Free chapter · Read without an account
PAGE 03
by Nanameera · WATA AL'UMMA
*WATA AL'UMMA.*
Page 03.
Tsallake shi ta yi ta nufi inda Golma yake a kwance ta durƙusa a gabansa. Cikin tashin hankali take faɗin
“Golma! Golma! Golma”
Babu alamar yana jin ta dan ba motsi yake ba. Ta ɗaga idanu tana kallon dogaran da ke tsaye cikin daka tsawa ta ce
“Ba zaku zo ku taimake shi ba?”
Ta ƙare maganar a zafafe. Jikinsu har rawa yake wajen durƙusowa, Suka yi kama kama a ka saɓa shi a kafaɗa sannan suka nufi cikin garin dashi. Shi kuwa Sudais da gudu ya ƙaraso inda Major yake kwance ya ɗago shi jikinsa ya fara girgiza shi yana cewa “Major! Fa'ik! Prince don Allah ka buɗe idanun ka. Stay still ka ji!”
Ya ƙare maganar yana dukan kumatunsa a hankali, Wani numfashi Major ya ja yana ƙoƙarin buɗe idanunsa. Sai dai sam ya gagara yin haka, Ya riƙe hannun Sudais da ke kan fuskarsa muryarsa na fita a sanyaye ya ce
“Ku kai ni asibiti...”
Ya ƙare maganar dakyar, Gyaɗa masa kai Sudais ya yi yana hawaye ya ce. “Yes! Yes yanzu zamu kai ka. Zan kai ka don't worry ka ji”
Bai sake cewa komai ba, Dan ya fara galabaita. Ganin haka ya sanya Sudais ya cire t-shirt ɗin da ke jikinsa ya yaga ta, Sannan ya ɗaure masa inda jinin ke zuba. Nan take ita ma farar rigar ta koma kalar ja saboda yanda jinin ke fita sosai, Ammar da ya ƙaraso wajen ya dafa shi cikin sanyin murya ya ce
“To me zamu yi yanzu? Ya zamu yi?”
Juyawa Sudais ya yi ya ɗan kalli in da jama'ar suke sai kuma ya mai da idanunsu kan Ammar ya ce
“Ba zasu bar mu ba yanzu. Amma dole mu kai shi asibiti, So nake na yi kira”
Ya ƙare maganar yana ƙoƙarin dauko wayarsa. Har sannan babu network, Sai dai yanzu ya sauka daga kan emergency call ɗin. Ya girgiza kansa ya ce“Har yanzu babu damar kira, Ban san wane irin gari ba ne wannan”
Bai kai ga rufe bakinsa ba wasu manyan mutane suka tsaya a kansu, Sudais ya ɗaga kai ya kalle su. Fuskarsu a haɗe kamar shanu, Wannan karon aro jarumta ya yi ya ci gaba da kallon su shi ma. Bayan wasu sakanni suka fara ƙoƙarin janye Major daga jikinsa, Ya riƙe shi gam yana yi musu wani irin mugun kallo ya shiga furta
“Ina za ku kai shi? Ƙarasa kashe shi zaku yi? To wallahi akan wannan mutumin sai an ƙona gaba ɗaya garin nan!”
Shi kaɗai yake maganarsa. Dan babu alamar suna fahimta, Ba su kuma fasa ƙoƙarin janye shin ba. Ganin haka ya sanya Ammar saka hannun wajen riƙe Major ɗin.
“Me ku ke jira?”
Suka tsinkayi siririyar muryarta daga bayansu. A tare suka juya suna kallon ta, Ta shiga ƙarasowa wajen tana tafe a hankali. Risinawa dogaran suka yi cike da girmamawa. Bata bi ta kansu ba ta kalli Major da ke kwance cikin jini sai kuma ta kalli ɗaya daga cikin dogarin ta ce
“Ku ɗauke shi!”. Ta ƙare maganar a zafafe. Sake risinawa suka yi sannan suka durƙusa suka ɗauke shi, Wannan karon sakinsa suka yi suna kallon ta. Suna nan tsaye har aka tafi da Major, Sudais ya miƙe yana kallonta ganin tana shirin barin wajen yasa ya ce
“Wace ce ke? Me ki ke taƙama dashi?”
Cak ta tsaya. Lokaci ɗaya kuma ta juyo tana kallon sa, Sai a sannan ya samu damar kallonta. Fara ce tas kuma asalin kyakkyawa, Ta ɗan yatsine fuska sai kuma ta juya ta bar wajen tana tafe kamar zata tashi sama. Kallon kallo aka shiga yi tsakanin sa shi da Ammar, Sudais ya kalli wayarsa ganin cajinsa saura 20 percent. Girgiza kansa ya yi sai kuma ya sake shiga kira ya gwada, A wannan karon ma dai babu Sa'a dan kiran bai shiga ba. Ya jima yana danna wayar kafin ya sauke idanunsa ya mai da ta aljihunsa, Ya kalli Ammar ya ce
“Kada fa su kashe shi”
Numfasawa Ammar ya yi ya ce“Nima tsoron da nake kenan.”
Sudais ya ɗaga idanunsa yana kallon sararin samaniya wadda ta yi duhu, Taurari sun fito gwanin ban sha'awa. Ya ɗaga hannunsa sama ya ce“Allah ka taimake mu, Ka fitar da mu daga wannan garin lafiya.” Ya lumshe idanunsa kafin ya shafi fuskarsa
“Sudais!”
Ya ji Ammar ya kira shi, Da sauri ya kalli gefensa jin ya ɗan yi nesa da shi. Sake ware idanunsa ya yi ganin wasu dogarai guda biyu suna jan sa, Ya ɗaga ƙafarsa don zuwa inda yake ya ji shima an riƙe shi ta baya. Ya juya don ganin wanda ya riƙe shin, Wani ƙaton mutumi ne. Ya fara ƙoƙarin kwace kansa sai dai sam ya kasa don ba wani kwari ne dashi ba, Suna ji suna gani aka tafi da su kowanne aka yi ɓangare daban da shi.
Hankalin Sudais bai sake tashi ba sai da ya ga an buɗe wani ƙaton ɗaki, Ya dinga kallon ɗakin ganin wasu irin kejina na katako, Wasu da mutane a ciki wasu kuma babu kowa. Ɗaya daga cikin kejinan aka buɗe aka tura shi ciki, ganin ana ƙoƙarin rufe kejin ba tare da an ce masa komai ba ya sanya shi tsugunawa. Yana ji yana gani aka rufe shi cikin keji tamkar wani zakara ko kuma tsuntsu, Ya dinga kallon mutane ta raga-ragar da ke tsakanin kowane katako. Rufe idanunsa ya yi yana tuna rabon da ya sha irin wannan wahalar, Tun lokacin da yake training ɗin shiga aikin soja, Ko da ya shiga aikin bai taɓa shan wahala irin wannan ba, Don ba ko ina ake fita da su ba. Bai kuma daɗe yana ƙaramin ma'aikaci ba ya samu babban matsayi kasancewar shi ɗan babba mutum. Ya daɗe idanunsa a rufe kafin ya ɗago jin wayarsa ta yi ƙara. Ya kalli aljihunsa ganin hasken wayar ya sanya shi sakin ajiyar zuciya, Da kyar ya ciro wayar daga aljihun. Takaici da baƙin ciki suka ishe shi lokacin da ya ga saƙon kamfani ne ya shigo, Kallon agogon wayar ya yi, Misalin ƙarfe 9:34 ne na dare. Ya matse gefen wayar ta mutu sannan ya mai da kansa kan cinyarsa yana kiran sunan Allah...
****
Washegari.
Durƙusawa ta yi kafin ta fito daga ɗakin nata. Ta tsaya a bakin ƙofar tana ƙarewa wajen kallo, Sanye take da zani ruwan ƙasa wanda ta ɗaura shi har kusan rabin cinyoyinta. Fararen ƙafafunta sun bayyana sai sheƙi suke, Ƙirjinta kuwa a rufe yake da wata irin fata mai kauri, Ta ɗaure har zuwa bayanta. Gashin kanta a ɗaure yake da zaren auduga, An yi masa ado da busassun ganyen bishiya. Wuyanta ɗauke yake da sarka ta tagulla, Yayin da hannunta ke ɗauke da abun ado na ƙasusuwan dabba. Fuskarta kuwa ta sha ado da baƙin jambaki, Idanunta ranbaɗe da kwalli, Sam bai hau da shuɗiyar ƙwayar idanun ba. Goshinta ɗauke yake da wani jan zane, mai cross kamar na krista, Yayin da gashi kanta yake har kusan goshinta a kwance. Gefenta hadimai ne guda biyu, Ɗaya hannunta riƙe da tabarma ɗayar kuma riƙe da mafici. Gimbiya Anna kenan, Ƴa tilo wajen sarki Golma ɗan Zukpa. Tana nan tsaye har bayan shuɗewar wasu mintuna, Kafin wani mutum ya ƙaraso wajen, Baƙi ne shi. Amma kana ganin shigarsa ka san ɗan babban mutum ne, Ya kalleta lokaci ɗaya ta sakar masa murmushi. Nan take kyawun da ke kan fuskarta ya bayyana. A hankali ya ƙaraso gabanta ya rungumeta, Ta saki ajiyar zuciya tana sake riƙe shi. Sun daɗe a haka kafin ya saketa yana kallon ta cikin yaren su ya ce
“Barka da Safiya Gimbiyata.”
Ɗan lumshe idanu ta yi, Kafin ta jinjina masa kai ta ce
“Ina ta jiran ka anan. Ko kana so gimbiya ta ɗaureka ne?”
Ta ƙare maganar tana tsuke fuska. Girgiza kansa ya yi cike da zolaya ya ce
“Ni na isa? Abar bauta Kara ta ƙara miki girma” Ya ƙare maganar yana risinawa, Ta jima tana kallon sa. Kafin ta ce“Kumzar zan je unguwa yanzu, Idan na dawo zamu haɗu”. Jinjina kansa ya yi cike da ladabi ya ce
”A dawo lafiya Gimbiyata.” Gyaɗa kanta kawai ta yi, Ya matsa gefe don ya bata damar wucewa. Gaba ta yi wanda hakan ya sanya hadiman bin bayanta, Ya jima tsaye a wajen har sai da ya daina hangota sannan ya a sauke numfashi ya juya ya nufi hanyar da ya fito.
A bakin wata bukka ta tsaya, Ba tare da ta ce komai ba ta tura ƙofar ta shiga. Su kuwa hadiman suka tsaya a wajen, Kai tsaye inda yake idanunta suka sauka, Kwance yake kan wani gadon katako wanda aka ɗora fata akai. Ta ƙarasa wajen ta tsaya tana kallon sa, Bata taɓa ganin mutane irin haka ba, Sai dai ta sha jin labarinsu. Ta jima a tsaye kafin ta nemi gefen gadon ta zauna tana ci gaba da kallonsa. Idanunsa a rufe yake, Ta kalli faffadan ƙirjinsa wanda yake a buɗe don an cire masa rigar, Yana numfashi har sannan. Ta sauke ajiyar zuciya sannan ta kalli gefen cikinsa inda aka rufe da wani ƙaton ganye. Aka kuma ɗaure da zaren auduga, Ta jima tana kallon wajen kafin a hankali ta kai hannunta na dama ta taɓa. Bai motsa ba, Wanda ke alamta cewa har sannan baya cikin hayyacinsa. Ɗan tsuke fuska Anna ta yi cikin yarensu ta ce
“Hii Zurma(Baƙo) Abar bauta Kara ta baka lafiya.” Ta ci gaba da kallon sa, Can kuma ta sake cewa“Me ya sa zaka taɓa Golma? Da ban taɓa ka ba ai.” Ta ƙare maganar tana marairaice fuska, Haka ta ci gaba da zama a dakin har kusan mintuna goma. Kafin daga bisani ta tashi ta fito, Tsaye ta sami hadimanta suna jiranta, Bata ce musu komai ba ta fara tafiya suka bi bayanta. Duk in da ta ratsa sai mutane sun risina mata. Wannan ke nuna irin girmanta da ake gani a garin. Kai tsaye gidansu ta koma, Ta ƙarasa fadar sarki inda ta same shi zaune kan karagar mulkin sa. Dogarin da ke tsaye gefensa yana masa fifita a hankali. Ɗan risinawa ta yi a gabansa ta ce
“Abar bauta Kara ta taimake ka.”
Fuskarsa a sake ya ce“An gaida gimbiya” Murmushi kawai ta yi sannan ta nemi gefe ɗaya kan tabarmar fatar ta zauna. Ganin haka ya sanya Sarki Golma gyara zama yana fuskantar ta sosai ya ce
“Anna!”
A sanyaye ta ɗago ta kalle shi. Kafin ta ce
“Na'am Golma”
“An kashe waɗancan mutanen?”
Da sauri ta kalle shi, Sai kuma ta girgiza kanta ta ce“A'a ranka shi daɗe.” Da mamaki Golma ya ce “Me ya sa?” shiru ta ɗan yi kamar me nazari. Can kuma ta numfasa ta ce
“Bana so a kashe su Golma, Ni a ganina a bar su sai ya fi. Idan ya so sai su zama bayin mu” Kallonta ya dinga yi. Ta sakar masa murmushi ba tare da ta ce komai ba. Gyaɗa kansa ya yi ya ce“Shikenan tun da kin ce haka. Amma da ba haka zan musu ba, Hukuncin kisa ne ya dace da su. Musamman wanda ya yi yunkurin cutar dani” Anna ta jinjina kanta cike da gamsuwa ta ce“Haka ne. Amma ai na hukunta shi, Kuma ba zai ƙara ba ni na sani.” Kasancewar Golma na yarda da maganarta fiye da ta kowa ya sanya ya haƙura da maganar kisan, Amma ya jaddada mata dole a mayar da su bayi. Bata ƙi ta ta sa ba ta amince masa, Sannan suka ci gaba da hirar su. Kafin daga bisani ta miƙe ta yi masa sallama ta bar fadar. Sashin matan Sarkin ta nufa, Kai tsaye kuma ɗakin da ke kusa da na sarkin ta shiga. Ba wani babba ba ne, amma ya sha ado da kayan kwalliya irin ta su. Ta ƙarasa ciki tana kallon matar da ke zaune gefen gado ta kishingiɗa. Sai da ta risina a gabanta ta ce
“Barka Golmanya. Abar bauta Kara ta taimake ki”
Ɗagowa wadda ta kira da Golmanyar ta yi. Farar bafulatanar mata ce, Mai matuƙar kama da ita. Sai dai kana ganinta ka san ta manyanta, Tana da ɗan jiki amma ba sosai ba. Jikinta sanye da kaya kusan irin na jikin Anna. Sai dai ita ta saki gashin kanta wanda ya zubo har kafaɗunta. Ba zata shige shekaru hamsin da haihuwa ba. Ta gyara zamanta tana cewa
“Tare da ke gimbiya”
Zama Anna ta yi gefen gadon tana murmushi ta ce“Lafiya yau Golmanya(Sarauniya) Bata fita fada ba?” Ɗan murmushi kawai matar ta yi sai kuma ta ce
“Ya jikin Zurman?”
Ɗan yatsine fuska Anna ta yi kana ta ce”Da sauƙi. Jore ya duba shi tun jiya, Ya ce zai tashi nan da kwana biyu.” Shiru Golmanya ta yi, Anna ta sake cewa “Golma ya yi magana akan su. Ya ce za'a kashe su ne a cinye saboda sun yi ƙoƙarin taɓa shi, Ni kuma na ce ya bari kawai su zama bayi.”
Da sauri Golmanya ta kalleta. Lokaci ɗaya ta miƙe tsaye tana girgiza kanta ta ce
“Lala ban yarda ba Anna! Ka da a bar su. Ki saka a mayar da su garin su, Ka da ƙaddarar rayuwa ta same su kamar yarda ta sameni. Ban amince ba!”
Ta ƙare maganar cikin ɓacin rai da ɗacin zuciya. Ita ko Anna kallonta kawai take, Can kuma ta miƙe tsaye ta harɗe hannayenta a ƙirji ta ce
“Kar ki damu. Ba zan bari a cutar da su ba, amma ba zan bari su tafi ba”
Tana kai wa nan ta juya da niyyar barin ɗakin.
“Me ya sa ba zaki bari su tafi ba? Mene ne shirin ki?”
Ta tsinkayi muryar Golmanya a sanyaye. Cak ta tsaya, sai kuma ta juyo ta kalleta. Bata ce komai ba ta juya ta fice daga ɗakin da sauri. Silalewa a kan gadon Golmanya ta yi, Lokaci ɗaya hawaye ya cika kurmin idonta. Cikin rawar murya ta ce
“Abar bauta Kara ki taimake su.”
**** Yammaci sakaliya aka buɗe ƙofar kurkukun, Sudais ya ɗago kansa a hankali yana kallon hasken da ya shigo ciki. Zuwa yanzu sam babu wani saurin kwari a jikinsa, Saboda azabar yunwa da ƙishirwar da yake ji. Duk da ɗazu an kawo musu abinci da ruwa ya ɗan sha ruwan wanda bai ma san daga inda yake ba. Kejin da yake ciki aka buɗe, Mutumin ya figo shi daga ciki. Ji ya yi ƙafafunsa sun gagara takawa sakamakon tsamin da suka yi na daɗewar da ya yi a tsugune. Mutumin kuwa ko a jikinsa ya shiga jan sa har suka fita daga kurkukun, Kamar kullum in da suka saba haɗuwa su yi maganganun su yau ma nan aka nufa da su. Sudais ya runtse idanunsa a zuciyarsa yana tunanin ko dai kashe su zasu yi. A haka har suka ƙarasa, A tsakiyar da'irar aka yi wurgi dashi kamar kayan wanki. Kallon kallo suka shiga yi shi da Ammar wanda shi ma aka cire masa rigar jikinsa, Rabon su da juna tun jiya da daddare. Major ne ya faɗo masa arai, Ko a wane hali yake? Sun jima a wajen kafin Anna ta zo, Mutanen garin suka shiga yi mata sujadda kamar yanda suka saba koda yaushe. Bayan ta amsa gaisuwar ta su a wulaƙance ta mai da Idanunta kan Ammar da Sudais, Kallon su ta dinga yi tana zagaye su. Cike da nuna isa da taƙama, Can kuma ta mai da idanunta kan jama'ar garin ta ce
“Duba da abin da wadannan mutanen suka aikata mana. Mun yanke shawarar mayar da su bayin garin nan na har abada!”
Ihu mutanen wajen suka saka, Har da masu tsalle. Wasu kuma na cewa
“A'a a cinye su!”
Nan take wajen har hargitse kowa da abin da yake cewa a yi. Ganin abun na su bana ƙare ba ne ya sanya Anna sakin wata gigitacciyar tsawa. Nan take kowa ya yi tsit, Gurin ya yi shiru, Fuskarta a haɗe kamar hadari take kallon kowa ɗaya bayan ɗaya, Kafin ta ce
“Ba shawara nake nema ba. Umarnin dana zartar ne ni da Golma!” Cike da girmamawa suka durƙusa suka sake yi mata sujadda. Ita kuwa ta ɗauke kanta tana kallon su Sudais waɗanda ke kallon jama'ar. Sai da ta basu dama su tashi tsaye sannan suka miƙe, Anna ta durƙusa tana kallon Sudais tana shirin yin magana ta ji taku mai kama da gudu ya cika ko ina. Da sauri ta miƙe tsaye, Sai dai ga mamakinta wasu tarin sojoji ne suka zagaye gaba ɗaya garin, waɗanda yawansu ya wuce a iya lissafa su, Kowannen su ɗauke da bindiga. A tare jama'ar garin suka juya suma suna kallon su, Sudais ya miƙe tsaye da kyar yana sakin Ajiyar zuciya gami da murmushi a lokaci guda....
***
Nanameera.