Free chapter · Read without an account

Chapter 39

by Narrnarhh Bukar · BAHAGON TUNANI BOOK 1,2&3

The Amazing Pen ✍️.......

BAHAGON TUNANI

بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم

039

Nan da nan jikinta ya ɗauki kakkarwa kamar ta ji kiɗin disko. Wata iriyar halitta ta gani mai mummunar siffa da ban tsoro tsaye a inda Boka Ataka ke zama. Lulluɓe take da baƙin mayafi sai dai fuskarta ce a buɗe,farin gashi buju-buju a fuskar,idanunta jajaye babu ɗigon baƙi,bakinta wawakeke babu haƙori ko ɗaya a ciki. Gwaggwon Bugaje bata san lokacin da ta saki fitsari ba jikinta na rawa tsaɓar yadda ta tsorata,bata taɓa ganin mummunar hallita irinta ba. Cike da ƙaraji mummunar halittar ta fara magana

''Ataka Kun tafka babban kuskuren karya sharuɗɗanmuuuu! Ataka ba za mu barku baaaa! Ataka mun yi miki kashedin kar mu sake ganinki a hamadarmuuuu! Ataka kin ƙi jiiiii! Ataka yau za mu hallakiiiii!"

''Naa roƙe Boka Ataka ka yi mini rai! Ba ni na karya sharaɗinku ba...''

''Ataka dole hunkunci ya hau kankiiii! Ataka yanzu za ku fara kurɓar madarar bala'i ku da ahalinkuuuu gabaɗaya! Ataka ba ma wasa da alƙawariii! Ataka ba za mu barku baaaaa!''

Babu shiri Gwaggwon Bugaje ta miƙe,ko tsayawa saka talmaki bata yi ba,juyowan da za ta yi kenan ta ji abu mai tsini ya caki idonta na hagu,nan take ta saki razananniyar ƙara tana riƙe idonta,wani irin azazzaben zufi ya ziyarci ƙwaƙwalwarta lokacin guda,ruwa ta ji yana zuba daga idon,tabbas idan bata yi wasa ba za ta halaka a wannan kogon. Gudu ta fara yi ta rufe idon da hannu ɗaya. Ihu take tana neman ceto a cikin kogon.

''Jama'aaaaa! A taimakeni za su kasheni!" Na shiga uku na lalaceeeee! ''

Ƙara ma motarta mai ta yi sosai ganin halittar ta rabu gida biyar suna binta,su ba a ƙasa ba kuma ba a sama ba. Da kyar ta yi nasarar fitowa daga kogon ta ci gaba da gudu a cikin hamadar. Duk da zafin da take ji a babban yatsanta bai hanata gudu ba,idanunta ɗaya da ta tabbatar da wuya bai tashi aiki ba sai raɗadi yake mata, lallai ta kawo kanta kogon mutuwa. Gudu take amma kamar bata motsawa daga inda take,ga halittun sai ƙara kusantota suke. Wannan shi aka kira da tashin hankali wanda ba a saka mai rana, idan da tasan abin da za ta fuskanta kenan me zai kawota hamadar Boka Ataka. Wasu maza biyu ta gani a wajen hamadar suna tafiya,ta juya baya ta ga halittun sun kusa zuwa inda take,babu shiri ta wage maƙogaronta ta ƙwalla ƙara da iya ƙarfinta tana kiran mutanen. Kamar an ce su duba hamadar boka Ataka,salati suka yi suna nufota,kafin su shigo cikin hamadar ta ji an hankaɗo waje da ƙarfi,take ƙugunta ya amsa. Cikin hanzari mazan suka nufota suna tambayar lafiya. A rikice take nuna hamadar tana faɗin

''Su ne! Ga su can suna kallona! Wayyo! Wayyo! Ku taimakeni za su kasheni!"

Ita kaɗai take ganinsu sun jeru a gaɓar hamadar sun fuskantarta da jajayen idanunsu masu firgitarwa. Mazan sai kallo inda take nuna musu suke amma kwata-kwata ba su ga komai ba,dusar ƙankara ce kaɗai ke zuba kamar koyaushe. Ɗaya daga cikinsu ya ce

''Baiwar Allah mu fa ba mu ga komai ba! ''

''Ka gansu can suna kallona wallahi su suka lahanta mini idona ɗaya'' ta yi maganar tana cire hannunta a saman idon. Waro idanunsu waje suka yi,ganin ƙwayar idon ta tsiyaye sai fatar kawai ta rage ta shige ciki kamar ido bai taɓa wanzuwa a wurin ba.

''Subhanallahi! Baiwar Allah me ya kai ki shiga hamadar boka Ataka kamar ba musulma ba!" Ɗaya daga cikinsu ya tambaya hankalinsa a tashe. Gwaggwon Bugaje da azaba ta gama mamaye ko'ina na jikinta ta ce

''Tsautsayi yaro! Wayyyyoooo ni Maimunatu za su kasheni" ta yi maganarr tana sake nuna hamadar ta hannu ɗaya. Ayatul kursiyy ɗaya daga cikinsu ya shiga karantawa yana fuskantar hamadar. Nan da nan Gwaggwon Bugaje ta nemi halittun da rasa. Juri ta fara gani, mutanen na koma mata bibbiyu. Jin kanta take kamar ana kwankwatsa shi da adda saboda yadda yake mata ciwo. A hankali tana lumshe idon mai lafiya tana buɗe shi.

''Ataka Ku jira ƙarshenkuuuuuu! Ataku duk sharaɗin da kuka karya sai kun fuskaci hukunci ku da ahalinkuuuuu"

Maganar da ta sauka a dodon kunnuwanta kenan kafin su ɓace. Ta nemi ganinta ta rasa,gangar jikinta ta saki kamar bata da rai. Da sauri ɗaya daga cikin ya ruga neman abin hawa don a kaita asibiti,da kyar ya samu mashina biyu suka taho tare. Aka cicciɓata saman mashin, ɗaya ya zauna a bayanta yana tallabota,ɗaya ya hau mashin na biyu suka nufi asibitin ƙauyen...✍️

^^^^^^^^^^^^^^

Barikin sojojin sama jihar Kaduna Nijeriya

A ɓangaren su HAFIZA bayan sun yi karin kumallo Jalil ya zo ya ɗaukesu a mashin zuwa gidan Momynsa a G.R.A. Da wuri Hamida da sauran yaran suka tafi makaranta. Tarba ta musamman ta musu,ta cika gabansu da kayan cima sannan ta samu wuri ta zauna.

"Wannan ɗawainiya haka maman Raihana?" Jamila ta faɗa tana kallon kayan gabanta murmushi kwance a fuskarta.

''Haba! Babu komai wallahi. Ya karin haƙurinmu?"

''Hakuri da godiya. Muna ƙara godiya sosai Allah ya saka da alkhairi ya bar zumunci''

''Babu komai wallahi. Yi wa kai ne. A nan HAFIZA za ta zauna ko tare zaku koma"

''A nan za ta zauna,ɗazu mahaifinta na ji yana cewa a wannan satin zai sakata boko. Ni zuwa gobe zan koma gida in shaa Allah''

''Allah sarki Mairi! Rayuwa kenan Allah ya albarkacesu bakiɗaya. Allah ya kai mu goben lafiya. Bismillah! Kar shayin ya huce''

'yar dariya Jamila ta yi ''Kusan a ƙoshe muke,amma bari mu saka albarka''

''Ammu ni a koshe nake'' HAFIZA ta faɗa cike da sanyin murya. Harar wasa momy ta mata tare da faɗin ''Ban san wannan zancen ba HAFIZA. Buɗe ciki ki ci abinci kin ji. Nan ma ai gidanku ne''

''Allah Momy cikina babu inda abinci zai shiga'' ta faɗa tana nuna mata ɗamamman cikinta. Girgiza kai momy ta yi ''Ni ban ga almar kin ci abinci a wannan cikin ba''

''Da kin daina ɓata miyon bakinki maman Raihana. Tun da ta ce miki ta koshi, ba ci za ta yi ba''

''To ai shikenan''

Sun ɗan taɓa hira daga bisani suka yi sallama,ta kira Jalil ya zo ya ɗaukesu. Block ɗinsu maman Jawaheer ya kaisu,sai dai ba su sameta ba suka juyo gida. Da Ɗayyaba suka ci karo a falon tana kallo,Jamila ko kallon inda take ba ta ja hannun HAFIZA suka wuce ɗakin yara. Gidan ya yi shiru baka jin motsin komai,duk yaran suna makaranta. Sahura ta tafi gidan maman 'yar gayu tsaigunta mata abin da ya faru da ita a Gusau. A saman gadon Hamida suka yada zango. Hannu biyu ta saka ta riƙo hannun HAFIZA tana dubanta murmushi kwance a fuskarta da ta ce

''HAFIZA ina so ki ci gaba da mayar da hankalinki a karatu kamar yadda na sanki,ban da shiga abin da bai shafeki ba musamman na gidan nan duk da na san babu ruwanki da mutane. Ki shiga jikin 'yar'uwarki da yayyayenki,duk abin da kike buƙata ki sanar musu. Ki bayyana damuwarki ga 'yan'uwanki kaɗai da mahaifinki. An jima zan zauna da su in shaa Allah. Zan dinga kawo muku ziyara akai-akai. Idan Sahura da yaranta sun miki wani abu na mugunta karki ɓoye ki sanar wa mahaifinki,idan ya ƙi ɗaukar mataki ki amsa wayar Yasir ko Jalil ki kirani. Da kaina zan zo na rama miki. Duk aikin da ya dace ki yi a gidan irin wanke-wanke,share da wankin bayi ki yi amma kar ki zama jakar gidan. Jalil ya ce cikin satin nan zai sakaki a makarantar Hadda,don haka ki mayar da hankali sosai a muraji'arki ban da wasa da tara ƙawaye duk da nasan halinki. Allah ya yi muku Albarka ya jiƙan Yaya,ya sa tana cikin Rahamarsa'' ta ƙarashe maganar ta rungumeta,hawaye suka shiga rige-rigen sauka daga gurbin idanunta. Kuka ya taso ma HAFIZA,gani take kamar a mafarki ne ba zahiri ba. Shikenan ita da ganin Ammunta sai a lahira,sun rabu kenan rabuwa ta har abada. Cikin kuka HAFIZA ta ce

''Ammu In shaa Allah zan kiyaye duk abin da kika faɗa mini,sannan zan mayar da hankalina sosai a karatu''

Ɗagota Jamila ta yi tana share mata hawaye,ita ma ta mata hawayenta.

''Yawwa HAFIZATA! Haka nake son ji! Ubangiji yana tare da ku,shi zai karesu daga sharrin masu sharri. Ki dage da addu'a kin ji,na san baki wasa a azkhar ɗinki don haka ki dage ban da mantuwa. Kin ga dai matar babanki da yaranta sun fi tsanar a kan yayyayenki ko?"

Jinjina ma kai ta yi tana kallon kwayar idanunta

''Yawwa don haka ki kiyaye,duk wata shawara ki yi ta da 'yar'uwarki ko yayyayenki,idan ta fi ƙarfinsu sai ki kirani kin ji!"

''Tom Ammu in shaa Allah''

''Yawwa 'yar albarka! Allah ya ma rayuwarku albarka. In shaa Allah za ku zamo fitila a gidan nan,ku ne a sama da yardar Allah. Ubangiji ya ci gaba da kareku''

''Ameen Ammu''

Kwanciya Jamila ta yi, HAFIZA ta nufi jakarta ta ɗauko drawing book ɗinta da writing box ta fara zane cike da ƙwarewa...✍️

^^^^^^^^^^^^^

Zaune suke a saman kujera mai cin mutum biyu. Maman 'yar gayu ta dafe ƙirji tana kallon bakin Sahura,hakoran robar ta cire tana nuna mata inda Jamila ta cire mata haƙora. Tsabar yadda maganar ta shigeta bata san ma lokacin ta buɗe baki hangaigai ba tana kallonta. Sai da Sahura ta ɗige aya sannan ta ja dogon numfashi ta sauke.

''Lallai wannan matar ta ciko uwar wuta! Ni haushin kima na ji wallahi! Tana mace kina mace za ki tsaya har ta miki irin wannan dukan,ta cire miki hakora,ta cire tsoron kitsonki har biyu! Haba don Allah! Wallahi kin ba ni kunya!"

Murmushin takaici Sahura ta yi tana binta da kallon da alama bata san wace ce Jamila ba. Gyara zamanta ta yi ta ce

''Hmmm! Maman 'yar gayu kenan! Duk yadda zan misalta miki wacece ƙanwar kishiyata ba za ki yarda ba. Wallahi ta fi wani namijin ƙarfi! Jinta take kamar doki! Duk yadda matan ɗakin suke soncetona daga hannunta sun kasa,Gwaggwota tun da ta yi wurgi da ita bata sake motsi ba. Ke a ranar na ga ruwan bala'i da tashin hankali. Ga 'yar iskar ta kulle ɗaki. Ai maman 'yar gayu ina faɗa miki ina cikin tashin hankali tsamo-tsamo. Ni babban damuwata mallakar da ta warware''

Ɗan waro idanu waje maman 'yar gayu ta yi tana faɗin

''Ta warware maman Hamid! Garin ya ya?"

''Sanadin tsinanniyar yarinyar kishiyata da ke hannunta wacce na faɗa miki baban Hamid yana yawan maganarta. Babban damuwata yadda yanzu ya juya mini baya,duk abin da zan yi a wurin ba ya ganin daidai ɗinsa. Ba ya shayin ko a gaban waye ya karta mini rashin mutunci.''

''Ni kuwa zan so ganin wannan shaiɗaniyar yarinyar. Amma ba ke za ki riƙeta dai ba ko?''

''Na so ƙin yarda tun a Gusau amma ya kafe,ke daga ƙarshe ma ya ce idan ba zan iya ba zai sawwaƙe mini ya auri wacca za ta riƙe mishi yara''

Da ƙarfi maman 'yar gayu ta daki cinyarta tana faɗin

''Jar ubaaa? Lallai Imam ci kai! Yaushe ya kwarkwance har haka kamar taɓaɓɓe. Ni wallahi tashi mu je yanzu na je na ga yarinyar da ƙanwar kishiyar taki. Sannan ki sha kuruminki ba dai 'yar'uwarki tana nan ba,zamu kulle ɗakin mu mata tsinannan dukan da ba za ta moru ba. Zan nuna mata ni cikakkiyar 'yar bariki ce ta gidi!" Ta yi maganar tana miƙewa. Sahura ta so hanata amma ina maman 'yar gayu ta yi nisa,burinta kawai ta yi arba da Jamila ta lillisata. Jinta take za ta iya ma mata goma duka ba mace ɗaya ba. Sosai ta shiga ɓacin rai da abin da aka ma aminiyarta. Wando ta saka ta zumbula hijabi suka fito da kulle ɗakinsu,sai surfa zagi take kamar ta ari baki. Zuciyar Sahura babu abin da take sai dukan uku-uku,tsoro ya gama mamaye zuciyar ta. Bata son maman 'yar gayu ta sha wahalar da ta sha a wurin Jamila. Don ta gasgata Jamila mata-maza ne,shi ya sa bata taɓa haihuwa ba.(Ke Sahura ki tsoron Allah😂 yanzu fisabilillah Jamila ce mata-maza don ta kirɓeki😂. Esteem fans yau fa akwai kallo a gidan Sahura. Zaƙaƙura maman 'yar gayu za ta je rama ma Sahura duka💃💃💃💃💃💃😂😂😂😂😂😂 )

^^^^^^^^^^^^

PHC Aouata,Bégajé yakin Zinder,ƙasar Nijar

Primary health care na ƙauyen suka kaita. Da taimakon nurses ta farfaɗo,sun goge inda jinin ta ɓata a fuskarta,sai suka tsayar da jinin,aka mata allurar rage raɗaɗi. Da gigitacciyar ƙara ta farka tana kiran Boka. Abu gwanin ban takaici,bayan ta dawo cikin hayyacinta mazan suka tambayi inda 'yan'uwanta suke su nemosu. Ba tare da dogon tunani ba ta sanar musu unguwa da abokiyar wasanta Sajida tare. Ba tare da ɓata lokaci ba suka wuce. Kallon ɗakin take cike da tsoron kar waɗannan halittun su bayyana a ɗakin. Har rana bata ga idon mutanen ba da abokiyar wasanta,ga shi bata fito da jakarta ba balle ta kira yi. Yo ma wa za ta kira tun da bata da layin ƙasar. Takaicin duniya ya lullubeta. Bata ga laifin kowa ba sai na HAFIZA domin ita ce silar warwarewar mallakar har ya yi sanadin tsiyayar idonta. Har ta cire rai da zuwan abokiyar wasanta ta ji sallamarta. Bata amsa ba kuma ta jita sarai. Sajida na shigowa ɗakin ta kwashe da dariya.

''Su Maimunareey ne a gadon asibiti da bandeji a ido! Kar dai ki ce mini garin yawon zuwa hamadar boka Ataka kika samu naki rabon''

Ta sake kwashe da dariya har da riƙe ciki, Gwaggwon Bugaje ta ƙufulu iya ƙufuluwa sai dai babu yadda ta iya. Ta san Sajida da dariyar mugunta.

''Zuwa gaishe ni kika zo yi ko mini dariya''

Cikin dariya Sajida ta ce

''Duka mana! Dariya da jinyar Maimunareey mai ido ɗaya'' ta sake kwashewa da dariya. Tsaki Gwaggwon Bugaje ta ja tana faɗin

''Ni dai ya za a yii ki kira mini Uwata a waya''

''Ai ban da lambarta. Ina wayar taki?"

''Na barta gidanki,ba da ita naje ba''

Wuri Sajida ta zauna a saman gadon tana kallonta ta ce

''Idan da ni ce ke,wallahi tuni zan ɗauki hanyar gaskiya! Don wannan abin da ya sameki ya nuna cewa har yanzu Ubangiji na sonki da rahama. Kukan kuciya dai jawabi ne,amma fa ga mai hankali''

Taɓe baki Gwaggwon ta yi sannan ta ce

''To malama babu ruwanki! Rayuwata ce! Ina da ikon yin rayuwa a yadda nake so! Don haka yanzu na fara zuwa wurin boka! Babu gudu babu ja da baya!"

''Yanzu kuwa kika fara ganin ba daidai ba! Idan baki yi wasa ba ɗaya idon da ya rage miki ya tsiyaye a garin yawan wurin bokaye. Bari na je gida na dauki wayar na kira miki Sahura. Sai na kawo miki abinci don na san hanjin cikinki suna kukan yunwa'' ta faɗa cike da shaƙiyanci. Gwaggwon Bugaje bata tanka mata har ta bar ɗakin. Gyara kwanciyarta ta yi tana yatsina fuska saboda ciwon da gangar jikinta ke mata musamman idonta. Duniyar tunani ta lula na yadda za ta shawo kan matsala gidan Sahura...✍️

^^^^^^^^^^^^

Barikin sojojin sama jihar Kaduna Nijeriya

A hanya bakin maman 'yar gayu ya kasa yin shiru,sai faɗin yadda za ta ci uban Jamila take,Sahura dai ta ja bakinta ta tsuke tana sauraronta har suka iso flat ɗin. Maman 'yar gayu ta fara shiga sai Sahura ta biyo bayanta. Ɗayyaba suka iske tana kallo. Cire hijab maman 'yar gayu ta yi tana wurgi da shi.

''Lafiyanki kuwa'' Ɗayyaba ta faɗa cike da mamaki. Jikin maman 'yar gayu na rawa irin jira take a ce kule ta ce as! Ta riƙe ƙugu tana duban Ɗayyaba ta ce

''Na zo mu rama ma maman Hamid dukan da wannan matsiyaciyar ta yi mata''

''Da waaa!" Ɗayyaba ta tambaya tana ware ido.

''Da ke mana!"

Tsam Ɗayyaba ta miƙe tana faɗin

''Wallahi ba da ni ba saka lallin kaza. Yaya Sahura baki faɗa mata wace ce ƙanwar kishiyarki ba?"

''Na faɗa mata taƙi yarda ya zan yi da ita!"

Ran maman 'yar gayu ya sake ɓaci ta ce

''Tun da kun zama sakarkaru ku fita na kulle flat ɗin! Ni zan iya da ita! Ita ɗin banza ita ɗin yofi!"

Jikinsu na rawa suka bar flat ɗin,har rige-rigen fita suke,Maman 'yar gayu ta kulle ƙofar sannan ta juyo ta ce

''Ina kike 'yar rainin hankali! Yau za ki gane kurenki a hannuna! Kina inaaaa!......"

Jamila da ke cikin dakin yara tare da HAFIZA ta ji kamar ana surutai a falo. Tsam ya miƙe ta fito falon ta bar HAFIZA na zane. Ta kusa isa ta ji muryar maman 'yar gayu tana faɗin

''Yau ko ni ko ke a gidan nan! Kamar yadda kika cire ma ƙawata hakora biyu ni duka zan cire miki! Na ce kina ina! Ko sai na shigo cikin neeee!"

''Gani!" Jamila ta faɗa tana shigowa falon. Ta fahimta matar da ita take tun da ta ambaci ramuwa,kenan ta zo rama ma aminiyar faɗa. Kallon ƙasa da sama maman 'yar gayu ta ma Jamila sannan ta ce...✍️

Narrnarhh Bukar's Amazing pen ✍️

***

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol