Free chapter · Read without an account
2
by Mahma Lamido · INAYATU
Gidan Hawa biyu ne, akwai ground floor, akwai first floor hakanan kuma Akwai second floor, katon gida ne da ba a jima da renovating din sa ba kab, yawan dakunan da ke gidan Tana da tabbacin ko rabin su mutanen gidan ba za su iya occupying ba.
Saman na Mahmaah ba wata hayaniyar mutane, saboda dama tayi limiting hawa saman tun da aka soma buki, suna amfani da kasan kawai.
Duka manyan mata ne a dakin, akwai iyayen su yan uwan mahaifin su hakanan kuma akwai yan uwan Mahmaah da mutanen arzikin ta.
tun da suka shigo dakin da sallama bakin ta idon Mahmaah na kan ta, har ta samu kan carpet kusa da Mahmaah tana gaishe ta da sauran mutanen da ke dakin.
Fadada fara'ar fuskar ta Mahmaah tayi, tana bin inaya da wani irin kallo kamar yau ta soma ganin ta kamar kuma mai kokarin ajiye kamannun a idanun ta.
"Lafiya kalau inaya, sai yanzu kike shigowa ko" murmushi kawai tayi tana sadda kan ta kasa ba tare da ta furta komai ba, lokuta da dama ta kan yi mamakin adadin soyayyar da iyalan gidan baba Dr ke mata.
Kallon ta mahmaah tayi da kyau tana karantar natsuwar ta, nutsuwar inaya na daga cikin attributes din ta da duk ta ganta sai tayi wa ya yan ta kwadayin nutsuwa kwatankwacin ta.
"In ji dai you have eaten, Amal an kawo wa inaya abinci" mahmaah ta tambaya
Dariya Amal tayi tana fadin "ki rabu da wannan mahmaah kin manta halin inaya na rashin son abinci, yana can ta baro kasa"
Mahmaah ta dan bata rai tace "aa aa inaya maza idan kin sauka ki samu abinda kika sanyawa cikin ki ina amfanin zama da yunwa
Murmushi kawai tayi Tana fadin "toh mahmaah"
ta mike tana nufar inda deden ta take zaune kan carpet da alama sallah ta sallame, idanun mahmaah kuma suna yi mata rakiya, har tana jin su a jikin ta duk da kuwa ta bata baya.
Kudin da dede ta yi alkawarin bata na liki idan sun zo ta karba, tana durkushe kan carpet din ta ji an rungumo ta ta baya, yan kananun hannayen da suka rungumo ta ta kalla kana ta waiwayo gana washe hakoran ta cikin fara'a
"Yunus my boyyyyy" ta fada tana rungume yaron da dududu ba zai yi kasa da shekara biyar ba cikin jikin ta, fara'ar fuskar ta na fadada.
Yaron ya makalkale wuyan ta shima cikin jin dadin ganin ta "Aunty inaya ina chocolate dina" ya fada kai tsaye har maganar ta shi ta sanya ta sakin murmushin ta na musamman.
Mahaifiyar yaron ta shigo dakin da sallama hannun ta dauke da kanwar Yunus din Amira da ko sa'adan sakina zata dan girme ta, tana rataye da handbag din ta da gyalen chantilly da ta yafa bayan ta yar aikin ta ce dauke da baby bag din Amira ta karaso dakin,
itama kai tsaye gurin maman ta nufa tana gaishe ta tare da sauran mutanen dakin.
Mahmaah tace "kema Zarah sai yanzu kike zuwa kalli time fa"
Zarah da kana gani ka ga yar gaye mai ji da gaye da kuma aji, very classy da ita ta murmusa Tana kallon agogon swatch da ke hannun ta tace "hmmm mahmaah baki ga har make up Dina yayi melting ba, ina gurin Hassy sai yanzu aka gama packaging souvenirs din bridesmaids, bana so yau su watse ba a basu kayan su ba"
Mahmaah tace eh gaskiya kam tunda yau is the last day, ta fada tana sake maida kallon ta kan inaya da ke durkushe har lokacin da Yunus jikin ta suna magana kasa kasa ko me suke cewa oho?
Bata San ta zurawa Inaya ido ba bare murmushin da ya sauka kan fuskar ta ba har sai da Inayar da ke rike da hannun Yunus ta bacewa ganin ta.
Ba mahaifiyar Inaya dede kawai ba ko Amal da ke bayan Inaya ta Lura da yawan kallon da mahmaah ke yiwa Inaya tun jiya, ko meye dalili oho?
"Wallahi i can swear inaya kallon da mahmaah ke miki yayi yawa tsakanin jiya da yau"
Inaya bata ba zancen muhimmanci ba tace "uwa ba zata kalli yar ta ba sai ace kallon yayi yawa, kai Amal kina da shirme Allah" duka Amal ta nada mata a kafada tana fadin "fuck you"
Yunus ya kama baki har da dan zaro kananun idanun sa yana fadin "bad words Aunty Amal daddy na yace bad word ne wannan" ya fada
"Zan Make ka yaron nan" Amal ta zare mishi ido
Tuni amarya ta sauko kasa hakanan buki ya soma gudana cikin tsari da burgewa, anyi kidi an sha rawa an kuma yi liki, yan uwan ango sun zo suma sunyi barin kudi mai ban mamaki, da gani kai ka San kwarya ta bi kwarya ce ake a nan.
taro ya tashi cikin San barka, yan kai amarya suka tsaya yayin da fiye da rabin wadan da suka zo bukin suka kama gaban su.
Cikin gida suka koma zuwa lokacin Ana ta kiraye kirayen magrib, dakin su Amal suka koma da yake ita tana fashin sallah sai tayi zaune kawai tana kallon su suna bada faralin da ke kan su.
Aunty Amina ta leko dakin, kanwar mahaifin su ce da suke uwa daya uba daya, Baba Dr, Abba da Aunty Amina su kadai mahaifiyar su ta haifa a gidan kafin Allah ya dauki ranta, saboda haka zata ce a duk cikin yan uwan Abban ta domin yana da su da yawa ta fi shakuwa da yan gidan baba Dr da ya yan Aunty Amina
"Inaya, ina inaya take? Tana dakin nan? Aunty Amina ta tambaya tana rarraba idon ta kan yan matan.
"Na'am Aunty gani nan"
"Yawwa inaya ta so ki ji" aunty Amina ta fada tana juyawa kusan lokaci daya ba tare da jiran amsar ta ba
Mikewa tayi ta bi bayan ta, saman mahmaah suka koma sai dai wannan Karon kitchen din sama suka wuce direct, ba kowa kitchen din idan ka cire amaryar da kan ta hanifa da Aunty ta jawo kitchen ta samu abinda ta sanyawa cikin ta.
"Amarya amarya" inaya ta fada ta nufo hanifa da ke kan kujera gaban kitchen island tana cin dirty rice din da aunty ta zuba mata da casserole.
Murmushi hanifa tayi tace "wai ke yarinyar nan tsayi kawai kike karawa ba kya kiba, Allah mijin ki na da aiki, damar abin ma dai kina da yan abubuwan nan da maza ke so da ba a San ya za a kwashe ba, eh Aunty"
Hanifa take fada tana tsokanar inaya, kasa tayi da kan ta wata irin kunyar aunty na lullube fa, ita kam hanifa ko a jikin ta, ita ta Lura yaran gidan nan fa abinda ke bata kunya su ba komai ba ne a gurin su.
"Amma dai ke kam hanifa ko kunya ta ba ki ji ba"
Aunty ta fada tana sauke idanun ta kan dan kirjin inaya sanin shi hanifa ke nufi, a rashin jiki irin na inaya zaka yi mamakin cikar kirjin ta da kugu duk da dai ba can ta ke da su irin hakanan ba, amma dai tana da din har ma hips din na ta sun so rinjayar jikin ta, domin gaban na ta dai dai dai yan abu uwan suke Aunty ta raya a ranta.
Duk kunya ta da da lullube inaya ganin kallon da aunty ke yi mata tana sake rufe kirjin ta da mayafi.
Hanifa tace "kina da aiki kuwa"
Aunty ta dara tana dora dan basket din da take hada abinci tun dazu kan table, waiwayo tayi tana kallon inaya tace "Yawwa inaya karbi abincin nan ki kai wa yayan ku bangaren sa"
Fara'a tace ta fadada har hakan na bayyanar da hakoran ta tace "lahh yah faisal ya zo, i thought he couldn't make it"