Free chapter · Read without an account

Page-34

by Aisha G Umar · “SANADIN ƘADDARATA”

*FASAHA WRITER'S ASSOCIATION*
     (*F.W.A)*©✍️
     ⭐⭐⭐

Ƙungiya masu aiki cikin salon hikima da fasaha gurin juya tunanin al-umma, kaifin alƙalumansu ya zarta takobi ©✍
___________________________________________________



بسم الله الرحمن الرحيم.
اللهم صلي وسلم على نبينا محمد. 




❁ 𝐒𝐀𝐍𝐀𝐃𝐈𝐍 Ƙ𝐀𝐃𝐃𝐀𝐑𝐀𝐓𝐀 ❁ 




Free book📓



By: _*🌹𝑍𝑎ℎ𝑟𝑎-𝑡𝑢𝑙-𝑄𝑎𝑙𝑎𝑚🖋️*_




Page3️⃣4️⃣





Wacece ke da ki ke son raɓar jikina?!" Ya faɗi cikin dakewa fiskarsa na yi mata kallon da ta kasa fassarawa, wani irin ƙara ya ziyarci zuciyarta saboda yadda maganar ya ratsa majiyarta.

"Mijina me ka ke faɗa ne? Me ya ke damunka? Wani laifi na aikata maka?" Sadiya ta faɗi cikin karyayyiyar murya, kawar da kansa ya yi gefe da alamu kalaman na ta sun ɗan shigeshi, amma kuma sai ya juya ya dubeta ya ce, "ina so gobe ki fitar da kayanki daga cikin ɗakin nan, Nusaiba tana son dawowa, ke kuma za ki koma inda ta ke yanzu, sannan za ki rinƙa yin girki kullum".

Kafin Faruq ya ƙarasa magana Nusaiba ta shigo tana wani ƙarewa ɗakin kallo cikin ƙyama, juyawa Faruq ya yi gunta, Sadiya kuma ba ra cire idonta kan Faruq ba, saboda tun da ya fara wancan maganar zuciyata ke harbawa

"Toh mu je ai ka gala sanar da ita ko?" Cewar Nusaiba tana murmushin gefen baki, da eh Faruq ya amsa ya juya yana ficewa, sai à sannan Sadiyata maida idonta kanta, tun da Nusaiban ta zo gidan ko sannu ba ta ce da ita ba, ganin ba ta kulata yasa Sadiya ma ba ta shiga sabgarta ba.

Nusaiba kuwa juyowa ta yi tana kallon Sadiya, kamar ba za ta ce komai ba, sai kuma ta ce, "am sunanki Sadiya ko? To don Allah Sadiya ayi mana abincin kari da wuri gobe, saboda ni dana tashi na ke neman abinci". Tana faɗi ta wuce.

Sadiya kuwa ƙasa ta sulale hawayen da ya cika mata ido tuni su ka fara zarya, kukanta ta ci ta ƙoshi sannan daga ƙarshe ta tashi ta koma kan gado ta kwanta. Washe gari aka yi musayan ɗaki kamar yadda Nusaiba ta nema, abun bai ba su Baaba haushi ba, saima daɗi da su ka ji.....

"Ku dakata ku dakata!" Faɗin Nusaiba wa su Badiyya da su ke ƙoƙarin shige mata ɗaki bayan Baaba ta fita yanzu, acewarsu sun zo kallon ɗaki da kuma taya ta murna ne. Bin ta da kallo kawai su ke yi domin kuwa gani su ka yi yanzu Baaba ta fita, kuma lafiya lau Nusaiban ta tarbeta, har da sunkui da kai, amma su za su shiga ta dakatar da su da ƙarfi kamar za ta rufe su da duka.

Nusaiba kuwa ƙare musu kallo ƙasa har sama ta yi ka na ta ce, "keh Fatima ina ku ke shirin shiga ne wai?" "Haba Anty Nusaiba, don kawai mun zo ganin ɗakinki ki ke mana rainin wayo? Haka jiya ma don mun zauna à gadonki ki ka yi mana rashin mutunci, to ke ba samu ma ki ka yi anzo wurinki ba, sai wani iyayi ki ke yi tun da ki ka shigo gidan nan!" Faɗin Fatima cikin haushi.

Badiyya ma ta ce, "eh wallahi, ita Sadiya har so take mu je gurinta, amma anty Nusaiba sai nunawa take kamar ba ta sanmu ba, ko da ace ba ki sanmu ba ai bai kamata ki ce mana haka ba" dariya Nusaiba takwashe da shi sai kuma ta tsaya ɗib kamar ba ita ta dara ba.

Ɗage yatsanta ta yi tana nunasu ta ce, "da alamu ku ƙananan 'yan iska ne ko? To bari ku ji! Ni ba shashashar can Sadiya ba ce, daga ku har ita zan iya juyawa yadda na ke so, ku shiga hankalinku da ni, ba na son sabgar karerere. Amma idan kuma faranta min rai ku ke son yi, to akwai kwanuka da dama nake son ba ita Sadiyar ta wanke min, amma tun da ku kunzo sai ku rage mata aiki" ta ƙarashe da sauke yatsar na ta, baƙin ciki a gurin Badiyya da Fatima ba a magana.

Tsaki Fatima ta ja sannan ta ce, "kin yi kaɗan ki samu aiki wallahi, ba ki isa ki zo gidan yayanmu ki ce za ki juya mu ba, ki tambayi Sadiya ta baki labarinmu! Ke don kin samu ma mun zo wurin ki?. Badiyya taho mu wuce" kafin su wuce Nusaiba ta sa hannunta biyu ta kamo rigarsu haɗi da janyosu baya da ƙarfi har sai da su ka kusa faɗuwa.

Sake su ta yi yayin da su kuma su ka juyo su na kallonta, wannan wani irin rainin wayo Nusaiba ke musu? Fatima ta yunƙura à zuciye za ta yi magana kawai sai ta dakata jin abun da Nusaiba ta ce, "ina za ku? Ba ku ji abun da na ce ba ne? Sai kun yi min wanke-wanke tukunna za ku fita!" "Cab ɗi jam, Nusaiba mu ki ke cewa ba zamu fita ba sai mun yi miki wanke-wanke? To ba za ai ba, ki yi abun da za ki yi, dama haka halinki ya ke ba mu sani ba?" Faɗin Fatima Badiyya kam gum ta yi da bakinta tana kallonsu yayin maganar kawai.

Nusaiba ta ce, "ai ba za ki tabbatar da halina ba sai nan gaba, ƙattan banza kawai kuna zaune ko mashinshini ba bu". Nan ma Fatima za ta yi magana kenan su ka ji sallamar shigowar Faruq, nan ta ke Nusaiba ta ɗaura hannu akai ta fara kukan munafurci, su Badiyya ba su gama gane manufar Nusaiba ba sai da Faruq ya taho da sauri yana tambayar me ya faru.

Nan Nusaiba ta ce da shi, "don na ce musu don Allah su wanke min kwanuka shine su ka yi ta min rashin kunya, har da mari na su ka yi", ba tare da sun ankara ko shaidawa Faruq gaskiya ba gaba ɗayansu ya kifa musu mari lafiyayyu a fiska, rai a ɓace ya ke cewa, "ko da ban aureta ba ba ta girmeku ba ne? To dole ku yi duk abun da ta baku umarni, kuna ji na?" juyawa su ka yi za su fice hannayensu kan kumatunsu hawaye ya ciko a idonsu, Faruq ya tsaidasu da cewa, "Idan ku ka sake ku ka fita ba tare da yi mata abun da ta ke so ba, sai na biku har inda ku ka je na lakaɗa muku shegen duka!".

Da jin haka su ka dakata haushi da takaici duk ya gama cikasu, amma yadda su ka ga Faruq ya sauya yanzu, to sun san fiye da haka ma zai aiwatar. Wucewa ɗaki ya yi, suna kallon Nusaiba ya yin da ta ke yi musu murmushin mugunta, ta naɗe hannayenta tana cewa, "ku shiga kitchen ku fitar da duk wani kwanukan da su ke ciki ku wanke su kun ji yaran ƙwarai?" Ta faɗi sannan ta juya ta shige ɗaki.

Sadiya duk tana jinsu amma ko fita inda su ke ba ta yi ba, domin à ganinta sun fi kusa tsakaninsu. Gaba ɗaya su Fatima su ka fitar da kwanukan da ke kitchen ɗin ga su da uban yawa, kuma ba wani datti garesu ba saboda Sadiya tana gyarawa, amma kuma Nusaiba ta ce musu duka, tasa kwanukan su ka yi a gaba suna kallo kamar su sa ihu.

Nan su ka fara yi sun ɗau lokaci akai duk sun bi sun gaji. Sai shiri su ke yi suna gamawa za su je su labartawa Baaba, Nusaiba ba za ta yi musu haka a banza ba. Da su ka kammala Nusaiba ta ce sai sun jere komai a mazauninsa, nan ma su ka cika kamar za su fashe saboda baƙin ciki, amma à haka su ka gama tun da Faruq ba fita ya yi ba.....

"Baaba wai sai na tsaya rantse miki ne? Na faɗa miki wallahi abun da Nusaiba ta yi mana kenan" faɗin Fatima bayan sun koma sashinsu suna. Tashi Baaba ta yi ta saɓi hijab ɗinta ta nufi gurin nusaiba, amma ko da ta shiga abun mamaki, sai Nusaiba ta sa kuka tana cewa Baaba, wai dama su Fatiman sun ce mata sai sun yi mata abun da su ka yiwa Sadiya, gashi sun je sun haɗata da ita..

Aikuwa Baaba ta amince da batunta, ta ba ta haƙuri sannan ta koma ta samu su Badiyya ta yi ta musu faɗa, tana cewa sun san cewa ita Sadiya ce ba ta so, amma akan me za su yiwa Nusaiba haka? Mamaki ne ya kashesu Fatima da jin haka, à lallai Nusaiba ta kere musu à fannin makirci. Gashi Lantana ba ta nan bare su sanar mata ita ta fahimcesu.

Sadiya ta cigaba da rayuwa a gidan Faruq a matsayin 'yar aikin Nusaiba, amma mai 'yanci saboda Nusaiba za ma ta ke da Sadiya kamar ba ta ma san da zamanta a gidan ba, ita dai kawai ta dafa mata abinci da sauran aikace-aikace. Sadiya ba ta shiga harkar Nusaiba ko kaɗan, sai addu'ar da ta sa agaba ba dare ba rana, tana cigaba da yin duk abun da Nusaiban ta ce mata tana buƙata, domin kuwa idan ma ba ta yi ba nan ne Nusaiban za ta sa Faruq ya zo yana yi mata masifa kamar zai bugeta.

Baaba kuwa kullum sai ta zo gurin Nusaiba ta duba ya take, ko za a samu labari mai daɗi, wato ko Nusaiba ta samu ciki, ita kuwa Nusaiba abun da Baabar ta ke mata ita ganin takurawa ta ke yi, don haka ta sanar da mahaifiyarta, Mairo ba ta tsaya sanya ba ta kwaso jiki ta zo gidan 'yarta, kamar abun arziƙi sashin Baaba ta biya kafin nan, su ka gaisa sosai har da ɗan taɓa hira, daga baya ta tashi ta ce bari ta leƙa Nusaiba.

Bayan Mairo ta isa gun Nusaiba su ka gaisa, daga nan su ka koma uwaɗɗaka, Nusaiba ta dubi Mairo ta ce, "Iya kamar yadda na ce miki, na gaji da wannan tsohuwar tana damuna, Baaba tana takura min da yawa, ko wani lokaci ta faɗo min ɗaki, ba ta bari na na sake yadda ya kamata, kuma kin ce min kada na yi mata wani rashin kunya inji shi bokan".

Sai da Mairo ta motsa bakinta sannan ta gyara zama tana duban 'yar na ta ta ce, "ba dai na ce ki kwantar da hankalinki ba? Ai kina sanar da ni a waya ban zauna ba, sai da na je na samo miki maganin matsalar, nima da kaina ba na so ki fiskanci takurawar uwar miji ba, in banda Talatu ina aje yin haka? Kin rinƙa takurawa suruka kenan?". Ta ƙarashe tare da ciro wata baƙar leda da ta ƙulle a bakin zaninta.

Ta cigaba da cewa, "kin ga na ƙulle à bakin zani ko? Haka bokan ya ce, wannan maganin da ki ke kallo sha yanzu magani yanzu ne, na musamman ne, ba a abinci za ki sa masa ba, sannan ba à ruwa ba, à ƙasan katifa za ki ijjeshi daidai gurin da ya ke kwanciya, da zarar kwana uku ya cika sai ki cire ki ƙona, da kin yi hakan kuwa ba wai Talatu mahaifiyarsa ba, ko waye ne bai isa ya juyashi ba, sai yadda ki ka cewa Faruq 'yata. Da zarar kin ce kar ya yi to fa babu uban da ya isa yasa shi ya yi, haka idan ki ka sa shi ba mai hanawa".

Nusaiba da ta tsaya tana sauraron maganar mahaifiyarta ta, cike da jin daɗi ta ce, Allah ya bar min ke Iya, indai kina nan to ban da matsala kuma" murmusawa Mairo ta yi ta ce, "ba za ki taɓa fiskantar wani wahala ba indai ina raye Nusaiba. To amma fa maganin ba haka kawai ya ke ba, akwai sharaɗi, kuma sharaɗin ba mai wahala ba ne, amma kuma mai wahala".

"Ina jinki Iya faɗa min" Faɗin Nusaiba, "ka da ki sake ko da wasa Faruq ya ji maganar, ina nufin kada ki bari ya ji magana ko kaɗan daga lamarin da mu ka yi masa". Sai da Nusaiba ta yi dariya domin kuwa ai wannan ba wani abun damuwa ba ne, ta ce. "Iya kenan to wannan ina wahala a ciki? Kada ki damu ba zan yi wannan saken ba". Haɗe idi su ka yi suna aikawa junansu kallon cika buri yazo......

HALIMA.

Zuba mata ido kawai ya ke yi ya ga ta shanye jus din, ita kuwa a ɗanɗanon farko ba ta ganewa test ɗin ba, amma ta kuma kaiwa na biyu, ana huɗu ne da sauri ta ijje cup akan table tana yamutsa fiska, cikin ɗan firgici S man ya ce, "ya dai? Ya ki ka ijje ba ki shanye ba?" "Ji na yi zuciyata na tashi, wannan lemon anya bai fara expire ba kuwa?" Ciki wayan cewa ya ce, "expire kuma? A ah ki dai daire ki sha zai yi miki amfani a jiki".

"A ah ni ya isheni, ina ganin babyn jikina baya son ɗanɗanon", S man bai so ba, amma gudun kadaya tsananta ta fiskanci wani abun, saboda ba lokacin ba ne yanzu. duk da haka ya ji daɗi tun da dai ta sha kaɗan, maganin kuwa ko yaya zai yi mata aiki. Matsowa ya yi kusa da Halima, hoton nan da ya ɗauka ya cire a aljihun wandonsa, "wannan wacece? A cikin akwatin nan na samu hoton" ya faɗi yana nuna mata. amsa ta yi don kallon hoton.

Wani irin jan tsaki ta yi ta kalli S man ta ce, "hoton Nuriyyah ne, kuma ina ganin Inna ba ta san da shi a ciki ba" S man kuwa cewa ya yi, "Nuriyyah kuma? Wacece ita à wurinki? Gyara zama Halima ta yi ta fara cewa, "yar mijin Inna da ya rasu ne", "tare da ita ku ke zaune dama? Amma ban taɓa ganinta ba", "da ne mu ke tare da ita, yanzu ban san inda ta ke ba, waya sani ma ko ta mutu". Jin jina kai kawai S man ya yi ba tare da ya sake ce mata komai ba. 

Har kwana biyu S man yana jiran jin aikin magani, amma shiru ba labari, ya riga da ya kammala duk abun da ya ke so, yau ya shirya tsaf don ya nunawa Halima asalinshi waye. Tana zaune ta ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya, ba ta ankara ba sai ji ta yi an watsa mata ruwa a fiska.

Firgigit ta juya aikuwa idonta akan S man da ya tsaya yana kallonta, share fiskanta ta yi da hannu ta miƙe tana kallonsa da sakin fiska ta ce, "my S man yau kuma wasa ka ke son mu yi?" Takowa ya yi har zuwa inda ta ke sannan ya ce, "ƙwarai kuwa babban wasa na ke son mu yi yau!" Halima ba ta fahimci yanayinsa ba, amma sai ta basar ta sake cewa, "to faɗa min daga ina zamu fara?" "Sai bayan kin bar gidan nan!".

Cikin rashin fahimta ta ce, "Ban gane ba S man" ba tare da ya yi magana ba ya haɗe fiskansa gam, wanda ya dawo kamar mugun da ya shahara, ya kama hannunta ya durfani ƙofar fita daga falo, bai tsaya ba sai da ya tsayar da ita a tsakiyar gidan, "ki fice daga gidan nan Halima!" Da tsananin mamaki Halima ta ke binsa da maga nanta, zuciyarta na bugawa bakinta na ɗan rawa ta ce, "ba... ban gane infice... daga gidan nan ba, kana cikin hankalinka kuwa S man?".

"Ke ce ba kya cikin hankalinki, da ki ka yarda da ni, kuma ki ka amince da zan iya yin rayuwa da ke!!" Cewar S man cikin tsawa fiskarsa babu annuri. Sumann tsaye Halima ta yi ta kasa buɗe baki bare wani harafi ya fito daga ciki.


Last page
___________________________________________________

Ah da kyau Nusaiba da su Fatima😁 

Ya ku ke ganin shirin Nusaiba zai kasance? Shin za ta yi nasarar kame Faruq haka? Hmm Baaba dai...

Ga kuma S man da Halima, tasha magani shiru, gashi yana shirin koranta, kuna ganin za ta tafi ɗin? Me tunaninku akai?


_*🌹𝑍𝑎ℎ𝑟𝑎-𝑡𝑢𝑙-𝑄𝑎𝑙𝑎𝑚🖋️*_

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.