Free chapter · Read without an account
E.P2️⃣8️⃣⏩2️⃣9️⃣
***
𝒀𝒂𝒓 𝑵𝒐𝒍𝒍𝒚𝒘𝒐𝒐𝒅
Story and writing✍️
```𝐏𝗿𝗲𝘁𝘁𝘆 𝐒𝐊
```
~SAKINA ABDULLAHI~
> *PRETTYN JAJIRTATTU 💪✍️
✽»≿━༺🌹﷽🌹༻━≾»✽
E.P2️⃣8⃣⏩2⃣9⃣.
_(Tunani)_
Tun bayan da suka je gidan su Ayan, ta shiga damuwa sosai, amma haka ta ɓoye masu Dad. Duk a zatonta maganar shike nan ba zai kuma tashi ba, sai dai bayan kwana biyu, Ayan ya zo ya ɗauke ta, asibiti suka je aka musu takadda na ƙarya, sannan Ayan ya biya wani doctor akan ko da sun dawo, ya musu result irin wannan.
Da haka ya mai da ita gida, ita dai tun a yanzu jikinta ya riga ya mutu sosai. Again after some days, suka zo aka yi baiko, ansa tana gama exam za'a yi auren.
Dad da Mom sun yi mamakin irin uzurin da suka zo da shi na auren da wuri, sai da su sun san idan lokaci ya rantse babu wanda zai iya dakatar da haka.
A yanzu har sun kawo komai saura akwati kaɗai, rana kawai ake jira, dan sun ce ba su son komai daga wajen Dad.
Duk ta shiga wani hali sosai, ita yanzu idan sun yi aure aka gano Babu ciki ba, duk da dama zama za su yi har ta haihu sai a kuma ɗaura musu auren, a cewar su Abba. ba ta san yarda za ta yi ba in suka gane, kullum dai Ayan ce mata yake *Kar ta damu* da haka ta ke rage ma kanta damuwa...
_Ci gaba_
Murmushi ta yi wanda ke da ma'anoni da dama, ita tasan akwai ƙura bayan aure dan kuwa tun a yanzu ta ga ƙiyayya ƙarara a cikin idanunwan Baba Yusuf da Baba Yunus, hmm balle ma mutanen gida.
_Ayan_
Shi komai da ke faruwa ko a jikinsa, ɓacin ran Ummee ne kawai baya so, dan ta yi fushi da shi, duk dan Ruma, yarinyar da yasan har ita Ummee ba sonta take ba.
Abin da be sani ba shine, tun faruwar komai, Ammee da matan gidan dukkansu, sun ƙara tsanar Ummeensa, da ƙanwarsa Sarah, abubuwa dai yana faruwa amma be sani ba, kuma sun kasa faɗa mai, sai dai in a gaban su Abba ne shine ake nan-nan da su.
Kallon wayarsa ya yi ganin hoton da A'isha ta tura sun shigo, sai ya latsa yana fara cin karo da nata.
Ta yi ƙyau sosai, doguwar riga ce jikinta, sannan ta yafa gyale, tana zaune ne a kan kujera aka mata hoton, sai wani shima ta yi ƙyau sosai, sanye take da dogon hijabi.
Na ƙarshen ne ya tsaya yana kallo sosai, in dai ba gizo ba, Rose ce jikin hoton nan, duk da ta ƙara girma amma ya ganeta.
Su biyu da A'isha ne suka yi hoton, A'isha na baya sai ita Shalele a gaba, kayansu iri ɗaya wasu lifaya mai kyau sosai.
Zooming pic ɗin ya yi yana ƙare ma fuskarta kallo sosai, murmushi ya yi sai kuma ya ce.
“Allah mai iko, ashe dai ina da rabon ganinki, ashe sirikata za ki zama, kai masha Allah.” ya faɗa tana tura ma A'isha saƙo.
‘Dear gaskiya na gode, sun yi ƙyau sosai, masha Allah kawai, amma fa Shalele ta fiki ƙyau.' ya tura mata yana fita a cikin chart ɗin.
Ganin new number an yi mai sallama sai ya shiga, profile ɗin da yaga wacce ke kai, tsaki ya ja dan ko jiya ya yi blocking wani numberta.
Ta turo saƙo dan haka ya shiga.
‘Assalam Babyna, Ruma ce, me yasa kake yawan blocking nawa? Hmmm ka yi ka gama dan aure na da kai wallahi babu mai hanawa. Ko ita waccan ƙaruwar taka ba za ta hana na aureka ba wallahi.' shike nan saƙon.
Tsaki ya ja sannan ya duba reply ɗin A'isha.
‘Nasan ta fini ƙyau.........Yanzu nake faɗa mata biki sai cewa ta yi, _Dad ne zai ba da sadaka na_ ' murmushi ya yi sai ya rubuta.
“Wasa nake dan kuwa kaf duniyar nan kinfi kowa ƙyau, hmmm Shalele sai addu'a.' da haka ya kashe datan yana aje wayar, lumshe idanunsa ya yi yana ji kamar wani abu na motsa zuciyar sa......
*Inayah*
Kallon Mubina da ta fitowa daga Kitchen riƙe da babban plate na jollof chicken spaghetti, yana ta tiriri. Zan iya cewa cikin sati biyu da wasu kwanaki na gama karantar Kowa na ajin mu, da ita Mubina.
Na lura babu mai jin kanta na hayaƙi, sai dai a wajen karatu kowa ita so take ta fi kowa, hatta Mubina sune kan gaba wajen ba da amsa a gaba class, abin da ɓan ta ɓa yi ba, dan kuwa Ni in ba fito da ni aka yi bana yi, haka kuma ko na sani ban faɗa, sai abu na gaba, bana tamabaya, ko da kowa zai yi Ni dai ba zan yi ba, hakan yasa ƴan class ɗin suke ganin kaman Banda brain kawai English ne na fi su ƙwarewa.
Ko a jikina in sun faɗa haka, dan Ni ban cika shiga irin wannan ba, da dai wata maganar ne to za a ji bakina.
Ajewa ta yi tana cewa.
“Inayah, me yasa ko na baki amsa, ki dinga tashi ko faɗa miki na dinga yi, wallahi ƴan ajin mu kallon..........” sai ta ga na yi murmushi.
“Kaman be dameki ba."
“Mubina, share kawai, yanzu muke waya da yayata wai bikinta friday, shine nake tunani, gashi ba zan samu zuwa ba.” na faɗa ina ɗaukan spoon.
“Masha Allah, amma ban ji daɗi ba, ace ba ƙya gida za'a sha shagali.”
“Ba'a min adalci ba sam.” na faɗa ina jin kaman da wani abu a ƙasa, A'isha ba ta faɗa min ba amma bakinta akwai magana haka kuma zuciyarta kaman a raunane take.
Bansan na yawaita tunani marasa ƙyau hakan yasa na ce.
“Mubina ban labarin ki mana.” murmushi tana mai cewa.
“Mu gama cin abincin.”
“A'a Please yanzu dai." Sai ta kuma wani murmushin ta na cewa.
“Toh ni ta ina zan fara?......."
“Ta ƙasa.” na faɗa ina son na manta yanayin A'isha a cikin kaina.
“Uhmm, a Abuja aka haife ni, Ni kaɗai ce mahaifiyata ta haifa, to ta rasu tin Ina yarinya, a wajen kakata na girma, sai dai bayan rasuwar ta shine na koma wajen matar Babana, ba ta wani matsala, zan iya ce miki rayuwa yana tafiya min yarda nake so ne." Ta kai nan tana kai abinci bakinta.
Murmushi na yi sannan na ce.
“Ya batun Saurayi? Oh sorry samari zan ce." Na faɗa da sigan zolaya.
Hannu takai min kaman za ta bugeni sai na kauce.
“Inayah, saurayi na ɗaya, kuma ina son shi sosai.”
“Masha Allah."
“Da na kammala karatun za mu yi aure insha Allah, yanzu haka aiki yake yi."
“Allah ya kaimu."
“Ameen, to ke fa? Samarin ki nawa?." Ɗan hararan wasa na yi mata.
“Banda ko ɗaya, kuma ba zan yi ba dan ba zan yi aure ba.” na faɗa be serious.
“Ban gane ba!?” murmushi na yi.
“Yes haka ne, banda saurayi, kuma ba zan yi ba, dan babu mai aure na nan gaba.”
“Subuhanallah, Inayah wanna wani irin magana ne?." Sai na dafa kafaɗarta ina cewa.
“Da gaske nake......”
“Haba Inayah, Allah ya miki ƙyau mai suna ƙyau, a dire kike amma me yasa kike faɗin haka?."
Sai da na furzar da iska daga bakina sannan na ce.
“Saboda babu wanda zai aura Ni idan na cika burina, babu wanda zai so Ni, dama haka nake so, babu aure a agender na, babu wanda zan dinga ma biyayya kamar baiwa, babu wanda zan dinga zama yana sani aiki ko ƴan gidansu........hmmm shi ya sa ban tsamman zan iya auran kowa." Na kai nan ina latsa wayana.
“Wani buri?."
“Ina so na zama ƴar Film, ke a ganin ki waye zai aura wacce take film?.” da mamaki take kallo na.
“Film kuma!? Ke yanzu Film kike so bayan kina karatun Gynecologist............””
“Eh."
“Film ba wani tawaya bane amma yana da matsaloli sosai, a gida ma nasan ba za su barki ba." Ta faɗa tana riƙo hannayena.
Kallonta na yi sai na yi murmushi.
“Hajiya nifa ba kannywood zan shiga ba. NOLLYWOOD 🔥 nake so.” na faɗa ina kallon gefe.
“Hmmm kinsha wani abu ne yau?." Sai na yi murmushi, tashi ta yi ta nufi room ɗin ta tana kuma cewa.
“Bansan irin wasan nan please.” jinjina kai na yi dan ba ta yarda ba kenan.
A hankali na furta.
“Lokaci! Lokaci!! Lokaci!!! Nake jira, ina nan da saving number A.G, so nake na yi karatu na cikakken tearm kafin na fara nemansa.” sai na kalla number da na yi saving da, *NOLLY A.G* wato number A.G , sumbatar wayar na yi ina lumshe ido na dan number kaɗai sani nishaɗi take.....................✍️
END.
> Toh na yi nan 🚶🚶🚶🚶🚶
*📢 Assalamu Alaikum Everyone!*
Muna farin cikin sanar da ku cewa za mu *buɗe Paid Group* na littafin *ƳAR NOLLYWOOD!* 🎬📖
Idan kina son:
✅ Sabbin *updates*
✅ Karantawa cikin jin daɗi da sauƙi
✅ Tare da wasu *garaɓasa na musamman*
To *ki shirya yanzu* cikin farashi mai sauƙi:
💰 *₦300 only* kafin mu gama.
🕒 Bayan an gama: *₦500*
🌟 *V.I.P Access*: *₦1000*
_Zamu kuma ba kowa *Document* da zarar mun kammala, da kuma password_
Kar ku bari a barku a baya, tafiyar na daban ne wannan karan, domin har yanzu wasa muke yi.
```Idan kun shirya, ku tuntuɓi wannan number:
***.```
~SING BY PRETTY SK~