Free chapter · Read without an account
Chapter 6
💫 ƘAUNA DA KADDARAH 💫
✍️Mrs Alkali
Page 6️⃣
GWARİNPA ESTATE.
Dr. Farida ta fito daga dakin ta cikin shigar aiki ,medical scrubs masu launin sky blue, farin lab coat a saman, su tana ƙamshin turare mai shegen dad'i da sanyaya rai, Gashinta yana sanye da medical cap.
A hankali Ta sauko zuwa falon, murmushi d'auke a saman fiskan ta.
cike da annashuwa tace.
"Assalamu Alaikum Dada… Good morning Ameer." Ta karasa maganar tare da kallon su.
cikin farin ciki dada ta ce.
"Wa alaikumus salam, ya'r albarka. Allah ya sa alheri ya cigaba da bibiyar rayuwar ki, har kin kammala shiri kenan?"
AMEER dake shirye tsaf cikin uniform din makaranta yace.
"Yes Ummi! Na shirya… kawai ke nake jiran kizo muyi breakfast ."
Dada ce tace.
"Ku zo ku ci kafin lokaci ya kure… ba zan yarda ku fita cikin yunwa ba."
Dariya Dr Farida tayi tare da zama akan d'aya daga cikin kujerun dake jere a dinning table din.
tea, bread, kwai, da fruits, sai flask da dada ta d'aura a tsakiyar table din.
AMEER dake shan kankana ne yace.
"Ummi, dada… zan iya kunna TV in duba morning news?"
Dr FARIDA ta kalli Umma, ta gyada kai a hankali tace.
"To na baka mintuna uku kawai."
Cikin jin dadi Ameer ya dauki remote, ya bude channel na Africa Sunrise News.
Ya samu Ana maimaita wani exclusive interview da babban Business Tycoon AA Turaki.
Sanye yake cikin manyan kaya, yana magana cike da nutsuwa da izza, yana bayyana irin taimakon da yake baiwa matasa da sabbin entrepreneurs, dakuma nasarorin da ya samu a rayuwa da irin gwagwarmayar da yasha kafin taka matakin.
Cike da nitsuwa yake jawabi a cikin TV
"...muna kokarin ganin an samu cigaba, musamman a fannin ilimi da lafiya. Kowa yana da damar cigaba matukar yana da niyyar aiki tukuru."
Ameer ne ya ke kallon shi cike da sha’awa.
Sai ya kalli Dr Farida yace.
"Ummi..! kin ga wannan mutumin ina matukar kaunar sa, nima irin sa nake so na zama idan na girma, amma ummi kin taba ganin AA Turaki?
Cike da basarwa, Dr Farida ta daure fuska tana kai bread cikin bakin ta tace.
"AA Turaki? A'a… ban sanshi ba sosai kuma ban taba ganin sa ba."
Dada ce ta dauki remote cikin sauri ta kashe TV din, tace
"Toh baki abun magana ba kaga lokaci na tafiya ba ne, Za ku makara fa.
Dr Farida ne tace.
"Tashi mu wuce kafin traffic ya fara."
Takara sa maganar tare da miƙewa a lokaci guda kuma tana goge bakinta da tissue.
Ameer ya tashi yana murmushi, Dr Farida ta mike ta dauki jakar aikinta, tana kokarin boye sauyin yanayin fuskarta.
"Okay ummi, cewar Ameer da ya bi bayan ta hannun sa rike da jakar makarantar sa.
A haka Suka karasa mota wata silver Toyota Corolla 2021, mai dauke da plate number na National Hospital.
Ta bude masa kofar baya, ya zauna. Ita kuma ta shiga driver's seat, ta kunna mota, suka kama hanya.
Ameer yana zaune yana kallon ta ya saki wani cute smile yace .
"Ummi, kin fi kowa kyau a cikin wannan uniform din ba kiga yadda kike da kyau ba."
murmushi ta sake tare da cewa.
"Kai Ameer, baka gajiya da shirme wlh."
Haka Dr Farida ta sauke shi a makaranta, ya yi mata bankwana.
İta kuma ta ci gaba da tafiya zuwa asibitin, dan da alama yau ta kusa makara.
Dr Farida tana parking a filin ajiye motoci na ma’aikata, tana jin sautin iska da shigowar wasu motocin cikin harabar parking lot din.
Wani black Toyota Camry ya shigo a dai-dai lokaci daya da ita.
Dr. Imam, ne cardiologist Dr ne a cikin asibitin wato likitan da ya shafi bangaren zuciya, ya fito cikin sauri da murmushi, yana nufeta tare dacewa.
"Dr. Farida! Good morning.
Ya Subhanallah, yau kin kara kyau fiye da kullum my Love."
Cike da nitsuwa Dr Farida ta dauki files dinta, ta juya tana fuskantar sa, tare da rufe murfin motar sa tana dan murmushi mai had'e da natsuwa da class tace.
"Good morning, Dr. Imam.
Ka ga lokacin aiki na Kara matsowa, ga shi yau mun makara ?" Tana fad'an haka ta wuce ta gaban sa.
Da sauri Dr İmam yana bita a baya, yana takawa a hankali yace.
"Wallahi har yanzu bana jin dadin yadda kike kaucewa maganar da ta shafi tsakanin mu dake.
Dr Farida, wannan zuciyar tawa tana bukatar kulawarki… ina da rauni akan soyayyar ki."
A haka Suka karasa harabar Office din OB GYN, suka shiga cikin block din a tare.
Bud'e office din ta dake jare tsaf tayi, ga wani irin ƙamshin Air freshner dake tashi wanda ya gauraya da asalin ƙamshin turaren jikin ta, DR. IMAM ne ya zauna a wata kujera da ke kusa da teburin ta ya sake cewa .
"Ni fa bana jin dadin yan da kika ki bani dama, Kin san zan iya turo iyayena a gobe in kin yarda. Amma sam kin ki ki bani daman hakan..."
Bayan Dr FARIDA ta zauna tana gyara files, cike da hikima da kame kai irin na matan da suka san kansu tace.
"Dr. Imam, kasan ina girmama ka. Kaima ka san yadda rayuwa take… akwai abubuwan da nake kokarin warwarewa kafin in baka damar turo da magabatan ka.
Dan Allah, ka je ka duba patients dinka, kaga Time ya küre,Idan ka gama, sai ka dawo mu karasa maganar."
Cike da so DR. IMAM yake kallonta .
"To, amma sai kin yi alkawarin cewa zaki shigo Office dina kafin na tashi."
murmushi, Dr Farida tay tana gyada kai alamar ta amince da hakan.
"Na amince. In Allah ya yarda."
DR. IMAM ne yace
"Okay, zanyi hakuri Zan jira amincewar ki."
Yana gama fadar haka Ya mike, ya fita ya nufi cardiology Ward in da a chan office din sa yake, Dr Farida ta sauke ajiyar zuciya a hankali, tana kallon kofar da ya fita, tabbas Dr İmam ya chanchanci a so shi, sai dai kuma zuciyar ta ta jima da rufe wannan babin a cikin rayuwar ta.
Cikin zuciyar ta tace.
"Allah Ka bani ikon zaben abun da zai amfaneni a rayuwa..."
Daga nan taba wa patients din ta damar shigowa ta hanyar kada yar kararrawar dake gaban teburin ta .
******
Zaune suke , a Wurin da suka saba haduwa ne, wata Private lounge a cikin wani luxury café da ke Maitama.
Anguwar na da nutsuwa, kuma wurin ya kasance mai tsit, babu hayaniyar komai.
Ramlart ta ke zaune cikin shigar mata masu class, sanye da riga da skirt na zamani, ga wasu manya gilashi a idonta, hannunta sanye da agogo mai tsada.
Zuly kuwa ta na zaune fuskarta cike da kwalliya , irin na ya'yan masu kudin nan marassa jin magana .
Zuly ce ta zuba ido cikin na Ramlart tace .
“Yanzu fa, da gaske Hajja ce ta fara shiga tsakanin ku da AA Turaki? ai kuwa ya kamata muta ka mata birki dan bazai yiwu taci zamanin ta ba sannan a yanzu tace zata had'a da naki ba, never wlh .
Wani irin ɓacin rai ne ya ziyarci fiskar Ramlart tace.
“Zuly... ke kanki kin san ba ta taɓa sona ba, Tun farko, ita ta shigo da ni saboda biyayya, ba domin ta yarda dani ba, sai don cikan burin ta akan danta, Yanzu kuma tana kokarin rabani da mijina.”
ZULY ce ta harare ta tace .
“To, me muke jira? Kin dai ce min tana issue n zuciya da hawan jini.
Me zai hana mu taimaka mata ta huta da wuri kawai?” ta karasa maganar tare da shekewa da Wani irin dariya.
Ramlart ta lumshe ido, tana sauke numfashi.
A zuciyarta, akwai rudani tsakanin gaskiya da makirci, amma kiyayya ta fi karfi a zuciyar ta.
cike da zafin rai Ramlart tace .
“In har hakan ne hanyar da zai sa ya dawo gareni... zan iya yin komai.”
ZULY ta d'an yi murmushi tace .
“To sai mu fara da abincin ta, Zan samo wani sinadari da ke kara tashin zuciya a jikin masu ciwon zuciya.
Karki damu sai ki ringa sa mata a tea ko soup ɗinta, da zaran taci ko da sau d'aya ne uhumm... sunan ta sorry.” takarasa maganar cike da makirin murmushi.
“Hakan zai yi, Amma sai dai mu yi hankali. Ba zan so a gane cewa ni na janyo hakan ba.” cewar Ramlart da ta gama yarda da maganar ZULY.
Zuly ce tace.
“Ki bar min wannan. Ai ni ce master planner. Kuma fa... idan ta mutu, babu mai hana ki warwasawa da mijinki kin ga gaba d'aya hankalin sa zai karkata kan ki ne, tun da bamu da matsala da wanchan Tsohon na shi kin ga sai kici karen ki babu babbaka.”
Ramlart ta lumshe ido tana murza zoben dake hannun ta, A cikin zuciyarta, soyayya ta rikide zuwa kishi, kishi ya rikide zuwa makirci.
don kuwa ji takeyi zata iya kawar da kowa akan hanyar ta muddin zai shiga tsakanin ta da AA Turaki.