Free chapter · Read without an account

GOMA

by ZAINAB M BAWA · LIKITAN RUHI

LIKITAN RUHI

Na

ZAYNAB BAWA

AREWABOOK@Zeeeyybawa

SHAFI NA  GOMA

   Mami ta kasance cikin farin cikin ganin Hammad ya shirya yatafi wajan aiki, domin Hammad yana ɗaukan tsawon lokaci batare da ya fita koda gate ba hakan kuma ba ƙaramun damun Mami yakeyi ba, kasancewarsa a cikin yanayi na shiru da kaɗaici yakansa taji kamar akwai wani abunda ta gaza bashi ta fuskar farin ciki tabbas tasan damuwa a wajan Hammad a yanayin da yake ciki za'a iya cewa kamar dole ce amma ita a nata ƙoƙarin ko ɗison damuwa batason gani a tattare dashi. Mami kaff cikin yaranta Hammad yafi soyuwa a gareta kodan ya kasance shine yafi kulawa a gareta sannan ya kasance shi ta fara mallaƙa a matsayin ɗa a kansa tafara amsa sunan uwa. ta samu Hammad tun a ƙananun shekarun da lokacin da take gani kamar bata isa amsa sunan uwa ba, daɗin daɗawa Hammad ya kasance ɗaya tamkar da dubu Hammad yanada kyawawan halayyar da nagartar da kaff yaranta babu mai makamancinsa, Hammad shine ake yiwa laƙani da Ɗa nagari saboda kyawawan ɗabi'unsa ga mahaifiyarsa.

AL-MALIK LAW FIRM

  Katafariyar Ma'aikatar shari'a ce wacce take dauke da lauyoyi sanannu masu zaman kansu da suka san makamar aiki cike da ilimi  da jajircewa wanda a halin yanzu ta shahara sosai a kaff faɗin ƙasar nan afannin ƙoƙari da kuma ƙwazo wajan gudanar da shari'a kowacce irice.

  Drivern Hammad yana isa bakin ma'aikatar  yaja ya tsaya haɗe da danna horn Sucurity dake tsaron gate na mashigar cikin ma'aikatan ya leko ganin motar Hammad ya sanya da sauri ya fito daga ɗakinsa ya a buɗe ƴar ƙaramar gate data rufe hanyar, sauƙar da glass ɗin ƙofar Hammad yayi yayinda security ɗin yaƙaraso cike da girmamawa yake gaishe da Hammad yayinda shikuma Hammad a nasa wajan ya miƙo masa hannu domin su gaisa hannu bibbiyu security ɗin ya riƙe hannun Hammad yana gaisheshi haɗeda tambayar jikinsa. Murmushi Hammad yayi sannan yace.

"Alhamdulillahi" Hammad ya faɗa yayinda shikuma securityn yaketa nuna farin cikinsa na ganin Hammad yau a wajan aiki domun akan kwashi lokaci bai leƙosu ba, Murmushi Kawai Hamnad yayi bayan sun gama gaisawa Driver ɗin yaja motar suka shige ciki Babbar ma'aikata ce sosai wacce take ƙunshe da ma'aikatan da a ƙalla yawansu yakai kimanin mutane ɗari biyu daga kan securities, cleaners  da interns zuwa saffa-saffan ma'aikata har izuwa ga manya-manyan ma'aikata tare dashi kansa mamallakin law Firm ɗin.

Ma’aikatar AL-MALIK ba ƙarama ba ce. Babban ginine wanda yake da tsayi sosai ginin ya tsaru matuka kamar alamar iko da martabar lauyoyin da ke cikinta. Tsarin ginin ya yi matuƙar tsaruwa, gabaki daya fentin ma’aikatar fari ne mai sheƙi suna yana sake haska kyawun ginin, windows na gilasai masu kyalli suka ƙara masa kyan gani. A saman katafaren ginin tambarin kamfanin. -AL MALIK LAW FIRM- ya tsaya a tsakiyar bango kamar garkuwa.

  Driver ɗin ya yi parking a waje na musamman da aka ware domin Hammad, domin wurin ya yi fadi ba tare da tudu ko gangare ba wanda hakan zai bashi damar tafiya a wheelchair ɗinsa ba tare da takuri ba, Nan take ɗaya daga cikin ma’aikatan parking unit ya ƙaraso da sauri ya buɗe ƙofar.

“Good morning sir,” ya faɗa yana sadda kansa.

Hammad ya amsa da murmushi mai cike nutsuwa, wanda yake da ikon kwantar da hankali koda mutum na cikin fargaba. “Morning,” ya ce, a taƙaice.

Driver ɗin ya zagaya ya ɗauko wheelchair ɗin daga cikin butt na motar ya kawoshi zuwa  bakin ƙofar da Hammad yake Da kulawa Hammad yahau kan wheelchair ɗin, A hankali Hammad ya danna Wheelchair ɗin ya fara tafiya cike da nutsuwa duk motsinsa akwai nustuwa da kamun kai, komai yakeyi cike da kulawa, an aganin Hammad za'aga mutumin da iyaye masu tarbiyya da ladabi suka raine shi.

Yana shiga cikin babban reception ɗin kamfanin, ma’aikata suka fara miƙewa tsaye suna gaishe shi cikin ladabi gabaki ɗaya illahirin fuskokinsu ya nuna mamaki da kuma jin daɗin ganinsa da sukayi

“Good morning.”

“Welcome sir.”

“Good to see you today, sir.” Wasu na Hausa, wasu na Turanci saboda tsarin ma’aikatar. Hammad yana amsawa cikin murmushin da shi kadai ya iya yi, murmushi mai taushi mai ɗauke da cikakken nutsuwa. Hammad bai da girman kai, amma yana tattare da wata nutsuwa da take sa kowa ya daraja shi.

  Hammad Ibn Muhammad Al-malik shine mamallakin wannan katafariyar ma’aikata.

Shi ne babban lauya, shugaba, kuma ginshikin dukkan al’amura. Duk da yanayin da ya tsinki kansa a ciki na takawa da keken guragu, babu mai kallonsa da raini domin halinsa, tunaninsa, iliminsa, da kwarjininsa sun fi ƙarfafa matsayinsa fiye ƙafafunsa. Ko a cikin ma’aikatan, ana ganin hakan.

Sectery ɗin Hammad na Al-malik, Mrs Farida, ta nufo wajansa da sauri fuskarta tana ɗauke da alamun murnanr ganinsa a wannna rana. Cikin nutsuwar da yafi buƙata a tattare da ma'aikatansa a koda yaushe ta fara gaidashi tana tambayar jikinsa saida ya amsa sannan ta miƙa masa wasu takardu:

“Sir, these are the files for today’s court sitting  Alhamdulillahi daka samu halarta yau domin babban zamane wannan daya kamata ace kayi nazari koda kaɗanne a kansa na tabbata baza'a rasa wasu taimako masu ƙarfi da zamu samu daga gareka ba  domin har a ta email na tura maka baka samu dubawa ba attorney ɗin da zai jagoranci ƙarar zai buƙaci wasu shawara daga gareka, idan babu damuwa zaka iya duba files ɗin?"

Hammad ya amshi takardan duk da ba aiki ne yau ya kawoshi ba amma bai musantta mata ba, duba kaɗan yayi sannan ya maida dubansa gareta ya miƙa mata file ɗin cikin nutsuwar da akoda yaushe yake tattare da ita yace. ,

“Send the documents to my office.”

“Yes sir,” ta amsa.

⸻

Hammad ya isa ofishinsa wanda yake a hawa na farko a yanzu saɓanin  a baya da yake can hawan ƙarshe,  A saman mashigar ofishin anyi rubutu a babban allo  C E O, SAN, HAMMAD IBN MUHAMMAD AL-MALIK anyi rubutu da babban baƙi. Babbar yatsarsa ya saka a mabuɗin ƙofar nan danan ƙofar ta ɗauki ƙara can tayi green alamun tayi recognizing mai wannna hannun ƙofar tana budewa ya shige ciki,

Cikin ofishinsa

Ofishin Hammad yana ɗaya daga cikin wanda yafi girma a ginin duk da bai kai ofishinsa na saman beni ba, Ofishin ya tsaru sosai  akwai saitin kujeru a office ɗin bayan teburin zamansa da yake ɗauke da sunansa a jiki. kujerun dakuma Fentin bango farare, Hakan yana nuni daya Hammad ba ƙaramin son launin fari yakeyi ba, teburin mai mahaukacin kyau da aka goge shi har yana yawo da haske. hakan zai ƙara tabbatar muku da irin tsabtar da Hammad yake da ita duk da baya zuwa office a koda yaushe amma ofishinsa a gyare yake tsaff-tsaff hatta da bangon ofishin mai gilashi kyalli yakeyi?, Yayu bangon ne da gislashi domin bangon yana bashi damar ganin tsirrai a waje wanda yasa aka shukasu na musamman domun mahangarsa. tsirran da ake iya hangowa daga ofishin yasa ofishin ya kasance mai natsuwar da ke daidaita zuciya.

A gefen ofishin akwai manyan buɗaddun ma'ajiyar littafai guda biyu cike da takardu, file-file da littattafan shari’a na kasashen duniya. Hammad ya kasance mai karatu yana da tunani, da nazari sannan kuma yana da zurfi da kuma kaifin basira duk wanda ya yi aiki a karkashin sa ya san babu shari’ar da ya shiga har ya yi kuskure. A tarihin shari'ar Hammad har yau babu wata shari'a data gagareshi. Shiyasa Hammad ba kowace irin shari'a yake amsa ba sai yayi bincike sosai ya tabbatar da ingancin wanda zai jagoranta.

A lokacin daya isa zuwa Babbanr kujerar dake office ɗin mai laushin gaske yayi kokarin canja mazauninsa daga kan wheel chair zuwa 3seater lumtsumammiya mai laushin gaske.

   A Ɓangare guda kuma zuciyarsa ba ta daina tunanin maganar Sagir ba. Wani yanki cikin shi na jin tsoron komawa cikin abinda zuciyarsa ta saduda tun a baya, wani yankin kuma na jin tamkar Ubangiji ne ke kaishi zuwa abin da zai zama chanjin rayuwarsa.Ya jingina da kujerar ya sauke numfashi mai nauyi.

“Ya Allah, kai ne masani gaibin komai…” Ya furta cikin sanyin murya.

A ƙan-ƙanin lokaci zuwan Hammad ya karaɗe gabaki ɗaya illahirin ma'aikatar wasunsu ƴan uwansu ma'aikata suka sanar dasu zuwansa wasu kuma ƙamshine ya sanar dasu hakan, domin kamshin turarensa mai sanyi ya cika dukkan corridor ɗin daya ratsa Kamshi ne mai ɗauke da natsuwa ba mai ƙarfi ba, amma wanda mutum ba zai iya mantawa da shi ba idan ya shaƙa sau ɗaya.

    Hammad bai daɗe da zama ba Mrs Farida ta shigo

hannunta ɗauke da file ta ƙaraso ta ajiye akan center table dake gabansa. Wannan file ɗin kawai ta kawo masa duk da kuwa akwai files daya kamata ace ya dubasu da yawa, Hammad ɗin data sani a baya bashine na yanzu ba domin Hammad ɗin baya duk yawan aiki baya sare masa guiwa Hammad ɗin yanzu kuwa sam baya ɗaukan strees saboda lafiyar jikinsa, a halin yanzu basu damu da lallai sai yayi aiki ba ganinsa a ma'aikatar kawai yakan faranta musu domin hakan yana nuni da cewa yana kan samun lafiya. Ajiyewa tayi ta fice yayinda shikuma yaci gaba da tunani akan maganar Sagir wanda kuma ba hakan yakeso ba domin kauda tunanin ya sanyashi shiryawa yafito office.

⸻

Wayarshi ce ta ɗau ruri.

Sunan Mami ya bayyana. Ya ɗan yi murmushi kafin ya daga wayar.

“Mami" ya kira da murya mai taushi.

“Hammad Habibi, na kira kawai naji ko ka isa lafiya.” Hammad ya ce,

"Na iso Mami." Cike da jin daɗi Mami tace.

“Toh Allah ya tsareka, ka kula da kanka. idan kasan zaka daɗe ka kirani kaji? Saina aiki maka da abunda zakaci" Murmushi Hammad yayi jin yanda Mami ke shagwaɓaci kosu Nimrah yara basu samu hakan daga gareta ba, zuciyar Hammad ta cika ƙaunar Maminsa yace:

“Toh Mami idan zan jima zan kiraki.”

Da suka gama magana, ya sauke wayar ya jingina a kujera....

#ZEE ALABURA

#LIKITAN-RUHI

#SOYAYYA

#ƘADDARA.

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.