Free chapter · Read without an account

ƊABI'A KO HALITTA 4

by Fatimaoumshaheed55 · ƊABI'A KO HALITTA

*ƊABI'A KO HALITTA*





Free book....




Shafi Na 4




Maman shaheed (Fatima Abubakar)


_Ango da Amarya_



Bayan fitar su hussy, su zakkiya suka fito da Amarya falo dan yi musu abin da ya tara su kamar yadda sameer ya buƙata, sa'ed ya buɗe taro da addu'a yayi nasiha, sameer ma ya ɗora da nashi, ƙawayen Amarya nata amsawa, a ƙarshe shadow ya rufe da addu'a baza kace shine mai tsokanar ango ba, an shiga fagen serious tongue, Har ƴa basu haƙuri da su zauna da juna da gaskia da Amana.

Aka shafa addu'a, sameer y ba ƙawayen Amarya kuɗin d ƴa hanasu ciniki a farko dan baya son wanan cinikin dan yasan ran abokin shi a kusa yake, ƙawayen amarya suka fice su uku dan an sami kuɗi zakkiya ma tama Amarya sallama ta bisu, sai haly da Jumana ta hana ta fita, ta ruƙunƙume ta, dole ta kamata ta kai ta ɗaki dan taji meye matsalar ta.

Suna shi ga, haleema tace "meye kuma?"

"Haly abun..." Jumana ta firta.

"ban gane ba, OK na fahimta ki nutsu ki dage da addu'a, Ina miki fatan komai yazo ƙarshe a yau...."

Da sauri Jumana ta girgiza, mata kai, Alama a'a.

"OK kin fison kita dakon...." bata bari haly ta faɗi abin da yake bakin ta ba, ta ce.
    "haly bazan iya ba ko da zan mutu kuwa, bazan iya ba wallahi"

Sosai ran haly y fara ɓaci tace "koda shine ya nema?"

Da sauri junana ta ɗago tana kallon ta cikin kaɗuwa ta ce "eh Bama ze nema ba na sani, nidai kawai a barni na mutu a haka kawai" ta fashe da kuka, da sauri haly ta toshe mata baki tana cewa.

     "ki rufa mana asiri kukan ki yayi yawa malama ni wallahi na gaji da baki baki sai na nuna miki fushi na tukunna haba duk kin gajiyar da ni a bikin nan y bazaki hango abin da ake hango miki ba, in wasu sun cutar da ke nima kina nufin zan ce kiyi abin da zaki cutu ne? "

Da sauri Jumana ta girgiza kai.

" to ki nutsu ki tsanan ta addu'a, kisa Allah a ranki kiyi bautar Aure, Allah baya haɗa maka biyu Kinji, nasan yadda kike ji Inaji ciwon a raina kema kin sani, Amman babu yadda zamuyi sai abin d Allah ya zaɓa mana"sai kuka ya ƙwace musu duk su biyun suka rungume juna suna tayi har zakkiya ta dawo, da Taimakon ta, ta samu ta raba su ta kama haleemah suka tafi.

Shima Ajmal har waje ya raka su sameer,yana fita yaga su hussy zasu shiga mota ya ƙarasa kusa da su, hassy tana ganin shi ta fara share hawayen da take ta adanawa, ashe ya ganta dan akwai haske kamar farin wata a ƙofar gidan, ya ƙarasa y kamata yace "meye kuma sis?" kai kawai ta girgiza mai alamar babu komai ta kasa magana, ya fahimci tausayin shi ne da murnar ya samu ƴanci yau, sai ya shafa kanta yace "ya isa kuje gida kuna isa ku kirani komai dare Kinji ko?" kai ta ɗaga mai alamar to. 

Shadow ƴa fito ya rungume shi suka rungumi juna, sai sameer yace "malam kar ka fara ka barshi ya tafi ya bar ƴar mutane dallah ita kaɗai" 

Shado ne ya bashi amsa d "ai kuma wasa y wuce kewar mutun ce ta fara addaba ta tun yanzu wallahi, sai da safe fatan Alkhairi da hak'uri da juna bro" ya shafa bayan Ajmal da ya tsaya kamar mai tuna wani abu. 

Sa'ed yace, "na ajiye ma ledojin a gefen dining, please Kayi abun d ya dace ko duka be samu ba dan Allah Kar mu ta abu ɗaya" kai kawai ya ɗaga musu, suka ɗaga mai hannu, suka tafi ya shige gida, har yayi gaba, sai ya dawo da baya ya ma gidan addu 'a ya tofe ko ina. 

Sosai yake mamakin Wai da gaske dai an mai aure, ya jima kafin ya shiga falon, ganin bata falon, sai hakan ya mai daɗi. 

Ko ina ya kama kallo a falon a zahiri ba kayan alatun yake kallo ko tsaruwar falon ba, neman Inda zega toilet yake ɗan sameer da sa'ed ma sun fi shi sanin kan gidan, dan shi yau shine zuwan shi na farko kamar yadda ƴan kawo amarya suka kawo ta, shima sai da aka kawo shi yau, haka itama ɓangaren Amaryar. 


Can y hango wani ɗakin da in be manta ba sameer yace a ciki kayan shi yake, sai kuma yaga toilet ɗin falon, Sai yaji bari ya shiga ɗakin dan gabatar da sallah isha. 

Yana shiga ya shaƙi wani ƙamshin turaren wuta ɗana jiki mai daɗi dan nan aka fara kai amaryar sai da haleemah ta zo tace ai ba nan bane ɗakin ta suka mai da ita nata suka turare nan din suku kulle, 

Sosai ya shiga cikin wani matsananci yanayi na shaƙar ƙamshin ban, dan sai da ya jingina da ƙofar ɗakin ya samu ya ɗan seta kan shi. 

Ganin hakan baze mai ba ya faɗa bathroom ɗin, Daga alwala besan lokacin da ya bige da wanka ba, sanan ya ɗora da alwalar ya fito ya ga akwatin shi ya duba jallabiyar da sameer ya siyo mai guda 6 ya zari ɗaya ya saka, ya nemi salaya sabuwa itama a cikin kayan shi da ya kasance duk aikin sameer ne, ya tada sallah, yana idarwa ya jima yana addu'a har da hawaye kafin ya faɗa dogon tunani da son sanin ina ya dosa da sabuwar rayuwar shi kuma. 


     _jumana_
Sosai taci kuka ta gode ma Allah, taga babu sarki sai Allah, ta tashi ta fara dube duben inda zata ga bathroom, tana ganin shi ta faɗa tayi alwala ta fito dan yin sallah da kai kukan ta wajen mai duka. 

Tana idar da sallah ta dinga addu'a tana hawaye da jerama Allah ikirari da ya kawo mata agaji a cikin rayuwar ta, koda ta idar a wajen ta zauna ranta fal tunanin wa aka aura mata, ya zatayi da matsalar ta da take ciki? Ko ze karɓi aure? To in y karɓa ma ai ita bata karɓa ba, kawai dai zatayi zaman wani lokaci ne kafin taji kutsarin iya firta Bata son Auren a zahiri ga hajiya da kawu Labaran... 

Duk yadda taso cire komai a ranta ta kasa, gashi ko yunwa bata ji rabon ta da abinci tun rana da sukaci tare da haleemah. 

Wata jaka ta ɗauko ta fara duba abin da yake ciki, ganin kayan gyara ne a ciki ta buga tsaki ta tura shi gefe, cikin ranta tana cewa" dama ya lafiyar kura bare taci ɗan mutum hakan ma a rabu ƙalau, yadda kuka kawo haka za kuzo ku ɗauke shirmen KU.... "


Ganin bata da mafita sai kawai ta kunna karatun Al_Qur'ani a wayar ta tasa suratun baƙra Audio Ko Zata samu sassauci zata fara gwada shawarar ƴan uwan maman ta da su zakkiya ta gani dan a baya duk yadda taso da jin karatun ƙur'ani sai kasala da wani abu su rufe ta ko su mantar da ita, yau ko tana tuna hakan taji ta saka har tana saurara. 


     _Ajmal_

Wayar shi ce ta kama ringing da kamar baze duba me kiran ba sai ya duba yana ganin number ummah yayi ajiyar zuciya ya ɗaga da girmamawa, sai yaji muryar safna. 

"hello yaya Ango mun dawo gida fa tun ɗazu waya ta ne babu kati, kuma ummha tace dan Allah ka samu kaci wani abu, ya sameer yace mata baka ci komai ba tun rana, kuma tace ka kula da ƴar mu........" be bari ta firta abin da zata ce ba yayi saurin tsai da ita. 

" OK, Naji, sai da safe mai surutu"ya kashe wayar y fara kallon haɗaɗen gadon da aka saka a ɗakin da yake amsa sunan nashi, gashi gadon y sa me shi b a cikin nishaɗi da farin ciki ba, har ji yayi gara ɗakin shi da katifar shi so dubu da haɗaɗen ɗakin da yake ciki a yanzu. 

Sosai ya fara tambayar kan shi me ya dace yayi a yanzu ne, sai y tuna da saƙon ummah, yace "dole na miki biyayya kin wuce Kice nayi abu naƙiyi indai har zan iya. 

Falo ya koma ya fara duba ledar da su sameer suka ce sun ajiye mai, a dining area... 

Wani irin faɗuwar gaba yaji a tare da shi, sakamakon ƙamshin turaren ta da ya kawo mai gulmar ta fito... 

Ita ma jin maƙogaron ta ya bushe tace bari ko ruwa ne ta nema ta sha sai ta kwanta tunda kowannen su yasan haɗa su akayi babu wanda ya taɓa ganin kowa dan haka basuyi mamakin rashin gaɗuwar su ba, ta fito daga gefen dining ɗin tana rufe fridge, shi Kuma ya ɗau ledar ze buɗe suka kusan cin karo da juna, atake wani mugun magana ɗisun saƙo ya ziyarci kowannen su, shi kam sai da ya runtse idon shi ma, itama ƙafar ta sai da ta mata nauyi.... 

Ajmal besan lokacin da ya miƙa mata ladar da take hanun shi ba ba tare da ya buɗe ba, burin shi ta wuce ta bar kusan tar shi, itama da sauri ta karɓa tayi gama kamar wacce taga wani mugun abu, yana jin ta rufo ɗakin yayi kyakyawan ajiyar zuciya, ya bude ledar yaga ashe Leda biyu sameer yayi kowacce Leda kaza da lemu ne acikin kamar yasan za'ayi haka. 

Yana ɗauka ya koma ɗaki ya murza ki itama ta murza key,ta koma tana ta ajiyar zuciya, ta bude ledar taga lemu da kaza bayan tasha ruwan ta ɗan sha lemun ta ajiye ta koma bathroom ta watsa ruwa ta zo ta canja kaya ta haye gado tayi addu'a, tana ta sauraron karatun har bacci ya ɗauke ta. 


 Ajmal ma ganin babu abin da zeci a gidan da yake ji kamar ba nashi ba ya samu ya ɗan ci kazar yana turawa kamar magani, ya haɗa da lemun badan yana jin daɗin su ba ya haye gado yana ta murƙususu....... 



_Hajiyar shagali_
"suhail wallahi idan ka sake kaje gidan Jumana wallahi sai ka haɗu da ɓacin rai na, dan naga baka da hankali, kuma jibi zaka bar garin nan ka komai Abuja, ban yadda ka sake zuwa ba sai da izinina" hajiya Uwar Amarya ta firta ga tilon ɗan da ta haifa. 

"yanzu mum kina nufin ko na gama karatu wai acan zan cigaba da zama?" suhail y tambaya 

"eh haka nake nufi" ta firta mai. 

"to saboda me ba akan kula jumana bane ko tausayin ta da nake yi kika ɗauke ni daga gidan ba ko Ince garin ma gaba ɗaya, to ai tabar gidan kuma na kusa kammala karatu na" y bata amsa. 

Sosai tayi mamakin kalaman shi Bata taɓa tunanin ze iya firta Mata yasan gudun da take yi ba, ashe yana ankare da komai? Lalai suhail ya fara girma, Amman a fili sai ta kawai da mamakin tace "ni bance maka haka ba in kuma titsiye ni kage to naji duka Sai na amsa maka, kuma haka na baka umarni ka ci gaba da zama a can, ana maka gata baka gani, ga Abuja, wayake ta wani kano?" 


"a hakan nake son Kano ai gari ba Kano ba dajin Allah ga mahaifa ta wayake ta kalan dangi" ya bata amsa ya tashi ya tafi fuuuuu. 

Tana ta kiran shi be ko saurare ta ba, anan ta fara tunanin lalai suhail ya balaga ya balage tasan me zatayi Kafin yafi ƙarfin ta dan bazata zuba mai ido ba. 





_mommah da ummah_
"Hassan ya kuka ga yadda yayan ku ya ƙarɓi Amaryar sa, kuna ganin baze bani matsala ba?" 

Mommah ta jefo ma su hussy tambayar da basu tsamace ta ba, dake suna da wayo, kuma basu san abin da ze ba yayan su matsala da sauri hassana tace "ai lafiya lau muka ɓaro shi har abokai suka kawo shi aka watse aka barsu, ya rako mu har mota ma, da alamun fa in sha Allahu....." 

"ya isa haka...." mommah ta dakatar da ita a hassale kamar ba ita taso taji yada akayi ba. Wani kallo hussy da hassy suka ma junan su, suka sulale suka gudu ɗaki suna ma yayan su addu'a samun sauƙi a wajen mommah.





***

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.