Free chapter · Read without an account
Chapter 3
***
Comments section Link
***
💫ƘAUNA DA KADDARAH 💫
✍️Mrs Alkali
Page 3️⃣
Aliyu Abdullahi Turaki shi ne cikakken sunansa wan da akeyi wa lakabi da AA Turaki, in da mahaifiyar sa kuma take kiran sa da suna "Yero" kasancewar sa d'an fari a gunta kuma da d'aya tiloh a gurin su, Alhaji Abdullahi Turaki bafulatani ne daga rugagen Gembu, cikin tsaunukan Mambila Plateau, wanda ya tashi cikin arziki na noma da kiwo asalin Mahaifinsa makiyayi ne mai daraja, amma daidai gwargwado ,mutumin kirki, ne amma babu isasshen ilimi, sai tarbiyya da gaskiya a wanchan lokacin.
Aliyu tun yana yaro, yana da hangen nesa da kwadayin canza rayuwarsa da ta iyayen sa, Duk da halin rashin wada ceccen ilimi da suke ciki a yankin su, haka ya dage da karatu yana tafiya makarantarsu mai nisan gaske daga gida, a koda yaushe, kafin wata ƙaddarah ta gifta musu, su ka baro ainihin yankin su sukayi hijira zuwa garin kano, anan garin kano ne Aliyu yaci gaba da karatun sa na secondary bayan doguwar jinya da sha fama da ita wanda iyayen sa suka cire rai da tashin sa cikin ikon Allah da karfin addu'ar su Allah ya sake daga kafad'un sa sai dai ya kamu da ciwon zuciya da ake kira da mild heart condition, saka makon damuwa da ba'cin rai da ya shiga a baya.
Bayan ya kammala karatun secondary school, da sakamako mai kyau, ya fito sabi da kwazon sa, a haka ya samu ya jona jami'ar Ahmadu Bello University , in da ya karanci business administration, bayan ya kammala ne ya fito da result in da ya zama first class ya samu scholarship daga wata NGO, Bayan ya gama digirin sa na farko, ya samu damar zuwa UK inda ya yi Master’s a fannin International Business Management a London School of Economics, bayan nan ne ya jona degree din sa na uku a UK wato Phd , bayan haka ya karbi horo na musamman daga Executive Education domin kara kwarewa a harkar jagorahn ci da nazarin kasuwan ci, Daga nan ne rayuwa ta fara sauyawa, inda yafara halartar tarurruka na musamman kamar su , project management profession, Business networking, digital marketing da sauran su.
Yana da kwarewa, hikima, da iya sadarwa da kowa, hakan yasa bayan ya dawo Najeriya, ya kafa kamfanin farko mai suna Turaki Global Ventures, wanda ya fara da kasuwancin shigo da kayayyaki daga kasar China da Turkey.
Zuwa cikin shekaru 10, AA Turaki ya zamo jigo a harkar kasuwanci a Afrika.
Yana da manyan kamfanoni a fannoni da dama kamar su:
- Turaki Holdings Ltd – kamfani na kudi da hannayen jari
- Turaki Oil & Gas – yana da rijiyoyin man fetur a Najeriya da Angola
*Turaki Real Estate – gini da mallakar manyan gine-gine a Dubai, Abuja, Accra, da Istanbul
- Turaki Agro & Food Ltd – kamfani mai sarrafa kayan gona da fitarwa zuwa waje
- Turaki Airlines (JV project)– wani kamfani da ke tattaunawa da gwamnatin kasar Qatar akan kafa jirgin sama
Duniya ta sanshi a matsayin "Africa's Silent Billionaire", saboda hankali da natsuwarsa, baya shiga barkwanci da fallasa sirrin rayuwar shi.
Hukumar Najeriya (Federal Government),ta ba shi lambar girmamawa, saboda gudunmawarsa ga ci gaban tattalin arziki, har ta zuba hannun jari a daya daga cikin kamfanoninsa na makamashi da man fetur.
Kasashe kamar UAE, Turkey, UK, China, Qatar, da Saudi Arabia suna da hannun jari a kamfanoninsa – sannan ya kasance memba ne a International Business Council.
Tattaunawarsa da kasashen duniya kan batutuwan kasuwanci da cigaban Afirka sun sa ana kiransa "Voice of Emerging African Capitalists".
5 YEARS BACK...
A lokacin da harkokin sa su ka kan kama ,zuwa wannan lokacin AA Turaki ya zama babban business tycoon a Africa baki daya, zuwa lokacin ya tattara iyayen sa sun koma Abuja da zama, duddah shi kan sa bai cika zama a Nigeria ba.
Hajiya Habiba wacce yake kira da Hajja tana zaune a kan kujera mai lallausan fata, a hankali ta gyara mayafinta .
Aliyu Turaki ne zaune a gaban ta ya na zaune cikin natsuwa, yana sauraron mahaifiyarsa.
da murmushi Hajja tace
"Yeroh yau kimanin shekara talatin da biyar fa kayi... Ba aure lokaci yayi da zaka samu mace mai tarbiyya da zaka kira taka.
Ga Ramlartu nan ’yar kawata ce, naga halinta tun tana da hankali naya ba da halinta.
Yarinya ce mai ladabi da hankali. Kuma ta na girmama ka sosai, uwa uba kuma tana mutuwar son ka."
Cikin nitsuwa Aliyu ya dago kai kadan, ya kalli mahaifiyarsa, sai ya sauke ajiyar wata nannauyan ajiyar zuciya.
"Ina jin ki Hajja, Idan kina ganin hakan shine mafi alheri, a gareni na yarda da zabin ki."
"Ya amince da auren ba tare da soyayya ba... saboda biyayya da girmama mahaifiyarsa.
Auren da aka daura cikin girma da kima amma zuciyar sa ba ta tare da auren, sabo gan gan jikin sa ne kawai a auren."
Haka ya ke zaman aure da ramlart duddah baya son ta amma bai taba yi mata wulakancin akan hakan ba , sai dai ita kanta ta san zuciyar Aliyu Turaki ba mallakin ta bace.
***********
CİGABAN LABARİ
GWARİNPA ESTATE.
Anguwar tana cikin wurare ne da gwamnati ke ware wa manyan ma’aikata. Unguwa ce mai tsari, tsafta da tsaro. Gidan da Dr. Farida ke zaune da mahaifiyarta da ɗanta yana cikin layi mai natsuwa Da babu hayaniya, a kusa da babban titin Estate din.
Kamar kullum, Dr. Farida ta iso gidan da motar ta Toyota Corolla 2021 – metallic grey, motar da asibitin National Hospital Abuja ya tanada mata a matsayin wani daga cikin fa’idar matsayinta a asibitin.
Motar ta tsaya a gaban gate din gidan, Gate man ne ya ruga da gudu ya bude, ganin motar ta ne yasa shi washe baki tare da gaishe ta yace "Welcome madam!" tana amsawa da murmushi d'auke akan fiskar ta, kutsa motar tata tayi cike da nitsuwa take tukin, d'an madai daicin parking space din dake cikin gidan ta nufa , parkin tayi tare da tattaro jakan Office din ta ta fito, had'e da rufo kofar motar, main parlourn ta nufa.
Cikin gidan, akwai kyakkyawan bungalow mai bene guda Daya, an tsara shi cikin salo irin na zamani, Gidan yana da veranda wan da aka kawata da furanni masu dad'n kamshi, a gefe guda akoi kujerun hutawa.
A cikin parlorn kuwa komai yana nan tsaf tsaff da shi ga kyawawan labulaye, kayan dakin masu simple ne babu hayaniya amma masu tsada,ne ga wani kamshi na turaren wuta da yake tashi, mai sanyaya zuciya.
A cikin gidan, tana tare da mahaifiyarta Hajiya Zainab wacce take kira da Dada dattijuwar mace mai launin fata, mai dan haske amma ba sosai chan ba, tana da kamun kai da halin kirki, da ɗanta Ameer kyakkyawan saurayi mai shekaru 14, fari ne sol, yana dauke da idanu masu kama da na uwarsa Dr farida.
Dr. Farida ne ta shigo cikin gidan cikin nutsuwa, tana sanye da kayan aikin ta, a hankali ta jingina da ƙofar parlor, tana kallon ɗanta, Ameer mai shekaru 14, kyakkyawan yaro ne da ya jima yana bin sahun mahaifiyar sa.
Yana da fata mai haske da laushi, fuskar sa na d'auke da annuri da manyan idanu irin na mahaifiyarsa, A lokacin yana zaune kan kujera yana karanta wani littafin sa na school wanda aka basu homework.
"Ummi welcome!" Ameer ya miƙe da sauri ya na mai rungume mahaifiyartasa.
Ba shiri Dr Farida ta saki murmushi, tare da cewa “Nagode masoyina, ka kammala karatun ka kenan?”
Mahaifiyarta, Dada ce , ta fito daga ɗakin girki rike da flask, a hannun ta.
fuskan dattijuwar na d'auke da nutsuwa da hikima. “Farida, sannu da dawowa, lale maraba , da gani Kin gaji da aiki?” ta karasa maganar tare da zuba mata idanun ta.
“ cike da nitsuwa tace Eh Dada, wallahi yau rana ce mai nauyi a gare ni yau na duba petient da yawa,” Farida ta ce yayin da take kokarin cire hijabin ta a lokaci guda tana kaiwa kan kujeran dake cikin parlorn.
Dada ce ta ajiye flask din a kan table, ta zauna kusa da ita, tana kallon ta cike da tausayin rayuwar yâr tata dake cike da jarrabawa da kaddarah.
“Farida,” dada ta fad'a cikin tausasawa, “Na san rayuwar ki ba abu bane mai sauki , Kin jure abubuwa da dama, amma Allah zai saka miki, ki Duba Ameer, ya girma cikin tarbiyyar da kika bashi , hakika ke din kin cika mai juriya.”
A hankali Dr Farida ta juyo, idonta ya gama cika da ƙwalla amma bata bari ta zubar da su ba. “Dada, kin yi ƙoƙari, a rayuwar mu, Ban taba jin nauyin rayuwa irin yau ba, Amma na godewa Allah da ya bani ke a matsayin ki na mahaifiya ta.”
Ameer ne ya matso kusa, da ita ya dafa kafaɗar ta, yace.
“Ummi, I’m proud of you.”
Mee too shine abunda ta iya fad'a masa tare da sake rungume shi tana mai sauke ajiyar zuciya.
Duk da cunkoson aiki da raɗaɗin abubuwan da suka gabata, arayuwar ta Dr Farida tana jin kwanciyar hankali a cikin wannan ƙaramin gidan nata tare da yaron ta da kuma mahaifiyar ta da ke ci gaba da ba ta ƙarfin guiwa akan rayuwa.
Dr. Farida ta daga kafarta a hankali ta mike inda take zaune a falon su, tana na mai kallon Ameer ,fuskar ta cike da nutsuwa da kwanciyar hankali, Tana murmushi kadan yayin da take duba lokaci a agogon bango.
Cikin natsuwa da tsafta irin ta likita mai kamala, ta mike tsaye tare da cewa.
"Dada Zan shiga na kimtsa jikina," ta karasa fada cikin d'an fara'a, tana kallon mahaifiyarta da dan nata.
Cikin nitsuwa Ta nufi dakin ta, tana taka tiles din fale-falen, kamar wacce bata son taka kasa kan bene masu sheki da kyan gani, ta nufa .
Dakin nata dan madai dai ci ne da ya cika da tsari da tsafta an kawata shi da kyawawan labulaye masu launin shudi da beige.
Gado ne mai dan faɗi, ya na lullube da farin bedsheet mai laushi da tawul dinta nade a gefen pillow.
A jikin bango kuwa akwai mirror mai fadi, wardrobe mai launin itace, da shelf ɗin da aka jerawa kayayyakin kula da fata da perfumes masu ƙamshin, gaske .
Cike da nitsuwa Ta shige bathroom nata, wanda ke hade da dakin.
Tana shiga ta kunna ruwan zafi ta dan surka dana sanyi yanda zai yimata dad'in amfani, ta shiga wanka tana jin sanyi da d'an nutsuwa a zuciyarta.
Bayan ta fito, ta shirya cikin kayan shan iska marassa nauyi masu shegen kyau, ta sanya turare wanda ya lullube dakin gaba d'aya da ƙamshi mai shegen dadi.
A mai makon ta zauna ta huta sai ma Ta sake fitowa zuwa falon su, inda mahaifiyarta dada ke dora abinci a kan dining table.
Yayin da Ameer na gefe yana ta buga game a waya yana dariya shi kad'ai.
A hankali Dr. Farida ta zauna a gefen su cikin jin daɗin kasancewa da iyalanta.
Ta dora hannunta a kafaɗar ɗanta tana kallon Dada dake kok'arin saving d'in su abinci tace.
"Allah ya bar min ku, Dada na, na gode da zama ginshikin farin cikin Rayuwa ta."
Cike da kulawa Dada ta d'an girgiza kanta tare da cewa.
"Allah ya barmu da kaunar juna ungo maza karb'a kifara cin abincin kar ya huce"
Haka ta gama saving din su gaba d'aya wajen ne ya d'auki shiru kowa ya maida hankali akan cin abincin sa dama haka al adar su take in amfara cin abinci to fa ba a magana sai an kammala.
Comment like and share plz.