Free chapter · Read without an account
Page 2
by ZAINAB LAMINU · ROMON BAKA
ROMON BAKA
PAGE___ 2
Bismillahir Rahmanir Rahim.
Tsayawa nayi ina taraddadin abinda zai faru idan na shiga. saida na dai-daita natsuwata kafin na tattaro ɗan sauran ƙwarin gwiwar da ya rage min na kama hannun ƙofar, turawa nayi a hankali kamar mai tsoron a kamani, na shiga ina sanɗa kamar ya kwarton da aka kama a turaka. Dube-dube na shiga a ɗakin kamar makahon da ya rasa ɗan jagora, ganin babu wanda zuciyar tawa take fargabar gani a ɗakin ne yasa na sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi sai kace wadda tayi tseren gudu.
Ajiye abincin nayi akan teburi ɗin dake tsakiyar ɗakin, ɗakin na fara bi da kallo idona ya sauka akan wani kati kamar na hoto ajiye a kan gado, jan ƙafafuna nayi zuwa inda katin yake ajiye, hannuna na rawa na kai zan ɗauka, amma sai naji an riƙe hannun nawa kafin ya kai ga isa kan katin hoton.
Ɗagowa nayi ina kallon Zayyan daya shigo, "Zayyan me kake ɓoyewa ne?". Nayi maganar hawaye na wanke fuskata, kallona yayi fuskar shi babu alamar rahama, kamar ba Zayyan ɗin dana sani ba a baya ba, mai fara'a da sakin fuska mai tattalin farin cikina, amma wannan Zayyan ɗin da yake tsaye a gabana ya bambanta da Zayyan ɗina, kwata-kwata ya sauya ya zama wani can da ban.
Magana ya fara cikin wata kausashshir murya yace, "Ban miki iyaka da shigo min ɗaki ba?, bance bana son na ƙara ganin ƙafarki a ɗaki na ba? matuƙar bani na neme ki ba, wai ni Aminatu yaushe raini irin haka ya shiga tsakanin mu dake har haka ne?".
Baya naja a tsorace nace, "Kayi haƙuri dan Allah Baban Irfan ban san ranka zai ɓaci ba". "Kin sani Aminatu kin san hakan zai ɓata min rai sarai ba wai baki sani ba, kina sane ke ƙaramar yarinyace da za kiyi abu kice baki sani". "Wallahi banyi da niyar na ɓata maka rai ba, dama abincin karyawar ka ne nace bari na kawo maka ɗaki tunda na san ba fitowa za kayi ba".
Saurin tarar nunfashin ta yayi yana cewa, "Ce miki aka yi ina ɓutar abinci ki?, idan ma abincin nake son ci nasan in da yake ajiye naje na ɗauka mana da kaina, amma shine kika biyo ni da shi kamar wani sa'anki, to kashedi na dake na ƙarshe ke nan kar na sake ganin ƙafarki a ɗakin nan in dai bani na nemi ki ba".
Ya ƙarasa maganar tasa a tsawace, saurin ja baya nayi gudun kada ya makeni ina ɗaga masa kaina, "Fita a nan".
Yayi min nuni da ƙofa, juyawa nayi na fita daga ɗakin ina jin zuciyata na suya kamar ana babbakata, dafe saitin zuciyar tawa nayi jin yadda ta riƙe, har nunfashi nayi min wahalar fita, kariyar Allah ce kawai ta mai dani ɗakina, abincin da ban ci ba kenan, ina shiga ɗakin nawa na duƙe a dokin ƙofa dan na gagara yin koda taku ɗaya ne da zummar na ƙarasa ciki, tilas na kai zaune a nan ina jingina da ƙofar da ta yi min shamaki da kaiwa ƙasa. ƙoƙarin jawo nunfashi nake yi jin yana shirin barin gangar jiki da rushi, nafi ƙarfin awa guda a wannan halin da Zayyan ya jefa zuciyata a ciki, dan ko tafiyar yara makaranta banji ba saboda mawuyacin halin da na shiga, tsabar yadda nunfashina yayi fitar burtu daga gangarjikina, ban tashi dawowa daga cikin halin ƙaƙaniƙayin da Zayyan ya jefa zuciyata ba, sai da naji kiran da Sayya take min, fitgigit na dawo haiyacina ina kalle-kalle kamar wanda ta warke makanta ko wanda ta dawo daga dogowar sumar wucin gadi.
"Ke Aminatu wai meke damunki ne tun ɗazu nazo gidan nan amma baki san nazo ba ko dai har yanzu zaman naku bai dai-daita tsakanin da Zayyan ɗin ba ne?, na shiga uku ni Sayya, me Zayyan ɗin yayi maki haka?, kimin! magana mana Aminatu". Kuka Amunatu ta fashe da shi tana faɗawa jikin Sayyan tare da ƙanƙameta tana faɗin Sayya "Me nayiwa Zayyan haka da zafi ne?, da zai rinƙa wulaƙanta ni, Sayya Zayyan baya sona Zayyan ya dena sona, Sayya ya zanyi da rayuwata?". Ta ƙarasa maganar da sakin wani kuka me cin rai.
"Haba Aminatu kiyi haƙuri ki dena wannan kukan haka mana, ba kiji yadda jikinki yayi zafi bane?, kiyi haƙuri taso mushiga ciki". Kamata tayi tamiƙar suka ƙarasa shiga cikin ɗakin, a gefen gado ta zaunar da ita kafin ta fita zuwa kitchen, ruwa mai sanyi ta ɗakko bata tayi ta sha, ajiyar zuciya ta shiga saukewa ajejjere sai da ta tabbatar da ta samu natsuwa yadda ya kamata sannan itama ta zauna a kusa da ita tana da fa kafaɗarta tace, "Meya faru ne?". Sai da Aminatu ta share hawayen fuskarta kafin ta labarta wa Sayya duk abinda ya faru tsakaninta da Zayyan ɗazu, haƙuri ta sake bata kafin tace,
"Abinda mu kayi ta ƙoƙarin ganin kin fahimta kenan a baya, amma baki saurari kowa ba Aminatu wannan abun muke maki gudu gashi kuma sai da ya riskeki, saboda banzar soyayyar da banga amfanin da tayi maki ba yanzu, sai ƙunci da baƙin ciki da suka yiwa rayuwarki dabaibayi duk ta dalilinta, dubi dan Allah dubi halin da kikeci ki a yanzu, amma a haka ya iya tsallakeki ya fita sabgar gaban shi".
"A'a Sayya wajen aiki ya tafi". Kallona Sayya take da dukkan maɗaukakin mamaki tace,
"Na shiga uku ni Sayya ke kuwa Aminatu me Zayyan yayi miki haka?, gaskiya na fara kokwanton ba haka Zayyan ya barki ba, amma ace duk irin abinda yayi maki har kina da bakin da zaki kare shi, gaskiya a binciki lamarin nan dan bai kamata a barki haka ba, dan ba haka Zayyan ya barki ba Aminatu".
"Wallahi Sayya ba abinda kike tunani bane, ni ba abinda Zayyan yayi min, karfa ki manta shi ɗin uban ƴaƴanane". "Ehhh lai-lai kuwa uban ƴaƴanki ke, yanzu Aminatu duk abinda Zayyan yayi maki har kina da zummar kice wani uban ƴaƴan kine shi, gaskiya sai yanzu na sake tabbatarwa da baki da hankali kuma wayonki na banza da wofine, ina hankalinki da tunaninki suka shiga ne Aminatu, da zaki zauna namiji ya rinƙa yi miki wannan gashin ƙumar yana gasa miki aya a hannu, kuma ki zuba ido kina kallon shi ke ga ƴar daɗi soyayya ko?, idan kin mutu ba shi da wata asara ko ta ɓawon kwai".
"Sayya kenan wallahi duk ba haka bane, Zayyan yana sona shima kamar yadda nake son shi, kawai dai ni nafi tunanin akwai abinda yake damun shi ne, shi yasa yake duk waɗan nan abubuwan".
Sayya kuwa da mamaki ne ya daskarar da ita, tana mamakin wannan wanne irin makahon so ne Aminatu ta ke yiwa Zayyan ɗin haka da bata ganin lefin shi.
Bata sake cewa komai ba a kan hakan tunda dai tasan komai za'a faɗawa Aminatu ba zata fahimta ba, domin wanda yayi nisa baya jin kira.
Ba ita ta bar gidan ba sai wajen azahar, dan sai da ta kamawa Aminatu ayyukan gidan kasanciwar jikinta babu ƙwari. Koda Sayya ta wuce cigaba nayi da zama a falon ina tunanin da ya riga ya zama kamar nunfashin da nake sha ƙane.
ABIDAH