Free chapter · Read without an account
Chapter 13
💫 ƘAUNA DA KADDARA 💫
✍️Mrs Alkali
Page 1️⃣3️⃣
Da misalin karfe 8 30pm na dare Babban falo na cikin gidan AA Turaki. Kowa yana zaune – Hajja, Alhaji Abdullahi Turaki, AA Turaki da Ramlart. cike da natsuwa, suke zaune da alama akoi wata muhimmiyar taron da zasu gabatar, ganin yanda kowa ya natsu ya bawa zaman muhimmanci.
AA Turaki ya yi gyaran Murya,a lokaci guda yana kallon kowa da ke cikin falon, da idanun sa masu kaifin basira:
"Alhmdulillah, nagode da ku ka halarci wannan zaman .Yana da muhimmanci a san gaskiya, musamman idan lafiyar mahaifiya ta shiga hadari, yana da muhimmanci, a san waye yake da alhakin faruwar hakan."
Ramlart ce ta daure fuskar ta, hannunta na Wani irin rawa. Ta kama hijab dinta da karfi ta rike ,don boye damuwar ta. Hajja na kallonta,cike da mamakin ganin yanda yanayin ta ya sauya a lokaci guda, Alhaji Abdullahi ya zuba idanun sa cikin natsuwa, yana karewa kowa kalloh ,dan bakaramin mamaki ya shiga ba da aka sanar dashi cewa Hajja taci wani sinadari a cikin abinci, wanda hakan harya kaita ga kwanciya a asibiti, Dan haka ne ma ya sa shi ya dawo cikin gaggawa.
AA Turaki ya juyo da remote, dauke a hannunsa ya danna yana cewa:
"Ga wani abu da zan so kowa ya kalla..."
Ya kunna TV, ya buɗe CCTV footage na kitchen na sashin Hajja.
Kamar wutar lantarki ne ya d'auke a dakin – shiru ne ya ratsa ko ina. Ramlart ta saki wani ihu cikin firgici, ta kifa kanta a gwiwa tana rusa kuka.
cikin kuka tace:
"Wallahi... Sharrin shaidan ne... Na yi kuskure kuyafe mini!"
Cike da mamaki da radadin zuciya Hajja da take cikin shock din abunda idanwan ta suke gane mata tace:
"Ke ce? Ramlart... Me na miki har kika son kashe ni?" Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un.
Alhaji Abdullahi ne ya tashi tsaye, ya dube ta da idanu masu cike da rashin yarda, na yanda ramlart tayi disappointing nasa, yace.
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un... Me nake gani haka ".
AA Turaki ne ya natsu yana kallon mahaifinsa, cikin Wani irin murya yace.
"Ina son ka min izini in sake ta. Wannan ba matar aure bace... Ba zan iya ci gaba da zama da ita ba." Ya karasa maganar cikin zafin rai.
Hajja ce ta yunkuro tana share hawayen ta tace
"Ni dai dama, na zaci ta kirki ce shiya sa na zaɓa maka ita , sabi da na yaba da hankalin ta!amma a yau ba zan hana Ka sake ta, ba Yero i!"
Alhaji Turaki ne ya daga hannu, yace
"A'a... a dakata da yanke hukunci. Wannan lamarin sai mun tattauna da iyayenta. Ba a yanke hukunci cikin fushi. Zamu tuntubi magabatan ta, in rai ya baci bai kamata hankali ya gushe ba."
Alhaji Abdullahi cike da gargaɗi yace.
"Ramlart, abin da kika aikata babbar fitina ce. Amma tun da kin karbi laifinki zamu ci gaba da bincike. Ba zamu yanke miki hukunci a cikin fushi ba."
Hajja ce ta share hawayen ta, tare da cewa.
"Ramlartu kinbani mamaki , amma kisani ba zan sake yarda da ke cikin sauƙi ba."
*Ramlart ce ta rushe da kuka, ta rarrafa kusa da AA Turaki tana kokarin riƙe kafafun sa tace.
"Don Allah... kayi hakuri. Ka bani dama na gyara..."
Wani irin kallo AA Turaki ya jefa mata a lokaci guda ya miƙe, yana duban ta da tsananin bacin rai a fuskar sa Yace:
"Ba ni da damar yanke hukunci yanzu... Kamar yan da Baffah ya ce ba za'a yanke miki hukunci a cikin fishi ba, amma nasan daya – bana jin zan iya sake aminta da ke a karo na biyu."
Wani irin kuka mai karfi Ramlart ta saki .
A bazata suka ji saukan muryan AA Turaki "Hajja kuyi hakuri amma ina son ramlart ta bar gidan nan har zuwa lokacin da Baffah ya gama binciken sa".
Hajja da Alhaji Abdullahi Turaki suna gefe suna sauraron sa cikin mamaki da kulawa.
Ramlart ta saki hawayen nadama tana kokarin yin magana, amma bakinta ya kasa furta komai.
Cike da dottaku Alhaji Abdullahi Turaki yace.
"Ramlartu, ki karɓi maganar mijinki da zuciya mai kyau. Ki koma gida, ki nutsu. Ki bani Lokaci na gana da iyayen ki kamar yanda suka bamu amanar ki Insha Allahu za a miki hukunci bisa adalci".
Cikin kunar Zuciya Hajja tace.
"Alhaji da kayi hakuri ka bar yaronnan ya sauwake mata, karfa kamanta rayuwata taso ta salwantar".
Alhaji Abdullahi ne ya dagawa Hajja hannun alamar yagama yanke hukuncin sa.
Ramlart ce ta miƙe a hankali, kamar kazar da kwai ya fashe mata a ciki. juyawa tayi da kwalla a idonta, zuciyarta cike da rauni da mamakin irin wannan hukunci daga gidan da take tunanin tana da iko da shi, ta gama mallakar shi, shin tayaya ma tayi sakacin mantawa da cewa za'a iya samun CC camera a kitchen, haka ta ja kafafun ta ta wuce zuwa part din ta domin iban kayan ta da zata tafi da su, a gefe guda kowa zuciyar ta na cike da tsoro da fargaban abunda zata fad'awa iyayen ta.
💫 ƘAUNA DA KADDARA 💫
✍️Mrs Alkali
Page 1️⃣4️⃣
UNGUWAR WUSE II ABUJA
Gida ne mai dauke da ginshiƙai masu salo na zamani .
Alhaji Musa Ibrahim tsohon ma’aikacin gwamnati ne wanda yayi aiki har tsawon shekaru fiye da 30 a Ma'aikatar Harkokin Cikin Gida kafin yayi ritaya. Mutum ne mai gaskiya, rikon amana da tsananin tsoron Allah. Bayan ritayarsa ya koma harkar koyarwa a masallacin unguwa da hidimar al’umma.
Yana tare da matar sa Hajiya Rakiya, uwargidan Alhaji Musa, mace ce mai nutsuwa da kamun kai, ta taso da 'ya'yanta cikin tsantsar tarbiyyar addini da mutunci. Yaya biyu mata Allah ya azurta su da samu , Aunty hauwa da kuma autar ta ramlart,Ta kasance uwa ta gari, mai tausayi da hakuri, kullum cikin rokon Allah da yi wa 'ya'yanta fatan alheri. Tana da nutsuwa da girmama kowa da kowa, komai matsayinsa.
A yanzu aunty hauwa tana gida a gaban iyayen ta tare da ya'yan ta guda biyu, sakamakon mijin ta da Allah yayiwa rasuwa kimanin watanni biyar dasu ka wuce, aunty hauwa macece mai sanyin hali da tsaron Allah, Şaban'ın ramlart da tun tashin ta ta kasance mai tsiwa da son abun duniya, amma a tashi d'aya baza ka taba gane hakan ba sai ka zauna da ita na tsawon lokaci, babu irin nasiha da fad'a da ba a mata a gidan shiya sa ma take badda sawo tana zuba iya shegen ta batare da sanin iyayen ta ba ita da aminiyar ta zuly.
Misalin karfe 8 00am na safe a daidai lokacin da Ramlart ta iso gidan su da jaka a hannun ta. Fuskar ta cike da damuwa da tashin hankali, amma duddah hakan tana ƙoƙarin danne komai, bata son a fahimci hakan.
Hajiya Rakiya zaune take A babban falon gidan, mata ce mai kamala tana sanye da hijabi, hannun ta na rike da littafi tana karatun Qur’ani. Alhaji musa, dattijo mai kamala yana zaune a gefen ta yana karanta jaridan daily trust. Agefe guda wasu yara biyu ne da ke wasa a gefe, suna ta ya'n tsalle tsallen su.
Aunty Hauwa ce ta shigo daga kitchen tana ɗauke da tray, a hannun ta.
A daidai lokacin ne ramlart ta turo k'ofar falon bakin ta d'auke da sallama.
Aunty hauwa ce ta amsa mata tare da juyawa, ganin kanwar ta ne yasa ta saki wani murmurmushi tare dacewa.
"Laa! Ramlart! Masha Allah, sannu da zuwa." Kece a gidan yau .
Yaran ne suka tashi da murna suka rungume Ramlart suna ihun ganin ta tare da cewa.
"Aunty Ramlart! Aunty Ramlart!" Oyoyohh.
Mami dake karatun Qurani ne ta juyo jin irin ihun da yaran keyi na murnan ganin ramlart din, ganin ramlart da tayi da jakane yasa ta rufe littafin hannun ta tare da ajiye shi a gefen table d'in dake kusa da ita tace.
"Ramlart? Lafiya kike tafe da sassafe haka ba tare da sanarwa ba?"
Wani irin murmushin dole RAMLART ta ƙoƙarta ta kwakulo shi a fatar baki tace.
"Wallahi Mami, kawai na gaji ne da komai. Ina bukatar hutu. Zuciyata na bukatar natsuwa, shine nace barin zo na ganku."
Sai a lokacin ne Baba ya kalle ta sosai kafin yace
"Ramlart, akwai abinda ke damunki. Ki gaya mana gaskiya. Mun san halinki."mu muka haifeki.
RAMLART ce ta zauna a ƙasa, ta dora kai a gwiwar Mami tace .
"Baba, Mami… babu wani abu. Komai dai dai yake. Ku yarda da magana ta hutawa nazoyi."
Mami ce ta shafa bayanta, cikin hikima tace.
"Ko da wani abu ne, ki sani iyayenki muna tare dake. Amma kina buƙatar fadin gaskiya don samun mafita, sabi da haka in akoi damuwa kisanar da mu."
Wasu hawaye ne suka gan garo mata, RAMLART ta sa hannu ta ɗan share hawayen, tana kallon gefe, sabi da bata son su fahimta:
"Na sani Mami... Amma yanzu ba zan iya ba. Kawai ku yarda dani."
Ta karasa maganar cikin karfin hali yayin da zuciyarta ke cike da tsoro da nadama – amma har yanzu ba ta da ƙarfin fadin abinda ya faru, wa su baba , dan kuwa tasan kwanan zancen .
Da misalin karfe 9 30pm na dare , falon ya lafa da hayaniya. Baba da Mami sun wuce ɗaki, yaran Aunty hauwa suna bacci, a d'akin su.Aunty Hauwa tana zaune da Ramlart a cikin falo, suna kallon wani series.
Aunty Hauwa ne ta zuba mata ido, tana kallon fuskarta da ke nuna alamar damuwa da ƙin gaskata cewa komai lafiya yake kamar yadda tafad'awa iyayen nasu.
Cikin murya mai rauni, cike da tausayi, Aunty hauwa tace:
"Ramlart... Kince komai lafiya, amma ni ‘yar uwa ce gareki. Kina cikin wani irin hali... kuma duk duniya bayan iyayen mu ba wanda yake fahimtar ki sama dani, idan ba ki fad'a mini damuwar ki ba wazaki fad'a wa."
Ramlart ta ɗan ɗaga ido, ta ƙara sadda kai Ƙasa, tana wasa da yatsun hannunta.
"Wallahi Aunty... Ina jin Wani irin Abu a raina, amma bani da ƙarfin gaya muku komai."
Cikin nazarin ta Aunty hauwa tace .
"Toh ki saurari zuciyarki. Idan akwai wani abu da ke cutar da ke a ciki, wallahi bayan iyayen mu dani ‘yar uwar ki ba wanda zaki iya fad'awa damuwar ki. Duk abinda zai faru, kisani muna tare da ke . Amma kisani ita gaskiya zata iya fitar da ke daga cikin duhu."
Jin abun da Aunty hauwa ta fad'a ne yasa Ramlart ta fashe da kuka, Aunty Hauwa ta rungume ta. Sai da ta dan yi kuka sosai kafin ta lafa, ta na ta sauke ajiyar Zuciya.
Cikin sanyi murya RAMLART tace .
"Aunty... Na shiga uku. Na aikata abu da har yanzu ban yarda da kaina ba... Amma ina jin tsoro, bana son su baba susani, in sunji zasuyi fishi dani."
*(Aunty Hauwa ta dafa kanta, tana girgiza kai da tausayi.)*
Aunty hauwa ce ta dafa kafadar ta tace .
"Ina tare da ke, ko me kika aikata. Amma dole ne ki tunkari su baba da abin da kika aikata. Idan ba yanzu ba, gobe zai iya bayyana. Karki bari shaitan ya ci gaba da rinjayar ki a al amuran rayuwar ki."
Ramlart ta share hawayenta, tana jinjina kai, alamar ta gamsu da maganar Aunty hauwa
Baba ne zaune a gefen gadon sa Mami ne ke shafa masa man zafi a kafafun sa, sanye yake da farar jallabiya .Haske kadan ne a cikin ɗakin.
Cikin nitsuwa Mami tace "Baban ramlart ,kasan fa har yanzu Ramlart bata ce mana komai ba akan dalilin zuwanta gida,kuma bata taba kwatanta hakan ba."
Ajiyar Zuciya Baba ya sauke yace"Na lura da ita tun lokacin da ta zo. Da alama akwai abinda ke damunta amma tana boyewa."
Cikin nitsuwa Mami tace:
"Na tambaye ta cikin lallama, sai tace hutu kawai take bukata. Amma ni uwa ce, ina ji a zuciyata akwai wani abu fiye da hakan."
Baba da ke kallon Mami yace:
"In har akwai wata matsala tsakaninta da mijinta, zai fi kyau mu bar ta ta bayyana da kanta. Amma in hakan ya gagara, zan tuntub'i Alhaji Abdullahi Turki sai muji me ke tafiya."
Mami ce ta dan girgiza kai tace:
"Allah ya shiryeta. Ina fatan kar hakan da muke tsoro ne ya faru... kar dai zaman aurenta ya fara tangal-tangal."
"Bana son kisaka damuwar komai a ranki Duka rayuwar jarabawa ce. Amma , dole mu yi addu’a sosai akan yaran mu." Cewar baba dake Shirin kwanciya dan tagama shafa masa man zafin.
Mami ce tace "insha Allahu, Zan yi azumi gobe, in roki Allah ya warware mata komai. Koda akwai kuskuren ta, Allah ya gyara tsakaninsu, dan inaji ajiki na zuwan nata bana banza bane."
Hakan yana da kyau Allah ya kaimu goben cewar baba.