Free chapter · Read without an account
8
SHIN SO DAYA NE?
Hafnancy...
Zazzafar soyayya, Cin amana, mugunta da kuma Sadaukarwa
#Free Book#
8.
Tafe muke cikin motar babu mai cewa juna kala har muka karasa fitowa daga cikin unguwar, sannu ahankali muka haye saman titi. Ya soma tuki cikin kwarewa ayayin da yake ta k'akk'aucewa ababen hawa.
"Ina kakai driver dinmu? "
Na sami kaina da k'awar da dogon silent dinmu ta hanyar jefo masa wannan tambayar.
Murmushin takaici naga yayi gami da fad'in"Zahrata Kenan...I can see that u don't trust me at all, direbanku na dakin mai gadinmu yana dan hutawa... "
Cikin yanayin damuwa nace"Toh idan ya fito yana nemana fa? Or lemme even say idan yaga dawowata dakai ah mota fah?....wani irin fassara kake tunanin zaiyi agame da fitar tawa dakai?"
Ganin baida niyyar cewa komai ya sanyani fadin"Mubeen pls speak out for Allah's sake.... "
"Don Allah Fadima can u atleast for once have sum rest of mind?.... Pls stop behaving lyk a kid... tun tasowarmu kike ta jefo min sum silly silly questions which shows that u don't trust me at all sai kace saceki zanyi?"
“Waya sani ko sacenin kake shirin yi?"
Na fadi hakan cikin tsananin b'acin rai.
Gani nayi yaci wani wawan birki don kadan ya rage ya bugi bayan wani mota adalilin furucin daya ji nayi.
Cikin tsananin b'acin rai naji yace"Fadima can u see what u almost tried to caused?.... Bana jin d'ad'in yadda baki bani trust bah at all... Shikenan since u don't have trust for me mu koma gida....... "
Yadda yayi maganar hakik'a ya matuk'ar bani tausayi,don haka da sauri nace"No, Mubeen d'ina am really sorry forgive me bazan k'ara bah... abinda yasa kaga ina haka its becuz of wat I encountered with ur family today....... "
Na danyi shiru can na cigaba"Mommy? Daddy? K'awar mominki? A friend from Zaria? Hanan and Jasmine?...... I nid sincere answers and explanations of this with immediate effect.... "
A kasalance naji ya furta"Its alright gimbiyata lemme find sumwhere to park... "
Sai alokacin na lura ashe har mun kai inda yake son muje.d'ago kaina nayi na zubawa wani Signboard idanuwa tare da karanta abinda aka rubuta ajikinsa. 'Grand square'
Adaidai lokacin ya k'arasa parking awurin parking lot na wurin.
Yace"Baby bismillah fito muje.. "
Atare muka fito, na soma kallon wurin kamar wata 'yar k'auye don hakik'a wurin yai min k'yau sosai Wanda har na kasa hakuri nace"Ina ne kuma nan? "
Murmushi yayi tare da fadin"'yar k'auye nan shine ake K'ira da 'Grand square'... Akwai supermarket da 'ice-cream joint' da dai sauransu.... So yanzu muje bangaren 'ice-cream joint'. "
Muka jera muna tafiya kamar wasu ma'aurata, mutanen wajen sai kallonmu ake don nasan mun matuk'ar birgesu. Kallon sararin samaniya nayi naga yadda ya had'e rai.
Atsorace nace"Mubeen had'ari faah kuma wallahi inason ace atleast zuwa karfe d'aya mun kama hanya.... "
Lak'atar hancina naga yayi wanda nake tunanin habit d'insa ne na yiwa mutum hakan,yace"Matsoraciya ruwa bazai sauko bah yanzu insha Allah... Kuma its juz five minutes after 12,and nace miki we ain't gonna spent more than 30mins here so kafin 1pm mun koma gida sai ku kama hanya.... Is dat taken matsoraciyata? "
"Uhmmm" kawai na iya cewa har muka shiga 'ice-cream joint' din. Yayi mana ordering 'vanilla ice-cream' wanda saida ya tambayeni nace masa shi nakeso kafin yayi ordering. I so much like 'vanilla flavored'
Wani centre plastic table muka nufa mai dauke da two plastic chairs. Zamar mu keda wuya sai gashi an kawo mana 'ice-cream' d'in shake da robobi. Mubeen ya biya sannan muka hau sha muna fira.
"Aha can u please gist me abouh d real 'DR. MUBARAK sitting next to me as promised? "
Yace"Of cours! Why not?..... Kamar yadda kika sani Sunana DR. MUBARAK MUSTAPHA MUHAMMAD wanda yake aiki ah 'Aminu kano teaching hospital'... Mahaifina retired custom ne... Matansa biyu... Haj. Fatima wacce itace ta farkon, sannan kuma mahaifiyata, Haj. Khadija wacce itace amarya.Dukkansu hatta mahaifina duk hausawa ne.Mahaifiyata nada shekaru kusan shidda kenan da rasuwa gashi yau Abba yabi sahunta."
Ahankali na furta"Allah ya jikansu da Rahama"
Yace"Aameen Zahra... 'Ya'yan Haj. fatima hudu... Engr. Mahmood Mustapha shine danta na farko, sannan Anty Maryam(tayi aure 'ya'yanta biyu) sai Usman, sannan autarta khairat, itama yanzu haka tana gidan mijinta da d'anta d'aya.
Mu biyu ne kacal agun mahaifiyata, Ni da 'yar kanwata Labeebah.... "
Da sauri nace"Then who is Hanan to your family don banji kayi including d'inta aciki bah..... "
Murmushi naga yayi tare da fadin"Zahra please calm down I will soon get to there... "
Ya cigaba"Gaba dayanmu Engr. Mahmood shine babba.Engr. na cikin wani hali na kuncin rayuwa adalilin rasuwar matarsa wacce suke masifar kaunar juna.Shekarunta kusan uku kenan da rasuwa amma har yau jinsa yake kamar yau ta rasu.Allah sarki Engr. tunda Zaynab ta rasu har yau yaki yin aure gashi bashi da d'a da ita. Akan kawo masa 'yan mata Kala Kala amma sai yace shi baiga mai kama da kuma hali irin na Zaynab dinsa ba, hakan da yakeyi idan an kawo masa en matan ne yasa aka daina aka zuba masa idanuwa kawai tare da sanyashi cikin du'a'i."
Cikin raunanniyar murya nace"Allah sarki... Allah ya kawo masa tallafin gaggawa... Ita kuma Zaynab Allah ya jik'anta." Tausayinsa kawai naji ya lullubemin zuciya.
"Aameen.... Toh daga shi, sai Anty Maryam, sannan Ni Mubarak.... Sauran duk kannena ne.Haj. Fatima wacce muke k'ira da mummy tana matuk'ar kaunata, ji take kamar ita ta haifeni donma zan iya cewa kamar tafi kaunata akan 'ya'yan data Haifa.Hakik'a sunyi zaman lafiya da ita da mahaifiyata, kuma nasan mahaifina ya koma ga mahaliccinsa yana matuk'ar alfahari da su... "
"Its okay... Atleast I have known a little abouh u.... Now answer the following questions.... Daddy? Mommy? Kawar mominki? Afriend from Zaria? And most important fara answering wannan questions din.... Wacece HANAN AND JASMINE.......... " Na masa wannan tambayar cikin k'osawa naji zancen.
Ahankali naji ya furta"Idan na baki Labarin Hanan da Jasmine zaiyi covering sauran tambayoyinki.... Ma'ana anan zaki sami amsoshin tambayoyinki..... "
Da sauri nace"Then bani labarinta......Tell me her position in ur family............."
Gyara zamarsa naga yayi, ido cikin ido yake kallona kafin ya fara magana.
Zai soma magana kenan mukaji k'arar tsawa wanda k'arar ba k'aramin tsoratani yayi ba, kuma adaidai lokacin text message ya shigo wayata daga Ash queen,kamar haka,
"Malama hope kina dai ganin had'ari koh? and dix is 15mins to 1pm... Don Allah duk inda kike ki taso mu kama hanya kada ruwan nan ya sauko bamu bar garin nan ba... "
Ina gama karantawa na d'ago kai ak'idime ina kallon Mubeen nace"Mubeen don Allah mu tafi kawai kada ruwan nan ya sauko ya tsayar damu anan, Gashi Ash ta min text wai inma taso mu kama hanya kawai, dan haka duk wani tattaunawa mu barshi zuwa lokacin da kai zaka kawo mun taka ziyarar.... " Na mik'e da niyyar fita a 'joint' din.
Da sauri naji yace"Don Allah Zahra ki tsaya ki saurareni don yau nake son muyi ta ta k'are... "
"No Mubeen bazan iya saurarenka yanzu ba don gaba d'aya hankalina ya k'arkata zuwa ga 'yan'uwana da kuma can gida Zaria..... " Na fadi hakan cikin k'osawar son mu bar wajen.
"Koda kuwa zan fadi miki cewar akwai dangantaka mai k'arfi tsakanina da HANAN... Shi d'in ma ba zaki tsaya ki saurareni ba...? "
Da sauri na kalleshi, na koma na zauna da mataccen jiki. Cikin rashin kuzari nace"Ban fahimta ba... Pls ka fitar dani acikin duhu.... "
Ahankali ya cigaba da magana kamar bai son yayi, yace"HANAN is my wife not a blood sis...sannan Jasmine 4years old daughter d'inmu ce........... "
Ak'idime na mike ina fadin"What????? Mubeen mai kunnuwa suke jiye mun?? Mubeen dama ashe kana da aure yaudarata kawai kake son kayi.... ? Dan Allah ka amsani.... " Na furta hakan already in tears Allah ma yasa inda muka zauna babu mai jin abinda muke fada sai dai yaga actions namu.
"Don Allah Zahra take it easy I can explain...."
Cike da tsiwa nace"Bayanin meh kuma zakayi??? Komai anan is clear and straight forward..... Hanan matarkace and Jasmine d'iyarka...Mubarak nidai kawai kawai ka yadda ka riga ka gama da rayuwata totally... " Na k'arashe maganata cikin tausayawa kaina, sannu ahankali na soma rera kuka mai tsuma zuciya.
Sai daya kyaleni nadan tab'a kukan maybe don na dan sami rest of mind ne don kun san ance wani kukan yakan yi reducing pains, zuciya takan sami dan sassauci.
Don kaina nayi shiru, na koma yin kukan zuci. Ganin nayi shiru ne ya bashi damar cigabawa"Hanan 'ya ce ga wata k'anwar Mummy. Mummy itace tayi rik'onta tun tana yarinya har zuwa sanda ta mallaki hankalin kanta.Tun tana k'aramarta yarinyar ta shaku dani, nima hakan na shaku da ita.
As time goes on, shakuwarmu ta wuce over wanda na lura ita yarinyar mah harta kamu da matsanancin sona, ni kuma har ga Allah Soyayyar wa da k'anwa kawai nake mata.
Ganin ta kamu da matsananciyar soyayyata ne ya sanya na soma k'aurace mata don bana son soyayyar ta mata yawa acikin zuciya har tazo mata illah.Ashe abinda ban sani bah kuwa shine, ashe dama can Mummy ta kudira aranta son ta had'amu aure ni da Hanan d'in.
Sanda tajewa Mahaifinmu da kudirin nan, nata atake yayi na'am da zancen tare da nuna mata lallai yama fita son wannan had'i.Mahaifiyata kuwa tama riga ta rasu kafin wannan zancen ya taso, koda yake even if she was alive,nasan bah zata hana hakan faruwa bah don yadda suke zaman lafiya da Mummy da kuma yadda taga Mommin ke masifar kaunata dole ta mata k'ara ta hanyar yin na'am da batun.
Lokacin da aka tunkareni da zancen,gaskiya bazan iya ce miki nayi murna da batun bah, haka zalika bazan iya ce miki ni banyi murna bah, but nadai san dad'ina d'aya, alokacin bani da wacce nake so... Ma'ana bani da kowacce budurwa don ni am not after ladies at all.
Don haka na amince Hanan ta zamo matata kamar yadda suke so, don ni Sam bana iya yiwa mummy gardama. Amincewa da nayi da request d'inta shine ya k'ara mata kaunata azuciyarta tare da k'ara min wani k'ima da daraja ah idanuwanta.
Ba'a wani dau tsawon lokaci bah magana ta gama kankamawa,aka bi aka bazawa dangi cewar ni ne zan auri Hanan. Ashekarar da Hanan din ta kammala secondary school d'inta toh ashekarar aka d'aura mana aure. Ayanzu haka shekarar nan ta kammala School of Health d'inta dake nan area Bridget kano.
Rayuwar aurena da Hanan rayuwace mukai mai cike da tsafta da mutunta juna, don Hanan yarinyace mai hankali, ladabi da biyyaya, tarbiyya, uwa-uba respect da Hakuri.Farko farkon aurenmu bana yadda mu zauna kusa da juna ko na bari wata dogon hira ta shiga tsakanina da ita don har lokacin kallon k'anwa nake mata, amma sannu ahankali Hanan yarinya mai basira,ilimi da kuma wayau tasan yadda tayi ta koya mini yadda zan sota wanda hakan ne ya janyo na soma had'a shimfid'a d'aya da ita har muka sami haihuwar mai sunan mummy FATEEMAH JASMINE (sunan step mum d'insa)..... My Zahra am so sorry I know u are hurt amma ya zama dole in gaya miki gaskiya "
Cike da takaici nace"hmm karka wani damu amma yanzu dai fad'a min wani irin basaja kuka had'a kai da ita akaina don na lura acikin dukkan family d'inka kamar ita kadai ce kawai tasan da alak'ar dake tsakanina dakau.... Ina sauraronka..... "
Kafin ya kai ga bani amsar tambayata, wayata ta hau ringing, 'Ummu Fadima' na gani akan screen din wayar as the caller. Gabana ne hau fad'iwa, cikin lokaci k'ank'ani na nemi hankalina na rasa don fargaba.
Da kyar na iya danna wurin 'receive' tare da mak'ale wayar akunne.Kafin nakai ka magana naji tace"'Yar Kareematu hope dai kun soma shirin tasowa don its pass 1pm already? "
Jin ta ambaci pass 1pm ya sanyani gwalalo idanuwa waje ina kallon Mubeen,Na dai sami kaina da furta"Insha Allahu Ummu Fadima yanzun mah muke shirin tasowa.. "
"Good.... Safe trip daugh... Allah ya saukeku lfy and please kindly extend my condolences greetings to my inlaw.. "
Murmushin takaici nayi tare da furta mata "okay" kawai, sannan tayi hang up.
Azuciyata nace"Ummu Fadima, Mubarak dake zaune agabana bana tsammanin zai tab'a iya zama sirikinki kasancewar yana da mata har ma da rabo atsakaninsu, Kuma kin sha fad'a mana cewar insha Allahu ke d'in ba zaki tab'a yadda 'ya'yanki su auri mai mata ba, sai dai azo asamesu daga baya, if possible ma a auresu su kadai, no second wife, nasan bazaki tab'a bari na auri Mubarak ba gashi ni kuma ina sonsa but not sure ko shi d'in ma zai iya aurena yadda ma na lura kamar soyayyata dashi sirri ne, danginsa basu da masaniya sai matarsa wacce hankali bazai iya daukar kalar takun basajan da aka daurata akai ba, maybe ma yaudarata kurum yake shirin yi.... "
"Hala Umma ce...... " hakan naji ya fada.
Kai kawai na daga masa alamar "Eh" tare da saurin mik'ewa ina fadin"Mubeen idan kana yiwa Allah ka tashi mu tafi its pass 1pm already............... "
Kafin na gama rufe baki sai kawai ji mukayi an kece da ruwan sama tamk'ar da bakin k'warya.
Cike da tausayin kaina and nearly in tears nace"Mubeen kaga burinka ya cika ko ?tun dazun nake tace maka mu tafi kada ruwan nan ya tsaremu anan amma kaki Ji... gashi irin wannan ruwan kafin ya tsaya sai ahankali..... Yanzu wani lokaci kake son mu bar Kano har mu kai Zaria ayau d'innan kafin Abbana ya Koma gida? "
Zaiyi magana kenan mu kaji k'arar text message ya shigo wayata. It's Ash again.
"Yanzu nasan kina cike da farin ciki tunda gashi har ruwan ya sakko ya samemu agarin mutane.... Kin ga kuwa sai ki zuba ruwa akasa kisha don murna becuz u are 2geda with ur man dan haka baki da wani sauran damuwa..... "
Guntun tsaki naja tare da furta"Banza mara hak'uri kawai..... inama ace kece a irin halin da nake ciki, ai dana ga yadda zakiyi... " share sak'on nayi ba tare dana maida mata da reply ba, sai mah kashe wayar dana yi gaba daya.
"My Zahra pls am so sorry duk ni na sanyaki cikin halin da kike ayanzu amma Mu d'an Kara hakuri insha Allah ruwan zai tsaya....... "
"For how long Mubeen.....? "Nayi masa tambayar nan cikin takaici.
"Very soon insha Allah..... " acewarsa
"Allah yasa" kawai na iya cewa.
Ya cigaba da tatsuniyar gizonsa"Aranar farkon dana soma jin muryarki awaya, ban mah fah ganki kenan bah, but aranar na soma experiencing abinda ake kira da 'NA GANI KUMA INA SO'..... Ma'ana aranar naga macen da naji at once na soma sonta becuz Hanan zabin iyaye ce, kuma sai bayan aure na soma sonta, amma ke kuma ni na gani nace ina so.
Hakan ya sanya na kasa hakuri sai dana bayyanawa Hanan batunki wanda tuni ni da ke mun riga da munyi nisa ah soyayya. Hakika zan iya cewa Hanan ta shiga wani hali sanda naje mata da zancenki wanda ni kaina saida na matuk'ar tausaya mata amma inaaa, idanuwana sun riga sun makance da soyayyarki balle ince zanyi back up don tausayinta.
Itace wacce ta bani shawarar naje na sanarwa da su Abba Zancenki don ita ashirye take ta zauna dake idan har sun amince, don ita ta fini k'aunar abinda nake 'So'.
Tuna mata da hud'ubar mummy agareni nayi, ah inda take yawan cewa "Mubarak wallahi ban yadda ko da wasa ka had'a Hanan da wata 'ya mace ba ko bayan raina ah kul! dinka....Kar inji kuma kar na gani kaci amanarta ta hanyar keeping side chicks awaje.......... "
Da sauri na tari numfashinsa"Wato yanzu nice side chick d'in kenan right...?
Yace"No my dear, to me u are not..... dalilin dayasa muka b'oyewa kowa na dangina relationship d'ina dake kenan gudun rigima tunda Hanan kadai akeso ta zauna agidana, amma with time zan san yadda zanyi in bullo musu da batunki "
"Haba, yanzu na gano bakin zaren.....kace dalilin dayasa banga an tarb'eni dak'yau amatsayin budurwarka ba kenan, kai da matarka kuka shirya basaja azuwan ni friend d'inka ce, daughter d'inku kuma kuka fad'a mata cewar k'awar mominta ce Ni........ Wao bravo!.... A job well done kunfa birgeni agaskiya, sai dai wani hanzari ba gudu ba ina fatan ka kwana da sanin Cewar ni ka Cuta? Meyasa baka tab'a fad'a mun cewa kana da aure ba har saida ka bari ka gama gina soyayyarka acikin zuciyata ta yadda kasan bazan tab'a iya rabuwa dakai ba ? Wani irin zalunci kenan ?"
"Dana kuskura na fad'a miki hakan, nasan da kin rabu dani wanda na kwana da sanin cewar bazan iya rayuwa babu ke ba, sabida son da nake miki Zahra 'SO' ne wanda ruwa bazai iya kashe kishinta ba, gaki da sunan Mummyna da kuma 'yata, hakan shi ya taimaka wajen dad'a mun muguwar k'aunarki azuci "
"Believe me idan nace maka ko ayanzu ban makaro wajen rabuwa dakai ba..... " Na furta hakan Wanda na tabbatar ni kaina bani da tabbas akan abunda na fad'an.
"Zahra wallahi ki yadda dani bazaki iya rayuwa babu ni ba... " Ya fad'i hakan yana kallon k'wayar idanuwana wanda hakan ba k'aramin sanya jikina Sanyi yayi ba. Kasa furta komai nayi sai aikin kallon juna muke Cike da shauk'in SO..............
Tofa Mubeen da Zarex yau fah ake yinta...
Shin Hanan d'in wacce iriyar macece haka ?
To be continued..
#’Yar Mutan Naija#
***.