Free chapter · Read without an account
Episode 2
by Zainab Musa Shehu · ALQAWARIN IYAYEH NE SILAR (PROMISE OF THE PARENT )
✍️✍️Writing.....✍️✍️
💍💍ALQAWARIN IYAYEH💍💍 (PROMISE OF THE PARENTS)
A mysterious,heart touching, romance and betrayal....
Anonymous pen....by Diamond lady
Episode————2
Auntyn ta kama hannunta tana dagota ta daura kanta a kafadarta tana dan shafa bayanta alamun tayi hakuri ta daina kwallan....,ta "kira sunan ta, Preesha"yanzu pa kikamun alqawari kuma har kin cigaba,kada ki zama mai karya alqawari mana,suna a haka ne wasu yan babies da baza su wuce shekaru 2 da Rabi ba mata,kyawawa ne sosai babies in,idan ka gansu kaman larabawa kaman Indiawa ba zaka tantance ba sbda kyawun yaran sosai,ga dressing na jikin su ya masu kyau sosai,kai in takaice maku duk haduwan kayan nan amma yaran su suka kara ma kayan kyau,suka rugo da gudu zuwa inda su ke suna ta dariya abinsu,d`an qaramin skirt ne iya cinyan yaran baby pink colour sai wata yar karaman riga bata kai cibiyan yaran ba white colour sai touch na baby pink ajiki da takalma da suka gaji da haduwa white colour suma rufaffu ne sai gashin su da aka kama shi gida biyu aka tupke wanda ya zubo gefen shoulders insu da headbands masu kyau da tsada suma baby pink ne da white a jikin su,suna ta gwarancin su gwanin shaawa suka tsaya agaban su ta juyo ta kallesu tayi murmushi ta duka tayi hugging nasu suma suna mata dariya sukayi hugging inta,yaran na daga cikin abinda take gani taji sanyi da qara hope a ranta cewa farin cikin ta zai dawo soon In Shaa Allah.Kasancewar magrib ta gabato ne ya sanya su tarkatawa su koma can cikin gidan nasu da bazaka taba cewa acikin Nigeria ka ke ba tsabar daula kayan alatun da aka shinfida ma gdn tundaga kan ginin har ta kayan cikin gidan abin kallo ne da shaawa da burgewa,ba kananun dukiya aka shinfida ma gdn ba.
Few years back.......
Wasu yan mata ne ke tafiya da alamun lectures suka gama suka pito za suje suyi sallah kafin su wuce gda.Tafe suke suna labari yanda lectures in nasu na yau ta kasance,suna tsinan lecturer da baida kirki sam,a haka har suka je inda aka ware domin yin sallah sbda musulmai kasancewar ba Nigeria bane,to babu masallatai kusa ballai ma kaji kiran sallah saidai ka duba time ka gani idan time yayi kayi sallah abin ka.suka shga sukayi alwala sukayi sallah su,suka pito domin wucewa gda.wata hadaddiyar numfasassar mota ce suka nupa,daya daga cikin yan matan ta latsa remote nan take motan tayi tsuwwa ta yi unlocking kanta aka juyo anata kallonsu kasan cewar wata sabuwar mota ce ba cikin wanda aka saba ganin su da su ba.Suna isa suka bude marfin motan suka shige ta yi ma motan key taja sukayi gaba cikin nutsuwa,suna cikin tafiya ne daya daga cikin yan matan biyu ta ce Preesha wai dan Allah mai yasa ba kya kula samarin da ke nemanki ne,ba kaman tsinan nan lecturer nan maybe da kina kula shi da mun samu sauki,wadda aka kira Preesha ta dan yi murmushi ta ce kema kinsan duk wannan abubuwan basa a gabana banajin zanyi wata soyayya yanzu duk bata time ne Ayusha,idan ma akwai wanda zan iya yin soyayya da shi kema kinsan bai wuce Yaya Mann ba,shi kuma wancan tsinan nan gantalallen ki kyaleshi Allah ya fi shi In Sha Allah babu abinda zai paru babu abinda zai iya mana.Ayusha tayi ajiyan zuciya tace to Ameen ya Allah,amma Preesh mai yasa kika ce Yaya Mann kawai, ga Yaya Aman ma ni nafi ganin kunfi dacewa ma da shi akan Yaya Mann, Preesha ta sauke ajiyar zuciya tayi wani murmushi ta ce "hmmm Ya Mann in dai kina ganin wannan Yaya Amann in, kaman wani monster bai da aiki sai pada da dambe da masifa" ni bana san shi bana iya zama da shi ma",shi kam Ya Mann ba ruwan shi so calm da shi,Ayusha tayi dariya ta ce to shikenan ma gani dai ai.. suna ta pira suka iso gda ko na ce mansions in su wanda da ka gani kasan wannan waje bana kananun hamshakan masu kudi bane tsabar tsaruwa da haduwa da sukayi, mansions in guda biyu ne amma iri daya komai kala daya ne,suka danna horn security suka bude musu gate in panka memen mansions in suka shige saida suka danyi tafiya kadan sannan suka qarasa gaban wani dan mini roundabout mai Zubar da ruwa gwanin shaawa water fountain kenan sannan suka zagaya suka tsaya wata qatuwar kofa ce da dan madaidacin Fili gaban kofan wanda ya sha ado da kayan gold da carpet wajen yayi kyau sosai,suka pito suka nupi kofan suka shiga ciki.....
Ku biyo ni domin jin yadda wannan tafiya zata kasance,nasan kuna so kuji mecece damuwan Preesha,wanene Mann wanene Amann sannan kuma mai ya paru har Preesha ta koma haka bayan dk wannan gata da jin dadi da su ke da...
Duk mai son mgn dani zai iya man mgn kaiyy tsaye ta wannan number...*** Whatsapp only