Free chapter · Read without an account

12

by Hafsat mustapha · SHIN SO DAYA NE?

SHIN SO DAYA NE?

Hafnancy...

Zazzafar soyayya, Cin amana, mugunta da kuma Sadaukarwa

#Free Book#

12.

"Haba Yaya Fadima its too early ki soma tunanin rabuwa da Mubarak don kawai yana da mata da 'ya."

Idanunta ya fara canza kala da alamun tana shirin zubar da hawaye.

Kasa-kasa da murya nayi, hankali tashe nace" Amma kina da hankali kuwa? Suhaima wai meyasa kike abu ne kamar kanwarki ce ta yayeki? Sbd Allah a gaban Leedar fa kike ambaton Mubarak, haka kwanaki ma kika bada labarin Leedar ga shi Mubarak. Idan kika rabani da samarin nawa shikenan ai kin huta."

"Yaya Fadima I’m so sorry wlh a rud’e nake, don Allah kar kiyi fushi kuma bazan gaji da gaya miki gaskiya ko a gaban wanene ba. Don girman Allah ina son please kiyi ma Mubarak Uzuri tare da bashi k'yakk'yawar fahimta, karki ga laifinsa, Ki sani Sonki ne ya saka ya b'oye miki komai dan atunaninsa idan har ya kuskura ya bayyana miki gaskiya da wuri to zaki rabu dashi, Yanzun kuma daya fito fili ya fad'a miki gaskiya, kina k'ok'arin break up dashi.... Wallahi sis karki kuskura! I repeat, karki sake kiyi gangancin barin Mubeen akan wannan Leedar d'in, ki sake zama kiyi tunani "

Yadda take zuba maganganun nan zaka san cewar ba'a cikin hayyacinta take yinsa ba. Kokarin katseta nake sai ji nayi an riga ni.

"Hey! guys wai meyake faruwa ne da har kuka tadani bacci da hayaniyarku?.... Huh? "

Ash queen ce ta tunkaro inda muke tana fad'in hakan.

Da sauri na amsa ta don bana son ta san abinda yake faruwa, nace"Ash kin mayi sallah kuwa? Don ni dai ko motsinki banji bah tunda kika kwanta jiya kamar wata sabuwar gawa.... "

Harara ta jefo min tare da fad'in"Eh fah alarammiya ina fah za kiji motsawar tawa?... Toh bari kiji yarinya komai da kika yi adaren jiya akan idanuwana ne, ke da kika yi kwanan dadduma kamar wacce taji an bata k'yautar Ajannah free shine take nuna godiyarta ga Allah?..... Kina kwantawa shidda ni kuma na mike na gabatar da tawa sallar kafin na koma second round na baccin..."

Dariya muka sanya nida Leedar don maganarta, sab'anin Suhaima wacce sa kai tayi tabar wajen fuskar nan ah murtuke babu koh d'igon annuri akansa,Ash dai binta tayi da idanuwa amma bata ce komai bah, kuma nasan ta d'ago wani abin wanda sam bah hakan naso bah.wallahi Suhaima is very annoying at times.

"Ash na Bash.... " hakan Leedar ya fad'a don ya dawo da hankalin Ash zuwa garemu.

Murmushi tayi masa tare da fad'in"Hey! Lee na Teema watsup!.... Sai yanzu na lura dakai.... Meya kawoka gidan surukai da sassafe haka bayan koh 'yan gidan mah basu gama tashiwa bah? " Ta fad'i hakan in a teasing way.

"Ash ai ni na riga da na zama d'an gida... Don haka ke zan mah yiwa tambayar koh meya kawoki gidanmu da safiyar Allahn nan? "

"Hmmm ina ruwan masu gida.... Toh don kaji, ni anan mah na kwana.... "Ta bashi amsa atakaice.

Murmushi yayi tare da fad'in"Ash kenan! Wato ke dai ba zaki taba canza halinki bah..... Hope dai kina kular min da aminina.....? "

Harara ta wurga masa tace"Kai Kanka kasan dai Ash bata d'aukar last..... Shi ne ma zance idan har beyi serious ba toh tabbas na kusa bashi red card..... "

Dariya muka sanya duka, nace"Ash ke dai wallahi akwai shirme....... "

Ignoring d'in maganata tayi ta hanyar fad'in"Alamu dai ya nuna ba'a son naji abinda ke faruwa don naga Suhaima ma barin falon tayi, yanzu na gane cewa family issue ne wanda bai kamata ace na tsoma dogon bakina aciki ba...... "

Da sauri nace"No Aysha wallahi ba abunda kike tunani akai bane, Bawai ina boye miki wani abun bane.... Alright naji zanyi bayani...... "

Taran numfashina tayi ta hanyar sanya 'yar yatsarta saman lips d'inta, tace"Shhhhh! Karki damu I understand.... Kuma ba wai fushi nayi bah... No, kawai gani nayi ke baki daukeni kamar yadda ni na daukeki amatsayin yar'uwa ba, kwata kwata ke d'in ba kiyi trusting d'ina ba...amma watakila kina tsoron karki gayamun sirrinki sannan inje in bazar dake awaje ne "

Kallon Leedar tayi, tace"Lee am sorry idan har maganganuna basu muku dad'i ba amma ya zama dole in gaya mata gaskiya "

Hannayenta na ruk'o nace"Haba Ayshata daina fadin hakan.... Fad'in cewar ban daukeki kamar yar'uwa ba ke kin san wannan ba gaskiya bane, sannan kuma wayace miki ni Fadima ban yadda dake ba ? Atunaninki har akwai abunda zan iya b'oye miki ? Ke ki saurari kanki fa ? Wallahi ko ban fad'a miki yanzu ba nan gaba dole zaki sani dan bani da amintacciya kamarki, Jeki zanzo na sameki muyi magana idan na sallami Leedar.... "

Daga kafadunta tayi,cikin salon yangarta tace"Anyway if u say so, sai na ji daga gareki d'in....bari inje in watsa ruwa sannan na wuce gida dan ba karamin kewar Mommyna nayi ba "

Murmushi nayi, Leedar yace"In bazaki damu ba kina iya bina sai na saukeki don daga nan unguwarku nayi... zan kaiwa wani tsohon abokina ziyara.. "

"Okay ka ban 20mins.... " Hakan tace ayayin data bar wajen da dan gudu- gudu don shiryawa.

Juyowa nayi ina kallonsa, ahankali nace"Lee kayi matuk'ar k'yau... inama ace ka cigaba da sanya kaftan don yana maka mugun k'yau.... "

Murmushi yayi tare da gyara zamar hularsa, yace"Kai prettynah stop teasing me mana... "

Nace"Its not a matter of teasing... Juz saying the fact.... Lee zauna mana tun d'azu muke tsaye sai kace wasu dogarai... "

Zama yayi kan wani one seater yana Murmushi, yace"Pretty tun jiya da kika fad'a min cewar zaku Kano ta'aziyya.... Abubuwa suka min yawa, kin san ina kan rubuta project work d'ina... "

Nace"Haka ne fa "

Ya cigaba"Wallahi sai wuraren yamma na tuna fa kince zaku ta'aziyya, kuma ban k'ira inji daga gareku ba, atake na shiga k'iran wayarki anata ce mun switched off har zuwa Yanzun switched off d'in ake cewa.... Pretty kin mugun d'aga min hankali, nace toh wat's wrong with my lady? Dalilin zuwana da safen nan kenan"

Sai ayanzu na tuna fa har yanzu wayata akashe take, don haka nace"Eyyah so sorry my best! Wallahi kanon ce sai ahankali, throughout babu wuta.. Kuma ana ta zuba ruwa tamk'ar da bakin k'warya, kai infact late muka dawo garin nan... "

Na bashi labarin yadda motarmu ta lalace da kuma yadda wani ya taimaka mana, amma koda wasa ban sake na bashi labarin yadda mukai da Mubeen da kuma wanda ya taimaka mana d'in ba Wato 'ENGR. MAHMOOD'...

Yace"Ikon Allah!.... Toh Allah ya kiyaye na gaba..... "

Ahankali nace"Ameen thumma amin"

"How far.... Ya kika gan Mubarak d'in? Hope he is that classic one da Fateena ke burin mallaka? Oya maza bani labari......

"Yea kaida ka sani... Mubeen ya hadu ta ko'ina... karka damu idan muka hadu next zakasha labari sosai, amma ayanzu tsoro nake kada wani yazo yaji ina baka labarinsa, let's close his chapter right away.... " Na fad'i hakan ina mai kallon wurare kada da gasken kila mah wani ya riga da yaji.

"Hope abinda naji Suhaima na fad'i relating to Mubarak, shima zaki bani labarinsa? " ba zato bah tsammani naji ya fadi hakan wanda tuni ni har na manta cewar munyi hakan da Suhaima agabansa.

Daga masa kai nayi alamar "Eh"... Adaidai Lokacin naji ana bugun kofar falon, da saurina naje na bude. Ganin Umma ce ya sanyani bud'e baki nace"Ummu Fadima ina kika je haka da farar safiyar nan ? "

Shigowa tayi tana fadin"Gidan Madam Iyabo na shiga gaida 'yarta Rose ta haihu.... "

"Wow Rose ta haihu? Toh Allah ya raya... Mai ta samu?"

Tace"Namiji.... " maganarta ta katse adaidai Lokacin Haidar ya russuna yana gaidata wanda na lura sam bata mah lura dashi acikin falon bah.

Cike da fara'a tace"A'ah Haidar kaine? Sannu da zuwa... Yasu ummar taka suke?"

Susa kai yayi, yace"Duk suna lafiya... "

Tace"Madallah... Kace wa Fareedah ina gaidata wai kwana biyu ta gujemu (kanwarsa).

Murmushi yayi, yace"Insha Allah Umma zan isar da sakonki gareta... "

Tace"Good... "

Tambayata tayi koh Abba ya tashi. Da mamaki nace"Laah! Umma dama ya dawo ne? "

Tace"Da sassafen nan ya dawo lokacin kuna baccinku na mamaki... "

Ta fadi hakan sanda tayi upstairs,sake cewa tayi"Ki tasar da kowa ayi breakfast baccin mamakin ya isa hakanan."

"Lee excuse me pls...." Na fadi hakan ayayin da nayi saurin barin wajen zuwa dakunan baccinmu don tada kowa. Dakinmu naje na sami Ash har ta kammala shirinta, da yake tana da wasu kaya agidanmu Wanda takan yi using aduk sanda ta kwana.

Na tada kowa amma Suhaima ce ban gani bah.Reading room namu na nufa inda nake tunanin nan zan ganta. Ai kuwa ina gama bude kofar dakin na hangota can ta sanya kanta kan table d'in karatu.

Magana take wanda ya cakud’e da kuka wanda hakan ya sanya na kasa kunnuwa ina sauraronta don ga dukkan alamu bata ma lura da tsayuwar mutum a bakin kofa ba.

Cewa tayi"Haba Aleeyunah ya zaka min hakan? Kafi kowa sanin cewa ina mutuwar sonka. soyayyarka ajinina take."

Dafe kirjinta tayi a daidai saitin zuciyarta tana jan numfashi dakyar.

"Tabbas *‘SO ƊAYA NE'* tak! Kuma kai nake yi ma wannan mahaukacin soyayyar. Na kasa son wani d’a namiji bayan kai, To amma meyasa kake kokarin zamo sanadi na ajalina ? Wallahi Haidar idan baka gaggauta rabuwa da Yaya Fad'ima ba to tabbas ana iya neman zuciyata a gurbinta a rasa..."

Gabana ne ya yanke ya fad'i jin furucin daya fito daga bakinta. A yau zargina ya tabbata gaskiya.... 'SUHAIMA SA'AD na Son 'ALI HAIDAR' d'ina.

Bazan iya cigaba da sauraron love stories d'inta ba kada ciwon zuciya ya farmun nan take, hakan yasa nayi gyaran murya,nace,

"Ke!! Malama idan kin gama abinda kike sai ki taho ayi breakfast.... "

Atsorace ta d'ago kai ta kalleni,fuskarta cike yake da tsoro don gani take kamar naji duk abinda ta fad'a from A-Z.

Ahankali na ji tace"Akoshe nake.... "

"Wannan kuma matsalarki....kila kin shirya fad'awa su Umma abinda ke damunki ne becuz idan ba'a ganki a dinning ba kin san za'a nemi jin dalili...... Sai kiyi kokarin bayyana musu sirrin zuciyarki.... "

Na fad’i hakan tare da kullo kofar da k’arfi, dinning na nufa straight don kowa ya hallara mu kad’ai ake jira har Leedar don ya riga ya zama d’an gida. Abba ne kawai bai tashi ba dan ina tsammanin ya kwaso gajiya sosai.

Ko minti biyu ba'a dauka bah sai ga Suhaimar tazo dinning din, wannan karon fuskarta asake maybe don kada adago cewar wani abin ke damunta.

Akayi breakfast cikin raha, annashuwa da kuma wasanni har muka kammala. Na raka Ash da Leedar ina jaddada mata cewar zanyi gisting d'inta ran Monday idan muka hadu a makaranta.

Tace"Allah ya kaimu sahibar... Take care". Suka shige motar Leedar sukayi gaba.....................

HAFNAN'S POV

Tofa!!! Anzo gun.... Yanzu zargin fadima Sa'ad kan kanwarta gaskiya ne ??Tana son Leedar.... Akwai rigima kenan

Again? Kun lura da wani abin mamaki da ni na lura dashi? Lyk kamar Leedar ya dade da sanin labarin Mubeen.... Wat's going on? Labarin nan akwai daure kai koh? Juz chill... Ku dai ku cigaba da bibiyar Hafnan!!!

Masu son double update kullum su nemeni, da 500naira d’inki kacal zaki mori karatunki, ta wannan asusun bankin 7065481260, Hafsat Mustapha, palmpay, sannan a turo da shaidar biya ta *** ko kuma a garzaya kan arewapen zai zama available soon.

To be continued..

#'Yar Mutan Naija#

***.

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.