Free chapter · Read without an account
Page 49 _ 50
💔NAUYIN BAKI....👄💔
Na
Uwar Batoorl.
𝗕𝗜𝗦𝗠𝗜𝗟𝗟𝗔𝗛𝗜𝗥 𝗥𝗔𝗛𝗠𝗔𝗡𝗜𝗥 𝗥𝗔𝗛𝗘𝗘𝗠
اللهم صلى و سلم على سيد نا رسولله SAW 🖤🤍
End of book1.
Last free page.
🅿️ 49 _ 50
⭐️
Umma ta na haurawa sama ɗakin Abba ta same shi har ya yi shirin kwanciya, sallamar da ta yi ya amsa yana ɗan sakin murmushi ya ce, "Umman amarya."
Da murmushi Umma ta ƙarisa wajan Abba ta na faɗin, "Barka da hutawa uban amarya, rankashidaɗe mijin Halimatu."
Jinjina kai Abba ya yi alamar ya amsa, sannan ya ɗaura da faɗin, "Wai yaronnan Abubakar ƙaura ya yi saboda maganar auta?"
Murmushi Umma ta yi tare da cewa, "Abbansu ni ma ban sani ba gaskiya, duk da ba na tunanin maganarta ne, dan mun yi magana da shi bayan dawowarku masallaci, daga haka kuma duk bamu san da tafiyar ba, sai da Khausar ta ƙira shi sannan muke jin wai ya tafi Adamawa, kuma kamar lamarin aikinsu ne ya kai shi."
"Shikkenan ai, Allah ya taimaka ya musu albarka duka, Allah ya kare shi ya dawo da shi lafiya, sai ya dawo za mu yi magana in sha Allah."
Da, "Amin", Umma ta amsa, sannan suka cigaba da tattaunawa a kan batun Sadeeq.
⭐️
SADIYA POV
Ƙayataccen Nupe day suka yi, an sha kyau, an sha hotuna da videos, an sha bidiri, duk wani abu na al'adun yaren sun yi, Sadiya amarya ta sha kyau kamar a sace ta a gudu, ƙawaye sun daddafi busy.
Washe-gari Juma'a aka gabatar da walima, inda aka gayyato fitacciyar malama ta zo ta gabatar da nasiha, jan hankali da shawarwari ga amarya da ma ɗaukacin mata, masu aure da marassa aure har ma zawarawa, sosai malamar ta yi nasiha mai ratsa zuciya da jiki, musamman akan yacce mutuwar aure ke yawaita, sai a rasa daga mazan ne ko matan ne, kuma ko ma daga waye ne, ana so dai mutum ya kiyaye haƙƙoƙin da ke a kansa, kabarin kowa daban, dan haka ba a tsammanin mace ko namiji wai ɗaya ya ce shi ma zai yi kaza tunda ɗayan na yi, kowa ya kiyaye kuma ya gyara tsakaninsa da ubangijinsa, lokaci ba ya jira, rayuwa gudu take, Allah ya datar da mu duniya da lahira, ya azurtamu da zaman lafiya da ta haƙuri, ya raya zuri'a ya albarkacesu, marassa aure daga zawarawa har budurwaye Allah ya kawo na gari, ya ba da haƙurin zama.
An raba kyautuka na gani na faɗa a wajan walimar, yayyun amarya su ne suka ba da gudumawar kyautukan, Khalid da Sa'ad.
Hidima ake da bidiri ba kama hannun yaro, kowa bai da burin da ya wuce, gobe ta yi cikin yardar Allah, a ɗaura aure a miƙa amarya gidanta a ƙarisa shagali.
A ɓangaren amarya da ƙawayenta sai raha da zolayarta suke yi, kowa da abinda yake faɗa, tijara irin ta ƙawaye duk sai cika Sadiya suke yi da shi, ita kuwa baiwar Allah wunin ranar gaba ɗaya tun da aka gabatar da walima cikin sanyin jiki take, ta rasa me ke mata daɗi, Haidar har sannan bai neme ta a waya ba, illa iyaka saƙon da ya turo mata wanda ya tabbatar mata da lallai Yaya Umar ya masa maganarta da Yaya Sadeeq, hakan ba ƙaramin damunta ya yi ba, duk yadda ta so ta samu yin magana da shi ya hana ta wannan damar, saƙon da duk take tura masa ba alamar ya buɗe balle arziƙin reply, ƙira kuma ba ya shiga ma layinsa ko ta ƙira, ta rasa me ke mata daɗi, ko da ta yiwa Zahra maganar haƙuri ta bata kawai, dan ko ita ta rasa ya za suyi, dan da alama Haidar ya hau dokin fushi sosai, sun ƙirasa ta wayar Zahra ma bai ɗauka ba.
Duniya ta yiwa Sadiya matuƙar zafi, har take lissafa ranakun shirye-shiryen bikinta, a cikin ranaku mafiya ciwo da ƙalubale a gare ta, gabas da yamma abubuwan ba sauƙi ba daɗi, har kowa ya yi bacci idanuwanta biyu ta kasa bacci, ga shi gobe ɗaurin aure amma Yaya Sadeeq ma bai dawo ba, ya na lafiya? Ya jikinsa? Da sauransu kaf yawo suke a kanta, zai samu zuwa bikin ma balle walicci, Yaya Umar da yayi shiru ya zuba mata idanuwa shi da Mama sun haƙura ne ko kuwa akwai abinda suke shiryawa? Waɗannan tambayoyi da suka mata caa a ka da zuciya ya sanya ta tashi ta ɗauro alwala kawai, ko da ta fito banɗaki, salla ta gabatar har dare ya raba, sai can wajajen asuba, ɓarawon bacci ya yi gaba da ita.
***
Kansancewar ana ida sallan Azahar za a ɗaura auren, tun kamun a ƙira salla Salma ta cancarawa mini ƙayataccen kwalliya mai muminin kyau, na haɗe cikin leshi ruwan sararin samaniya, wanda ya sha ɗinkin riga half gown da straight skirt, manyan duwatsun da aka yi adon leshin da su jefi-jefi, ba ƙaramin sake ƙawata leshin suka yi da ɗinkin ba, tamkar matashiyar ɗawisu haka na fito saboda haɗuwa da kyau.
Hira da dariya muke yi da ƙawayena, suna tsokanata, wai yanzu kam na girma na fita sahun ƴammata na koma sahun matan aure.
"Muna nan muna jiran Al-Sad ɗin ya ƙira ya shaida miki an ɗaura", faɗin su Nussy ƙawaye, da su ma suke a shirye, so suke su yi mini video wai idan ina waya da Haidar ɗin.
Daga cikin ɗakin da muke muka fara jiyo hayaniya-hayaniya a cikin gida, a maimakon sanarwar an ɗaura aure sai salati da koke-koken wasu jama'a, hakan ya sanya ƙawayena kaf suka miƙe dan ficewa su jiyo me ke faruwa, ni ma da nake zaune zuciyata na mugun bugawa, gabana na faɗuwa tamkar numfashina zai yanke, ganin shiru ba wacce ta dawo ɗakin a cikinsu, ga tsanantar hayaniyar fiye da ɗazu, sai na miƙe da sauri dan na fice na gano wa kaina abinda ke faruwa, saboda na cika da tsoro da kuma fargaba, gidan aure da ya kamata ya cika da shewa da guɗa, ya na ƙoƙarin komawa gidan makokin da ba ma fata, hakan ya sanya na fita na fara tambayar me ke faruwa, amma ba wanda ya ba ni amsa saboda kusan dukka jama'ar kuka suke, wasu kuma salati suke yi, hakan ya sake birkita ni na kiɗime, mayafin da nake rufe da shi ma sake shi nayi ya faɗi, ban tsaya bi ta kan shi ba kai tsaye na nufi wajan da na hangi a Mama zaune ta na kuka, ga jama'a ana bata haƙuri, cikin damuwa da muryar da ke nuni da ina gaf da fashewa da kuka na ce, "Mama menene? Me ke faruwa?", na faɗa ina durƙushe a gabanta, hannayena a saman guiwanta.
Mama cikin kuka ta ce, "Sadiya mun rasa mai babban suna, Babana ya tafi ya barmu, Sadiya Yayanki Sadeeq ya rasu."
Wani irin zaro idanuwana na yi, cikin rashin fahimta da gasƙata abinda Mama ta faɗa, na miƙe tsaye na juya da nufin dubo Umma, a cikin cunkosan jama'ar da firgici ya sa na kasa shaida su balle banbance su, domin na san ko da Mama za ta ce Yaya Sadeeq ya rasu saboda ba ɗanta ba ne, ai Umma ta san zafin shi, ita ta haife shi ba za ta faɗa hakan ba, sai dai ban yi taku uku cikakku ba, wasu jama'a suka shigo cicciɓe da mutum a cikin taburma a naɗe, cikin mutanen har da Sa'ad, Khalid da Abba da Yaya Umar, kana ganin idanuwansu ka san suna cikin damuwa da alhini, Khalid da Sa'ad hawaye ma suke yi, Umar kuma jijiyoyin kansa sun yi mugun tashuwa, Abba ba a magana, domin tashin hankali ne da dammuwa kwance ƙarara a kan fiskarsa.
"Jama'a ku gyara a ajiye gawan", wani bawan Allah ya faɗa hakan cikin waɗanda suka cicciɓo gawar.
"Abubakar Sadeeq mutumin kirki ne, addu'a yake buƙata ba kuka ba, halinsa na gari ya bi shi", wani mutumin ya kuma faɗan haka.
Idanuwana a kan su har suka shumfiɗe mutumin da suka shigo da shi cikin taburma a ƙasa, a mugun haukace na yi wajan dan a ganina ƙarya kawai ake yi, kawai an yi wa Yaya Sadeeqna haka ne don ba'a son shi, in ba haka ba ya za'a yi a ce ya mutu.
Ina isa kan gawan kamun na tsugunna, Yaya Umar ya sha gabana, ba tare da na ankara ba sai jin sauƙar gigitattun maruka na yi hagu da dama, bai jira na gama dawowa hayyacina ba, ya nuna ni da yatsa, cikin yanayin da ke nuni da baƙin ciki da damuwa gami da tsanata da yake yi, ya ce, "Ke ce kika kashe shi, ke ce silar mutuwarsa, ke ce ajalinsa, me za kiyi kuma a kan gawarsa? burinki ya gama cika kin auri wanda kike so, shi kuma da ba kya so kin zama sanadiyar mutuwarsa, Sadiya babu mu babu ke, ki je ga ki ga duniya ga Haidar, tunda kika zama sanadin na rasa Aminina to a wajanmu ke ma matacciya ce."
Mama cikin kuka ta taso daga inda take zaune ta nufo mu, ta na isowa bata yi wata-wata ba ita ma ta kwashe ni da mari, ta kuma rufeni da duka, sannan ta ce, "Na yafe ki Sadiya, na yafe wa Aliyu ke, ke ce sanadin rasa mutum mai karamci da mutunci irin babana, ki je ki zauna da wanda kika zaɓa, domin baki zaɓemu ba kuma ba ki ɗauke mu a komai ba, da kin ɗauke mu a komai, to tabbas za ki ji shawarar mu ki auri wanda muka so ki aura, amma tunda kika bijire har haka ta faru, ki je ga ki ga Aliyu nan, ba na son na sake kallon fiskar mai kama da ke balle ke Sadiya, ko mutuwa nayi ba na buƙatarki kan gawata", ƙarishe maganar Mama ta yi tare da yanke jiki ta faɗi.
Ban samu damar magana ba, daga Yaya Umar har Mama ba wanda ya barni na ja numfashi da niyar yin magana, hakan ya sanya cikin tarin ciwon abinda nake ji a zuciyata, na buɗe baki da niyar sakin ƙara, amma ban kai ga yin ƙarar ba zafin wani abu da ya daki bakina ya katse ni, ko da na kai dubana sai kuɗaɗe na gani, ina ƙoƙarin ɗago kai na, sai kalaman Yaya Umar suka dirar mini a kunne, kalaman da ke nuni da shi ne ya jefe ni da kuɗin.
Ya na nuni da hanyar ficewa a palourn ya ce, "Ga ƙudin sadakinki nan, ki tattara naki ya naki, ki fice a gidannan, kar ki yi kuskuren zuwa kan gawar Aminina balle na uwar da ta yafe wa wanda kike so ke, kika sake kika waiwayo gidannan to ke ma gawarki za a fitar wallahi, ki je mun yafe ki matacciya kike a wajanmu daga yau."
Kuka kawai na fashe da shi mai cin zuciya, ina ƙoƙarin durƙushewa a wajan, sai Yaya Umar ya yi saurin riƙo hannuna ya fara ja na ya nufi ƙofa dan fitar da ni a gidan, duk kukan da nake yi da ƙoƙarin turjewa kamar ba na yi, abinda ya daɗa tsorata ni da fitar da ni a birki, bai wuce ganin kowa da kowa na tsaye amma an rasa mai cetona, an rasa mai ba wa su Yaya Umar haƙuri, an rasa mai saka baki a barni, na je ga Yaya Sadeeqna da ake masa kallon ya mutu, an rasa mai taimaka mini na je kan mahaifiyata da ta faɗi ban san a mace take ko a raye ba, su Abba su aunty Kulu kowa ma ba wanda ya ce komai, Umma ta na durƙushe gaban gawar da aka ce ta Yaya Sadeeq ne, ta na kuka ita da Aunty Khausar, ko ɗagowa su kalleni ba suyi ba balle su tausaya mini.
"Wayyo Mama, Umma ku taimakeni, Abba, gwaggo na, auntyna, Yaya Umar ka yi haƙuri na tuba, ka ƙyaleni na yi magana da Yaya Sadeeq, Yaya Umar Mama kar ta tafi ta barmu, ka barni na yi magana da Mama ta yafe mini, wallahi na fasa auren Haidar, Yaya Sadeeq nake so, shi zan aura, na tuba zan auri wanda kuke so na aura, Yaya Umar kar Yaya Sadeeq ya mutu bai aureni ba wallahi ina son shi, na tsani Haidar, Yaya Umar zan mutu, zuciyata.....", sumbatu da kuka kawai nake yi, ta inda nake shiga ba ta nan nake fita ba, neman agaji da magiya ba kalan da ban yi ba, amma sai da Yaya Umar ya kai ni har ƙofar gida, sai sannan ya tsaya tare da ƙwaɗa mini wani mahaukacin mari, ya nuna ni da yatsa bai ce komai ba, yayi ƙwafa kawai ya hankaɗa ni ya tura ƙofar gidan ya rufe bayan ya shige.
Durƙusawa na yi a wajan ina dafe da kunci saboda azahar marin, don marin da Yaya Umar ya mini ya tafi da ji na da ganina na wasu daƙiƙu,ko da na ga ya garƙame ƙofar gidan, hakan ya sa cikin wani mahaukacin karaji na ɗaura hannuwana duka biyu a kai na, sannan na tsala wani irin razanannen ihu mai ratsa dodon kunne da gusar da ji na wasu daƙiƙu.
***
"Sadiya, Sadiya, Sadiyaaaaa", Umma ta ƙira sunanta da ƙarfi ta na jijjigata.
⭐️
ALIYU HAIDAR POV
***
Hajiya ce a zaune ta tusa Alhaji a gaba, ta na masa bayani, shi kuma sauraranta yake da dukka na zomayensa, bai ce komai ba har sai da ta kammala bayaninta ta yi shiru dan kanta, sannan Alhaji ya muskuta tare da jan gauron numfashi ya ce, "Hajiya duk sai bayani kike yi, wanda sam ba na fahimta wallahi, na kasa gane me kike nufi."
Hajiya ɓata fiska ta yi ba sosai ba, sannan ta ce, "Magana ta gaskiya kuma ta domin Allah, ka san me nake nufi Alhaji, ai ba tun yau ba nayi maka maganar."
"In ma na sani to na mance", Alhaji ya faɗa murya ba amo, saboda ba son jan maganan yake yi ba, ba ya son abinda zai sa Hajiya ta dage sai ta takurawa Haidar, amma yana ganin alamar ta yi nisa kuma ta gama shirinta.
Hajiya ba ta damu da yanayin amsar da Alhaji ya bata ba, ta ce, "Ai mai nema ba ya fushi Alhaji, ko me kai da ɗanka za ku ce it won't bother me, damuwata kawai a yi auren duka biyu lokaci ɗaya, tun sanda muka yi maganar lefe da kai na sanar maka, so nake ya auresu lokaci ɗaya, ko da bata tare ba to kawai dai a haɗa auren, yanzu ana satin biki, jiya har an kai lefen ita Sadiya, na san kuma ya gama sallamarta da kuɗaɗen hidindimun da za ta yi, amma mu nan ko sisi ba a bai wa Husna ba, hakan kuma bai kamata ba."
Guntun murmushi Alhaji ya yi, sannan ya ce, "Idan ban yi ƙarya ba ai maganar lefe, ce mini kika yi, kin raba musu su biyu, duk da ba haka ya kamata ki yi ba amma na yi shiru ban ce miki komai ba, Hajiya bansan meyasa kike dagewa har haka ba, amma dai ina binku da fatan alkairi, ni ba ni zan bayar da kuɗin hidima ba, shi zai bayar da kansa, sai ki same shi ku yi magana, maganar lefe ce ke kaina dama, da an kai wa sadiya set uku yacce muka yi, to da yanzu ita ma ukun za a haɗo mata, amma tunda kin raba musu, shikkenan kuɗaɗena sun huta, Aliyu ya yi sauran hidimar matansa tunda shi zai zauna da su ba ni ba, maganar gida ma duka kin hutar da ni."
"Amma ai Alhaji mun yi da kai za ka masa magana idan lokaci ya yi."
"Lokacin ai ina nufin bayan bikinsa da Sadiya ne, amma tunda kin dage yanzu sai dai a haɗa sai ki masa magana da kanki, ni dai ina muku fatan alkairi duka, Rabbi ya ba da zaman lafiya da ta haƙuri ya haɗe kawunansu."
"Amin Ya Rabbi", Hajiya ta amsa rai ba daɗi, domin ta san za su kai ruwa rana ne kawai da Haidar, tunda ita ba iya ɗaukar kuturun zuciyarsa za ta yi ba, abinda ya sa kenan ta ce Alhajin ya yi masa magana, tunda shi Alhaji ya na iyawa da zuciyar Haidar ɗin, amma tunda haka ne ba matsala ai ita ta haife shi ba shi ya haifeta ba, za ta san yadda za ta yi.
Daga haka Alhaji ya ci gaba da aikin da yake yi a na'urarsa, Hajiya kuma ta tashi ta fice a ɗakin ta wuce nata ɗakin, ta na shiga wayarta na soma kukan neman agaji, kai tsaye inda ta ajiye sa a kan bedside drawer ta nufa, amsa ƙiran ta yi, tare da zaunawa a bakin gadon, ta kara wayar a kunnenta, ba ta ci wasu mintuna ba ta gama wayar, sai da ta tura wa matar da suka yi magana, kuɗin da ta buƙata, sannan Hajiya ta aje wayar ta na faɗin, "Ina daidai da zuciyarka da shegen kafiya da taurin kanka, idan an ɗaura auren ka sako mini ita a take, kuma duk kuɗaɗen da na kashe sai ka biya ninkinsu."
Da yamma Nihal ta shirya dan zuwa Henna partyn Sadiya, sai Hajiya ta hanata tare da rufe ta da faɗa, a kan ba ta son Husna ba ta kishin Husna, idan ba haka ba mai zai hana ta tsaya a yi cocktail partyn da Husna za ta yi, dan dole Nihal ta haƙura da zuwa Henna partyn, ta tsaya wajan su Husna aka yi cocktail partyn.
Washe-gari nan ma ta so zuwa Nupe day, amma ƴan uwan Hajiya da suka zo, suka cinyeta da magana, dole ta tsaya aka yi Berom day da ita, kasancewar su ƙabilar Berom ne a nan yankin Jos, kuma sun gabatar da shagalin ranar yaren nasu, cikin ado da al'adun yarensu, kama daga shigarsu, abinci har da waƙoƙin duk na yaren ne.
Haka ranar Waliman ma again Nihal bata samu zuwa ba, baƙin ciki kamar ta haɗiye zuciya, hakan ya sa ta samu Haidar da maganar hanata zuwa da Hajiya ta yi, amma Haidar da yake cike da taƙaicin maganar da Umar ya faɗa masa, zuciyarsa a cunkushe ga rashin waya da Sadiya, hakan ya sa ya ce da Nihal, ta yi zamanta kar ta damu.
A zahiri ne ya faɗa wa Nihal haka, amma a baɗini a zuciyarsa ya ji ba daɗi na haka da Hajiya ta yi, abun ya haɗe masa ga maganar Umar, ga fushi da yake yi da Sadiya, ga kuma abubuwan da Hajiya ke masa, sai dai tattara komai yayi ya aje a gefe ya bar shungullolin bikin kawai a gabansa, don ga gudu ba ja da baya a aurensa da Sadiya.
Lamura na ta tafiya har dai ranar Asabar, wacce ta kasance ranar ɗaurin aure, aka ce rana ba ta ƙarya sai dai uwar ɗiya ta ji kunya.
Haidar tun wuri ya shirya, suka nufi masallacin da za a ɗaura auren shi da abokanansa, dan a babban masallacin Juma'a ta garin gaba ɗaya za a gabatar da ɗaurin auren, ko da suka isa ba jimawa Alhaji da ta shi tawagar suka iso, ga su Abba da tawagar sa mutanen Minna, baffanu da kawunai da yayyun su Sadiya.
Saɓanin ko da yaushe da idan Haidar ya haɗu da su Umar ya ke gaisawa da su cikin mutuntawa, fara'a da kuma girmamawa, to wannan karon wani irin kallo yake bin su da shi, musamman ma yadda yake kallon Sadeeq, sai dai saɓanin Umar shi Sadeeq normal fiskarsa yake kuma haka ya kalli Haidar, dan kallo ɗaya ya masa bai sake kallon inda yake ba, kuma fiskar Sadeeq a yalwace da murmushin da ya sake ƙawata shi, ya kuma sake fidda kamalarsa da kamewarsa.
Umar wani irin kallo mai wuyar fassara yake aikawa Haidar, saboda ya na tuna maganar da suka yi ranar da ya sanar masa ya yi haƙuri, amma Haidar ya shafe wa idanuwansa toka ya faɗa masa maganganu, wanda ba a karan kansa ne ya dame shi ba, wanda ya faɗa a kan Sadeeq ne ya fi damunsa.
Kallon-kallo ke gudana tsakanin Haidar da Umar, har dai aka fara shirye-shiryen gabatar da ɗaurin aure.
Ko da Haidar ya ga mazaunin da Sadeeq ya zauna, ba ƙaramin ɓaci ransa ya yi ba, domin muddin Umar ya ce zai ta da maganar hana sa auren Sadiya a masallacin, to komai zai faru sai dai ya faru, kai komai ma na iya faruwa amma ba zai iya bar wa Sadeeq Sadiyarsa ba, ba ya jin ko zai mutu ne zai bar Sadeeq ya auri Sadiya, kishi ma ba zai barsa ba kar a kai ga son da yake mata.
Wani irin kallo yake yi wa Sadeeq, kallo mai ma'anoni da yawa, domin ya rasa kunya zai ce wa Sadeeq ya ji, ko asara zai ce yayi na son yarinyar da ta ɗaukesa fiye da yayanta ciki ɗaya, haka kawai ya dinga nuna shi mutumin kirki ne shi mai son abinda Sadiya take so ne, amma ashe da lauje cikin naɗi, shiri yake ya kassarata ya rusa ta, don ba ko wai yana da tabbacin shi Sadiya take so, daga ƙiran da take masa da saƙo ya san shi take so, ko damuwar da ya ji ranar a muryarta, bai da haufi ba zai wuce a kan maganar Sadeeq ba ne, shiyasa ya haƙura amma sai ya nuna mata muhimmancin sanar da shi halin da ake ciki tukunna.
Nisa da Haidar ya yi cikin tunani ya hana shi sanin me ke tafiya a wajen, sai ji yayi ana shafa fatiha, hakan bai kaɗa masa zuciya ba kamar jin da yayi Alhaji na cewa, "Yauwa sai a ɗaura na ita Husna da shi Aliyun, ga sadaki nan."
"Whatt? Husna dai?...", maganar da Haidar ya yi a fili ba tare da ya sani ba ya katse saboda kallon da Alhaji ya masa, sannan ne ya san ba a zuciyarsa ya yi maganar ba kamar yadda ya yi tsammani.
Wani irin tuƙuƙi Haidar ke ji a zuciyarsa, hakan ya sanya bai jira an gama ida ɗaurin auren ba ya miƙe ya bar wajan, Alhaji bai yi yunƙurin tsayar da shi ba sanin halinsa, sai da aka kammala komai sannan jama'a suka fara ficewa a masallacin.
Haidar da idanuwansa ke kan ƙofar, ya na ido biyu da Sadeeq da ya fito ya na sakin murmushi, wani irin sake baƙancewa zuciyarsa ta yi, kai tsaye ya nufi Sadeeq ya na huci, ya na isa ya tsaya a gabansa, a fusace ya buɗe baki tare da cewa...
****
MADALLA MA SHA ALLAH MUN KAMMALA BOOK 1 WANDA YA KASANCE FREE.
SAI MUN HAƊU DA KU A BOOK 2 NA ƘARSHE IN SHA ALLAH, A NAN ZA MU WARWARE KOMAI.
MASU DARAJA HABIBTIES WAI YAYA NE?🤣🤣
KUNA DA TAMBAYOYI DA YAWA KO?
DA WA AKA ƊAURA AUREN?
HAIDAR BAI MA SAN DA BATUN AUREN HUSNA BA, SHIN YANZU DA AKA ƊAURA ZAI AMSA KO ZAI SAKAR WA HAJIYA ƳAR TA? KUN SAN HAIDAR DA ZUCIYARSA TUNDA GA SHI YA NA LARA SADIYA MA DA YAKE SO😂
ABUBAKAR SADEEQ FA?
TO WAI ITA SADIYA A WANI HALI MA TAKE CIKI TUKUNNA?
ME KE TAFIYA ME KE FARUWA?
TAMBAYOYIN DA YAWA HAR MA DA ƊAURE KAI, BALLE AMSOSHIN, KU DAI KU BIYA 500 NAKU KACAL KU MORE WANNAN TAFIYA, DOMIN HAR YANZU MA TUKUNNA BA MU JI ASALIN SU SADIYA BA BALLE AMINCIN TSAKANINSU DA SU SADEEQ.
MU JE ZUWA MASU DARAJA HABIBTIES NA UWAR BATOORL.
Sai da kuuuuuuuu🫶❤️
***
Za ku iya samun littafin a waɗannan manhajoji.
●BAKANDAMIYA HIKAYA.
●WATTPAD
@Uwarbatoorl96
●AREWABOOKS.
@Uwarbatoorl96
***
a kan Naira #500.
Idan littafi ya zama completel 1k yake in sha Allah.
# Hareeyh
# ***
# 𝘾𝙤𝙢𝙢𝙚𝙣𝙩
# 𝙇𝙞𝙠𝙚 &
# 𝙨𝙝𝙖𝙧𝙚