Free chapter · Read without an account

Page 1

by ZAINAB LAMINU · ROMON BAKA

*ROMON BAKA*

     *WRITTEN BY*
*ZAINAB LAMINU SANI*
      *(Abidah)*

*First class writer's association*

Wannan labari ƙirƙirarren labarine duk wanda ko duk wacce tayi labarin nan yayi dai-dai da rayuwarta to arashi a ka samu.

Bismillahir Rahmanir Rahim.

"Aminatu kiyi haƙuri, komai me wucewa ne a rayuwar nan, babu abinda baya wucewa kin ji, ki cigaba da haƙuri in sha Allahu komai zai zama tarihi za ki ga kamar ba ai ba a rayuwar ki, za kiyi farin ciki kamar kowa amma sai kin yi haƙuri kin juriyare komai kin mai da komai ba komai ba a gurin ki kin ji Aminatu na. Nasan kina yi amma ki ƙara a kan wanda na san ki da shi, nasan zaki fuskanci ƙalubale da yawa a zamantakewar ki dama rayuwar ki, ballema da Allah ya haɗa ki da mugun miji, sai kin yi haƙuri kin san duk wanda a ka cewa ya yi haƙuri an zalince shi ne, Aminatu da sannu komai zai shuɗe".
Kalaman mahaifina na shekarun baya suka kutso min cikin tunani na,wani kuka mai ƙarfi ya sake ƙwace min sanda nake tuno maganganun kamar a sannan yake yi min su.

"Allah sarki Baba a she kai ka hango min abinda ni ban hangowa kai na ba, kaicon zuciyata da kika hana ni ganin abinda mutane da yawa suke ta ƙoƙarin ganin sun fahimtar da ni, kaico na!". Na ƙarasa maganar ina gursheƙin kuka.
Saurin share hawayen dake kan fuskata nayi, ina miƙewa daga durƙuson da nayi, saboda jin shigowar motar Baban Irfan fitowa nayi daga ɗakin nasa na fito falo.

Jin ana ƙwanƙwasa ƙofar ne ya saka nayi wata irin zabura sai kuma na isa jikin ƙofar da sauri zuciyata na gudu kamar zata faso ƙirjina ta fito, saboda gudun abinda ka iyi zuwa ya dawo, hannuna na rawa kamar yadda ilahirin jikina ke rawa na buɗe ƙofar, take kuwa tayo baya idanuwanna suka yi arba da wanda suke fargabar gani, zuciyata ta matse a ƙirjina,duk da kuwa ya kasance mafi soyuwa a guri na.

"Sannu da zuwa". Baki na yayi ƙarfin halin furtawa yana rawa, saboda cin karo da wani mugun kallo da yake min, muƙut na haɗiyi yawu, saboda yadda kallon nasa ya dirar min kamar an bugamin icce, hannu na miƙa zan amshi jakar hannun shi amma sai ya ɗaga min hannu a lamar baya buƙata, ciki ya wuce ba tare da ya amsa ko sannu da zuwan da na yi masa ba, ina ganin shigewarsa na saki hannun ƙofar ina jingina da ita tare da sake sakin wani marayan kuka mai taɓa zuciyar me sauraro, dan kuka ne da yake fitowa tun daga ƙasan zuciyata, saboda samun irin wannan tarbar daga gurin mutumin da ban taɓa tsammani ba.

"Ummin mu! kuka kike kema naga Yah Irfan shima yana kuka". Wata ƙaramar murya ta faɗa tana ɗora hannuta a kafaɗata, saurin share hawaye na nayi ina juyowa, hannun yarinyar na riƙo ina sakar mata murmushin da iya karsa kan leɓe na ce, "A'a Ayshat ba kuka nake ba kin ji". "Ummin mu to idon ki ya yi ja?". Yarinyar ta sake faɗa, "Ehh Aysha yaji ne ya shigar min ciki, maza ki je ki kwanta kin ga akwai school gobe kin ji". "To Ummin mu kema za ki yi barcin ko?". Kai na ɗaga mata alamar zanyi, sannan ta wuce ɗakin su.

Bani na tashi daga gurin nan ba sai da naga agogo ya nuna ƙarfe ɗaya saura na dare, kafin na iya jan shanyayyun ƙafafuwana da nakeji kamar ba a jikina suke ba, na nufi ɗaki na ina haɗa hanya tsabar hajijuyar dake neman zubar da ni, koda na shiga ban kwanta ba zama nayi ina sake buɗe wani sabon babin tunanin yadda rayuwa take juyin waina da ni, kai na haɗe da gwiwa ina cigaba da sanbatu kamar wata zararriya, kuka nake ina faɗin "Wayy! wayy! rayuwa me yasa?, me yasa ne sai nii?, wai ni ka ɗai ce a duniyar nan ne da nake fuskantar ƙalubale irin haka?, tunda na tashi a rayuwata ban san wani abu wai farin ciki ba, na ɗauka da zarar na haura waccan rayuwar shi ke nan, a she tsugunno ba ta ƙarewa rayuwa ta ba, me yasa rayuwa kika zaɓa min haka?, wai dai ko gaggawa nake ne a cikin lamura na ne,da nake dakushewa kafin na kai ga nasara?, na ɗauka jajircewa tana saurin kai mutum ga nasarar sa ne, amma ni me yasa tawa jajircewar a kullum ta kan zuwa da ƙalubale ne, bata kai ni ga nasara ta kamar kowa?, kaicona kaicon zuciyata da tarufe min ido a dai-dai gaɓar da ya kamata a ce na ɓuɗe tunani da zuciya dan ganin abinda ya dace da rayuwata.

Amma inaah so da ƙaunar da nakewa Zayyan ya hana nayi amfani da waɗan nan damarmakin guda biyu da hannuna wajen zaɓar abokin rayuwa na gari, amma duk sai banyi hakan ba na afka kogin son wanda bani bace a gaban shi ba, ire-iren wa ɗan nan sabbatun na dinga yi.

Ganin fa wankin hula na neman kaini dare ne, ya saka ni miƙewa daga kan gadon da nake, alwala na ɗauro kafin na zo na tayar da sallah, najima ina miƙawa ubangiji kukana kan waɗann shuɗaɗɗun alamuran da suka yiwa rayuwata ƙawanya a ɗan ƙanƙanin lokaci.

Dan na san shi kaɗaine zai iya fitar da ni daga cikin wannan halin da nake ciki, domin ƙudura da buwaya duk nasa ne, shine mai jujjuya alamura a duk sanda ya so, a kuma lokacin da ya so.

Allah maji roƙon bayin sa, sai ga shi duk wani ƙunci da baƙin ciki dama wani mikin zuciya duk sun kwaranye.

Yadda naga rana haka naga dare, dan ban tashi a nan in da na gama munajati da ubangiji ba sai da na ji kiran sallah a kunne na, miƙewa nayi na ɗaura alwala kafin na kabbara sallah koda na idar zama na cigaba dayi ina addu'o'i a kan Allah ya kawo gyara a zamana da Zayyan, dan duk da halin da zuciya da gangarjiki suke ciki ban taɓa jin son rabuwa da Zayyan ba, na gwammaci shanye dukkan wani abu da zai min, wannan shi ne adadin ƙaunar da nake masa.

Duk da barcin dake idona, amma ban iya komawa ba, kicin na shiga dan samamana abin karin kumallo, sai da na gama haɗa komai sannan na kawo falo.
Ajiyewa nayi nabnufi ɗakin yara, koda na shiga tsayawa nayi ina kallon yaran nawa da nake matuƙar so, tashin su nayi na yi musu wanka.

Sai da na gama shiryasu sannan muka fito falo dan yin karin kumallo, abincin na zu ba musu kafin nima na zuba nawa, amma koda na zuba sai na gagara ci, dan na kasa kai koda lokaci ɗaya baki na, miƙewa nayi ina nufar kicin wani abincin na zuba da ban na nufi ɗakin Zayyan da shi, duk da yadda zuciyata take lugudan daka amma ban tsaya ba, sai da na dangana da ƙofar ɗakin na shi.

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.