahi"

''Assalamu Alaikum'' Dauda Imamu ya yi sallama yana shigowa ɗakin,Sahura bata iya amsa sallamar ba saboda mutuwar tsayen da ta yi tana kallon Jalil bakinta sake tsabar mamakinsa. Bata taɓa tunanin Jalil haka yake ba,ido cikin ido yake faɗa mata baƙar magana babu tsoro balle firgici. Muryar Gwaggwon Bugaje ce ta farautota daga duniyar tunani.

''Dauda! Yanzu tarbiyyar daka ba yaranka kenan! Suna zagin matarka kamar sa'anninsu!''

Dauda Imamu da bai fahimci inda maganarta ta dosa ba ya ce

''Gwaggo ban fahimceki ba,me ke faruwa ne? Wa ya yi zagin a cikinsu?"

''Jalil mana mai ido kamar na mujiya! ''

Juyowa Dauda Imamu ya yi wurin Jalil ya ce

''Jalil da gaske zaginta ka yi...''

''Ƙarya zan yi mishi Dauda!''cewar Gwaggwon Bugaje tana katse maganarsa.

''A'a Gwaggo mamaki ne ya saka ni faɗin haka.''

Wani irin zafi zuciyar Jalil take yana kallon Gwaggwon Bugaje cike da tsana. Yasir da Hamida rataye da jakukkunansu suna jiran umarni. Sauran yaran gidan ma sun fito idan ka cire Nu'aymah sun tsatstsaya suna kallon ikon Allah. Hamid ne kaɗai bai fito ba yana can yana sharɓar baccin asarar da ya saba duk safe. Sake juyowa Dauda Imamu ya yi yana fuskantar Jalil fuskarsa a ɗaure ya ce

''Jalil rashin kunyarka har ta kai ga zagi matata!'' ya yi maganar yana nuna kansa.

'' A'a Abba ban zageta ba! Kawai don na zo kiransu Yasir saboda sammako nake so mu yi zuwa Gusau shi ne ta ce ba za su ba. Jiya Ammu Jamila ta kira ni cikin dare  suna asibiti Ammu na cikin mawuyacin hali. Mene ne haɗinta da Ammuna da za ta hanasu zuwa''

''To na ce ba za su je ba! Makaranta za su!'' cewar Sahura wadda sai yanzu ta yi magana.

''Baki isa ki hanasu zuwa ba wallahi'' cewar Jalil yana buɗe mata manyan idanunsa.

''Jalil ka hakura ka je kai kaɗai mana tun da ta ce makaranta za su je''  cewar Dauda Imamu don kwata-kwata baya son ɓacin ranta. Ƙunci Jalil ya ji a cikin ransa yana bin Abbansu da kallo,matar nan ta gama cutar su, yanzu ƙiri-ƙiri ta katange Abbansu zuwa wurin Ammunsu sannan kuma yanzu tana niyyar hana su zuwa wurin Ammunsu dubata. Me take so da su ne,wani irin son zuciya ne da ita haka, kanta da 'ya'yanta ta sani su kuma ko oho,wata shari'ar sai a lahira don ba za su taɓa yafe zaluncin da ta musu tun suna yara har zuwa girmansu ba.

''Ka ji dai da kunnuwanka ubanka ya ce ba sai sun je ba tun da baka jin maganata. Idan kuma ka yi jayayya zan saka shi ya tsine maka!'' ta yi maganar cike da izza da iko.

Shiru ɗakin ya yi kowa na jiran abin da Jalil zai ce. Hamida sai hawaye take jin da wuya ta je ganin Ammunta,fuskar Yasir bata nuna yanayinsa ba,ya dai ɗan dukar da kansa ƙasa. Dauda Imamu ya tsaya yana jiran umarnin Sahura,shi dai burinsa kar ran Sahura ya ɓaci,yayin da su Gwaggwon Bugaje ransu fes suna jiran ganin yadda wasan zata kaya. Buɗar bakin Jalil ya ce

''Muhsin''

Mushin da ke gefansa yana bin 'yan ɗakin da kallo ya amsa ''Na'am ɗan'uwa''

''Kira Madam Ngozi yanzu ka ba ni wayar!"

''Ok" ya faɗa yana ciro wayarsa. Tsuru-tsuru Sahura ta yi ƙirijin na duka,sunan madam Ngozi da ya ambata kaɗai ya birkita mata lissafi balle kuma ta ganta a zahiri. Babu shiri Sahura ta ce

''Hamida! Yasir ku ta fi Allah ya tsare hanya! Shege ya san abin da ya taka shi ya sa yake gaggasa mini magana son ransa''

Munafikin murmushi Jalil ya yi sannan ya miƙa ma Muhsin wayarsa,daman plan suka haɗa mata,idan taƙi yarda da tafiyan su Yasir sai su yi kiran ƙarya a waya. Tabbas haƙarsu ta cimma ruwa,tun kan su yi kiran har ta tsorata. Lallai madam Ngozi ce babban makaminsa, cewar Jalil a ransa suna tafiya, zuwa lokacin har rana ta ɓullo. Keke napep ɗaya suka hau su hudun zuwa bakin gate ɗin barikin. Officer Kabir ya turo ma Jalil dubu ashirin a account saboda tafiyar,tun jiya da yamma ya sanar masa a waya rashin lafiyar Ammunsa kasancewar baya garin, momy kuma ta ba su dubu goma su ƙara da yake tare da Muhsin za a yi tafiyar.

A falon Gwaggwon Bugaje ta harari Sahura tana faɗin

''Yanzu saboda an kira kirista soja kike saurin tsorata,sai ka ce baki haihu ba! Kin manta halin ɗan yau ne! Ƙila ma karya suke ba itan za su kira ba. Kawai don sun fahimci nan ne makasarki''

''Kuma fa maganarki tana kan hanya! Ƙila ƙarya suke don Jalil ya san ina matuƙar tsoron Madam Ngozi. Shegen ɗuniya! Za ka iya tafiya Baban Hamid daman a kan Jalil ne na kiraka"

''To ranki shi daɗe'' ya amsa yana barin gidan.

Taɓe baki Gwaggwon Bugaje ta yi cike da jin haushi,don ta so Sahura ta hanasu zuwa ganin uwarsu.

''Ni wallahi ban ga abin damuwa a nan ba. Mene ne na son hanasu zuwa wurin uwarsu tun da bata da lafiya,rashin lafiya ai ya shafe komai" cewar Ɗayyaba.

Harara kowannansu ya wurga mata. Sahura ta ce

''Allah ya wadaran naka ya lalace! Ɗayyaba kar dai irin wannan tausayin kike nunawa a gidan mijinki! Indai kuwa haka ne dole mallakarki ta yi saurin warwarewa''

''Faɗa mata dai' cewar Gwaggwon Bugaje tana sake hararta.

''Ai babu tausayi a wannan harkar idan kina son mallakarki ta ɗaure''

'' Ai auta kwata-kwata bata jin maganata,ta ga yadda nake nuna isa a gidana amma ita tausayi ya mata mugun kamu.''

''Hmmm gwara ki sauya kam''

Ɗayyaba bata amsa musu ba sai ma wucewarta ɗaki ta yi ta kwanta,duk rashin imaninta ba za ta taɓa yin abin da uwarta da Sahura suke yi ba. Tabbas tana mulkar mijinta amma ba a irin wannan sigar zaluncin ba. Kicin Sahura ta shiga tun da yau baiwarsu ta su bata nan. Gwaggwon Bugaje ta saka Amina ta kunna mata kallo ta zauna...✍️

^^^^^^^^^^^^^

Yariman Bakura specialist hospital

*Ƙarfe 10:12am na safe

Likita ɗaya da nurses biyu suka shigo dubata. A hankali numfashinta ke tafiya da taimakon oxygen,cikin dare aka maƙala mata shi,sai aka ƙara mata ruwa da magungunan gaggawa (IV drug) a ciki,sun samu tana bacci. Ɗan dubata likitan ya yi ya tambayi Jamila yanayin jikinta ba shi amsa. 'yan rubuce-rubuce ya yi sannan ya ce

''Zuwa an jima idan result ya fito zan sanar da ku''

'' To likita! Me ke dumunta? Don Allah likita ka taimake ni wallahi bana son na rasa 'yar'uwata ita kaɗai ta rage mini a duniya'' Jamila ta faɗa cikin raunin murya ƙwalla na taruwa a idanunta. Murmushin karfafawa ya yi yana faɗin

''Ki kwantar da hankalinki! In shaa Allah za ta samu sauƙi,sai sakamakon gwajin da muka mata ya fito sannan za mu san ainihin abin da ke damunta''

''Allah ya amsa"

''Ameen ''ya faɗa yana sakar ma HAFIZA murmushi. Tamke fuska HAFIZA ta yi tana juyar da fuskarta gefe tare da cunno baki,don ta tsani kallo. Bayan fitarsu da 'yan wasu mintoci tawagar mutanen Mada suka yi sallama,da yake da suka zo asibitin sun kira Jamila sai ta sanar musu lambar ɗakin. Kawu Rabi'u,Mamman,mijin Jamila wanda ya kasance direbansu sai uwar gidan Kawu Rabi'u da ɗan uwan mahaifinsu Mairi. Sun yi tsaye kowanne yana dubanta duk da bacci take har zuwa lokacin. Kawu Rabi'u ya dubi Jamila ya ce

''Me likitan ya ce yake damunta?"

''Ya ce sai zuwa an jima idan sakamakon gwajin da suka mata ya fito zai san abin da ke damunta''

Sauke numfashi ya yi yana faɗin

''Kin sanar ma mijinta da yaranta kuwa?"

''Yaran kawai na sanar musu amma ban da lambar mijinta haka ma Yaya bata da lambarsa''

''A'a! Ita Mairin bata da lambarsa! Mijin nata a ce bata da lambarsa!" Ya maimaita yana kallon Jamila.

''Kawu rabon da ta saka shi a ido ai tafi shekara huɗu yanzu. Kishiyarta kwata-kwata ta hana shi zuwa''

''Amma baki sanar mini abin ya kai har haka ba Jamila?" Ya faɗa cike da damuwa.

"Ni ma da kyar ta sanar mini ka santa da zurfin ciki, ta gwammace ta bar komai a cikinta a kan ta faɗa ma kowa.''

''Gaskiya tura ta kai bango yanzu! Dole na yi zama da shi,ya sawwaƙe mata ta san babu igiyar aure a kanta,da wannan auran da bai da maraba da babu,yaran ma dole su dawo hannunta,wannan ai zalunci ne! Ka bar mata har shekara huɗu bata tako zuwa inda take ba! Duk da na san sharrin matarsa ce amma abun ya yi yawa gaskiya,ya saketa kawai!''

''Ni ma dai abin da na gani kenan Malam,ya saketa kawai tun da yanzu hankalinsa ba a kanta yake ba,ba dole ta shiga kunci ba,babu miji babu yara kusa da ita! Ni ai na ga ma ƙoƙarinta na tsawon shekaru '' cewar uwar gidan Kawu Rabi'u.

''Maganarku tana kan layi,yanzu mu jira samun lafiyarta tukunna,idan ta kama har kotu ne sai mu je a sawwaƙe mata wannan zaluncin da me ya yi kama'' Ɗan uwan mahaifinsu Jamila ya faɗa fuskarsa shimfiɗe da damuwa.

'' Mu jira samun lafiyarta tukunna kamar yadda ka ce, dole mu bi mata haƙƙinta don abun ya yi yawa! Ubangiji ya tashi kafaɗunki Mairi! Ya baki lafiya mai amfani,ya sa zakkar jiki ce.''

''Ameen'' duka 'yan ɗakin suka amsa.

''Assalamu Alaikum'' Sadiƙu ya yi sallama yana shigowa ɗakin matarsa na biye a bayanshi. Dukkaninsu suka amsa,cike da girmamawa ya gaida su sannan ya tambayi ya mai jiki, suka amsa da Alhamdulillah. Shekara uku kenan da auransa, duk da ya yi aura bai fasa ɗawainiya da su Mairi ba,cinsu,shansu da lafiyarsu yana bakin ƙoƙarinsa. Har gida wani lokacin yake zuwa da kansa ya kawo musu cefane ya gaisheta. Kuɗin makarantar HAFIZA boko da hadda shi yake biya,duk da kasancewar dukiyar Dauda Imamu yake juyawa amma samun kamarsa mai adalci da matukar wuya. Duk sallah yana ma Mairi da HAFIZA ɗinkuna kala bibbiyu wani lokacin idan kasuwa ta buɗe sosai har kala biyar yake ma HAFIZA,ranar jajibari yakan aiko da kaji ko ginsamin naman shanu. Mairi kullum cikin yi masa godiya take saboda taimakon da yake musu akodayaushe.

Sadiƙu bai daɗe da zuwa ba wata nurse ta shigo ɗakin da sallama. A tare suka amsa mata. Duba ruwan da aka saka ta yi da na'urar shaƙar iska sannan ta ce

''Ina mijinta yake''

''Bai riga da ya shigo ba'' cewar Kawu Rabi'u.

''Babu wakilinsa a nan,saboda sakamako ne ya fito muke son sanar masa. Sannan kun yi yawa a ɗakin mara lafiya gaskiya saboda a condition ɗin da take ba a son hayaniya''

''To. Za mu gyara in shaa Allah,daman ba magana muke a ɗakin ba,idan na ji abin da ke damunta sai mu ɗauki hanya ba a garin nan mu ke ba''

''Ok toh. Daman hayaniyar ce ba a so,tun da ba daɗewa za ku yi ba shikenan. Bari na yi maka jagora zuwa ɗakin Likitan '' ta yi maganar tana yin gaba ya biyota a baya.

''Ni ma kawu zan je'' cewar Jamila tana miƙewa.

''To mu je'' ya faɗa yana barin ɗakin.

Kai tsaye nurse ɗin ta nuna musu ofis ɗin likitan sannan ta wuce. A kujerun da aka tanadar na masu rashin lafiya suka zauna suna fuskantar likitan. Fuskarsa a matuƙar ɗaure ya ce

''Kai ne mijin?"

Da sauri Kawo Rabi'u ya girgiza masa kai yana faɗin

''Ba ni ba ne likita,kawutna ne sai kuma ƙanwarta'' ya faɗa yana nuna Jamila. Iska likitan ya furzar yana gyara neck tie ɗinsa. File ɗin da ke gefansa ya ɗauko ya buɗe, takardu biyu ya ciro ya ɗora a saman file ɗin sannan ya ɗago yana dubansu. Tagwayen ajiyar zuciya ya sauke ya ma rasa ta inda zai fara musu bayanin,a gefe guda sun tsura masa idanu suna jiran bayaninsa musamman Jamila da zuciyarta ke dukan uku-uku. Daga ƙarshe likitan ya fara maganar cike da damuwa bayyane a fuskarsa mararan.

''Da farko dai mun gano ta daɗe tana fama da ciwon zuciya wanda a hankali ta fara kamuwa sakamakon tsananin damuwa,ƙunci ko tashin hankali. A lokacin da kuka kawota asibiti a sume mun yi binciken gaggawa,inda muka gano jininta ya yi ƙasa a turance muna kiransa da Hypotension . Sannan tana fama da arrhythmia ma'ana bugun zuciyarta ba ya tafiya daidai yadda lafiyayyen zuciya ce bugawa. Sai kuma bata da isasshen iskar oxygen a jiki. Alhamdulillah mun yi nasarar farfado da ita daga suman da ta yi, sai muka yi gwaje-gwaje har huɗu wanda yau sakamakon ya fito''

Ɗan numfasawa ya yi yana bin su da kallo har yana iya hango tashin hankali a kwayar idanunsu musamman macen da ta fara zubar hawaye. Gyara zamansa ya yi yana ɗaukar takarda daya sannan ya ce

''Mun yi mata Blood test wato gwajin jini,inda sakamakon ya nuna cewa; Haemoglobin ɗinta ya yi ƙasa sosai,sannan akwai severe anemia wanda shi ne ya sanyata suma. Sannan Cardiac enzymes sun tashi aiki wanda yake nuna raunin tsokar zuciyarta. Sai gwajin ECG,wata nu'ara ce da muke amfani da ita wurin gano yanayin bugun zuciya,a gwajin da muka mata mun gano zuciyarta bata bugawa a daidai, wanda hakan na nuna cewa zuciyarta tana cikin hatsarin tsayawa...''

''Hasbunallahu wani'imal wakil! Allamma ajurni fi musibati war zuƙni Khairan Minha! Allah mun tuba ka yafe mana ba don halinmu ba! Likita! Kana nufin zuciyar yayata na gab da daina aiki?!" Jamila ta faɗa hawaye na gangaro mata bisa kunci. Cike da tabbatarwa likita ya ce....✍️

Narrnarhh Bukar's Amazing pen

***

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol