Free chapter · Read without an account
ƊABI'A KO HALITTA 5
*ƊABI'A KO HALITTA*
Free book...
Shafi Na 5
Maman shaheed (Fatima Abubakar)
_Ajmal & jumana_
Washe gari ango da Amarya kowa ya tashi ya gabatar da sallah a makare kowanne ya tashi, dan shi Ajmal rasa maka ma yayi dan besan inda masallaci yake bane da a masallaci zeje yayi sallah, Amman yace dole anjima ya fita ya duba yanayin unguwar.
Jumana ma amakaran ta tashi tayi sallah, ta shiga aikin tunanin makomar Auren ta da irin rayuwar da zasuyi da wanan bawan Allah da suka kasa kallon juna.
Bayan Ajmal y fito daga wanka ya shirya, ya cigaba da zaman ɗaki, da yaji alamun yunwa ya ɗauko ragowar kazar shi ya cinye ya kora da ruwa da lemu dan yasan babu t inda ze samu abin kari.
Jumana ma hakan take, a tunanin ta inta sarrafa wani abun ma ba lalai yaci ba kuma ita dan dai cikin ta ko haka zata iya zama, sai d taji azabar ƙugin da cikin ta yake ta rasa yadda zatayi gashi da abu mai zafi ta saba karyawa irin su tea Ko kunu first Kafin taci Komai, ledar kazar ta ɗauko ta bude taga bazata iya ci ba dama da zafi ne, sai ta ajiye ta koma ta kwanta tana ta lissafin dokin Rano, Ganin yunwar ba ƙanwar uwata bace basu haɗa dangi na kusa ko na nesa ba gashi yunwa bata san taurin kai ba dole ta sakko ta fara shirin leƙa falo don ta lalubo kitchen taga me Zata iya sarafawa.
Da sanɗa ta buɗe ƙofar, yaji buɗe ƙofar ta Sai yayi wani guntun tsakanin yana ganin duk an cuce su ita a takure shima a takure.
Ko da ta fara dube dube ta hango kitchen a gefen dining da saɗan ta tafi ta ɓuɗe ta shiga tana sauke ajiyar zuciya kamar mara gaskia.
Gas ta fara kunawa taga Anyi refilling ɗin Shi ajiyar zuciya ta sauke, ta samo bottle Wata ta kunna gas ɗin ta juye a ƙaramar nonstick pot ta ɗora a wuta ta nemo kofi tana jira yayi zafi ta juye, sai ta hango oven tayi tunanin gasa kazar ta, ta tafi ta ɗauko ta zo ta kunna tasa kazar dan ta dumama, sosai kitchen ɗin ta ƴa haɗu Amman ba shine a gaban ta ba ko bi ta kayan da aka loda a kitchen ɗin batayi ba burin ta ma ta bar kitchen ɗin.
Bayan ta juye ruwan zafin a cup Sai ta fara zare ido tana neman kayan shayi kamar ta ajiye, ta dinga lalube bata gani ba ranta kawai sai taji ya ɓaci, har ta haƙura ta ɗauki kazar Zata tafi, sai taga Leda da abu aciki akan dining, Sai taji zuciyar ta na mata umarnin ta ɓuɗe daga meye aciki, har zata ƙi bin umarnin zuciyar Sai da ta buɗe, tana buɗewa tayi e eyes da gwangwanin millo batasan lokacin da murmushin ganin mutumin ya kubce Mata ba, ba tare da ta sani ba, dan tun da aka fara bikin ta shine murmushin ta na farko ganin kayan shayi, bata tsaya wata wata ba ta suri ledar kamar Tata takai ɗaki ta ajiye da kazar hanun ta, ta dawo ta sake ɗaukan ruwan zafin ta, ta fice a kitchen, ta tafi ɗaki ta murza key ta baje a ƙasa ta fara haɗa tea Jikin ta Har rawa yake dake tana da Ulcer, dan sai da ta fara Afa madarar ma tunda Bata da magani a kusa dan kamar Ulcer nason tashi ma dan taji yunwa ba kaɗan ba.
Ajmal Najin ta koma shima ya fito, ya ɗauki ruwa har ce wuce ya leƙa kitchen Yana tunanin Uwar me zeyi ma a kitchen ɗin, makulin Gidan ya ɗauka da Sameer ya bashi dama a falo ya ajiye bayan y kulle gidan jiya, fita yayi y buɗe yace bari ya zaga yaga inda masalin unguwar yake ko ze samu sanyi ya ratsa shi in y bar gidan ma.
Jumana kuwa sai da ta ƙoshi sanan ta maida kayan gefe, ta koma kogin tunani kuma, tana cikin haka taji saƙo ya shigo wayar ta, da kamar bazata kula ba sai ta ɗauko, ta duba taga haly ce ta turo mata da saƙon
"ƙawata base na Kira Ki ba kema bance ki kira ni ba da sanyin safiyar nan, na miki saƙon nan ne kawai don Naji kin kwana, lafiya, ko kin kirani ma bazan ɗauka ba, Amman anjima ko gobe zanzo, Ina muku fatan Alkhairi keda mijin Ki" shine abin da ta rubuta mata.
Sosai ta sake murmushi gami da ajiyar zuciya a karo na biyu, sai taji kalmar miji ta tsaya mata a rai.
Tasan ko ta kira haly ba ɗagawan zatayi ba tunda tace bazata ɗagan ba, dan haka batayi yunƙurin kiran ta ba.
Ajmal sosai ya zazagaya unguwar har sun gaisa da wani maƙocin su, yake tambayar sa badai shine ango gidan ba, Ajmal ba dan yaso ba ya amsa mai da shine, dan mutumin akwai surutu shi ya ɗan ja Ajmal ɗin ma da hira har ya ɗan jima a wajen, Amman kuma ta wani gefe yaji daɗin surutun mutumin Dan ya nuna mai masallatan unguwar har guda biyu da kantunan unguwar saboda siyaya Sai surutun da be tambaye shi ba, kaf sai da ya mai bayanin maƙotan su har da sana'ar da kowa yake yi da iya adadin da matan da kowannen su yake aure, banda yaran gida shima dan Ajmal ya dakatar da shi, ne, ƙarshe yaso sanin sana'ar Ajmal ɗin, ataƙai ce yace mai shi ƙaramin ɗan Kasuwa ne, sukayi canjen number da maƙocin ya nema, Ajmal ya bashi second number shi da be fiye amfani da ita ba dan baya son damuwa, Yamai sallama suka rabu, har yana Agaida Amarya, Ajmal Ko amsa mai beyi ba ya shige gida.
Tun dawowan shi gidan yake ƙare ma gidan kallo, babu laifi gida yayi komai ya ƙawata gidan babu wanda ze kushe har da filawowi da parking space ɗin da mota biyu zasu iya tsayawa ga shi gidan na ɗauke da 3 toilets Ne 3 bedrooms one parlor Sai dining area, Ko hasidin iza hasada yasan Gidan ya wuce a kushe, Amman babu yabo babu fallasa Ajmal yake bin gidan da kallo har ya shiga falon ya koma ɗakin shi yana tunanin meye makomar shi da yarinyar nan ne wai ya suke so yayi ne mommah da iyayen yarinyar?
Rasa amsar da zeba kan shi yayi dole ya ɗauki wayar shi ya kunna data ya fara ganin saƙonin da abokanai da ƴan uwa suke ta mai Allah ya sanya Alkhairi, da godiya da Amin ya dinga bin su.
Daga baya sukayi waya da Sameer, akan ze fita kasuwa Sameer na ta hanashi, Wai uwar me zeyi a gidan in ya zauna, har suka kusan faɗa ma, Sameer ƴa kashe wayar shi.
Har rana ta farayi Ango da Amarya ana wasan ɓuya, suna zaman ɗaki, Jumana kuwa sai da ta gaji ta kira haleema ta dinga mata magiya shine ta amince tace zata zo to, dan babu wanda yazo anan ta sake gane cewa lalai bata da gata sai daga wajen Allah, bayan haleema tazo tana ta bugu jumana bata ji ba sai Ajmal ne ya fita yana tsaki yaje ya buɗe mata, suna ganin juna, kowa ya tsaya na yana ma ɗan uwan shi sannu, ya bata hanya ta wuce tana gaishe shi, tana tambayar shi Amarya yace tana ciki amai makon yace tana lafiya.
A kusan tare suka shiga falon, ya wuce ɗakin shi ta wuce na jumana, yana jin yadda jumana ta rungume ta tana murnar ganin ta daga baya ta rushe da kuka haleema na rarashin ta. Ajmal ya taɓe baki yana kukan daɗi kike ni dama zanyi kukan da ba kwaɗo ba inji gaya.
"baby meye kuma na kuka nifa indai haka zaki dinga yi wlh sai na dena zuwa dan bazan dinga zuwa ina sama mijin ki amaryar shi kuka ba" dake tun suna school d baby suke kiranta sunan d Dady ta yake kiranta da shi tayi ta shagwaɓa.
"miji Hmmm ke kika ga wani miji, ni wallahi da ina da hali yanzu tare zamu bar gidan nan" jumana ta furta tana turo baki.
"ke asiri kike son tona ma kanki? Kar ki ƙara maimaitawa, Aure fa ba abin wasa bane, kiyi haƙuri baby da sannu komai ze zama tarihi in sha Allah," ta furta tana shafa mata baya, alamar rarashi.
Sosai haleema tafi jumana Wayo sakamakon suna da banbancin reno, ita haleema a tsayayye gida ta taso kuma na masu ƙaramin ƙarfi kuma ta taso cikin yayu da ƙanne, ita ko jumana a gaban mahaifin da da mahaifiyar ta a sangarce da gata ta taso duk da mahaifiyar ta na ƙoƙarin seta ta da ganin tayi mata tarbiyar tsayayya da ɗanka ze iya rayuwa a duk halin da ya tsinci kanshi, dadyn ta ne yake shagwaɓa ta, dalilin da yasa hakan duk ya ja mata shiga wani taskun rayuwar bayan barin mahaifan ta duniya riƙon ta ya koma hanun mum/hajiya, ƙawayen ta kuma su kira da da hajiyan shagali...
"yanzu dai meye matsalar gaya min, Wai ma kinyi breakfast kin ba mijin Ki?" haly ta wurgo mata tambaya.
Amsa mata tayi da "breakfast Kuma? Tab! Mutum da bama yaso mu haɗu, ke Nifa kowa ta kanshi yake tun jiya da kuka garƙamemu gida ɗaya, bance mai ba be ce min ba, ke ni badan badan ba ma mu ta zama a hakan"
"kai wai kina nufin ko gaisa wa ba kuyi ba, Naji ajiya shi ya kamata ya fara nemann ki da be nemeki ba be kamata ki neme shi ba yau kuma ke ya kamata ki gaishe shi ki bashi abin da zeci ko da bazeci ba kin fita, dan akwai abokin shi Sameer da Ko sa'ed Ne suna da kirki wallah ya nuna min kayan tea da su indomei Har da su ƙwai da ya kawo dan ni na adana miki ma a kitchen da hannu na kinƙi nutsuwa ne jiya Sam har na tafi bamuyi maganar ba" Halima ta faɗa.
"to ai ni dai...."
Haleem ta katse ta "ke me? Ni fa baby in da bamu sami matsala da ke ba yanzu ne zamu samu, saboda ina gano miki ƴanci da kika samu ke kuma baki gano ma kanki, and Ko babu komai nan gidan d kike ɗaukan mijin ki kamar maƙiyin ki yafi zama da hajjaju, ki faɗi tsakani da Allah?"
" umm eh nima na sani, but..... "
" but what? Ki fara mu'amalantan shi kafin ki yanke mai hukunci, kin san dai babu yadda za'ayi ya zama wicked Kamar wanan mamar taki....."sai kuma haleema ta dafe goshi.
" eh da hakan ze kasance zanfi farin ciki, Amman fa ba'a gane maci tuwo Sai miya ya ƙare, taya zan fahimce shi ya rufe duk ƙofar da zan gane hakan? Halee"
"baki so bane Ai da kin samu, ni wlh da inada yadda zanyi da nasa ya dawo dake hayyacin ki Ko ta hanyar......" sai Halee ta yi shiru ta kasa ƙarasa wa.
"ƙarasa ko ta hanyar ya min fyaɗe ko shine abin da kike son cewa? To wai dan Kinga ina yawan ce miki ina Jina cikin wani yanayi na buƙatuwar..... " haleema bata Bari ta ƙarasa ba ta rufe mata baki.
" ya isa ba haka nake nufi ba mubar zancen kafin ki fara min kuka, yanzu tashi muje kitchen mijinki yaci girgin Ki kai ko baze ci ba ai baze ce ba a bashi ba" har jumana zatayi gardama Halee ta girgiza mata kai, ta kamo ta badan ranta naso ba, ta nufi kitchen da ita.
***