Free chapter · Read without an account
Part 4
by Aisha Hamza · BADAƘALA
BADAKALA ✍️ Aisha Hamza (CHEFMUAYSH)
Sama sama gwaggo ta amsa mata suka gaisa kafin tasamu waje ta zauna ta haɗe rai tace gwaggo zuwa nayi inji Ayrah lafiya kwana biyu ina aikowa kiranta bata zuwa
Inno tasan gwaggo ba kanwar lasa bace ba shiyasa take sassauta kalamanta
Gwaggo tace batada lafiya gatanan kwance ta cigaba da duba littafin ta bata ƙara bi ta kanta ba har Inno tagaji da zama tarasa abinda zata faɗa Saida ta mike kafin tace to gwaggo a daiyi hakuri damu don munzama ciwon ido kuma wallahi
Ayrah sai ta ci-gaba damin tallah akan me aita lallabaku amma baku gani
Sakin baki gwaggo tayi duk da tasan halin Inno ɗin zata aikata abinda yafi haka amma saita share da'ita har tayi waje tana yan surutai
Surutan data fara ne ya farkar da Ayrah daga baccin da takeyi a firgice ganin gwaggo ta zuba mata idone yasa tace gwaggo hayaniya nakeji a gidan lafiya kuwa
Gwaggo tace Inno ce tazo nemanki dan jimm Ayrah tayi kafin tace gwaggo me tace kuma
Gwaggo tace ba wannan ba dai kina bacci Uncle Sameer yayi miki sako gashinan cikin leda saiki tashi ki duba
Har saurin kai idonta take inda gwaggon ta nuna mata kusa da inda take kwance hannu ta zura tajawo ledar mai layi layi yellow tafara dubawa
Slice bread ne a ciki tare da madara sachet uku da milo sachet biyu sai soyayyar awara da zafinta kallon gwaggo tayi tace yaushe yakawo ne
Gwaggo tace bai dade da aiken ba saiga Inno ta shigo ta kuma cewa waya aiko gwaggo tace ke bansani ba kin isheni da tambaya tambai
Murmushi Ayrah tayi tasamu ta tashi zaune tana faɗin yi hakuri gwaggona ai ya kamata ki saba hakanan da tambayoyin nan nawa wai nace gwaggo Umma barira ta shigo kuwa
Gwaggo ta kuma cewa itama ta kawo abinci gashi can a kwano don ni har naci nawa kunu da kosai ne kafin ki tambaya me takawo
Sosai Ayrah ta kyalkyale da dariya tace kai gwaggo wato kinsan tambayoyin nawa bari kibani amsa kafin na tambaya
Gwaggo tace ai yanzu dai bari in kwalla ma barira kira taxo ta kamaki ki tashi ki wanke bakinki kizo ki karya
Saida barira ta taimaka mata ta wanke bakinta tadawo daki kafin tace mata don Allah ta haɗa mata ruwan zafi a ƙaramin kofi
Barira tanada kirki Sosai taje ta dafa mata a dan madaidaicin jug takawo mata tace gwaggo tahada musu shayi tunda ga bread Uncle Sameer yakawo musu
A kwana na uku saboda bata da kan jiki ta mike saidai takan ɗan dingisa wani lokacin taji daɗin yanda uncle Sameer yake kula da'ita sosai don yana yawan yimata aike har ta kagara takoma makaranta domin tayi masa godiya da kuma Khairiyya da take yawan kawo mata ziyara kuma indai tazo saita dameta da zancen Uncle Sameer din don tagama lura da Khairiyya tafara sonshi ne
wasa wasa har aka kwana bakwai da zuwan Inno malam bai ƙara koda tako kafar sa gidan ba kuma bai aiko musu da komai naci kamar yanda aka saba saidai idan uncle Sameer yamata aike ko kuma barira takawo musu
Sosai abin yafara damun gwaggo harta fara zancen da Ayrah, nikam Ayrah anya kuwa lafiya gidan can kwana biyu banji motsin kowa yazo ba koda kuwa waccan ja'irar ce tana nufin zainaba
Ayrah da ta idar da Sallah tana dauke abin sallah da tayi bata bata amsa ba sukaji sallamar barira ta shigo hannunta riƙe da kwanoni guda biyu
Da sauri Ayrah ta tarbe ta tana faɗin sannu umma barira yauwa ta amsa ta zauna ƙasa ta shiga gaisar da gwaggo ɗin Saida suka gama gaisawa gwaggo tace nikam barira dannan bakuyi waya dashi ba
Murmushi barira tayi don ba ƙaramin jin kunyar gwaggon take ba tace ah ah gwaggo jiya munyi waya da daddare don yace yau zai kirama a hadashi daku
Gwaggo tace Allah sarki Iroro na da yananan da bazai barni cikin damuwa ba shar ƙwalla ta zubo mata da sauri ta kauda kanta don karsu gani
Amma hakan bai hana Ayrah shiga tashin hankali ba tana saurin ajiye abincin haba gwaggo kiyi hakuri menene na kuka kuma Nima yanzu saiki sanya ni wallahi ta faɗa tana kwabe fuska
Saida ta tabbatar ta kwantar wa da gwaggon hankali kafin tace yanzu bari in tashi naje gidan kila ma baban ne ba lafiya shiyasa kikaji kwana biyu shuru
Bata dai ce kala ba don tanajin zafin abinda ɗan nata yakeyi duk da tana zargin ba laifinsa bane ba amma bata da tabbas don ɗan yanzu idan yayi abu iyaye sukan ɗauke kai su nuna kawai wanine yake sanyashi bayan wasu yaran nasu shaidanun kansu ne dama
Ai kuwa hakan tayi don hankalin ta yaƙi kwanciya da yanayin gwaggon na yau takasa gane kanta gaba ɗaya sai wasu maganganu take da batasan kansu ba
Koda taje gidan a kofar gida sukaci karo da bawale dan Inno na farko ya fito sai mazurai yake yana uban sauri daga ganinsa zaka san ba abin arziki ya shuka ba
Kaɗan ya rage su bangaji juna itada shi da sauri ta kauce hanya tabashi waje ya wuce yana hura hanci
Halima ta tarar tana girki a gaban murhu sae hayaki ke faman tashi ya cika gidan sallamar tace tadawo da haliman dubanta tana amsawa tareda matse idanunta da suka cika hayaki
Saeda ta gaishe ta Halima tace Ayrah kwana biyu shuru na ɗauka jikin nakine yaki don malam ya faɗamin bakida lafiya naso na dubaki wallahi Hauwa ke ƙyanda itama tana daki kwance
Waje tasamu tsakar gidan saman wata tsohuwar kujera ta zauna tana faɗin Allah sarki naji sauki ma ya jikin Hauwa ɗin
Da sauƙi ta amsa mata dai-dai nan Inno ta fito jikinta da alamar lema daga banɗaki daga gani wanka ta fito tana cika tana batsewa
Harta zura kai daki Ayrah ta katseta da faɗin Inno inayini juyowa tayi ta watsa mata wani dan iskan kallo ta shigewar ta daki ta kyaleta abin bai wani dameta ba saboda tasan hali dama
Wajen minti talatin tana zaune suna ɗan fira jefi jefi saiga Inno ɗin tafito a fusace tafara faɗin wane dan iskan ne ya shigar min daki tafara yan tsine tsine itadai halima ko kallon inda take batayi ba
Ayrah kuwa tuni ziciyarta ta shiga lugude don batason tashin hankali dukda tasaba da masifar Inno ɗin kafin ta ankara ta janye kujerar da Ayrah take zaune ji kake dif Ayrah ta fado ƙasa don zata iya cewa mazaunanta ma sun samu matsala saboda azabar zafin datakeji
Shegiya yar iska kinzo ne daman domin ki lalubemin yan canji na ko hawayene kawai kebin kuncinta don tagaza furta kalma don ta bugu dai-dai gwargwado
Halima ce tayo kanta ganin abin nata yawuce gona da iri tace haba Inno ke masifar nan wai daɗi take maki ne a rayuwa bakison zaman lafiya ko kaɗan
Ina zanso zaman lafiya tunda ba'a nemeni dashi ba tafada tana yarfa hannuwa cikin tsiwa daga shiga wanka anshigo an sacemin kuɗi a daki kuma bana raba ɗayan biyu wannan tsinanniyar yarinyarce ta shigar min daki
Halima ta katse ta da faɗin to dankine tsinuwar taki zata bi don shi nagani yafito da kuɗi a hannusa yayi waje
Sankam tayi don tasan zai aikata fiye da haka ma amma cikin dakiya da nuna rashin gaskiya kai tsaye sai tafara faɗin sharri zaki yiwa ɗan nawa to ta Allah ba taki ba munafuka tayi daki
Murmushi halima tasaki tana faɗin kinji dashi dai tana kamo hannun Ayrah data duke tana kuka saboda mazaunanta da suka bugu da ƙasa
Sallamar baba ce tadawo da halima duban kofar gidan shine kuwa hannunsa rike da leda mai layi layi yana sauri duk da yagansu amma sai ya nemi wucewa dakin Inno kai tsaye
Daƙyar ta mike tare da faɗin Baba cikin dasasshiyar muryarta da tasha kuka tsayawa yayi cak baiko juyo ba itama bata damu saiya juyo ɗin ba don sako kawai take son tabashi kafin tace dama gwaggo ce take son ganinka
Baiko tanka ba yayi gaba abinsa dakin inno, halima dai ta bata hakuri ta cigaba da aikinta fitowa tayi daga gidan ta nufi hanyar gidan gwaggo zuciyarta babu daɗi ko kaɗan
Kamar daga sama taji sallamar sa wanda ko bata juya ba tasan wanene duk yanda taso ɓoye damuwarta hakan ya gagara don Saida ya fahimta
Ayrah wasan ɓuya kika komaa ne kinji sauƙi amma kinki dawowa makaranta saboda kar naganki ko
Murmushin da baikai zuci ba tayi tareda faɗin ah ah wlh Uncle Sameer bahaka bane ba gobe dama nake shirin komawa kuma inshaa Allah zaka ganni
Murmushin ya maida mata kafin yace gaskiya nidai ki dawo gaba ɗaya makarantar taku babu daɗi saboda bakinan
Yaso yabata mamaki sai kuma ta tuna da halayen nasa da yasaba mata dasu tadan taɓe lips dinta kafin ta fara masa godiya akan alkhairan da yayi mata da yake aiko mata gida
Dan yatsan sa ya dora saman lips dinsa alamun shuru bayason godiyar tata a tare suka jera suna tafiya gwanin burgewa suna ɗan fira jefi jefi
Ai kuwa a kofar gida saiga Khairiyya ta fito da alamu wajen Ayrah tazo akace batanan da Murmushi Ayrah ta nufe ta tana faɗin laaa Khairiyya kinzo bananan koh
Saɓanin martanin Murmushin sai taga ta kalla Uncle Sameer ta daure fuska ganin Ayrah ta zuba mata ido ya maido da hankalinta tana faɗin nazo bakinan Ayrah dama in duba lafiyar ki ashe kuna tare da uncle ma
Basarwa Ayrah tayi don ta gama fuskantar aminiyar tata sai tace yanzu muka haɗu dashi ma wallahi mu shiga ciki ta faɗa tana yin gaba bata ko ƙara juyawa ba
Haɗe rai Khairiyya tayi tana masa kallon ƙasa da sama zata shige gidan itama itadai Ayrah batasan ya suka ƙare ba don Saida ta ɗan jima da shiga kafin Khairiyya ta shigo
Me yafaru ne Khairiyya naga kina harara na ya faɗa yana lumshe idanuwansa da suke masu kyau da sheki babu komai ta faɗa tana yamutse fuska
Ɓoye man zakiyi ko ya faɗa yana harde hannuwansa saman kirjinsa sarai yasan abinda take nufi amma yaƙi yarda ya nuna mata kishi take da Ayrah shi kuma so yake ta nuna masa abinda ke ranta don wani abun ko a makaranta da gayya yake ma Ayrah don yaga yanda zatayi
Murguda baki tayi ta shige cikin gidan ta barshi tsaye mai makon haushi ma shi abin nata dariya yabashi
Harga Allah da farko Ayrah yake bala'in so amma ganin batashi take ba kuma bata cika sakar masa ba sai Khairiyya da take mugun nuna kaunarsa a fili yasa ya hakura da son Ayrah kwata kwata domin tuni ya fara son Khairiyya ɗin saidai yanda take nuna kishinsa ko a ina yasa yake nuna kamar ba sonta ɗin yake ba yasha gwada ta sauda dama amma sai yaga da gaske dai kishin sa take ya dade a tsaye kafin wani message ya shigo wayar sa da sauri yabar kofar gidan yawuce quarters ɗin da yake da zama na malaman makarantar
Sanda suka shiga gidan gwaggo tana banɗaki zaman fira suka zauna da yanda zasu tsara rayuwar su idan sunje boarding don labarin kaɗai ba ƙaramar nishadi yake basu ba
Suna cikin fira gwaggo ta shigo dakin, nan Khairiyya ta shiga gaisheta ta amsa mata ba yabo ba fallasa Ayrah ta katse gwaggo da faɗin wai gwaggona bakida lafiya ne naganki wani iri don Allah banajin daɗin ganinki haka
Khairiyya ta ɗora da faɗin wallahi kuwa haka ne gwaggo in kina cikin damuwa muma bazamu ji daɗi ba
Kakalo Murmushi kawai tayi akan fuskarta tace to shuwagabannin tambaya zaku fara ko to ni Babu abinda yake damuna ciwon kaine kuma ya sauka nasha magani
Sauke ajiyar zuciya Ayrah tayi tareda mikewa tana taɓa kan gwaggon data zauna kan gado su kuma suna saman katifar ƙasa sai kuma takara dawowa ta zauna
Sai wajen maghrib Khairiyya tayi gida sun sha fira hada gwaggon ma data ware kafin ta tafi saboda yanda suke saka ta a zancen su dole ta biye musu
Sallah maghrib suke saiga barira ta shigo daidai gwaggo na shafa addu'a da take barira tace gashi ana waya ta mika mata yar ƙaramar wayar tata
Iroro ne suka shiga gaisawa da gwaggon tashi sun dade suna magana karshe yace mata gobe zai taho yagansu sai ya kwana biyu ya koma
Gwaggon tace masa ah ah yayi zaman sa ba yace da sai sallah zaizo ba ƙarshe dai yace shidai kawai yanxu gidan yake son zuwa don dole ta kyale sa
Wajen karfe biyu na dare Ayrah ta farka duk jikinta batajin daɗi don tarasa menene yake damunta alwala ta dauro tazo tafara sallah yau gwaggo bata tashi sallah ba
Tana zaune saman abin sallah kamar daga sama taji gwaggo ta kira sunanta juyowa tayi tana fuskantar ta
Gwaggo ta tashi zaune tafara magana wadda ita Ayrah badan tana fahimtar duk abinda take cewa ba ma
Ayrah ke yarinya ce har yanzu ina tausayin rayuwar ki bansan ya rayuwa zata kasance miki bayan babu ni ba amma abinda zan faɗa maki shine komai kuncin da rayuwa zatayi koda wasa karki bari mutuncin ki ya zube a Matsayin ki na diya mace
Shuru Ayrah tayi tana sauraren ta ta cigaba da faɗin akwai sakon ki a kasan gadon nan kinsha tambayar menene a ciki ban faɗa miki ba yau ɗin ma ba faɗa mikin zanyi ba don Nima bansan menene a ciki ba
Amma nasan abu ne mai muhimmanci ki adana shi karkiyi wasa dashi gadonki ne da iyayenki suka bar mulki duk randa kikaji kina sha'awar sanin wani abu dangane da wannan akwatin nasan zaki iya kokarin gwada buɗe sa amma babu makulli a jikinsa kece zaki nemo
Ayrah tadan gyara zama tare da faɗin gwaggo meye haka mai muhimmanci da za'a ce nice zan nemo makullan kuma bayan ke kince baida mukullin ma
Gwaggo tace Karki tambaye ni akan duk abinda nake faɗa miki yanzu kawai kiyi abinda nace ɗin nasan sai nan gaba zaki fahimci magana ta amma ina so ki sanyata a kwakwalwar ki
Gwaggo ta cigaba da faɗin Allah ne ya hadani dake Ayrah banida wata alaƙa ta jini ta kusa ko nesa dake amma ina matuƙar kaunarki nasan iyayenki ma suna sonki ni kaina bansan meye silar rabuwar ki dasu ba amma tsoho ya tabbatar min da iyayenki mutanen kirki ne kafin ya tafi gwaggo ta ci-gaba da bawa Ayrah labarin yanda akai tazo gareta tun farko amma abinda bata sani ba tun batayi nisa da zancen ba Ayrah tafara bacci
Shurun da taji yayi yawa ne ya sanya ta kiran sunan Ayrah jin shurun kuwa ya tabbatar mata da baccin take sosai gwaggo abin ya daure mata kai domin ita sheda ce akan duk sanda akeyi wa Ayrah zancen iyayen nata tabbas saidai aga tafara bacci ko kuma ta fita kuma bazata ƙara tada zancen da kanta ba duk da tambayar da take dashi kamar yar jarida tun abin gwaggo naganin ko fushi take da iyayen nata har ta daina abin yake daure mata kai don Ayrah bata taɓa zama taji wani abu dangane da iyayenta ba bare ace taji sunyi wani ba dai-dai ɗin bane wanda ita kanta gwaggon batasan kowa na Ayrah ɗin ba sai tsoho daya damka mata amanarta yatafi wanda taji labarin daga baya shima akace mata ya rasu duk da bata da tabbas
Washe gari da wuri Ayrah ta shirya ta tafi makaranta ai kuwa yan ajinsu akayo mata caaa ana tambayar jikinta domin duk tanada kyakkyawar alaƙa tare dasu wasu ma makotansu ne a gida duk aikin Khairiyya ne ta faɗa musu batajin daɗi
Malam shafi’u ne ya shigo da tulun takardu a hannunsa bayan sun gaishe sa kafin yace duk wanda yaji sunansa to next week zasu fara exam wanda kuma bai ji sunan shi ba to bandashi
Nan ya fara kiran sunayen su ɗaya bayan ɗaya har ya gama Ayrah ta mike tace malam banji sunana ba yace mata ta biyosa office
Badan taso ba saboda dama ba shiri suke dashi ba saboda shegen son matan sa ta bishi a bakin kofa ta tsaya tana wasa da yan yatsun hannunta
Malam shafi'u yasamu waje ya zauna yana faɗin shigo man Ayrah ko tsorona kikeji,
ah ah tafada kanta a ƙasa tana ƙarasa shigowa cikin office ɗin
Har sauri yake yana shirin rufe office ɗin takau haɗe gabas da yamma juyowa yayi yana watse mata hakoransa munana da goro yafara kashewa
Cikin ƙarfin hali tace malam ka buɗe min kofa na fita yake mata haƙora ya karayi yana matsowa yace haba Ayrah wai tun yaushe nake son ki bani dama koda sau ɗaya ne mu mori juna amma kin kiya yanzu da kingama makarantar nan ina zankara ganinki wata fa zaki koma yanayi yana lashe baki kamar wani tsohon maye
Zufa ta ko'ina ce tafara keto mata harta buɗe baki zatayi magana aka kwankwaso kofar cije baki yayi da ɗan guntun tsoki yana faɗin who's that daga can waje ba'a amsa ba aka cigaba da bugawa da karfi ba yanda ya iya dole ya gyara nutsuwarsa ya tafi budewa
Ita kuwa Ayrah banda alhamdulillah babu abinda take jerawa a cikin zuciyarta bai bari na wajen ya shigo ba sai dai taji yana faɗin to bari ya dauko takardun yazo
Wucewa akayi ya dawo yana ƙwafa yana faɗin kinci Sa'a amma kin cuceni yarinyar nan ina ganin kayan more wa a jikinki amma kin hanani gashinan kinja banji daɗin ba anzo ana wani nemana
Ita dai bata furta kalma ba yanayin waje itama ta fito ta nufi ajinsu a hanya ta haɗu da Khairiyya domin sun fito break nan Khairiyya ke tambayar ta abinda yafaru
Bata faɗa mata ba sai cewa tayi kawai suna zuwa saiga wani yazo ance uncle ɗin yazo Khairiyya tace Uncle Sameer ne fa nice nan na tura shi nace wancan dan iskan ya kiraki yaje yaga me yakeyi kuma yace Karki damu da sunanki dama sharrinsa ne kawai
Numfashi Ayrah kawai ta sauke tace muje suka koma aji suna ɗan duba littattafan su saboda gabatowar jarabawar da zasuyi
Sosai zuciyarta ke harbawa da ƙarfi wanda har hakan yaƙi boyuwa a fuskarta tunda Anty Jamila ta shigo babu abinda tagane har Saida taji ta kira sunanta tana tambayar ta akan abinda take magana akai tsuru tsuru tayi don batasan me ake cewa ba ma
Har wasu yan ajin nasu sunfara mata dariya wai ta dabarbarce sun dauka don ance babu sunanta ne a masu jarabawar basu san me yafaru ba tunda ba faɗa musu akayi ba
Tuni sarkin zuciya Khairiyya ta kufula da abinda ake ma Ayrah ta mike tana faɗin Aunty jamila Ayrah bata da lafiya ne dama yauma tadawo makarantar
Dolenta ta kyaleta tace ta zauna badan Khairiyya ba ita gaba ɗaya ma kanta ya kulle tarasa meke mata daɗi ta kagara ta koma gida
Basu wani dade sosai ba aka tashi a hanyar su ta dawowa aka fara kiran sallah azahar
Da yake ta kofar gidan su Ayrah khairiyya take bi suna tafe tanajan Ayrah da fira tana tambayar ta wai me yake damunta
Ganin dandazon mutane a kofar gidan ne yasa suka tsaya turus suna kallon kallo itada Ayrah tashin hankalin da ba'a samashi lokaci
Da sauri Ayrah tana bangaje mutanen da suka cika kofar gidan ta faɗa ciki Khairiyya na biye da'ita barira ce ta tareta a kofar dakin da mata suke zaune wasu nata matsar kwalla itama bariran kuka take sosai kamar ranta zai fita
😩Meyake faruwa ne jama'a a gidansu Ayrah ku cigaba da bibiyar mu dan jin yanda zata kaya 😮💨
***