Free chapter · Read without an account

E.P1️⃣4️⃣⏩1️⃣5️⃣

by PRETTY SK NOVERLIST · 𝒀𝒂𝒓 𝑵𝒐𝒍𝒍𝒚𝒘𝒐𝒐𝒅

💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️

🕊️ *May Allah keep us united, uplift us, and make our pens a means of positive change.*

Much love and respect to each and every one of you. ❤️🔥  
*Keep shining, JAW family!* 🌺

     *JARUMAI WRITER'S TEAM📚✍️*


𝒀𝒂𝒓 𝑵𝒐𝒍𝒍𝒚𝒘𝒐𝒐𝒅

Story and writing✍️
      ```PRETTY SK```
           ~SAKINA ABDULLAHI~
> *PRETTYN JAJIRTATTU 💪✍️

       
 ✽‌»‌≿━༺🌹﷽🌹༻━≾»‌✽
 



E.P1️⃣4️⃣⏩1️⃣5️⃣.


“Na haƙura da auren.......... Wallahi bazan iya wannan abun ba, ai wannan mutumcin harda na wa, da iyayenmu, da yaranmu duk zai zube, a'a......aa....... a'a Gaskiya. ” takai nan ta fashewa da kuka.


Take ya kwashe da dariya, yana dubanta, ganin irin dariyar da yake yi yasa ta kai hannu za ta fita daga cikin motan da sauri ya sa luck.

“Ai sai ki tsaya kiji gaba ɗaya maganar, ke kinsan ina da ilimin addini, ba yarda zan yi na kauce hanya, balle Zina, abu mafi muni. Kawai zamu yi basaja ne akan mun aikata haka, kuma ke kince idan ban aureki ba, za ki faɗa ma duniya saboda kina ɗauke da cikina a yanzu.” zaro idanuwa ta yi tana cewa.

“Innalillah, ta ya zamu yi irin wannan ƙaryan, kai ba ka ganin zai zo da matsala?.”

“Ko ɗaya, ai maganar daga familyna zuwa kanmu ne kawai, nasan yarda suke son mutumcin kansu ba za su bari hakan ta faru ba, dan sun san waye Mahaifinki, abokin kasuwancin sune.” jinjina kai ta yi tana maimaita abinda ya ce, tabbas a baki ya ya sauƙin faɗa, amma kuwa yana da girma fiye da a mai da shi abun wasa.

“Za ka fuskanci matsala sosai kuma nima haka idan na shiga gidan na ku haka.” ta faɗa bayan kukan na ta ya tsaya.

Iska ya furzar daga bakinsa sannan ya ce.

“Na sani, kuma nasan sharaɗin ɗaya ne, dole su aura min Ruma.” shuru ya yi, itama haka sai can ta katse shurun da cewa.



“Hmmmmmm da in rasaka gaba ɗaya ƙwanda mu yi hakan kuma zan iya rayuwa da ita Ruma ɗin. Duk da ina da zafin kishi.” sai ta share hawayenta.

“Yi min bayanin yarda tsarin yake.” ta kuma faɗa, with confidence.



Murmushi ya yi sannan take ya koro mata yarda ya tsara, dan kuwa wannan tsarin na sa tun kafin ya fara sake mata ya yi shi. 


Ita dai jin yarda ya koro zancen ne ya bata mamaki, kaman wanda ya shekara yana tsara plane. 

Bayan ta fahimta ne suka canza hira zuwa na soyayya.





      *Inayah*


___________Tsaki na ja, ina ganin ai A'isha ta jima da fita, gashi a waje ne balle in ce tana cikin gidan nan, duk na bi na damu, kallon Mom na yi dake cin abinci.

“Mom zan leƙa na dubota, karfa a ce sace ta aka yi, mu muna nan zaune” na faɗa ina nuna damuwa.

“Kin iya neman rigima ne ai, amma je ki.........” ai ba ta ƙarasa ba na yi waje da sauri.

Tabbas ina da neman magana dan kuwa yau tun safe nake ɓata ma A'isha rai, sai dai ba da gangan na fasa mata wayaba bisa tsautsayi ne amma A'isha ta wani hau min masifa.




Me gadi na ganina ya washe baki yana cewa.

“Shalele ina zuwa?.” 

“Baba Rabe duba Aunty zan yi kar a sace ta.” murmushi ya yi yana miƙewa.

“Zauna ai ba fita zan yi ba, leƙawa zanyi.” sai ya zauna yana kai Radio wajen kunninsa.

“To shalele.” ya faɗa yana lumshe idanunsa.

 

Ta saƙon get na leƙa, wata arniyar mota na gani, kafin na yi wani yinƙuri har A'isha ta fito ta ɗayan ɓangaren.

Ɓangaren dake gefana na ga an buɗe shima, take na ji abu na min yawo a ƙafata, da sauri na kalla a ɗan tsorace dan ma ban saki ihu ba, ashe igiyar riga nane, tsaki na kuma ja, ina mai da idanuwana wajen.

Wani dogon namiji na gaji cikin manyan kaya har da hula, yana da faɗi sosai, kaman wanda ke ɗaga ƙarfe, ban ga fuskansa ba dan haka na taɓe ƙaramin bakina.




A gaban A'isha ya tsaya yana goge mata fuska, da wani abu wanda ban tantance menene ba, sannan yana yi mata magana, wanda ban jin komai.


 
Kallon rigar na wa na kuma yi ina jin kaman na yi dambe da rigar saboda ban samu ganin fuskar Saurayin A'isha ba, so nake na ba Mom labarin komai da na gani kuma inason na karanci yanayinsu.



Ƙarar motar ne yasa na mai da idanuna wajen, ashe har ya wuce, ai da mugun gudu na bi bayan ɗakin mu, kamar wacce ta ga mugun abu.

Ta ɗayan ƙofar Kitchen na shiga ina mai da nunfashi kamar wacce aka biyo.


Ina shigowa falo na ƙura ma A'isha ido wacce ke ma Mom magana, dan itama shigowarta kenan.



“Mom wallahi A'isha ta yi kuka, kinsan menene........dukanta ya yi a cikin mota, sannan ya mata kashedi akan dole ta aureshi. Na gaji ai, shine saboda rainin wayau ya fito yana ba ta haƙuri harda share............... ” da sauri Aisha ta janyo Ni kusa da ita, Ita dai Mom ko kallona ba ta yi ba, dan kuwa tasan halina.

Zama A'isha ta yi tana riƙe da ni, zaunar da ni ta yi sannan ta ce.

“Inayah, me yasa kike son ɓata min rai? Me yasa kullum kike sani magana? Ba ki sona ne ko mene, ban fahimta ba kimin bayani?." Ta faɗa cike da raunin da ya sa Mom ta mai da hankalinta akan mu.

“Ki faɗa min.......ina jinki?." Da sauri na miƙe tsaye ina girgiza kai.

“Aisha, ban tsane ki ba............”

“Karya ne Inayah.” ta faɗa tana share hawaye wanda suka zubo mata.

Da sauri na isa gabata ina mai ɗago fuskarta.

*“Ban da ƙannai wanda zan sanya kuka, banda wanda zan duka ya yi kuka...........kawai ina miki wasu abun ne saboda na samu abokin faɗa, ke kuma komai da gaske kike ɗauka...........shine matsalarki............wallahi A'isha Ina miki muguwar soyayya. Na yarda ni ina sanyaki kuka, amma wallahi.......wallahi.......wallahi duk uban da ya sanya ki kuka a rayuwa, bayan ni sai na sa shi shima, duk wanda ya ɓata miki rai wallahi sai na rama miki........koda ko waye, na fita ne dan ga saurayinki, so nake na fahimci waye shi, dan wallahi bazan yarda wani ya sa ki kuka ba................wannan alƙawari na ne duk wanda ya saki kuma sai na rama miki, kisa wannan a kanki............har abada.”* 

Da haka ya bar musu falon, cikin zafi-zafi da ɓacin rai na haye stairs, saboda sauri, bibbiyu nake haɗawa.


Da idanu suka bi ni dan kallon yarinya suke min, amma a yanzu sai suka ji maganganuna suna shiga kansu. 

Mom ta taso har zuwa in da A'isha take zaune, zama ta yi, da sauri suka rungume juna cikin soyayya.

“Mom wacce irin ƙanwa nake da ita?, sam ba a fahimtar ta, tana da shiga rai ga gundura, wallahi ni kaina ina mugun son Inayah.” ta faɗa wani kukan na kwace mata.

“Mu yi ta mata addu'a kawai, sai kace mai iska. Dama ina faɗa miki duk soyayya ce yasa take ɓa ta miki rai.” 

“Hmmmmm Inayah.” Sai Mom ta saketa.

“Akwai in da sanya mutum damuwa ya zama soyayya?."

“To ku na ku haka yake.” sai suka yi murmushi suna ƙara jin soyayyar Inayah har cikin ɓargo da jininsu.............✍️
END.

> Hmmmmm karku manta furucinta dan nan gaba zai ƙara bayyana........a wata siga............


> Ayan da A'isha wannan wani irin ganganci ne, lallaikam.

> Me kuke tunanin zai faru?

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.