Free chapter · Read without an account

Episode 5

by Zainab Musa Shehu · ALQAWARIN IYAYEH NE SILAR (PROMISE OF THE PARENT )

✍️✍️Writing.....✍️✍️

‎

‎

‎

‎                   💍💍ALQAWARIN IYAYEH💍💍 (PROMISE OF THE PARENTS)

‎

‎

‎A mysterious,heart touching, romance and betrayal....

‎

‎

‎Anonymous pen....by Diamond lady

‎

‎

‎

‎Episode 5

‎

‎

‎Suka amsa ma Papa da Ameen suka tashi suka wuce dayan bangaren mansion in....

‎Suna shga suka samu daddy da Maa zaune suma a parlor,sukayi musu sallama suka amsa musu sannan suka shiga suka zauna suna musu sannu da gda sannan suka gaida su,suka amsa musu cikin kulawa, sannan suka tashi suka nupi bangaren su suna ta labarin su. Bangaren su Preesha ko tana can ta cika pamm kaman zata fashe tsaban takaicin abinda ya paru a dinning da suna dinner dazu,Ayusha ko na gefe tana ta dariya tana ce mata "haba ya isa haka mana Preesh meye haka ne",shi pa Ya Amann ba ruwan shi ni banga me yayi anan ba kece baki da gsky anan pa,ya zaki gaida daya baki gaida daya ba kuma kice bazaar miki mgn ba ai kema kinsan bata yiwuwa kawai ki gaida su gaba daya shikenan ba wanda zaya miki mgn akan bakiyi daidai ba, Preesha tace "to ai idan pa ma na gaida shi baya amsa man shyasa ni na daina gaida shi,"amma kinga dan mugun abu a gaban su Papa ya amsa  man kuma ni nasan da biyu yayi hakan sbda shi kada aga laifin shi idan bai amsa man ba,agaban su baya nuna komai amma idan mu kadai ne baki ga abinda yake man ba,mugun kawai Ayusha dai bata pasa dariyan ta ba dariyan ta take tayi tana cewa "ku dai ake ji, ni na rasa meyasa kuke haka samm ba kwa zama waje guda lfy sai kun saida hali" kaman makiyan da suka shekara saba'in da gaba kwata kwata ku ba kwa haduwa a zauna lfy,ni dai kinga kwanciya ta ma, goodnight,Ayusha tayi juyawanta ta kwanta.Preesha kam rai abace haka ta kwanta ranan sbda abinda Ya Amann yayi mata.washe gari wajen 7:30 na safe suka tashi suka para shirin tafiya School sbda suna da lecture in safe ta 9:00am haka suka gama shiryawa suka pito kasa sunyi kyau yau ma sosai kaman dai kullum,suna saukowa downstairs suka ga Mommah tana jera warmers a dining da masu aikin su a gefe, kasancewan Papa bayasan abincin masu aiki shyasa Mommah ke shiga kitchen da kanta masu aikin saidai kawai su dan kama mata abinda baa rasa ba ba su miko mata abu ko su kawo mata abu kaza haka dai har tayi aikinta ta gama,randa su Preesha ke gda kuma hada su ake shga kitchen tare sukeyin aikin da Mommah,suna iso wa dining in hugging Mommah sukayi suna ce mata "good morning Mommah" tace musu "morning an tashi lfy yaran Mommah tana shafa fuskokin su",suka amsa mata da fine Alhamdulillah tace tow "Maa Shaa Allah ku zauna kuyi breakfast sannan sai ku wuce" suka amsa mata da toww suka ja kujerun dining table in suna zama domin cin abincin, Irish ne soyayye da wainar kawai sai doya soyayya da kwai sai pepper soup na kaji ga kuma pepper soup na kifi sai ruwan zafi da kunun alkama da shinkafa daya hadu ya sha Madara fari tass da shi,suka zuba Irish in da pepper soup in kajin da kunun suna sha a hankali cikin natsuwa,suna ta cikin abincin su sai ga Papa ya pito shima don zuwa dining in yayi breakfast,yana isowa suka gaida shi ya amsa su sannan suka cigaba da cin abincin shima Mommah tayi "serving in shi ya para cin nashi,"can kawai kaman daga sama Preesha taji "Papa na ce ma Mommah "ina su Amann ne basu shgo ba"Mommah tace "aee basu shigo ba"yace ok a kira su mana naga Amann yana son kunun nan Mann ma haka, Mommah tace "to shikenan Papa yanzu kuwa ni ina ni ina bari yaran Papa basu sha kunun nan ba yau suna gari tana dariya tayi maganan," Papa "yace ahh tow yawwa gara a kira su dai"Mommah tace "su Preesha suje su kira su kafin time in pitan su yayi"Ayusha ta ce to Mommah"Preesha kam ai an ida kashe ta da bakin ciki tama rasa me zatayi kawai ta "tashi ta wuce Ayusha na binta a baya suka nupi dayan bangaren mansion in wanda idan baku manta ba nace "muku kala daya ne dana su Preesha komai da komai kawai kayan cikin ne suka dan bambamta sbda kowa da raayin colours na shi,"suna shiga Daddy da Maa suma "suna dining suna kokarin para breakfast"suka qarasa suka gaida su suka amsa musu sannan suka wuce bangaren su Mann.Suna isa Preesha ta toge bakin kofa taki karasawa ciki sukayi knocking, saida suka ba su umarnin shigowa,Ayusha ce "tayi sallama sannan ta shga parlon su tana gaida su suka "amsa mata cike da kulawa sannan tace "musu Papa ne yace "a kira su suzo yau anyi kunun da suke so cike da faraa da jin dadi Mann yace "aikam gamu nan zuwa yanzu dama munyi missing kunun nan sosai,"Mann ne yace "waye ne a bakin kofa yaga shadow a wajen"Ayusha tace "kaima dai Ya Mann kasan waye ne zaiyi hakan Preesha ce,Ya Mann yayi magana ya ce " Preesha come in mana mai yasa zaki tsaya anan wajen"duk sai taji kunya hakanan dai ta qarasa ciki tana sosa keya tace"Ya Mann good morning" ya amsa mata "morning Preesha how are you?" tace "I'm fine Alhamdulillah Ya Mann, yace "Maa Shaa Allah" sai kuma ta "juya ta maida kallonta kan Amann da kwata kwata basu yake kallo ba hankalin shi na wani wajen daban a zahiri idan ka kalle shi,amma kuma shi yana jin duk abinda sukeyi kawai sharewa yayi,ta ce "good morning Ya Amann" da farko bai kalleta ba kaman kuma bazaiyi magana ba,sai kuma ya wani juyo ya kalleta ya tabe baki yace "ki rike abinki yau kuma da kilbibin da kika zo kenan"taji wani bakin ciki ya tokare ta ita zai ma haka ma dan ya samu ta gaida shi tayi kwafa tace "da ni kake zancen wlh bashi ka ci", Ya Mann ne yace "haba Amann gaida ka pa tayi,Amann yace and sooo? Mann yace ka amsa ta mana wai ku yaushe dan Allah zaku daina wannan rashin jituwan ne? Amann yace "duk randa ta shirya ta bar wannan dan iskan rawan kai da  taurin kan nata ta dauki tarbiyan da ake mata"yarinya kullum sai shegen taurin kan tsiya",ita dai bata ce komai sbda tsoronsa da sukeyi saidai kawai hararan shi da takeyi kasa kasa,a cikin ranta kuma tace "wane taurin kai gareta dan Allah in ba munafuncin mutumin nan ba da ya sa mata Ido kawai baya so ya ganta tana walwala tana jin dadi....

‎

‎

‎

‎

‎

‎Ku biyo ni domin jin yadda wannan tafiya zata kasance,nasan kuna so kuji mecece damuwan Preesha,wanene Mann wanene Amann sannan kuma mai ya paru har Preesha ta koma haka bayan dk wannan gata da jin dadi da su ke da...

‎

‎

‎Duk mai son mgn dani zai iya man mgn kaiyy tsaye ta wannan number...***   Whatsapp only.

‎

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol