Free chapter · Read without an account

E.P1️⃣5️⃣⏩1️⃣6️⃣

by PRETTY SK NOVERLIST · 𝒀𝒂𝒓 𝑵𝒐𝒍𝒍𝒚𝒘𝒐𝒐𝒅

***


> Jiya munyi mistake ɗin number, Amma haka ne. Muje zuwa.




💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️

🕊️ *May Allah keep us united, uplift us, and make our pens a means of positive change.*

Much love and respect to each and every one of you. ❤️🔥  
*Keep shining, JAW family!* 🌺

   *JARUMAI WRITER'S TEAM📚✍️*


𝒀𝒂𝒓 𝑵𝒐𝒍𝒍𝒚𝒘𝒐𝒐𝒅

Story and writing✍️
      ```PRETTY SK```
           ~SAKINA ABDULLAHI~
> *PRETTYN JAJIRTATTU 💪✍️

       
 ✽‌»‌≿━༺🌹﷽🌹༻━≾»‌✽
 


E.P1️⃣5⃣⏩1️⃣6⃣.


______________________________Ina shiga ɗakina na kwanta kan gado, gaba ɗaya na ƙosa result ɗina na waec ya fito, zaman gidan nan duk ya isheni, nasan saura lokacin kaɗan na tafi Legos Wanda da ƙyar Mom ta yarda, Ina fatan komai da na tsara ya yi yarda nake so. 

A hankali na kulle idanunwa take wani ɓari na zuciyata ya min tambayar da tunda nake be ta ɓa min ba.

“Inayah.......kina so ki jefa kanki ga halaka, *NOLLYWOOD* ba wajen zuwan mata masu kammun kai bane, tsakani da Allah haka ya dace? Ko karatun islamiya ba ki so, why?.”

Shuru na yi ina maimaita maganar, da sauri na miƙe tsaye sai kuma na nufa jakkanta, takaddun Islamiya na fiddo da su, zan iya cewa na manta rabon da na yi maraja'a.

Na iya Arabic sosai, dan bama yin magana da Hausa a Islamiyya.

Ba laifi na yi karatun sosai, sai da na bi gaba ɗaya takaddun na, Fiƙihu, Hadith, nahwu, insha'i, sarfu da sauransu, sannan na ɗauki Alqur'ani.

Na haddace izu 30 gan, daga lokacin kuma na sanya wasa sosai, har zuwa yanzu ban iya haɗa 60 ba, da yake ma be dame ni ba. (Astagafirullah 😓)

Ina da kaifin hadda sosai, nan fa na fara maraja'an al'qur'ani cikin zazzaƙan muryana mai cike da taushi, ko Ni kaina nasan ina da zaƙin murya, sannan duk wanda ya sanni haka yake cewa.
 

Duk wanda ya ji karantun nan zai rantse wata Hafiza ce wacce ta ke da cikakkiyar hankali take rerowa.


Ina tsaka da karatu sai ga A'isha ta shigo tana sakarmin murmushi, da yake na kai aya sai na tsaya ina mai da mata murmushin. 

Zama ta yi gefan takadduna tana cewa.

“Ina alfari da sabuwar ƙanwar da nake gani a yau, haka nake so ki zama, ba irin wancan ba mai son abin da Allah ya hana.” nasan me take nufi dan haka na ce.

“Insha Allah na sauya daga yarda nake, kuma za ku yi alfahari da nan gaba.” na faɗa amma a zuciya kuwa cewa na yi. *‘Film ɗaya kawai zan yi, ai ba yawa.’*


“Mu yi musaffa.” ta faɗa tana gyara zamanta murmushi na yi duk da nasan A'isha ƙwarowace a karatun Alkur'ani, dan shekara biyu kenan da haɗa sittin, sannan tana zuwa musabaƙa sosai, in da ta ciyo ƙyatuttuka, amma haka mu ka fara yi cikin nishaɗi.


Sallah da cikin abinci ne kawai ya yake rabamu, tare muka shiga kitchen, Aisha ta dafa wa kanta taliya, muna yi muna hira wanda muka manta rabon da su yi tsabar rashin jituwa.

Dining area muka koma in da muka fara cin abincin abinci, sai a lokacin Mom and Dad suka fito, suma wajen mu suka nufa, zama suka yi in da Dad ke cewa.

“Congratulation my Daughter u get 200 score in your Waec.” wani irin ihu na sa ina ɗaga hannu, da sauri A'isha ta buge min kai.

“Alhamdullah.” ta faɗa sai na maimaita ina miƙewa, rungume Dad na yi da Mom Ina jin daɗi.


“Sai ki fara shiri dan kuwa tuni an sama miki gurbi a school, ko zuwa next week sai tafiya.” murmushi na yi a raina ina cewa. ‘Saura abu ɗaya.' a fili kuwa cewa na yi.

“Dad amma ba a hostel zan zauna ba ko?." Kamar yarda na yi tsammani kallona suke yi cike da neman ƙarin bayani.

“Shalele, me yasa kika ce haka?.” Faɗin Mom sai na ce

“Eh to a makarantu irin haka, sai kuga mata suna ɓata ƴan uwansu, ko da wasu ba su so dole ake musu, gaskiya ni ina jin tsoron Hostel, in dai anan zan zauna gaskiya na fasa.........na haƙura.” na faɗa ina ɓoye damuwan dake fuskanta, a raina kuma ina fatan su yarda, dan wallahi ƙarya nake ba zan iya fasawa ba.

“Gaskiya zan fi so ki zauna a Hostel, akwai masu tsaro sosai ba wani abu ai.” 

“Mom. Wallahi banso........” da sauri A'isha ta katse Ni.

“Why not a kai ta gidan friend ɗin ta, sai su dinga zuwa tare da komawa gida, sai mu roƙa ta zauna da su.” Gaba na ne ya faɗi dan babu wanda na sani a can ɗin.

“Shawarar nan ta yi, na yarda.” faɗin Dad sai Mom ta ce.

“Nima haka.” sai na yi murmushi dan jin sun yarda.



Falo muka dawo dukkan mu, A'isha na latsa waya sai murmushi take yi, Mom da Dad kallo suke yi, in da ni kuma na faɗa duniyar tunani.

‘Yanzu idan muka je Lagos, wani waje zan kai Dad? Kuma ta ya zan tsallake wannan ƙaryar? Oh Allah ka taimake Ni, ya zan yi?. So nake na zauna a gidan haya ba Hostel ba saboda babu mai takura min, na fita shooting yarda nake so.....................”

“Inayah! Inayah!! Inayah!!!." Da sauri na dawo duniyar mutane, a ɗan zabure na kallon Dad dake kirana.

”Me kike tunani?."

“Dad.........ba........ba komai." na faɗa ina turo baki tare sosa kaina.

“Ok, je room ɗina, za ki ga wani bag da na dawo dashi ɗazu, na aje a wajen bookshelf ɗaga sama.” na ɗaga mai kai ina miƙewa.





Ɗakin na shiga, ban nufa in da ya aikeni kai tsaye ba, sai gaban mirrow na tsaya nufa, na fara taɓe-taɓe, harda ƙwaɗa Jallabiyar Dad, Dan Ina son jallabiyar maza, shi yasa Mom ta hanani zuwa ɗakin, in dai na shiga saina sanya kayansa duk da sun yi min mugun yawa.




“Ba ki gani ba?.” na jiyo ya faɗa da ƙarfi.

“Gani nan zuwa............" Da haka na cire rigar da sauri, a wajen dana ɗauka na ajiye, sannan na nufa wajen da ya aike Ni, na ɗauka, sai na yi waje har da gudu-gudu.




“Dad, wani book na gani shine na fara dubawa, gaskiya ya yi daɗi." Na faɗa ina bashi Jakkan. 

“Wani book kenan?.” murmushi na ɗan yi dan bansan me zance ba.

“Ban duba sunan ba, kawai karantawa na yi.” ya ɗaga min kai yana buɗe jakkan.


Zama na yi sai kawai na ga A'isha ta nufo ni tana murmushi da na ɗauka na mugunta ne, take na haɗe giran sama da ƙasa, aikuwa tana zuwa ta kullemin ido tana cewa.

“Tashi, muje.”

“Malama sake ni.” 

“Shalele ku zo ta nan." Dad ya faɗa, sai na yi shuru muna takawa, a gabansa muka tsaya sannan na ji ya sanya min abu a cikin hannuna. Sai A'isha ta buɗe min idanuna tana cewa.

“Suprise.”

Zaro dara-daran idanuwana na yi ina kallon wata haɗɗiyar waya a hannuna.

 Tsabar an shammace ni da min bazata, sai da na durgushe ina kallon wayar. 

Hawaye ne na ji sun cika min ido, da sauri na je wayar ina rungumesa tare da mai godiya wanda bansan menake furtawa ba amma nasan godiya dai nake yi.


Daga shi na rungume Mom wacce ke ta murmushi.

“Yanzu nawa ya huta." Sai na ɗaga mata kai, A'isha na nuna mawa tare da cewa.

“Ashenty......oh Aunty Aisha, kin gani."

“Tubuli-wayuklifullahu ta'ala.” ta faɗa tana kallon wayarta ƙirar Samsung. 

“Thanks." Na faɗa ina nufa stairs da gudu. 

Ɗakina na shiga tare da aje wayar kan mudubu na fara rawar murna, sai dai na yi kaman na minti 3 sannan na tsaya, sai kuma na tsaya sai na fara gode wa Ubangiji. 

Sai da na natsu tukun na kalla wayar da ƙyau, irin na A'isha ne wanda aka siyamata bayan da na fasa mata na ta. 


Murmushi na kuma yi sannan na sumbaci wayar, sai na rungumeta a saitin zuciyata, ina jin soyayyar wayar yana shiga cikin jikina.

A kunne take dan haka na latsa, wayyo daɗi, ji nake kaman a mafarki na mallaka waya, dan kuwa wancan muna gama exam na bar ma ƙawata.


“Allah na gode ma." Na faɗa ina shiga nan in fita nan, har da layin MTN a ciki.

Jin wayar na ringing har sai da na tsorata, har ina sakin wayar kan gado.

(DAD❤️) sunan da ya fito kenan, sai da na sauke ajiyan zuciya sannan na ɗauka ina washe baki.

“Shalele sauko ƙasa." 

“To, Dad." Da haka na katse kiran sannan na mai da hulana na fito.

Kamar yadda na barsu haka na sake su, sai na nufa su, a tsakiyar su Mom na zauna.

“Shalele." 

“Yes Dad." Na faɗa ina kwantawa akan cinyar mom.

“Na baki waya yanzu, dan kin kai riƙewa, ina so ki yi koyi da Yayarki, kamar yarda take yi da waya, babu kallon banza, banda chart da ƙawayen banza, no Facebook by now, sannan in ba group na education ba banyarda ba, banda waya da maza da sunan classmate. Ki kama kanki, ki kula, kin ga wannan wayar, takan jefa mutum masifar duniya da lahira, Na aminta da tarbiyyar da na baku kuma karki ban kunya.” ya kai maganar cikin rauni da lallashi. 

Tashi na yi na rungumesa ta gefe ina jin babu daɗi


“Tabbas A'isha ba ta saɓa mana, mun yadda da ita, kema muna so ki zama haka. Duk da ke za ki yi nisa da mu amma a kodayaushe ki dinga tunawa da Allah na kallon ki, ki sa wannan a ranki, amanar kanki za mu baki, kisani idan kika ci Allah zai tambayeki, kuma ke kiwon da Allah ya bamu ne, za mu so mu rabu a duniya lafiya, mu haɗu a aljanna cikin amincinsa.” 

“Insha Allah Mom bazan baku kunya ba.” na faɗa ina share hawaye.

“Amma Dad ai zan iya kallo a YouTube?." Na tambaya duk da wallahi babu mai hanani kallon finafinan *NOLLYWOOD.*

“Eh, amma kisan me kike kalla, banda na lalata yara, kuma banda abin da be kamata ba." 

“Dama ni Film kawai, irin series haka." 

“Za ki iya but banda Nigeria Film.” A'isha ta faɗa da sigan zolaya, hararar wasa na yi mata.

“Ai Nigeria Film kala-kala ne, kaman *The king -........." Da sauri na katse Dad.

“Like, *Two father - How to bake - Treasure in the sky - Poor Mom and Rich Mom - To kill a monkey - Our problems - Maids - Love is blind etc. Ai is normal kallon su.” na faɗa ba tare da nasan aika-aikan da na yi ba.

“A ina kika san wa'inna fina-finan?." Rintse ido na yi ina haɗiye miyau, dan kuwa wa'inna kaɗan ne daga wanda ma kalla a school.

“Da ke fa nake?." Ya kuma tamabaya, dan a gida ban kallo a tv, ko na na fara za'a mai da sunna tv ko labarai.

“Da........dama ranar a wayar A'isha ne na ga an yi posting a facebook, na dukka postern kuma aka rubuta, yara za su kalla." Na faɗa ina fatan ƙaryar ya fitar da Ni.

“Ai banda Facebook a waya na." Aisha ta faɗa tana danne dariyar dake cinta.

“To a ina kika kalla?.” Mom ta tamabaye ni.

“To na manta amma a cikin wayoyin kune." 

“Nima banda Facebook a ciki." Sai na ji kaman Mom ta ƙwalamin abu ne a kai.

Fuska na haɗe ina shirin fashewa da kuka, dan in Dad ya gane ƙwarya nake, zai amshe wayar ne, dan ya tsana ƙarya.


Jin sun washe da dariya, ya sa na san wasa suke mun, ai da biyu na miƙe, ni a dole na yi fushi, na dau wayata ina hucewa da gudu.

“Ku dena zolayar min Shalele." Dad ya faɗa yana mai da hankalinsa a kan Tv.


Ina shiga ɗakina na kulle sannan na haye gado dan yau babu barci, sai dai babu komai akan wayar, amma akwai data, da haka na kunna na shiga Tiktok, sai dai Ni ban son kallon raye-raye da shirme na mutane, dan haka na koma Youtube, ai wani ɗan ihu na yi ganin ga fina-finai kaman hauka sun fito.

“School mate." Na faɗa ina kallon poster na wasu ƴam mata da samari cikin uniform na school, sun yi ƙyau sosai, duk da fuskokinsu babu alamun wasa a ciki, da haka na shiga dan kallon Film ɗin ina ji raina fes banda wata matsala................✍️
END

> Ƴar NOLLYWOOD 🔥😁, hmmmm akwai abu.

> Har yanzu ba mu fara wasan ba GUY'S 🥴🥴🥴.

> INAYAH an yi waya, gaskiya zan zo kallo nima.

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.