Free chapter · Read without an account

SHA SHIDA

by ZAINAB M BAWA · LIKITAN RUHI

LIKITAN RUHI

Na

ZAYNAB BAWA

Arewabook @Zeeeyybawa

SHAFI NA GOMA  SHA SHIDA

“Tunda baki zuwa, nima babu yanda zan je. Wallahi, duk mu zauna. Nasan Mami zata ji babu daɗi, amma zan zauna, zan bata hakuri daga baya. Hamrah, kuma, nasan fushi zata yi dani, tunda tsawon shekaru biyar ba ta taba yi celebrating  bikin ranar haihuwata ba, sai wannan karo.” Sunan Mami da ta ambata ya kusa tsayar da numfashina. Na ɗaga idona na kalleta, ina maimaita sunan a cikin zuciyata, yanda ta ambaci sunan kamar ya fito da wani irin sihiri da ya ja hankalina. ina cikin nanata sunan na ji tana ci gaba da faɗin, muryarta cike da nauyi sai dai kalaman suna fitowa da kulawa domin ƴan uwana sam basason su furta abunda zai iya taɓamun jin kimata.

“Ameerah, kin san dai, duk cikin ‘yan uwana babu wacce nake ƙauna kamar ke, Kuma kowa ya shaida hakan, Kasancewarki a cikin wani hali, nima sai da ya ragemin walwalata, amma a lokaci guda labarin zuwanki ya ba ni farin ciki mara misaltuwa, Allah kaɗai zai iya bayyana irin farin cikin da na tsinci kaina a ciki da naji cewa zaki zo zaria, a tunanin zan iya taimaka wajan rage wasu damuwowinki, Amma ashe, ba haka bane, Abunda nake tunani daban ne, ashe banda wani matsayi a wajanki yanzu. Sam, bakya sakin jiki dani, bakya hira dani, ko abu na, baki bakya iyaci sai nake ga kamar ma kinfi sakewa idan babu kowa a tare dake. tun zuwan ki naketa cikawa ƙawayena baki inata Allah-Allah na nuna musu ke cikin alfahari na bigi kirji na kiraki da ƴar uwata amma kinƙi bada damar hakan". Ajiyar zuciya na sauƙe gaba ɗaya jikina ya yi sanyi. A cikin sanyin murya, nace mata:

“Waacece Mamin?”

“Mahaifiyar su ƙawata kenan,” ta amsa babu ɓata lokac, zuciyata ta ƙaru da son ganin Mami. Amma fuska ta ta kasa bayyana hakan. Cikin sanyin jiki, nace:

“Kiyi hakuri, Miemie. In sha Allah zan gyara. Amma ki sani, bana tunanin yanda nake jinki a raina. Kina jin kwatankwacin hakan? Wani irin lamarine ya shigo rayuwata da duk yanda zanyi miki bayani, bazaki gane ba. Yanzu barina shirya mutafi. Fuskarta ta cika da fara’a cikin jin daɗi,

“Yawwa, Ameerah ta barina amso aikan wajan Ummi,” tana gama fadin hakan ta mike, tana yin ƙaramin tsalle, fuskarta cike da annashuwa. Tana fita na canja rigata zuwa abaya, na saka inner cap mai launi ɗaya da rigar, na ɗauko flat takalmi. Na ɗauki ƙwalin abayar abayas kenan ina yafaww. Miemie ta shigo, ta taja hannuna da saurinta, tana faɗin:

“Muje-muje, mun yi latti!” Na janye hannuna daga gareta a hankali, na ɗan ja da baya, kamar wacce ta tuna wani abu, sannan na ce:

“Miemie, ban ɗauko gilashi na ba.” Maganar ta fito cikin murya mai ɗauke da damuwa. Yanayin da na faɗa ya bayyana rashin jin daɗina. Amma Miemie ba ta bari nayi baya sosai ba, ta sake kama hannuna da ƙarfi, kamar tana tsoron in ɓace daga gabanta. Idanuwanta sun cika da kulawa, ta ce.

“Da Allah ki share batun gilashin nan. Idanuwanki sun fi kyau haka. Ke ba ki san irin yadda nake ji game da su ba. da ba zaki dinga ɓoyesu cikin gilashi ba, Tun da nake, ban taɓa kallon mai irin waɗannan idanu ba sai ke kaɗai. Ke ɗaya ce ta daban. Being unique is good, malama. Duk inda kika je, ki fito daban. Shi ne ainihin magana.”

Na haɗiye numfashi. Zuciyata tana bugawa da ƙarfi, ba tsoro nake ji ba, A'a bansan irin mutane da zan haɗu da su a can ba, bansan yaya zasu ɗauki kalar halittar da Allah ya yi wa idona ba.

“Miemie, don Allah" na faɗa inaja da baya,"Hakan shine ya sa ba na son shiga cikin jama’a. Ana yawan kallona kamar wani abin al’ajabi. Wasu ma tsoron idanuwana suke ji.” Miemie ko kaɗan ba ta tsaya ta saurare ni ba. Ta ci gaba da tafiya, tana jan hannuna, tana faɗin:

“Karki damu da inda za mu je. Mutanen can sun saba hulɗa da kowane iri na mutane. Idanuwanki ba za su ba su tsoro ba.” Na kalli a bayanta,  Ba don raina ya so ba, na bita. ba muyi wata tafiya mai nisa sosai ba muka kai tsakiyar layi, sannan idanuwana suka fara hango wani gida da ya bambanta da duk gidajen da ke kewaye da shi. Gida ne da tun daga nesa tsaruwarsa take ɗaukar ido, girma da tsaruwarsa ba irin sauran gidajen layin ba ne. A zahiri, a duk layin babu gidan da ya kai shi girma ko ƙayatarwa kamar an gina shi ne don ya zama abin kallo, kuma tun kafin ka isa ƙofarsa  yake ɗaukan hankalinka gaba ɗaya.

Mun kusa ƙarasawa ƙofar wannan ƙaton gidan kafin Miemie ta dai-daita nutsuwarsa ta fara tafiya a hankali sannan kuma ta saki hannuna data damƙemin shi kamar zata cire. tana gyara veil ɗin kanta ta fara faɗin.

"Ameerah kinsan Yaya Ibrahim jiya ya dawo gida weekend daga kaduna, lokacin kina asibiti, kin  dawo kuma ya fita, yau ma sassafe ya fice amma idan munci sa'a zamu sameshi wajansu Yaya sageer da Yaya Hammad" Daga Hammad har shi kansa Sageer data faɗi duk ban sansu ba, Yaya Ibrahim kuma shine second born ɗin Abba daga Anty Hadiza sai shi yana aiki a Kaduna tunda nazo bai dawo weekend ba sai wannan satin. Ajiyar zuciya kawai na sauƙe ba tare da nace komai ba A lokacin muka ƙaraso ƙofar wannan gida mai girman da yafi kaff gidajen layin girma. Baƙin ƙofar dake gefen gate mukaje Miemie ta danna ƙofar babu jimawa aka bude mana, kallona tayi tace.

"Muje" binta nayi a baya ta shige cikin gidan, Gidane wanda ya wadatu ta  shuke-shuke na mabanbantan nau'ikan Furanni wanda suka sanya harabar gidan take fitar da wani irin ƙamshi mai daɗin gaske, tunda muka shiga gidan nake karantar yanayinsa da ma'aikatan cikinsa da suketa girgiza-girza, gidane mai girman domin daga waje bai nuna girmansa gabaki ɗaya ba, sai da mukayi tafiya sosai ta cikin driveway kafin muka nufi hannun damarmu yanda wata Veranda take mai masifar kyau da tsaruwa tun daga nesa muke hango mutane a ciki ta gilashi masu ruwan garai da suke kewaye da wajan.

Da sauri-sauri gudu-gudu Miemie ta ƙarasa cikin wajan. Na bita a baya cikin nutsuwar da akoda yaushe bana bari ta gushe daga gareni, da ƴar gajeruwar sallama nashiga wajan wanda nasan koda wajan baya cike da jama'a babu wanda zaiji. A bakin mashigar na tsaya ina karantar mutanen ciki, gefe ɗaya ƙawayen su Miemie ne domin naga yanda suke magana cike da sabo ya nuna hakan,  wata daga cikin ƴan matan sai tura baki take Miemie tana bata haƙuri inaji tana shaida mata test ta rubuta a makaranta yanzu dawowarta. Can gefe kuma mazane a zaune akan kujerun ban kalli gefensu ba amma ina iya jiyo maganganunsu. Miemie ce naji ta fara faɗin.

"Ina ƴar uwata Ameerah da nake baku labarinta? Toh yau har da ita nazo nan" Ɗaya daga cikin friend ɗin natane naji tana faɗin.

"Yau Allah yayi zamuga Ameerar da hirarta da hotunanta suka cika idanuwanmu da kunnuwanmu tana ina?" Sai a lokacin Miemie ta juyo gareni ta riƙo hannuna muka ƙarasa wajan friend ɗin nata, kamo kafaɗata tayi ta kwantar da kanta tana faɗin.

"Dan Allah yaya kukaga kamanninmu?”  ina jinsu wasu suna fadin, muna kama wasu kuma sun cewa sam bamuyi kamanni ba nidai bance komai ba, nayi shiru ina sauraronsu.

“Ameerah” naji sautin muryar yaya Ibrahim a kunnuwana ya kira sunana.

A hankali na juya kaina izuwa ɓarin da naji sautin ya taho, abokan Yaya Ibrahim suna zaune kusa da shi, kowa na kallon inda kiran ya nufa, kamar yadda ni ma na bi sautin da idanuwana.  A lokaci guda, ba tare da wani shiri ba, idanuwana suka sauka a kansa A lokacin da shima ya kalleni idanuwanmu suka sarƙe cikin na juna. Grey green eyes ɗina da ban cika buɗesu akan kowa ba suka nutse cikin nasa.

Hammad a lokacin da idanuwansa suka sauƙa cikin nawa ji yayi tamkar walƙiya ta daki zuciyarsa. Duk da ba sanyi ake yi sosai ba amma a lokaci guda Wata irin rawar sanyi da ɗumi sun ratsashi, Tamkar ɗaukewar ruwan sama haka lokaci guda suka ɗauƙe. Idanuwana sun kafe a kansa ƙawayen Miemie jin sunata magana ban kula ba yasa suka kalli yanda nake kallo, dama abokanan Yaya Ibrahim already mu suke kallo.

Cikin ƙanƙanin lokaci, Veranda ya ɗauki shiru. Babu ƙwararran motsi, babu magana A lokaci guda kamar an ja hankalin kowa da igiya guda ɗaya,  Ban ɗauke idanuwana daga nasa ba, kamar yadda shima ya gaza ɗauke nasa daga cikin nawa. Mun tsaya muna kallon juna kallon yayi tsawo da zurfi, mai ɗauke da tarin ma'anoni daga kowane ɓangare.  naji wajan ya ɗauki shiru kuma na tabbata kanmu ido ya dawo amma ban ɗauke idanuwana daga cikin  nasa ba kamar yanda shima ya kasa ɗauke nasa idanuwan  acikin nawa, kallon juna mukeyi sosai amma ni a nawa fannin bawai gaza ɗauke idanuwana nayi ba, A’a. Na san abinda nake yi. Kallon nasa nake cikin cikakkiyar nutsuwa, ba tare da kunya ba, Shi kuma Hammad a ahalin yanzu na fahimci irin kallon da yake yimun kallona yake da idanuwansa masu cike da tarin tambayoyi.

Sageer dake gefe kallona yakeyi cike mamaki, har ya buɗe baki ya fara magana, Yaya ibrahim ya taɓashi yana kallonsa ya girgiza masa kai alamun kar yace komai. Mutanen cikin verenda ba yawa suke dashi ba gabaki ɗaya ƴan matan su takwas ne banda ni kaina sai maza su biyar gabaki ɗaya hankalinsu ya tattaro kanmu nida Hammad da muke kallon juna. Ko ince da nake kallonsa ko kunya babu kuma ban ɗauke idanuwana ba.

#ZEE ALABURA

#LIKITAN-RUHI

#SOYAYYA

#ƘADDARA.....

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol