Free chapter 路 Read without an account

8

by Mahma Lamido 路 INAYATU

THE SILENT INTRUDER


   Kwance ta ke tsakiyar gado ta barbaza takardu a gaban ta tana dubawa a lokacin da kiran FaceTime ya shigo wayar ta from Amal.

    Murmushi tayi tana kwanciya ringingine kan filo tare da daga kiran dogon bakin gashin ta na fulanin usul na barbazuwa kan filon.

     "Show off, ana yi muna show off din gashi" Amal ta fada kai tsaye bayan ta daga wayar, karamin Tsaki ta ja tana tattare gashin ta "kiyi sauri ki cinye gashin Amal, dama tun kwanaki da na ga yana tsintsinkewa na ce ke ce"


Amal ta sanya dariyar shaqiyanci tana fadin "da yake kin san ni dangin mayu ne, idan ma maita nake yi, Inaya Beldo ke ma kina gadon ta"

    Dariya zancen na Amal ya sanya ta itama, ta dara tana fadin kina Ina haka, this doesn't look like hostel

     "Yi hakuri mama Inaya ba yawon banza na je ba, muna Aso rock gidan Yaya Em for the weekend" Amal ta fada kai tsaye tana haska mata fuskar yaya Em da ke zaune kan couch da MacBook din sa gaban sa yana operating.

     Ya tankwashe kafa cikin fararen kayan Tommy Hilfiger faffadar riga mai gajeren wando wato three quarter.

     Bugun zuciyar ta ya tsanan ta kamar zata balla kirjin ta a lokacin da tayi tozali da kyakkyawar fuskar sa mai cike da gargasara wato Beard da ta Hana ta sukunin ta ta hana ta baccin ta a yan kwanakin nan Amal na fadin "say hi"

    Wani kallo ya jefawa Amal mai cike da kashedi a lokacin da ya dago kansa yana ajiye mug din da ke hannun sa yayin da Adam apple din sa ke kai kawo kamar zai fito ta makoshin na sa

    "Sorry sir" Amal ta fada tana bar masa falon sanin yanzu sai su bata.


     Ta sauke ajiyar zuciya mai nauyi tana ji idanun ta na tara hawayen da bata san dalilin su ba.


   "Halin yaya em sai shi inaya, wallahi matar shi tana cikin aiki" Amal ta fada tana dorawa da "dama tun dazu zaman nawa ya ishe shi, kora ta ne dai ba zaiyi ba, gwara in ba shi guri in rufawa kai na asiri in koma hostel a complete piece di na"

     Waje ta fito gabakidaya tana nuna mata harabar estate din su Emran "estate din nan na su yaya Em yana burge ni, serenity din shi kamar kina turai"

     Da Amal zata Lura da ta fahimci hirar ta su ta daina armashi, da ta fahimci hankalin ta baya tare da ita, da ta fahimci ta Lula a sabuwar duniyar ta, duniyar ta ta tunani.

      Ashe koshin wahala ta keyi, Ashe yaya em yana da matar sa, kila ma yar gaye wacce ta fita, domin hausawa suka ce babban goro ai sai magogin karfe.

     Musamman ta ga yanayin sa a lokacin da Amal ke kara masa wayar, yanayin sa na nuni da bai gane ko wacece Amal din ta hada sa da ita ba.

    Dukunkunewa tayi kan gado bayan sunyi sallama da Amal, ta rasa takamaiman abinda ke damun ta.

      Shin sanin yana da mata ko kuma disappointment na rashin gane ta da bai yi ba, encounters din su suka dawo mata Sabo, tana tuna yanda ya kira sunan ta.

    "Thank you INAYA" muryar sa tayi echoing a kwakwalwar ta, yanayin yanda ya yi addressing na ta kamar sun jima da sanin juna, Ashe ita kadai ce ke wahala da tunanin sa shi har ya manta da wata halitta inaya da ya hadu da ita a gidan iyayen sa.


      Karatun da ta daina ganewa ta tattare takardun ta ajiye gefe, har akayi kiran sallar magrib ta tashi ta fada toilet.

     Washegari a mugun latti ta tashi saboda baccin da ya ki daukar ta a Daren jiya, gashi bata gama karatun ba bare tayi revising da safe kamar yanda ta saba a duk lokacin da ta ke da test ko exam, kafin ta fita gida sai ta tabbata tayi revising kab abinda ta karanta, Idan ba haka ba sai tayi ta manta abinda ta san ta karanta amma Gashi ya bace mata saboda rashin revision.

    To a yau ko karatun bata gama ba bare revision wanda sai a mota ta danyi revising abinda ta karanta sama sama.

     Ko da ta iso har an fara shiga sai tace Mamman driver ya jira ta kawai ta zana test din ta fito tunda test din ne kadai ya shigo da ita school.


     Rai ba dadi ta fito bayan kammala test din kamar ta fasa kuka haka ta ke ji, ga questions ta sani, ta karanta amma answers sun kwanta mata, hawaye suka tarar mata a lokacin da ta ji  kowa na fadar saukin da test din tayi, amma ga ta one of the toppers na su a yau abinda ta tabuka a test din bai ta ka kara ya karya ba, tana da tabbacin idan bata dage a exam ba zatayi carrying course din.

      Dede na kitchen suna aikin abinci, jin motsin ta ya sanya ta lekowa tana fadin "ya ya test din"

Alhamdulillah ta amsa tana fadawa daki ba tare da ta amsa yaya karatun da Inna mai aikin su ke yi mata ba.


     Kan gado ta fada tana fashewa da kuka, kuka ba na jarabawar da ta kasa amsawa kawai ba, har da na mummunan labarin da ya riske ta jiya da yanda tunanin Emran ke neman hana ta nutsuwar ta har yana taba karatun ta.

    "Me ke damun ki Inaya" ta tambayi kanta yafi bila adadin yayin da kasan zuciyar ta ke amsa ta da "koshin wahala"


     Tuni fuskar ta kumbura idanun suka kada, bayi ta fada ta wanke fuskar ta tare da dauro alwala ta fito, sallar Zuhr tayi kana ta koma kan gado tana dukunkunewa.

     Inna tayi knocking tana turo kofar dakin 

"Matar manya Allah ya sa dai lafiya" inna ta tambaya ganin yau bata taya su aikin girki ba kamar yanda ta saba idan ta dawo ta tarar suna yi.

    Murmushi tayi marar armashi tana fadin "ba komai inna"

   "Tohhhh in kince haka, dama hajiya ce tace a dubo ki, ki zo" Inna ta fada ta juya tana bar mata dakin 

     

      Mikewa tayi jiki a sanyaye rike da wayar ta, kitchen ta wuce kai tsaye inda ta ke jin motsin su har lokacin.

   Dede ta kalli fuskar autar ta ta da ta dan tasa, cikin kulawa ta ke tambayar "lafiya inaya na gan ki haka"

   "Ba komai Dede" ta amsa

"Ba komai shine fuskar ki ta tasa haka alamar kuka, ke kalle ni nan lafiya" Dede ta sake tambaya a karo na biyu

    Hawaye suka kawo idon ta Tana fadin "test din mu ne Dede banyi abin kwarai ba yau" ta karashe tana dora kan ta a kafadun Dede

    "Ashsha Ashsha matar manya, ni na san ba lafiya ba" inna da ke yankar lettuce ta fada, ta kan kira ta da matar manya domin a cewar ta inayar kalar matan manya ce, bata yi kalar matan yara ko kananan mutane ba.


     Dede tace "in kin fadi gwaji sai kuka inaya, bayan akwai exam that you can cover up da shi, haba dai Auta, idan wani ya gan ki yanzu ai sai yace yarinyar goye ce"

    Siririn murmushi tayi Inna na Taya ta

 "ai yarinyar goye ma ba zata yi wata tabarar autar ta ki ba hajiya" inna ta fada

    "Su Farrah zasu shigo fa, mai kuka tanadar mu su" Dede ta fada

     Kamar tayi tsalle ta dira gaban Dede tana fadin "da gaske Dede, yaushe, shine Aunty halima bata gayamin ba"

     Dede tace "Chan tsakanin ku ne, nima dazu Abba ke gayamin yace a zo daukar su Airport gobe"

     Cikin tsokana tace "shi wa kenan Dede" sanin ko sama da kasa zata hade tsabar fulatanci Dede ba zata fadi sunan babban yayan su ba Murtala da ke zama Lagos da iyalin sa, yana aiki da NPA wato Nigerian port authority, matar shi daya halima da ya yan su uku, Yan biyu Farid da Farrah sai last born da yaci sunan kakan su Beldo wato Bello kenan a fulatance.


       Like, share and comment please馃槉

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.