Free chapter · Read without an account
E.P9️⃣⏩1️⃣0️⃣
*𝒀𝒂𝒓 𝑵𝒐𝒍𝒍𝒚𝒘𝒐𝒐𝒅*
_TAP THIS LINK TO JOIN MY GROUP👇_
***
_TAP THIS LINK TO JOIN MY CHANNEL👇_
***
_TAP THIS LINK TO JOIN IN AREWAPEN 👇_
https://arewapen.com/u/prettys01
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
🕊️ *May Allah keep us united, uplift us, and make our pens a means of positive change.*
Much love and respect to each and every one of you. ❤️🔥
*Keep shining, JAW family!* 🌺
*JARUMAI WRITER'S TEAM📚✍️*
𝒀𝒂𝒓 𝑵𝒐𝒍𝒍𝒚𝒘𝒐𝒐𝒅
Story and writing✍️
```PRETTY SK```
~SAKINA ABDULLAHI~
> *PRETTYN JAJIRTATTU 💪✍️
✽»≿━༺🌹﷽🌹༻━≾»✽
E.P9️⃣⏩🔟
________Inayah, yau makarantar bai min daɗi ba saboda, Jennifer ba ta zo school ba, haka dai school ɗin ya zama min lami, ko da A'isha ta zo ɗauka ta ban yi mata magana ba har muka koma gida, na dai lura sai faman murmushi take yi, sai nima na shareta saboda abin da ta yi min na ɗazu ya ɓa ta min rai sosai.
Bayan ta yi parking na fito fuskana babu yabo ba fallasa.
Ina shiga falo na nufi Kitchen aje lunch bag ɗina na yi sannan na fito sai na ga mom na saukowa daga stairs, murmushi take yimin sai dai Ni na kuma ɗaure fuska.
Jakkana na ɗauka na yi hanyar room ɗina , har zan wuceta sai ta riƙon.
“Waya ta ɓa shalele?.” ta faɗa tana dawo dani gabata, shuru na yi ban yi magana ba, sai ta ɗaga mun fuskanta na kalleta.
“Me aka miki?.” ta faɗa dan yanayin da na koma.
“Babu komai..........ina zuwa." Na faɗa ina wucewa, bina ta yi da ido dan kuwa yanayin na wa ba magana abin ka da kullum ina nishaɗi.
“Ke kin yi ma Shalele wani abu ne?." Mom ta tambaya A'isha wacce ta zauna a falo bayan shigowar ta.
“Haka na ganta, ko magana ba mu yi ba, sai dai ko tun faɗar safe da muka yi ne." Sai ta ɗaga kai tana zama a kujera, sai dai jikinta ya yi sanyi, dan Inayah sam ba haka take ba.
“Hajiya, yau fa Shalele ba ta ci komai ba, da alamun ko buɗe lunch bag ɗin ba ta buɗe ba. Sannan ga wannan a ciki"
Mai aikin su wato Rabi, ta faɗa tana miƙa ma A'isha ₦500, sai A'isha ta yi mata alamar ta wuce da shi, sai ta yi godiya tana koma wa Kitchen.
Mom ta kalla A'isha da ta ɗan zaro ido, a ce tun safe mutum be ci komai yanzu ana shirin kiran sallar magrib.
“Da matsala me aka mata?.” A'isha ta faɗa cike da damuwa.
“Muje room ɗin." Da haka suka nufa room ɗin Inayah.
Ina shiga ɗakina na kulle ko ina sannan na kashe haske, kwanciya na yi kan gado ko takalmi ban cire ba, gaba ɗaya haushin kowa na ke ji, so nake yau a gidan kowa ranshi ya ɓaci dan kuwa abinda A'isha ta min ya ɓa ta min rai, sannan ga Jennifer da ta ƙi zuwa school, sai abu ya haɗe min, shi yasa ko magana banyi da kowa ba.
Jin ana buga min ƙofa yasa na yi wani murmushi sannan na yi magana a hankali.
“Ai yau sai hankalin kowa ya tashi, hmmm." Na yi ƙwafa ina toshe kunnuwana.
Mom da hankalinta in ya yi dubu ya tashi ta kira Dad a waya akan Inayah ba lafiya. Sun bubbuga ƙofar kamar me amma na kasa tashi.
Nikam wani wahalalliyar barci ne ma ya ɗauke ni.
Dad a ɗan ruɗe ya shigo gidan dan kuwa Allah ya dasa musu soyayyata kamar me.
Lokacin har an yi sallar isha'i, dan daga office ɗin sa zuwa nan akwai nisa, ina jin muryan Dad na tashi daga kwancen, bayi na shiga na yi wanka tare da alwala, lokacin dana fito na dena jin motsin kowa a wajen, sallah na yi magrib da isha'i sannan na zura kayan barci, yunwa nake ji sosai dan haka na buɗe ƙofar na fita ina ƙara haɗe rai.
Ga yunga da ya cinye Ni hakan yasa tafiyata ta koma kamar mara lafiya.
Mom, Dad, da A'isha suna tsaye kaman wa'inda aka yi wa mutuwa, sai suka ganni a falon, da sauri Mom ta nufoni tana riƙeni dan ganin kaman zan faɗi.
“Inayah....Inayah....." Mom ta faɗa sai na kalleta.
“Meke damunki?.” ta tambaya idanunta na cika da hawaye, a cikin raina kuwa nishaɗi ya kamani dan kuwa yau *Film* ake yi a gidan nan, tun yanzu ƙwanda na dinga practice.
“Shalele ba ki jin muna dukan ƙofar ɗakin ki bane?.” A'isha ta faɗa tana riƙoni.
Har lokacin na ƙi magana. Dad sai ya riƙo ni yana kwantar da murya.
“Tell me My bloodline. What's wrong with you?.” sai ga hawaye ya zubo min sai ya sa hannunsa ya sharemin.
“A....A...abinci.” na faɗa da ƙyar, ai da sauri A'isha ta nufa Kitchen, Tea ta haɗo min sannan Dad ya ban a baki, sai da na ƙoshi sannan na ce.
“Ku kwantar da hankalinku, kawai wani abu ne ke damuna....." Na faɗa cikin sanyin murya.
“Shalele faɗa min meke damunki, ko kina wa'inda suka fimune?.” na girgiza wa Mom kai.
A cikin raina kuwa dariya na ke yi, sai daurewa nake yi saboda karta kuɓuce min.
“Kuna so na zama Doctor ko?." Suka ɗaga mun kai.
“Ra'ayin ku shine nawa, akwai wata ƙawata, tare muke, ina sonta sosai, to ra'ayin mu ya zo ɗaya, ita dama a can wajen iyayenta za ta ƙarasa, shine jiya suka ɗauke wai a can za ta yi waec....... So nake mu yi University ɗaya......dan Allah ku taimaka.........” sai na fashe da kuka, kallona kawai suke yi dan ba su fahimci in da na nufa ba.
“Yanzu me kike so?." Dad ya tamabaye ni.
“*University College of Medicine (LASUCOM)*......” da sauri Mom ta ce.
“You mean Lagos State University?." Na ɗaga mata kai.
“Alfarma ce kawai, amma in ba ku so shike nan, dama kawai ina so ne mu yi karatu tare.” da haka na miƙe tsaye ina son na wuce, ga wani ɗan jiri da ke ɗibana.
“Ki yi ƙoƙari a weac Ni kuma zan kai ki.” sai na rungume Dad.
“Dad har Legos....gaskiya a'a?." Faɗin Mom, ita dai A'isha kallon mu kawai take.
“Shike nan, in dai ɗayan ku bai so ba za Ni ba." Na faɗa ina barin falon, da ido suka bini har na ɓa ce musu.
“Inayah problem, yanzu duk makarantu sai na can? Kuma akan wannan ne ta hora kanta da yunwa.” Mom ta faɗa sai A'isha ta ce.
“Kunsan halinta ai, akwai sa abu a rai, Allah dai ya ƙyauta, duk da ɗaga wa mutane hankali a banza.” A'ishah ta faɗa tana nufan Kitchen dan haɗa ma kanta abinci, ita haka Allah ya yi ta, tun tana ƙarama in aka dafa abu aka ba ta ba ta ci sai dai in Mom ta yi, tana ƙara girma kuwa ita ke girka ma kanta abinci, haka take ko ina ta je ba ta cin abu sai in da ita aka yi making.
Ina shiga room ɗina na daka wani tsalle sai gaba mirrow, dariyar ce ta ƙwace min, ai kuwa nai ta yi kaman mahaukaciya, sannan na ce.
“Hmmm ai ƙwanciyar hankalinku shine ku turani *Lagos State University College of Medicine (LASUCOM)* Hahahahahah ga ni ga NOLLYWOOD...... Sai ni ƳAR NOLLYWOOD insha Allah.” na faɗa ina sumbatar kai na ta mudubi.
Ni fa tun ainiyi *HOLLYWOOD* shi nake so, amma nasan ba zan samu daman zuwa U.S ba balle na shiga *HOLLYWOOD* har na yi Film, sai kawai buri na ya dawo *NOLLYWOOD* kuma insha Allah ko Film ɗaya ne sai na yi.
_______Aisha complex ta haɗa, anan ta sha dan ita ba wani abinci take ci sosai ba, tana gamawa ta koma room ɗin ta, a al'adance kullum sai ta yi wanka da daddare, sannan ta yi sallah kafin ta kwanta, haka yau ma bayan ta gama komai ta kwanta, take yau ɗin ta ya faɗo mata, tabbas yau rana ce da ba za ta manta da shi ba.
Jin sautin S.M.S ya sa ta duba, ganin M.D ya mata reply da.
*GOOD NIGHT It’s just been a day that you are gone and already it feels like ages. There’s no reason left to wake up in the morning, please come back soon. Thank you so much Eeshert.*
Murmushi ta yi sannan ta kalla wanda ta tura mai.
*Hello! My name is Night. I came here to kidnap your stress; Kill your strain. My weapon is deep sleep and my path is Sweet Dream. So please kindly co-operate and handover yourself! Good Night My.....*.
Murmushi ta kuma yi sannan ta lumshe idanunta, tana hasasho fuskar Ayan, ƙyaƙyƙyawan sauri mai Capacity. take barci ya ɗauke ta cike da zazzafan soyayyar Ayan........................✍️
END
> Ƴar NOLLYWOOD 🙆🙆🙆 Inayah gagara kowa kenan, hmmm ko ya za ta kasance......????
> Ba ku yi comments da Likes shi yasa Update yake zuwa a haka.
Na so kuban haɗin kai da a 2week za mu kammala........😏😏😏.
#LIKES👍
#SHARE😁
#COMMENTS🥰👌