Free chapter · Read without an account

Chapter 42

by Narrnarhh Bukar · BAHAGON TUNANI BOOK 1,2&3

The Amazing Pen ✍️.......

BAHAGON TUNANI

بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم

042

Kamar kurayen da suka ga abin farautarsu, kallon tsana suke binta da shi. A tsawace Gwaggwon Bugaje ta ce

''Dan gemun ubanki da gashin hammatar uwarki kafin ta rasu ki zo nan!''

Dummmmm! Ƙirjin HAFIZA ya buga da ƙarfi,tun da ta zo duniya bata taɓa jin irin zagin nan ba sai a bakin tsohuwar nan,abin da yafi raunata zuciyarta,Ammunta da ta zaga tana kwance cikin ƙabarinta. Take ta runtse ido hawaye na gangarowa saman kuncinta.

''Ba dake nake ba annamimiya!" Gwaggwon Bugaje ta sake faɗa a tsawace,zabura HAFIZA ta yi tana ƙarasowa inda suke da sauri. A gabansu ta tsaya idanunta na kallon ƙasa. Kallonta suke cike da tsana musamman Gwaggwon Bugaje da take ganin ita ce silar tsiyayewan idonta ɗaya.

''Me kika taka dan gashin hammatar ubanki! Na ce me kika taka da kika zamar mana ƙarfen ƙafa ni da ɗiyarta!" Gwaggwon Bugaje ta faɗa tana zare mata ido dayanta. (My Esteem fans kun ji ƙarfin halin Gwaggwon Bugaje mai ido ɗaya😂 duk ta bi ta rikita HAFIZARMU fisabilillah! Da alama har yanzu bata saduda ba😂 amma duniya ce! Za ta koya mata babban darasi. Mu je Maha!🚶🚶🚶😂)

Sosai kalaman Gwaggwon Bugaje suka daki zuciyar HAFIZA duk da ƙarancin shekarunta,ita kuwa me ta tare musu,mene ne haɗin biri da gada,me suke nufi da ita ne! Ba su ba ba yaran ba,duk wanda ya ɗebo kashi a kanta yake saukewa bata ji bata gani ba.

''Wai ba dai take ba yar ƙalbu uba! Mayya mai zubin aljanun ruwa''

Bakin HAFIZA na rawa ta ɗan ɗago ta dubesu,zuciyarta ta karanto addu'ar neman tsari daga garesu ta ce

''Ku yi haƙuri...'' daga haka ta rushe da matsanancin kuka. Ba wai tsoronsu take ji ba,ba wai bata da bakin ramawa ba ne,sai dai ba haka Ammunta ta bata tarbiyya ba. A kullum cikin ce mata take Komi babba zai fada miki,duk rashin daɗinsa da dacewarsa ki ba shi hakuri ko da kuwa ke kike da gaskiya. Ba a samun yaron kirki da mayar da magana ga wanda ya girme shi ko ya haife shi,ki zama mai haƙuri akodayaushe, kin ga mai hakuri HAFIZATA,shi kaɗai ne a faɗin duniyar nan yake iya dafa dutse ya sha romansa hankali kwance,komai aka miki kar ki rama HAFIZA,ki bar wa Allah sakayya ki ga yadda Ubangiji zai yi ikonsa. Allah ya miki albarka ke da 'yan'uwanki Autata wannan ce nahisar da Mairi ta mata ana sauran sati uku ta bar duniya. Magana mara daɗi Gwaggwon Bugaje da Sahura suka shiga antaya mata babu kaƙƙautawa,Mairi kuwa ta sha zagi a wurinsu duk don su baƙanta ranta,kamar kuwa sun sani,ranta ya sosu da kalamansu a kan Ammunta. Ana haka Dauda Imamu ya shigo falon da sallama a bakinsa. Kamar haɗin baki kowannansu ya yi gum da bakinsa, kasancewar kujerar da suke zaune tana fuskantar kofar, HAFIZA ta juya ma ƙofar baya. Sahura bata yi tunanin dawowarsa yanzu ba,don sai tara ta gitta yake dawowa gidan. Dukkaninsu sun sha jinin jikinsu. Cike da barikanci Sahura ta miƙe zuwa wurin HAFIZA tana sauya yanayinta zuwa na damuwa

''Ayya HAFIZATA kin ga gababanki nan ya zo a daidai sai ya kai ki asibiti a dubaki?"

''Subhanallah bata jin daɗi ne? '' ya yi maganar yana ƙarasowa inda suke. Dubanta ya yi hankalinsa a tashe ya ce

''HAFIZATA baki da lafiya ne?"

Shiru HAFIZA ta yi tana kallon su Sahura, Gwaggwon Bugaje sai ƙyafta mata ido take alama ta ce ''Eh'' Tuno da zagin da suka ma Ammunta da ita karan kanta ta ce

''Abba lafiyata lau! Na fito zan je kicin na ɗauki tsitsiya suka tsareni. Kaka sai ce mini take me na taka da zan zamo musu ƙarfen ƙafa. Abba sai zagin Ammuna suke tana kwance cikin ƙabari...'' kuka mai sauti ta saki wanda yafi na farkon,don kalamansu sun yi matuƙar ƙuntata ran HAFIZA. Ran Dauda Imamu ya yi matukar ɓaci da abin da HAFIZA ta faɗa, musamman zagin da ta ce sun yi ma matarsa abar ƙaunarsa. Kafin ya ce wani abu zurum!  Sahura ta ce

''Kai amma an yi maƙaryaciyar yarinya! Yaushe Gwaggwo ta zagi Mairi! Ce nake ke da kanki ki zo wurinmu kina faɗa mana da zazzaɓi kika kwana''

Cikin kuka HAFIZA ta ce

''Ni ban ce muku ba! Lafiyata lau"

Murmushin takaici Dauda Imamu ya yi yana binsu da kallon mamaki.

''Na san za ku aikata abin da ya fi wannan ma!...''

''Kai Dauda! Ka ji tsoron Allah wace riba zan samu idan na ƙuntata ma marainiyar Allah!"

Dariya maganarta ta ba shi da takaici a lokaci ɗaya.

''Riba kuwa mai tsoka Gwaggwo! Tun ba yau ba na fahimce ki da Sahura kun tsanar da kuke maHAFIZA. Idan kin manta bari na tuna miki,a lokacin da kuke asibiti wani irin suna ne baki kira HAFIZA ba san da na je tare da ita,har ce mata kika yi zabiya! Ko kin zaci na manta ne!''

Girgiza kai Gwaggwon Bugaje ta shiga yi tana matsar ƙwallar ƙarya.

''Ka ba ni mamaki Dauda! Ina matsayin matar kawunka kuma sirikarka kake faɗan wannan muggan kalaman masu susan rai! Amma babu komai ba laifinka ba ne! Laifina ne da na zo gidanka!"

''Ke dai kika juya maganar zuwa wata sigar da ta ƙona miki rai!" Ya fada yana goge ma HAFIZA hawayen da suka wanke fuskarta. Duka yaran gidan sun fito falon suna kallon abin da ke faruwa,Ɗayyaba da ke kicin ita ma ta leƙo tana kallonsu. Sosai ranta ya sosu da abin da mijin yayarta ya ma mahaifiyarta,take tsanar HAFIZA ta sake linkuwa a cikin zuciyarta. Tabbas sai ta koya mata hankali. Yaran ma ransu ya yi mugun ɓaci da abin da HAFIZA ta saka babansu ya ma mamansu da kakarsu. Ƙowanne ya ƙullacceta a rai idan ka cire Maryam, Hamida ji take kamar an tsomata cikin aljanna,yau dai Abbanta ya rama mata cin kashin da Gwaggwon Bugaje take mata a duk zuwanta gidan. Jalil da zuwansa kenan ya riski fadan da ake,daɗi sosai ya ji a ransa,dole yau ya kira Ammu Jamila ya fada mata daddaɗan labari,Abbansu dai ya dawo cikin hayyacinsa. Cike da ɓacin rai Sahura ta dubi Dauda Imamu ta ce

''A gaskiya ka ba ni mamaki baban Hamid! Ban yi zaton....'' kasa karasa maganar ta yi saboda mummunan kallon da ya wurga mata mai haɗe da kashedin ta ja bakinta,aikuwa gum ta yi. Bai ce komai ba ya ja hannun HAFIZA, ya zo wucewa ya kalli yaran,ai kafin ya ce wani abu kowanne ya kama gabansa,zuwa yanzu mugun shakkarsa suke. Waɗanda suka shirya suka fito karyawa,sauran suka koma ɗaki. Daman Halima da Maryam ce ba su gama saka kaya ba. Aunty Saudah ma ta fito falon. Zaunar da ita ya yi a saman gadon, shi ma ya zauna kusa da ita. Ta dukar da kanta ƙasa tana ajiyar zuciya akai-akai.

''Uwata!" Ya kira sunanta da murya mai tsananin taushi.

''Na'am Abba''

Ajiyar zuciya ya sauki mai ƙarfi,mai damu da wanzuwansu Halima a ɗakin ba ya fara magana

''Ki yi haƙuri kin yi HAFIZA. Duk abin da aka miki wanda kika ji ranki ba zai ɗauka ba ki sanar mini. Kin ji''

''Tom Abba in shaa Allah ''

Murmushi ya yi ya ɗan shafa kanta ya ce

''Yanzu ki je ki yi wanka ki shirya,an jima zan kai ki bokonsa Nu'aymah''

''To Abba'' ta faɗa cike da murna wanda ya kasa ɓoyuwa a kyakkyawar fuskarta. Murmushi ya yi ya miƙe tare da barin ɗakin zuwa ɗakinsu.

A falo bayan fitar Dauda Imamu Gwaggwon Bugaje ta rushe da kuka ita ta fasa zuwa asibitin yau za ta koma Sakkwato. Sahura,Ɗayyaba da yaran suka shiga lallashinta. Jalil ya yi kane-kane a one sitter yana latsa wayarsa, lokaci bayan lokaci yana kallonsu yana murmushi. Daɗi sosai yake ji a ranta,tun kan aje ko'ina Ubangiji ya fara saka musu zalincin da aka musu. Hamida mayar ta hankalinta ta yi ta kammala shan kunun za ta wuce Jalil ya ciro ɗari biyu ya bata kuɗin break,ta masa godiya ta bar flat ɗin. Yasir bai san wainar da ake toyawa a gidan ba,daga sallar asuba ya wuce wurin aikinsa na pop da yake yi tare da abokansa a wajen barikin,da kayansa a jaka ya tafi masallacin shi ya sa bai dawo gidan ba. Duk kuɗin da ya samu yana tara su a account ɗinsa saboda makaranta,yana rage ma haifinsa ɗawainiya musamman na kuɗin mota tun da ba shi kaɗai ba ne a gidan.

Ɗa ƙyar suka shawo kanta har ta tsagaita kukan, amma ta ce zuwa gobe za ta goma Sakkwato tun da gori ake mata. (A ji tsoron Allah Gwaggwon Bugaje 😂 yaushe aka miki gorin gida 😂) Lallaɓata Sahura ta yi ta wuce ɗakinsu Aunty Saudah ta yi wanka,ta sirka mata ruwan wanka ta kai mata bayi lokacin HAFIZA ta fi daga wanka sannan ta dawo falon ta zauna,sai a sannan su Amina suka samu damar kammala karin. Sahura ta basu kuɗin kashewa suka bar flat ɗin. Ya rage daga Jalil,Sahura, Ɗayyaba da Aunty Saudah a falon. Bini-bini Sahura na aikama Jalil muguwar harara,yana hankalce da ita sai dai ya yi murmushi. Duk wannan dambarwar da ake a gidan Hamid bai sani ba,yana cikin ɗaki yana baccin asarar da ya saba. Ɗaki Ɗayyaba ta wuce ganin Dauda Imamu ya fito. Kusa da Sahura ya zauna. Sahura ta dubi Aunty Saudah ta ce

''Aunty Saudah je ki haɗo ma babanku abin kari''

''Ciwon hannu kike da ba za ki je ki haɗa mini da kanki ba?" Ya faɗa ba tare da ya kalleta ba.

''A'a!'' ta faɗa tana miƙewa da sauri ta wuce kicin. Bayan tafiyanta Jalil ya rissina ya gaida shi,cike da kulawa ya amsa. A gabansa ta ajiye sannan ta samu wuri ta zauna. A nutse ya fara cin abincin bayan ya yi bismillah. A can ɗakin yara koda Gwaggwon Bugaje ta shiga ta iske HAFIZA na wanka,ruwan da Hamida ta rage mata ta yi amfani da shi. Sai da ta jira ta fito sannan Sahura ta shiga da ruwan bayi sai Gwaggwon Bugaje ta shiga. Ko kallon inda HAFIZA take bata yi ba,dole idan ta koma gida su sake sabon shiri na musamman,bata ƙi HAFIZA ta halaka ba idan har ɗiyarta Sahura ta za ɗaukaka a gidan,ya zaman tana baza iko kamar da. Fitowar Gwaggwon Bugaje daidai da shigowar Ɗayyaba,sai da ta aikama HAFIZA mummunan kallon sannan ta samu wuri ta zauna. Hira suka shiga yi kamar ba su san da wanzuwanta a ɗakin ba. Ko a jikin HAFIZA, alla-alla take ta kammala shiri ta fito ta sami Abbanta, ɗauki take za ta shiga sabuwar makaranta sabuwar rayuwa.

A falo bayan Dauda Imamu ya kammala karya kumallo Aunty Saudah ta kai kayan kicin ta dawo. Zamanta keda wuya Dauda Imamu ya jefo mata tambaya.

''Saudah kika ce iyayen saurayinki suna son turowa ko?"

''Eh Baba'' ta faɗa da sanyin murya

''Kafin su turo,yau idan na fita zan yi bincike da kaina in shaa Allah ''

''To Abba'' ta furta tana jin sanyi a ranta,ta ƙosa ta auri Alhaji Shu'aibu shanawa,don kullum cikin kashe ruhinta da kalaman soyayya yake,tare da alƙawarin tarin farinciki da jin daɗi a rayuwar auransu.

''Ni ban ga amfanin binciken nan ba baban Hamid! Mutumin yana da kirki sosai da ibada ga girmama na gaba da shi,idan ya ganni har durkusawa yake ya gaida ni'' Sahura ta fada cike da tabbatarwa. Ɗan murmushi Dauda Imamu ya yi

''Sai kuma aka ce miki duk da kyawawan halayansa da ke bayyane ba za a binciki yadda yake mu'amala da mutane ba? Ba kwanakin baya mun yi maganar ba duk da na manta abubuwan da kika ce mini. Kin ga shi aure ba abun wasa ba ne,rayuwa ce ta dindindin da za a gina,dole ayi bincike me kyau tukunna''

''A yi bincike lafiya'' ta faɗa a iya fatar bakinta,ta yi amanna duk sukan da zai kawo ba za tta amince ba,haka kurum tana kallon idan hutu da jin dadi yake ya mata buƙulu,bata manta kwanakin baya da yake cikin ƙasƙashin ikonta,yana kawo mata suka da nuna baya goyon bayan auran balle yanzu da yake jin kansa mai jan wuya ne,ko sama za su je su dawo tana nan a kan bakanta babu gudu babu ja da ya baya. Dauda Imamu ya buɗe baki da niyyar bata amsa Hamida ya fito daga ɗaki, bakinsa duk miyon bacci alamar yanzu ya tashi daga bacci. Yana haɗa ido da mahaifinsa hantar cikinta ta yi mugun kaɗawa,wannan shi ake kira da Ali ya ga Ali,domin bai manta abin da mahaifinsa ya ce jiya ba. Ya juya zai koma ɗaki ya ji muryarsa mai cike da gargaɗi

''Idan ka kuskura ka ƙara taku ɗaya za ka sha mamakina''

Cak Hamid ya tsaya gabansa na faɗuwa,babu shiri ya t ƙaraso cikin falon daidai da fitowan HAFIZA sanye cikin kayan makarantarta na can,ta rataya ƙatuwar jakarta. Hankali Dauda Imamu sai ya rabu gida biyu,nuni ya mata da hannu alamar ta zo ta zauna sannan ya juya wurin Hamid fuskarsa matuƙar ɗaure tamkar bai san wata aba ita dariya ba. Madadin HAFIZA ta zauna,sai kawai ta ajiye jakarta ta nufi kicin ta haɗo abin kari ta dawo falon. Har ta dawo Dauda Imamu bai daina yi ma Hamid kallon ƙurilla yana nazartarsa ba. Ganin alamomin shaye-shaye sun fara bayyana a jikinsa sai ya ce

''Saboda kai raina ni,daga ganina za ka juya ko?"

Da sauri Hamid ya girgiza kansa yana faɗin

''A'a baba brush me zan je ɗaukowa''

''Mayar da ni brush mana! Ka ce mini jiya a gidan abokinsa ka kai dare ko?"

Da sauri Hamid ya ce

''Eh baba''

Wani irin kallo Jalil ya sama irin na makaryaci na ajin farko,babu abin da bai sani ba a game da Hamid,yana sane da duk motsinsa,ya bari ranar da mahaifinsa ya gano da kansa sai ya bayyana abin da ya sani. Kafin Dauda Imamu ya ce wani abu carab Jalil ya caɓe da cewa...✍️

Narrnarhh Bukar's Amazing pen ✍️

***

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.