Free chapter · Read without an account
Chapter 37
The Amazing Pen ✍️.......
BAHAGON TUNANI
بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم
037
Wani irin kukan kura Jamila ta yi ta cacumi wuyan Sahura da hannu ɗaya,ta kai ma bakinta kafirin naushi,ji kake ƙum! Saukan hannun Jamila a bakin Sahura ya sabbaba mata saki razananniyar ƙara saboda sihirtaccen zafin da ya ziyarci ƙwaƙwalwarta. Wani sabon naushin ta kuma kai ma bakin, wanda ya fi na da farkon,take bakin Sahura ya cika da jini,hakoran gabanta biyu suka fara girgiɗi kamar za su fita. Kafin Sahura ta farfaɗo daga azababben ciwon da bakinta ya fara ta ji ta shaƙe wuyanta da matuƙar ƙarfi. Nan da nan 'yan ɗaki suka miƙe suna salati da sallalami. Gwaggwon Bugaje ta yi suman zaune ganin yadda Jamila take nuƙurƙusar Sahura, saurin miƙewa jikinta na tsuma. Yadda Jamila ta shaƙe wuyan Sahura ya yi matuƙar ɗaga hankalinta,ga wani irin kakari da Sahura take idanunta sun firfito tamkar ta yi arba da mala'ikan mutuwa,fuskarta ta sauya zuwa ja abinka da farar mace. Hannu Gwaggwon Bugaje ta saka tana ƙoƙarin cire hannun Jamila daga wuyan Sahura,sai dai kamar da dutse take.
''Dan ubanki ki sakar mini ɗiyata! Ki saketa karki kashe mini ita! Wallahi sai na yi shari'ah da ke idan ɗiyata ta mutu!"
Da hannu ɗaya Jamila ta bangaje Gwaggwon Bugaje,ji kake Tim! Ta faɗi a ƙasa har tana bige kanta da tebirin ɗakin,nan da nan goshinta ya tsage yana fitar da jini,ga babban yatsanta da take tunanin ya yi targaɗe ko gocewar ƙashi saboda azababben zugin da yake mata. Sosai 'yan ɗakin suka cika da tsoron Jamila kar ta kashe Sahura,wasu daga ciki suka yo kansu don su taimaki Sahura,duk yadda suka yi ƙokarin cire hannun Jamila daga wuyan Sahura hakan ya faskara,daga ƙarshe da Jamila ta yi ma Sahura wata iriyar jijjiga sai da matan suka matsa gefe hankalinsu a matuƙar tashe. Cilar da Sahura Jamila ta yi tana wani irin huci tamkar zakanya a fagen daga. Cike da amo ta fara magana tana duban Sahura da ke baje a ƙwasa
''Yau baki da mai cetonki Sahura! Wallahi wallahi sai na illata rayuwarki kamar yadda kika zama silar mutuwar tilon 'yar'uwarta'' tana faɗin haka ta haye ruwan cikinta,Sahura ta yi matuƙar galabaitar da ko ɗa yatsa ta gagara ɗagawa, akai-akai take sauke numfashi, kafin ta gama dawowa cikin hayyacinta ta ji Jamila a saman cikinta,waro jajayen idanunta ta yi waje,jinta take ina ma ta mutu ko za ta hutu da wannan bala'in da take ciki. Tun da ta zo duniya bata taɓa riskar kanta cikin wannan tashin hankalin ba sai yau,babu inda ba ya mata ciwo a cikinta,tabbas ta san haƙoranta biyu na gaba sun tashi aiki. Kafinta ta ari mayafin natsuwa ta ji hannayen Jamila biyu a saman gashinta. Wuya ta yi wuya tsarki da jajjagen attarugu,an ya ba yau za taa yi bankwana da duniya ba. Hannu biyu Jamila ta saka a tsorayen gashinta ta ja da matuƙar ƙarfi,tun daga tushe gashin suka fita. Take jini ya fara ɓulɓulowa daga tsorayen gashin,duk da hakan Jamila bata bar dukan Sahura ba kamar Allah ya aikota,burinta ta rama ma yayarta muguntar da ta mata,ta mata illatar da ta san ba za ta moru a duniya ba kamar yadda ta zama silar mutuwar yayarta saboda son Zuciyarta. Ihu matan ɗakin suka fara ganin da gaske Jamila lahanta Sahura takke shirin yi. A rikice 'yan waje suka leko ta windon ɗakin,babu shiri Ɗayyaba da Aunty Saudah duka saki gigitacciyar ƙara. Aunty Saudah ta kira sunan mamanta da iya ƙarfinta. Sama-sama Sahura take jin ihun mutane,daga karshe ganinta ya yi ɓatan dabo. A ruɗe Ɗayyaba ta shiga jan kofar ɗakin tana ambaton sunan Sahura, Yaranta sai ihun kiran sunanta suke. Gwaggwon Bugaje na ji amma bata da bakin magana sabooda yadda jikinta ya turare da raɗaɗi musamman babban yatsan,tana ji tana gani wata take niyyar halakar mata da ɗiyarta da tafi soyuwa a gareta,zuciyarta na tafarfasa, idanunta sai zubar hawaye suke. Da gudu Amina ta yi waje neman ɗauki,ko mintuna biyar bata yi ba ta dawo tare da Dauda Imamu da sauran masu zaman makoki. Leka windon Dauda Imamu ya yi,lokaci guda tashin hankali ya ziyarci zuciyarshi ganin Sahura ƙawance cikin jini Jamila a saman ruwan cikinta tana dukanta. Da sauri yaje wurin ƙofar don ya buɗe sai dai ya jita a garƙame,ya jijjiga da iya ƙarfinsa amma ya gagara buɗeta,cikin hanzari ya dawo wurin windon yana jijjigashi amma kamar yana ƙara masa ƙarfi,tuno da windon uwar ɗaka na katakone sai ya ruga da gudu zuwa back yard ɗin gidan ya fara jijjiga windon. Kawu Rabi'u sai roƙon Jamila yake a kan ta barta haka kar ta kasheta tun da kamar ta sume amma ina Jamila ta daɗe da nisan kiwo,ta zama tamkar kurma,bebiya, burinta kawai ta rama ma 'yar'uwarta. Har mijinta sai da ya mata magana amma kamar da dutse yake. Kuka sosai su Aunty Saudah suke,Hamid ma ya bi babansa back yard ɗin don taimaka masa. A gefe guda Jalil da Yasir zuciyoyinsu fal da farinciki musamman Jalil da yake ji kamar an yi mishi bushara da gidan aljanna,dole ya yi sadaka don ƙara gode masa. Hamida da su Jawaheer suna wurin kicin sun yi cirko-cirko,yayinn da HAFIZA ke alwalarta cikin natsuwa kamar bata san dawan garin ba. Bayan ta kammala ta koma kusa da su Raihana tana kallon yadda yaran Sahura suke kuka,tabe baki ta yi a rants tana furta 'Allah ya ƙara'.
Da ƙyar Dauda Imamu da Hamid suka yi nasarar ɓalle windon ɗakin suka shiga. Dauda Imamu na zuwa falon ya daka ma Jamila wata gigitacciyar tsawa.
''Baki da hankali ne kike son kashe mini mata!"
A matuƙar hasale Jamila ta miƙe daga saman cikin Sahura ta ce
''Ban da hankali Dauda! Ke har kana da bakin magana! Mugu azzalumi! Silarka da wannan tsinanniyar matarka na rasa tilon yayata! Na rasa me ba ni shawara! Mai tausayina!''
Dauda Imamu zai ɗauke fuskarta da mari mijinta ya riƙe hannunsa tare da faɗin
''Wallahi karka kuskura ka taɓa mini mata! Kai saboda tsabar rashin kunya idan aka barka sai da duketa! Lallai Dauda! '' kamar ya sani ya biyo bayansu ta windon.
Duban Jamila ya yi ya ɗan sassauta muryarsa ya ce
''Jamilaa ba ni key a buɗe ɗakin mu kai matar nan asibiti,ko babu komai kin rama ba 'yar'uwarki zaluncin da ta mata''
Kallonsa ta yi sai ya marairaice fuska alammar ta yi haƙuri, ciro key ɗin ta yi ta wurga ma Dauda Imamu a fuska, lokaci guda kuka ya taso mata,da sauri ta nufi ɗakinsu HAFIZA ta rufe ɗakin. Da taimakon matan ɗakin aka fito da Sahura kamar gawa wajen gidan. A motar mijin Jamila aka sakata, Gwaggwon Bugaje na biye da su Ɗayyaba ta riko hannunta tana ɗingishi suka shiga motar. Aunty Saudah da Amina suka zauna a mazaunin gaba,Ɗayyaba da Gwaggwon Bugaje suka zauna a mazaunin baya,ɗaura kan Sahura da ya jike da jini Ɗayyaba ta yi saman cinyarta tana kuka. Motar ya kunna suka wuce asibiti.
A cikin gida Dauda Imamu ya fito kenan idanunsa suka sauka a kan HAFIZA. Cak ya tsaya yana kallonta,takowa ta yi zuwa inda yake idanunta ba su bar kallonshi ba. A hankali ya furta
''HAFIZA!"
''Na'am Abba! Na yi kewarka sosai Abba!" ta faɗa muryarta na rawa kamar za ta yi kuka. Rungumeta ya yi tsam a jikinsa,nan take sanyi ya ji a ransa, wata iriyar natsuwa ya ji tana lulluɓe ko'ina na jikinsa.
''Uba ya ga 'ya ya manta da kowa'' cewar Kawu Rabi'u yana fitowa daga ɗakin fuskarsa kwance da murmushi, murmushin Dauda Imamu ya yi yana shafa bayan HAFIZA. Ɗan ɗago da haɓarta ya yi fuskarsa shimfiɗe da murmushi ya ce
''Kin girma sosai HAFIZA''
''Eh Abba. Sallah zan yi,da na idar zan zo wurinka''
''To shikenan HAFIZA,ki yi mini addu'a da Ammunki''
''To'' ta faɗa tana nufar ciki. Bin ƙofar ya yi da kallo,tausayinta na mamayeshi rabon da ya ganta kusan shekara huɗu kenan da 'yan wasu watanni. Muryar Nu'aymah ya ji a kusa da shi tana faɗin
''Baba ka kai ni wurin mama''
Sai a sannan ya tuna da Sahura na asibiti,amsar lambar mijin Jamila ya yi hannun Yasir ya kirashi. Sunan asibitin ya tambaya sannan suka yi sallama. Duban Yasir ya yi ya ce
''Ka rakasu asibitin yariman baruka,idan ka je ka kira mijin Jamila ya sanar maka inda suke.''
Tun da Dauda Imamu ya amsashi sunan Sahura annurin fuskar Yasir ta ɗauke,nan da nan ƙwaƙwalwarsa ta tuna masa da irin cin kashin da ta ma Ammunsu a ranar da za ta bar duniya. Ba tare da doguwa shawara ya ce
''Abba zan je duk inda ka aikeni duk nisansa amma zuwa asibiti wurin Baaba Sahura wallahi ba zan je ba.'' yana faɗin haka ya yi wucewarshi waje ya bar shi hangame da baki. Ya san Jalil ba zuwa zai yi ba shi ya sa bai ma tunkareshi da maganar ba. Fita ya yi ya samu Sadiƙu ya roki ya rakasu Hamid asibiti wurin mahaifiyarsu don shi ba yanzu zai je ba,sai HAFIZA ta idar da salla za su je tare. Ba shi lambar mijin Jamila ya yi sannan ya samu wuri inda su Mamman suke ya zaune . Saɗiku da su Hamid suka nufi hanyar titi.
^^^^^^^^^^^^^
A can asibiti da ƙyar suka amshi Sahura,don sun ce sai an zo da policeman saboda raunikanta sun yi yawa. A emergency room suka wuce da ita a saman gadon marasa lafiya. Likita da nurses biyu suka duƙuffa a kanta don farfaɗo da ita daga suman da ta yi. Bayan sun yi nasarar farfado da ita sai aka mata ɗinki har biyu a inda Jamila ta ciro tsorayen gashin,sun cire hakoranta biyu na gaba ssaboda sun tashi aiki sai dai ta maƙala na roba. Duk inda ta ji rauni sai da suka gyara sannan suka da ita ɗakin marasa lafiya aka ɗora mata drip. Wata nurse ta gyara ma Gwaggwon Bugaje babban yatsanta,sai ta wanke inda ta ji rauni a goshi ta manna bandeji tare da bata maganin rage zugi. Mijin Jamila ya biya kuɗin asibitin sannan ya wuce,don ko da Sadiƙu ya kirashi ba ya asibitin sai kwantancen ɗakin ya mishi. Saɗiku na kai su ɗakin ya fitowarsa, daman Dauda Imamu ne ya sa ya zo asibiti,har yanzu yana jin zafin abin da ta ma uwar ɗakinsa wanda silarta ta rasu.
Baccin wahala take tana numfashi da sauri da sauri, Gwaggwon Bugaje zaune suka da ita, Yaranta kuma suna zaune a wani gadon da babu kowa sun yi jugum-jugum. Aunty Saudah ta ɗora Maryam a saman cinyarta tana sanar ma Alhaji Shu'aibu shanawa a waya abin da ya faru da mahaifiyarsu,hatsari ta ce mahaifiyarta ta yi haƙoranta biyu sun fita,sosai ya tausaya mata bayan sun gama waya ya turo da dubu goma ta account ɗinta su kara na asibiti. Duk wanda ya ga Sahura a lokacin zai yi tunanin mummunan hatsari ta yi domin fuskarta ta sauya,bakinta ya kumbura ya yi suntum! Idonta ɗaya yafi ɗayan girma, kanta ya sha bandeji. Dole Aunty Saudah ta ce hatsiri mahaifiyarta ta yi,don bata da maraba da wanda ya yi hatsari. Shiru ɗakin ya yi kowa na karatun zuci,can Gwaggwon Bugaje ta dubi Hamid ta ce
''Wai ina mahaifinku ne har yanzu bai iso ba?''
''Mun barshi a gida granny''
''A gida! Ya manta Uwata na asibiti ne ko me yake nufi'' ta fada ranta a ɓace. Ɗaga kafadunsa ya yi irin i don't know ɗin nan. A kufule ta ce
''Kira mini lambarsa yanzu ka ba ni''
''Ban da kati a waya''
''Bari na kirashi granny '' Aunty Saudah ta faɗa tana kunna wayarta, ringing take har ta katse bai daga ba,ta sake kira nan ma bai ɗaga ba,kusan sau biyar tana kiransa tana ringing amma bai ɗaga ba,haka ta hakura ta sanar ma Gwaggwon Bugaje wayarshi bata shiga, sosai ranta ya ƙara ɓaci a saman na da,me yake nufi da haka ne,ya kama shi ne a sahun gaba a ɗawainiya da Sahura a asibiti. Abin da ba su sani ba wayar na hannun HAFIZA tana game a ciki,tana sane taƙi bashi wayar don ta ga sunan da ta yi kiran 'YATA SAUDATU ya bayyana a srceen ɗin wayar,ta tabbata yarinyar kishiyar Ammunsu ce take kiran,saboda mahaifiyarsu na asibiti,duk kiran da za ta yi har katse bata ɗagawa,siririn tsaki ta ja tana ci gaba da game ɗinta,a gefe guda Dauda Imamu na amsa gaisuwar malam makarantar da ya koyar.
Tun Gwaggwon Bugaje da yaran Sahura suna saka ran zuwan Dauda Imamu a nan kusa har suka hakura. Sai bayan isha'i Sahura ta farka da ihu tana sumbatu
''Wayyo ni Sahura na mutu na lalace! Karki cire mini tsoron gashina!...."
Da sauri Ɗayyaba da yaranta suka matso inda take suna mata sannu,sumbatu take sosai alamar ta yi mummunan mafarki. Riko hannunta Gwaggwon Bugaje ta yi cike da tausayi tana murzawa a hankali har ta yi shiru,da kyar take iya buɗe idanunta saboda zafin da suke mata. A raunace ta ce
''Ina Baban Hamid,ya zo ya siyo mini yogurt mai sanyi na sha,zuciyata zafi take mini''
''Ai bai ma zo asibitin ba balle ya siyo miki Uwata'' Gwaggwon Bugaje ta faɗa cike da takaici. Da sauri ta juyo inda Gwaggwon Bugaje take zaune duk da raɗaɗin da take ji a ko'ina na jikinta hakan bai hanata juyowa ba tsabar mamaki.
''Gwaggwo Baban Hamid bai zo ba? Kina nufin ba da shi aka kawo ni asibitin nan ba?''
''Ba da shi ba ne uwata! Tun ɗazu nake mamakinsa,Saudatu ta kirasa amma bai ɗaga kiran ba balle na san me ya hana shi zuwa bayan ya san a sume aka kawoki Asibitin''
Kasa magana Sahura ta yi,gabanta ya shiga faɗuwa,tambayar kanta take 'Me ke shirin faruwa da ni Sahura! Ta ya Baban Hamid zai ƙi zuwa bayan ya san halin da nake ciki! Wata zuciyarta ta ce 'Kwantar da hankalinki Sahura ƙila yana can yana hukunta Jamila ne a police station' sanyi ta ji a ranta tare da gasgata zuciyarta. Yunwa kowannansu yake ji,don ma Aunty Saudah ta siyo musu fura sun sha. Babu wanda a cikinsu ya yi tunanin gabatar da Sallah. Wata nurse ta shigo ta cire ledar ruwan ganin ya ƙare tare ta tambayar yanayin cikinta,bata daɗe da fita ba Dauda Imamu ya yi sallama HAFIZA na biye da shi a baya. Wani irin motsawa zuciyar Sahura ta yi,motsawar da takusan tafiya ta numfashinta,ba ita kadai ba har ta da 'yan ɗakin sai da suka yi mamakin ganin HAFIZA. Duk da ciwon da bakinta yake mata sakamakon hakoran da aka cire amma baai hanata motsawa ba,a ɗan tsawace ta ce
''Wace ce nake gani a bayanka?"
Kallon HAFIZA ya yi sannan ya ce
''HAFIZA mana!''
Sake tunzura ta yi jin yadda ya amsa mata.
''Tun kafin raina ya ɓaci ka fitar da ita daga nan ɗaki...''
''Baki isa ba!" Ya faɗa a matuƙar tsawace yana katse sauran maganarta.
''Ni zan maka magana ka ɗaga mini murya!"
Mummunan kallo ya wurga mata sannan ya ce...✍️
Narrnarhh Bukar's Amazing pen ✍️