Free chapter · Read without an account
Chapter: 3 (the accidental marriage)
RA'AYIN ZUCI....
Tun daga wannan maganar ban ƙara firta komai ba. haka tafiyar ta kasance a tsakaninmu tamkar masu ciwon baki. wanda hakan ba ƙaramin daɗi yaymin a raina ba don ban shirya yin magana mai tsaho dashi ba, har lokacin zuciyata a hasale take dashi. na kasa manta abinda kunnuwana sukai katarin ji yana furtawa ga abokinsa Doctor Umar, har yanzu ban huce da jin zafin kaifafan kalaman da suka ratso ta tsakanin laɓɓansa ba wayanda naji yana furtawa ga likitan dake karanta masa halinda rayuwata ke ciki ba ɗazu. wannan yasa na maida hankalina ga window ɗin motar ina kallon yanda mutane keta hada-hadarsu.komawa nayi na jigina bayana a jikin kujerar da nake zaune akai tareda lumshe idanuna, a haka ya juya kan motar ya shiga cikin layin mu har lokacin ban motsa ba.Horn ya yi a bakin get kimanin wucewar mintuna uku, sannan ya tsayar da motar banyi motsin kirki ba balle in samu ƙarfin gwiwar fita daga motar. Inaji ya buɗe motar ya fita ba tareda yace dani ƙala ba, nima banyi gigin dakatar dashi ba don banga dalilina nayin hakan ba.Murɗe kujerar motar nayi ta yanda zanji daɗin jingina kamar yanda nake buƙata, na jima ina tufka da warwara a ƙalla sai da na shafe mintuna shabiyar sannan na buɗe motar na fita. Cikin rashin guzari nake tafiya tamkar wadda na shekara ina jinya, komai na rayuwata yanzu baya min daɗi kamar yanda na baiyana a baya. A haka na isa jikin ƙofar falon zuciyata cike taf da tarin fargabar abinda zan tarar, tura ƙofar nayi daga can ƙasan maƙoshina nayi sallama. Abin takaici yanda nabar falon na tafi Asibiti ba haka na dawo na sameshi ba, kamar zan kurma ihu haka na dinga bin pillows ɗin da aka baza a tsakar falon da kallo.
Ajiyar zuciya na sauke mai zurfin sosai ina jin yanda takaicin abin ke ƙara mamayata. Daga can ƙasan ruhina na ce,"ya ubangiji ka ƙaramin haƙuri akan duk abinda zan gani na ɓacin rai a cikin gidanan, sannan ka nuna min ranar da zanji daɗin zama a ɗakin mijina kamar yanda sauran mata sukeji a ɗakunansu." nayi adɗu'ar cikin gajeran sautin da babu me iya jina.Takun takalman da naji sautinsu na fitowa daga hanyar kicin ɗina ce, tasa na juya da hanzari ina kallon Direction ɗin gurin. bisa ga mamakina Faridah Attahiru ce hannunta ɗauke da soyayyen ƙwai cikin faranti, kamar yanda nai kasaƙe ina kallonta itama ido ta zuba min tana kallona. Kimanin gushewar mintuna uku sannan na sauke idanuna ƙasa don bansan abinda ya kamata ince da ita ba.Ɗan gajeran murmushi ta saki wanda sautinsa ya kutsa cikin kunnena sannan ta ce,"kin daɗe sosai a inda kikaje Bilkisu. Nayi zaton a can inda kika kai ziyarar zaki kwana."ta firta hakan tana ƙara tsareni da manyan idanunta, waƴanda babu komai a cikinsu face tsantsar fitsara da rashin kunya.Ka sa amsa mata nayi don bansan abinda ya kamata ince mata ba, a nitse na lumshe idanuna sannan na ƙara buɗesu tar akanta na ce,"idan zaki soya ƙwai don Allah ki dena soyawa a nan. Ƙamshinsa yana ɗaga min hankali sosai." nayi maganar a sanyaye tamkar ba daga tsakanin laɓɓana ta ratso ta fito ba.
Tsareni tayi da ido cikin tsananin mamakin jin abinda na firta, amma da yake ƴar duniyace sai ta gaggauta shanye mamakinta ta ce,"masu baiwar ɗuwawun haihuwa su ya kamata su firta haka a martaba maganarsu, ba juya irinki ba wadda baki iya komai ba sai dai kici kiyi kashi, ina ganin zaifi miki alkhairi ki tanadi hujjar da zaki gamsar da Hajiya akan fitar da kikayi." ta firta hakan tana jifana da kallon ƙasƙanci, wanda yasa naji a zuciyata na muzanta ainun. Zuciyata ce ta yi wata irin motsawa wadda ta sa allon ƙirjina ya fara barazanar darewa gida biyu, cikin wani irin yanayi mai narka zuciya na sauke mata rinannun idanuna cikin nata, cikin yanayi irin na zallar kaɗuwa. duk yanda naso na daure a wannan taƙin juriyata sai da ta raunata ainun, sai kawai na samu kaina da yin murmushi wanda ya taimaka wajen baiyana halinda zuciyata ke ciki. Kasa cewa komai nayi na daure na danne zuciyata gudun kar in rusa ribar haƙurina ta hanyar biyewa Shirman Faridah Attahiru!
Haka na raba ta jikin kujerar data raba tsakanina da ita na wuce kicin, don in kaucewa ganin fuskarta wadda a yau ta rikiɗe ta zame min baƙa sanadin gorin haihuwar da tayi min. tsintsiya na ɗakko da abin kwashe shara na ajiye mayafina da jakata na fara ƙoƙarin gyara falon. Duk don in hana zuciyata damar da zata tsinduma a cikin halwar tunanin da ka iya zama ajalina, mintuna goma ne suka ɗaukeni na kammala gyaran falon, sannan na fita da sharar na zuba a inda aka tanada don hakan. Turaren wuta na kunna a electric burner. cikin gajeran lokaci falon ya biɗe da ni'imtaccen ƙamshi tamkar ba shi ba, sai da na tabbatar falon ya dawo hankalinsa sannan na kwashi jakata da mayafina na wuce ɗaki. Har lokacin ƙirjina bai dena harbawa ba, wani irin ƙunci da zafine ke huda zuciyata tamkar ana rura min wuta haka nakeji. zama nayi a bakin gado ina tunanin yanda zanci gaba da rayuwa a tsakanin mutanen dake ƙuntata rayuwata ta hanyar yimin gori, haƙiƙa akwai ciwo idan akai maka gori akan abinda ba kaine zaka baiwa kanka ba, "mai yasa Faridah Attahiru ke ƙuntata min ta hanyar gasa min duk maganar data fito daga bakinta?" na firta hakan a cikin raina, amma dana tuna cewa Hajiyama yimin take sena ƙara jin cewa na karaya.Mayafin Abayar jikina na zame ya koma kan kafaɗuna, sannan na mike na fara takawa a hankali cikin rashin guzari ina kai komo. Ban sameshi a ɗakin ba sai ƙarar ruwan da nakeji alamar yana toilet, zama nayi a ƙasan kafet ɗin daya mamaye ɗakin nayi shiru ina tunanin makomar rayuwata. Sai kawai na saka fuskata a tsakanin ƙafafuna na fashe da wani irin kuka mai tsuma zuciya da ruhi, kuka nakeyi sosai har jikina yana rawa.
A haka Ya fito daga toilet ɗin cikin nutsuwa yana gyara zaman agogon fatar dake ɗaure a tsintsiyar hannunsa, tsayawa yayi cak a lokacin da kunnuwansa suka tsinkayo masa sautin kukana, wanda ke fitowa kai tsaye daga ƙasan zuciyata ba tareda wani shamaki ba. Hakanan sai yaji jikinsa yay bala'in sanyi don sarai ya san ba'a kyauta min, "to amma ya zeyi ya canza wannan murɗaɗɗiyar tifkar da aka jima ana tifkawa?" ya aiyana hakan a ƙarƙashin zuciyarsa wadda yake jin tana harbawa. Cikin ragowar guzarin da yay masa saura. A hankali yake takowa har ya iso inda nake zaune, risinawa yayi tareda zama a gefena ya jani jikinsa ya rungume. Yana jin yanda nake rera kukan tamkar wadda ke shirin shidewa. Al'amarin daya ƙara raunanata zuciyarsa kenan ya ƙara ƙanƙameni cikin ruƙonsa, tamkar zai maidani ɗaya daga cikin ƙasusuwan da ubangiji ya shirya a tsakanin ƙirjinsa!
ka na kallon irin riƙon da Yusuf yayi mini za ka fahimci so yake ya rarrasheni amma gabaɗaya he don't know where to start. bayana kawai ya ke shafawa tamkar wanda aka saka gam aka manne masa baki, da ƙyar ya iya tattaro kalmar dake maƙale a tsakanin maƙogaronsa ya ce,"kiyi haƙuri Bilkisu!"
Wannan Kalmar hakurin da bakinsa ya firta yasa naji tamkar ya watsamin ruwan tafasashiyar dalma a fatar jikina, "hmmm lallai wasu mazan Sam ba su da kunya ko miskala zarratan."
Ƙara sautin kukana nayi cikin wata marainiyar murya wadda ke baiyana raunin zuciyata a fili, ina jin yadda zuciyata ke dunƙulewa a tsakanin ƙirjina, so nake nayi magana Amma na ka sa saboda nauyin da bakina ya yi. kafin nayi wani yunƙuri naji an turo ƙofar ɗakin ba tareda yin sallama ba, dukda cewa ban ɗaga kai na kalli bakin ƙofar ba, na riga gama sanin wadda ke tsaye a gurin.
Da ga bakin ƙofar take aika masa da wani irin kallon Wanda tasirinsa ya hautsina ƴaƴan hanjinsa, ba tareda ta janye idanunta daga kansa ba ta ce,"sannu Ayu uban bibiko. idan ka gama nacin rungumar tata sai ku fito ku sameni Kai da Ita a falo, tunda ta gama kanainayeka a ɗaki da jaraba kamar akanta aka fara mu'amilar Aure." Hajiya ta firta haka ta na aika masa da wata danƙareriyar harara, sannan ta juya ta bar gurin fuskarta a ɗaure babu alamun wasa ko kaɗan.
Zame jikina nayi daga ruƙon da ya yi min ina ƙara jin zafin ƙiyayyar da nayi katari da ita a tsakiyar idanun Hajiya,ƙwallar dake ɓoye cikin ƙwayar idanuna ne ya zubo a fuskata. Cikin guzarin da yayi mini saura na kai hannu na sharcesu da bayan hannuna, sannan na miƙe ina ƙoƙarin saita nutsuwata wadda ta jima da ƙwacewa daga gareni.
Hmmm mutane da yawa kanyi raddi da dogon sharhi akan Auren soyayyah, har ka ji wasu matan suna kauɗi da iyayin cewa,"jin daɗin aure shine mutum ya auri wanda zuciyarsa keso."
Yes da gaske auren soyayya ni'imane amma idan kayi Dace. Ni a gareni ba shi da wa ta maraba da auren ƙaddara, wanda gwagwarmayar rayuwa da zanan ƙaddara suka rataya mini shi, a ƙarshe ga shi ya zame mini kara da kiyashi ɗaukar mara sani!
Abin takaici har yau zuciyata ta ka sa goge son da take masa daga cikinta, dukda cewa ba na samun farin cikin ɗari bisa ɗari daga gareshi, babbar tawa jarrabawar da ubangiji yayi mini ita ce soyayyar Yusuf Attahiru. Mutumin da ya samu nasarar mamaye duk wani lungu da saƙo na jikina, a cikin kwanaki bakwai kacal ya sauya alƙibilar rayuwata sannan ya kafa gwamnatinsa a cikin zuciyata. A nawa tunanin Idan har zan iyayi masa wannan soyayyar, kamata ya yi ya zama mai tsaya mini a cikin duk wasu al'amuran rayuwata no matter what. Shirune ya biyo bayan fitarta na mintuna uku, sannan ya yunƙura ya mike still idanunsa na kaina ya ce,"kiyi haƙuri Bilkisu in sha Allah komai zeyi dai-dai." ya firta haka yana me janye idanunsa daga kaina.
Cikin rashin guzari ya ke ɗaga ƙafarsa tamkar wanda ke counting steps ɗinshi, a haka ya ɓace mini da gani ya barni ina sharar ƙwallar da ta gaza tsayawa a idanuna. Da ƙyar na iya tattaro guzarin da ya jima da yin ƙaura daga gareni na yunƙura na miƙe, tareda wawurar mayafin abayar dake jikina nabi bayansa cikin rashin sanin dalilin kiran. A hankali nake tafiya harna isa falon, a zaune na sameshi a ƙasan kafet kansa a ƙasa yana sauraren Hajiya tamkar mai neman gafara daga gareta. Haka na ƙarasa na zauna daga can gefe ba tareda na bari mun haɗa idanu da ita ba, kallo ɗaya tayi min ta janye idanunta tareda gyara zama akan kujerar da take kai ta ce,"Yusuf!"
Ta kira sunansa da wani irin sauti wanda ya haifar masa da faɗuwar gaba, a nitse ya ɗaga kansa ya kalleta sannan ya sake yin ƙasa da kansa ya ce,"na'am Hajiya."
"So nake ka ƙara Aure tunda ita wannan ta kasa haihuwa." cewar Hajiya cikin maɗaukakin ɓacin rai da umarni.
Gabana ne ya yi wata irin faɗuwa wadda ta sa nayi saurin dafe ƙirjina, Amma sai na daure na karfafa kaina ina me tsumayin Jin amsar da za ta fito daga bakinsa, Jin amsar sa ita kadai ce za ta sharemin tantama daga zargin da zuciyata ke masa tun bayan fitowata daga Asibitin su Doctor Umar. Sosai na tsaida idanuna akansa numfashina yana fita da kyar, zuciyata na tsananta bugu tamkar za ta dako tsalle ta fito waje. shi kansa a wannan gaɓar ya razana da ganin yanayina, amma da yake sawun giwa ya take na raƙumi dole ta sa yay ƙasa da kansa, don ba zai iya jurar kallon tsakiyar idanuna a wannan lokaci ba. Fitina ce tsantsa a idona irin wadda bai taba cin Karo da ita a tareda ni ba. Wannan ya sa ya sha jinin jikinsa tamkar ƙasa ta tsage ya shige ciki haka yake ji saboda kunya....
"Na riga na yanke hukuncin za ka auri Aisha yar ƙanin mahaifinka, mun riga mun gama zartar da hukunci tareda Babanta. Umarni nake baka ba shawara ba, ruwanka kayi mini biyayya ko kuma ka bijirewa umarnina." Hajiya ta ƙare maganar tana miƙewa cikin nutsuwa ta bar mana falon ya rage daga ni sai shi.
Har lokacin ƙirjina bai dena dokawa ba, yunƙurawa nayi na miƙe ba tareda nace da shi ƙala ba na koma ɗaki. Ina shiga na fashe da wani sabon kukan da ya ninka wanda nayi da farko, a haka ya shigo ya sameni ina wannan aikin tamkar wadda akai min bushara da mutuwar Baffana. Cikin rashin guzari ya shigo ɗakin, ganina da yayi a wannan yanayi yasa yaji jikinsa yayi bala'in sanyi. Ya jima a tsaye ya na kallon yanda nake kuka kamar zan haɗiye raina, cikin sauran guzarin da ya rage masa ya ɗaga ƙafafunsa waƴanda suka jima da sagewa ya nufeni. Cikin nutsuwa ya sa hannu ya jani jikinsa ya rungumeni ƙam, yana jin yanda zuciyata ke bugawa daƙarfi da ƙarfi.
Cikin wata tattausar murya wadda ban taɓa jin sautinta a tareda shi ba ya ce,"kiyi haƙuri Bilkisu in sha Allah komai zaiyi dai-dai"
Janye jikina daga ruƙon da ya yi mini nayi ina kallonsa da idanuna waƴanda suka jima da jiƙewa da hawaye na ce," when? Yaushe koman zai yi dai-dai din?" na firta muryata na karyewa
"ki yarda dani na miki alƙawari komai zai yi dai-dai."
Raina ne ya yi masifar ɓaci for the first time tunda mukai Aure da shi, miƙewa nayi tsaye don na fahimci Raina mini hankali kawai yake kokarin yi na ce "ka da ka aikata kuskuren da zai haifar da saɓani mai girma a tsakaninmu Yusuf. Idan ka aikata hakan tamkar ka na nufin rabuwarmu da juna na har abada ne wllh ka ji na rantse maka." na firta haka cikin mawuyacin hali. zuciyata na tsananta bugu tamkar za ta tsaga ƙirjina ta fito waje.
Tsareni ya yi da idanu yana karantar yanayina, sannan ya yi murmushi mai sauti ya ce,"wata saɗaukarwar ba sai da alaƙar jini akeyinta ba Bilkisu. idan ta kama dole sai na Auri Aisha Sulaiman ki sani ba ni da wani zaɓi wanda ya wuce in cika Umarnin mahaifiyata." ya firta haka ya na wadata fuskarsa da ƙayataccen murmushi, wanda ya taimaka wajen binne halinda zuciyarsa take ciki.
Daskarewa nayi a tsaye tamkar mutum-mutumin da aka sassaƙa da ɗanyen itace, tsoro ne ya baiyana ƙarara akan fuskata wanda ya rikiɗe ya haifar mini da rawar jiki. Da ƙyar na iya haɗo kalmomin da suka sarƙafe harshena na ce,"wannan maganar ta ka ta sa naji a raina ina zarginka Yusuf. Ga dukkan alamu Aurenka da Aisha Sulaiman shiryayen al'amarine, Wanda aka Jima anayi masa tanadi. Ko da ya ke ka na da ikon aurenta kamar yadda mahaifiyarka ta umarceka, sai dai inaso ka sani na rantse da zatin Allah sai dai ka zauna da ita bayan ka yanke igiyar auren dake tsakanina da Kai!." nayi maganar ina kai hannu ga jakata wadda na ajiye a kan gado tun shigowata ɗakin.
Cikin ɓacin rai da wutar kishi na nufi ƙofar fita daga ɗakin tareda fushin da ban taɓa sanin ina da irinsa ba. Da wani irin sauri ya sa hannu ya fuzgoni na faɗa jikinsa, sai dai har lokacin ya ka sa sarrafani, ƙanƙameni yayi tamkar zai tsaga ƙirjinsa ya turani ciki. Duk da fuskarsa ba ta nuna halin da yake ciki ba, amma yanayin jikinsa ya jima da baiyana asiri dake boye a cikin kirjinsa, ta hanyar bugawar da zuciyarsa keyi da ƙarfin gaske. Cikin rikitaccen yanayi ya kai fuskarsa dab da tawa fuskar yana huci ya ce,"Aurena da ke na har abadane banga wanda ya isa ya kawo ƙarshensa ba!" yayi maganar cikin tsantsar fisata da bacin Rai.
Fizge jikina nayi da karfi sannan na dubeshi cikin yanayin da bai taba ganina a ciki ba na ce," ta ya akai aurena da kai ya zama na har abada bayan ba daga sama aka daurashi ba? Kai wllh ko daga sama aka daura aurena da kai yau seka sakeni don ba zan hada inuwa ɗaya da Aisha Sulaiman ba!" nayi maganar cikin fisatar da ta zarce tunaninsa.
"what do you mean by this statement Bilkisu?"
"Abinda nake nufi a fili yake ban boye maka ba Yusuf Attahiru."
Kura mini idanu yayi cikin tsananin kaduwar Jin na kirashi da full name dinsa, wanda ban taba yin hakan a gabansa yaji ba. takowa yayi har gaba na, sannan ya rankwafo sosai Yana kallon tsakiyar idona tareda Kai hannunsa Saman kaina ya dafa ya ce,"I'm sure something is botherng you in your head, shiyasa kike magana irin haka."
ture hannunsa daga kaina nayi, cikin zafin nama ya fuzgoni na fada jikinsa, kafin inyi wani yunkuri naji saukar laɓɓansa a saman nawa. daskarewa nayi don ko da wasa ban taba kawoma Raina irin wannan abin zai samu muhali a tsakanin mu nan kusa ba, wata irin sumbata yake mini mai wahalar siffantawa, cikin gajeran lokaci ya saukar mini da gagarumar kasala wadda tayi nasarar sauyawa tunanina alƙibila. Seda na bari ya shagala a duniyar da yake kokarin jefa mu nasa karfi na tureshi daga jikina. Kafin nayi wani yunkuri ya sake danƙoni da da karfin gaske har sai da ƙashin haƙarƙarina yayi qara.
Da wannan damar yayi amfani ya samu abinda yake so ba tareda munkai ruwa rana da juna ba, sai dai har cikin zuciyata na ƙudurta cewar ba zan haɗa inuwa ɗaya da Aisha Sulaiman ba. Dole a cikin biyu za'ai ɗaya don ba zan taba yin saken da wankin hula zai kaini ga dare ba!
Bai sarara mini ba sai da ya samu biyan buƙatar kansa sannan ya dai-daita nutsuwarsa har lokacin yana manne dani ya ce,"karki ƙara firta kalmar rabuwa a gaban idanuna bilkisu. muddin ki ka ƙara ambata kalmar saki zan ƙullaceki a raina na iya tsahon rayuwata!"
Banza nayi masa don banda amsar da zan iya ba shi saboda haushinsa da ya gama cika min zuciya. Gyara rukon da yayi mini yayi sannan yaci gaba da cewa," ta ya kike zaton yusuf zai iya rayuwa ba tareda Bilkisu Ibrahim Saminaka a duniyarsa ba?" yayi maganar yana ƙokarin jefa ƙwayar idanunsa cikin tawa.
Ɗaure fuska nayi don har lokacin ban sauka daga dokin ɓacin ran da na hau ba, babban burina shine ya sakeni in nisanta kaina da shi. Don wllh gabaɗayansa haushinsa nakeji kamar in rufeshi da duka haka zuciyata ke aiyana min, janye jikina nayi daga ruƙon da yayi min, cikin wata daƙilalliyar murya na ce,"ba na jin kasancewata a duniyarka yana da wani mahimmanci, kai da za'a danƙarowa sabuwar amarya wadda keda ɗuwawun haihuwa ai bai kamata kayi marmarin zama da juya kamar Bilkisu ba!" nayi maganar ina miƙewa daga saman gadon na faɗa toilet har lokacin zuciyata ba ta dena tafasa ba. Idanunsa na kaina har na bace masa da gani ya kasa kyakkyawan motsi, saboda yanda kalamaina suka shigeshi, nan take ya Kara Shan jinin jikinsa akan abinda ya ke shirin aikatawa da sunan umarnin uwa.
Ina shiga toilet ɗin na maida ƙofar na rufe tareda jingina bayana jikin ƙofar na fashe da kuka mara sauti. A wannan yanayin da nake ciki ubangiji ne kaɗai ya san yaƙin da ake gwabzawa a tsakiyar zuciyata, banyi zaton haka kishi yake da raɗaɗi a rai ba sai yau da abin ya faɗo kaina. Tambaya ɗaya zuciyata ke min "ta ya zan iya sharing Yusuf da wata ɗiya mace a duniya?"
Zubewa nayi akan ƙafafuna na fashe da wani marayan kuka wanda ke barazanar dagargaza zuciyata in to pieces. wannan shi ake kira gobara daga kogi maganinta sai ikon Allah, to in banda abin hajiya mai ya sa ba zata nema masa wata macen a gari ya aura ba sai Aisha Sulaiman? Yarinyar da kaf duniya babu wanda ta raina sama dani. Duhu ne ya mamaye ganina ba tareda na ankara ba, in banda a zaune nake na tabbata idan jiri ya ɗebeni seya watsar dani a ƙasa. Ina nan durƙushe naji alamar fitarsa daga ɗakin cikin zafin nama na buɗe ƙofar toilet ɗin na fito, saboda ɓacin rai ko gabana ba na iya gani sosai naje na dannawa ƙofar ɗakin key. still idanuna ba su dena ɓarin hawaye ba, toilet ɗin na koma na sakarwa kaina ruwa har lokacin kuka nake, a haka na tsarkake jikina na ɗauro alwala na fito. A haka nayi sallar magariba ba tareda na san abinda nake fada a cikin sallar ba, ina nan zaune aka fara kiraye-kirayen sallar isha'i, haka na miƙe jiki baɓu ƙwari na kabbara.
Bayan na idar miƙewa nayi tareda ninke sallayar na nufi gado ko hijjabin ban cire ba, ina jinsa ya dawo yana buga min ƙofa nayi banza da shi. Haka ya ƙaraci bugun ƙofar ya haƙura ya koma falo ya kwanta, bacci akace ɓarawo a wannan daren duk iya satarsa ka sa ɗauka ta yayi. Yanda naga rana haka naga dare.
Washe gari da safe sai wajen ƙarfe takwas sannan bacci ya samu nasarar ɗaukata still ban buɗe ƙofarba, a yanda zuciyata ke tafasa akan maganar ƙarin auren da hajiya ta umarci yusuf ji nake kamar in cinnawa gidan wuta kowa ma ya huta. "Ashe dama haka mata keji a zukatansu idan akai musu busharar gaiyato musu kishiya a gidan aurensu?" Na aiyana hakan a cikin raina.
Wasu kuraman hawayene suka fara kwaranya a kumatuna, ina tsaka da zancen zuci aka fara kwankwasa min kofa. Biris nayi kamar banji bugun kofar ba naci gaba da sharar hawayena, a tunanina Yusuf ya jima da fita office wannan yasa naji haushinsa da kishinsa sun kara kamani, wato don renin hankali ya gama biyan bukatarsa da ni shine yanzu zai kara aure su maidani bora.
Dafe kaina nayi wanda ke kokarin sarawa saboda tashin hankalin da ya dabaibaye min zuciya, Lumshe zagayayyun idanuna nayi ina tunanin majinginar da zan jingina da ita naji dadi, ya Naimah ce ta fado min a rai Amma cikin sauri na kauda tunanin sanar da ita halin da nake ciki. hakanan sai naji bazan iya gaya mata halinda nake ciki ba, a tsarin rayuwata kai qara baya daya daga cikin dabi'una. Ajiyar zuciya na suke mai nauyi ina jin yanda zuciyata ke takurewa a guri guda tamkar dunkulen da aka sarrafa da garin rogo.
"Wa zan baiyanawa damuwata ya fahimci halin da nake ciki ba tareda ya tauye mini hakki ba?" nayiwa kaina wannan tambayar daga can kasan zuciyata.
"Ya ilahi" na firta cikin wani kassararren sauti Mai tsuma zuciya da ɓargon jiki. A dai-dai lokacin aka Kara buga kofar dakin tamkar Mai bugawar zai karya kofar, a fusace na mike na nufi kofar zuciyata na tafasa, a zatona Faridah ce Amma ina bude kofar idanuna sukayiwa kansu ma sauki cikin idon Hajiya.Nan take nayi kasa da kaina na kasa cewa komai tamkar wadda aka sanya gam aka likewa Baki. har lokacin ba ta janye idanunta daga kaina ba, don ina jin tasirinsu a gabadaya ilahirin jikina, gyara tsaiwa tayi sannan tayi murmushi mai zurfi ta ce,"wllhi baki daukeni matsayin mahaifiyarki ba Bilkisu, na tabbata inda uwarki Asma'u ce ba za ki yi gangancin barinta da yunwa kamar yadda kikayi min yau ba!" Hajiya ta fadi maganar cikin son ta cusa min haushi.
Yes, she succeeded in annoying me as she wanted, Amma kuma se nayi shiru bance komai ba, cikin ikon Allah da hikimarsa nayi nasarar boye fishina in front of her, cikin sanyin murya wadda ba ta fita sosai na ce"don Allah kiyi hakuri bacci ne ya kwasheni shiyasa ban fito na dora ba. Amma yanzu zan haɗa miki" nayi maganar ina kokarin fita daga dakin jikina a mace.
Bayan rigata ta riko da karfi kamar za ta jefar Dani ta ce,"nafi karfin rashin kunyarki da duk wani tashen balagarki. Idan ma akan maganar auren Yusuf ne yasa kika tsiro da wannan tsiyar da kika tsotsa a nonon uwarki. to wllh sai dai ki mutu, Amma aure kam babu fashi sai anyi shi saboda yusuf ba zai kare a kanki ba"
Tunda ta fara magana zuciyata ya karye hawaye masu zafi suka Fara kwaranya a kumatuna, sosai naji ciwon kalamanta Amma ko giyar wake nasha na san ba zan iyay mata martani ko raddi akansu ba. duk da cewa banida daraja a idanunta I have to respect her because I am marrying her son, ko za ta zagi iyayena so dubu a gaban idanuna ba zan iya daga kai na kalleta ba saboda na mari tarbiya a gurin Inno da Mahaifiyata.
Tsaki taja mai Kara sannan ta juya ta barni a tsaye ina kukan baƙin cikin da ta kinsan min, duk da haka banda wani zabi haka na shiga kicin na hada musu breakfast sannan na dauka na Kai musu bangarensu. babu kowa a falon sai Faridah Attahiru wadda ke zaune a kan kujera ta Dora ƙafa ɗaya kan daya, sallama nayi ba tareda na kalli inda take ba na wuce inda na saba ajiye musu abinci na dire na fice ba tareda na ba ta damar kallon fuskata ba. A wannan rana haka nayi wunin baqin ciki da bacin Rai wanda ban san ranar gushewarsa ba, a haka Yusuf ya dawo daga office ya sameni a rikice kamar bani ba, sam ba na iya jurar tashin hankali yanzu zakuga na fita daga haiyacina. Ina kallonsa ya shigo dakin ya ajiye briefcase dinsa a inda ya Saba ajiyewa, sannan ya fara ƙokarin sassauta necktie din dake daure a wuyansa.
Ƙokarin fita ya farayi still ban motsa daga inda nake zaune ba, don na kudirtawa kaina cewar sena nuna mai ni jinin Ibrahim Saminaka ce. Tunda ya nuna mini halin ko in kula wllh sai na raunata ta sa zuciyar kamar yadda yayi mini, tunda haka ya zaɓa from today we will start the game, and we will see who will fall
Chubado 🥰
***