Free chapter · Read without an account
1
**********Tsaye yake a gaban windown ɗin ɗakin sa yana ƙarewa windown kitchen ɗin gidan su kallo. Daga ɗakin sa zuwa window kitchen ɗin gidan na su yana iya hangen duk wanda ya shiga kitchen ɗin da kuma me ake yi a cikin sa. Saboda girman windown kitchen ɗin na su. Sai de idan a lungu ko kofar shiga kitchen ɗin mutum ya tsaya ko kuma yana wurin gas..amma muddin a tsaye mutum yake a jikin sink ko yana aiki yana iya gani.
Ajiyar zuciya ya sauke a karo na ba adadi yana furzar da iskar dake bakin sa. Tunda ya zo gidan yau kimamamin da wata shida kenan, be taɓa ganin ta yi fashin zuwa ba, amma yau kwanan ta shida bata zo ba. A kullum yana tashi daga bacci ya saba window yake fara buɗewa, yana buɗewa kuwa zai ganta tana wanke wanke ko tana kai kawo acikin kitchen ɗin. Magana bata taɓa haɗa su ba idan aka ɗauke gaisuwa, shi bama tsayawa ba ne ya yi ta magana a cikin kannan nasa sai de kawai ya bi su da murmushi ko ya bi su da kallo. Ita ɗin ma hakanne, sai de ya lura akwai shaƙuwa sosai a tsakanin ta da Mujahid, da kuma Haisam wanda yake yaro ne ƙarami shekarar sa bakwai, Be taɓa ganin ainahinin fuskarta ba saboda a kullum akwai haukar da take sawa a fuskarta, ita ce shafa kwalli ta ja shi ta yi hawayen masoyi, ta ci janbanki nan raɗau ta zo ta yi ɗigo-ɗigo a fuskarta. Ta ja jagira ta ci uwar foundation da concealar. A duk sanda take dariya ko surutu sai de ya kalleta kawai, dan haka nan yake jin a jikin sa bata da hankali , yo marar hankali mana, shi kaɗai yasan abinda take yi a windown ɗakin sa, ga wasu iirin kayan da take sawa, kullum ɗingilallun kaya ne. Zai iya cewa a zuwan sa da ya yi ya hardace iya adadin kayan da take sawa. Sun kode, sun tsufa sun ji jiki gashi sun yi mata kaɗan. Dukanta bata fi sa'ar Sakina ba. Shekara goma sha huɗu kenan. Wani sa'in idan tana Abu zaka ga kamar ta fi kaf kowa hankali, amma idan ta keɓe taab, zaka ga hauka, ita kaɗai take magana da kan ta, ko ta samu ƴar galala take yi ita kaɗai tana yi tana surutu, zata yi creating mutanen da babu su, tana yi tana sauya magana, tun be saba ba, da abinda yake ji a wurin windown sa a duk sanda ta gama aiki kuma su Sakina sun tafi Islamiyya da yamma zata je bayan ɗakin sa ta yi ta tana aikin surutu, sai de idan ranar be fita ba yana gida, Windown ɗakin na sa biyu ne, ɗaya ya hangota a kitchen ɗin, ɗayan kuma ana take zama inda suke wanki da kuma irin haka idan aikin ya ta so ko na babbar sallah ko wani abu anan ake yi. Dan haka yake yawan jinta duk abinda take yi. Wani sa'in sai de kawai ya tashi ya buɗe na saitin gadon sa ya zauna ya yi ta kallam haukar na ta har ta tafi gida. Be san sunanta ba, amma ya ji suna ce mata Baby.....
Kiran da aka yi masa ne a waya ya sa shi kallan wayar da ke kan windown yana kallon sunan be ɗaga ba har ta katse, kafin a hankali ya sake sakin ajiyar zuciya yana furzar da iskar dake bakin sa. Sai kuma ya juyo a hankali yana kallan agogon ɗakin nasa. Sosai ya zubawa agogon ido, be taɓa tunanin haka ya ɓata lokaci ba sai a yanzu. Da ya kalla agogon. Yakan tashi karfe bakwai ne, zuwa takwas ya kammala komai nasa wani sa'in kafin tara ya je wurin aikin sa. Amma a yau kam, gashi har goma be shirya ba, balle ya yi haramar tafiya. Ji ya yi ana knocking ƙofar a hankali ana kuma kiran sunansa.
"Yaya a ciki?
Cewar Ƙanin na sa yana shigowa. Sai kuma ya tsaya yana sosa kai ganinsa a tsaye da kayan bacci.
"Yaya Sahal dan Allah na ce daman turare zan fesa".
Ya faɗa yana so sa kai. Be kula shi ba ya yi hanyar toilet. Da sanda yake shigowa ya yi abinda ya ga dama yana tambayar sa ne? Yana ganin haka ya wuce da sauri ya fara fesa turaren sannan ya buɗe drawer ya zabi kayan sawa dan akwai wurin zuwa idan aka jima zai je dinner dan haka sai tashi kan abokansa.
A shirye tsaf ya shirya ya sha ƙanan kayan sai zuba ƙamshi yake yi abinsa, yana ɗaura agogo ya fito, yana kallan lokaci, kafin ya wuce cikin gidan. Ya tarar da Abbah a zaune a ƙasan carpet ya gama karyawa. Sai Haisam dake gefen sa yana kallo. A ladabce ya sake gaida Abbahn na su bayan ta asuba da suka yi sannan ya gaida Ummie.
"Ya zancen aikin?.
Gyara zaman sa ya yi Ummie na kiran Sakinah ta kawo masa abinci. Abbah ya faɗa masa yana kallonsa. A sanyaye ya sunkuyar da kan sa ƙasa..
Ya ce, "Abbah, dan Allah ka yi haƙuri da zancen aikin nan".
Shiru Abbahn ya yi kafin ya ce, "Kasan de abinda Yaya yace akan wannan maganar ko?
Shiru ya yi be ce komai ba. Lokacin Sakinah ta kawo masa abinci, jin ya yi shiru yasa Abbah ta shi suna masa a dawo lafiya ya fita dan yasan ba zai sake cewa komai ba kuma.
"Nifa gani nake kawai ka je ka fara aiki a companyn nan, bana son abinda zai je kuma ya dawo komai kai na zai koma kuma ka san da hakan ko?
Mallam Ummie ya yi da ta yi maganar Sannan ya kalla abincin da ya zuba. Be ce komai ba ya fara shan shayinsa. Kafin ya ɗaga kai ya kalleta sai kuma ya ɗauka spoon ya fara shan roman da ya zuba kafin ya fara cin masar. Har yanzun kuma be ce da ita komai ba. Dan ran sa da zuciyarsa tafasa suke yi sosai. Allah ne kawai ya san ya yake ji a ran sa. Game da Abbahn masa har Ummien ma. Shikenan kawai dan suna gaba da shi sai abinda suka ce masa? Wallahi da ya yi aikin companyn nan ya gwammace ya cigaba da a shagon da ya gina da kuɗin sa. Be yi niyyar zama a shagon ba, amma tunda aka fara yi masa zancen ya yi aiki a Companyn Kawun sa ya ji kwara ya bar career ɗin sa ya yi kasuwancin sa. Zai fi masa wannan zaman companyn rashin mutunci na Kawunsu. Sani ne ba su yi ba, amma haushin Kawun su yake ji da Antyn na su wacce take itama Yayace a wurin Abbah......
"Magana take yi maka zaka kama hanya ka fita".
Ummie ta faɗa ganin yarda ya kama hanya zai fita batare da yace mata komai ba. Dawowa ya yi zauna kawai batare da ya kalleta ba.
"Kawai ka karɓa aikin nan, gobe Mami zata zo, kar ta zo ta ji baka amsa aikin nan ba dan Allah".
Kallanta ya yi yana jin zuciyarsa tana tafasa, to shikam dan Allah ko guduwa zai yi ne? Idan ya tafi ya je ina? Me yake da shi da zai iya riƙe kan sa? Bashi da abin faɗa shiyasasa ya yi shiru har ta gaji dan kan ta Sannan tace ya tafi.
Sakinah ta ce, "Wai Ummie Ya Sahal haka yake tun yana yaro?
Ummie ta ce, "A hakan wai an samu cigaba".
Dariya salimah ta tasa da fitowar ta kenan tana zama ta ce, "Cigaba a hakan?
Ummie itama murmushi ta yi kawai.
"Ya Mujahid ya zo ya bani kuɗina da ya ara dan ba zan bar masa ba".
Cewar Salimah. Sakinah ta ce, "Yaya Sakinah daman ke ce kike bar masa. Danni kam, wallahi ko me za'a yi na dena bar masa kuɗina, ko Abbah yace babu canji an haɗa mu da shi, sai na bishi min nemo tare".
"Nima na dena ara masa ai".
Ummie ta ce, "Muna nan zaki ji kin bashi".
Zata yi magana ya shigo yana sauke numfashi.
"Wai dan Allah yaushe Baby zata dawo? Wallahi nagaji".
Ummie ta ce, "Allah yasa kada ta dawo. Daman ma su tashi su bar garin".
A tare suka zuba zabura suka haɗa baki har Haisam wurin cewa, "Kaiiii Ummie".......
*********Nufar ƙaramin super market ɗin sa ya yi da da aka sa mini mart a saman wurin. Ƙarama ce amma ya zuba kaya sosai kuma be wani zuba riba ba sosai ba, hakan yasa ma aka san shagon da wuri haka saboda arahar wurin. Wasu saboda arahar suke zuwa su kuma yi sari. Tun yana Amsterdam yake turo kuɗin sa ana gina masa. Wasu kayan ma daga can ya siyo su da zai taho musamman kayan sawa da sauran su. Kawai kayan kitchen ne babu a wurin,amma komai akwai babu abinda babu.
Ajiyar zuciya kawai ya sauke yana zama a kujerar dake office ɗin sa, shima ɗan ƙarami ne office ne, kawai camera ya duba yaga komai lafiya sannan ya dawo cikin shagon ya zauna.
Kulle idan sa kawai ya yi yana jin ran sa sosai babu daɗi, tsaki kawai ya ja yana jin ba daɗi a ran sa. Ba za'a bar mutum ya yi abinda yake so a duniyar nan dole sai an takura masa? Kawunsu bashi da wani buri da ya wuce ya ƙuntatawa mutum, shi a ganin sa, taimakone wai hakan yake. Amma ba taimako ne ba, shi a wurinsa.
Ganin zaman ba zai yi masa yasa shi jan tsaki yana shiga office ɗin sa, ya fara duba Companyn da zai haɗa hannu da su, suna kawo masa kaya, direct daga wurin su saboda haka zai fi araha. Har dare yana nan sai karfe tara sannan ya tashi ya wuce gida. Bema shiga wurin su ba, balle suyi tunanin sake yi masa maganar da suka yi masa ran sa ya ɓaci a banza, ta kofar bata ya shiga kitchen ya haɗa abinda zai haɗa sannan ya fito kawai ci ya yi sannan ya kwanta dan bacci ya ke ji be jin zai iya jimawa be yi kwance ba. Ya gama komai nasa da ya saba sannan ya yi wutri daga ƙarshe ya kwanta. Ya fara bacci kenan ya ji sheshshekar kuka sosai tana damunsa..
A hankali ya buɗe idon sa kawai, shi be tashi ba, shi be kunna haske ba, kawai idan ya buɗe be motsa. Jin sosai kukan ma ƙara volume ake yi yasa shi kulle idan sa sosai yana jan tsaki ya yi juyi ya kulle idan sa wai ko zai yi bacci. Amma ya kasa, yana da wani abu ko motsi ya ji, ba zai taɓa iya bacci ba. A hankali ya ta shi zaune yana tunanin to waye ne a wannan daren yake wannan uban kukan? Kamar wanda aka yi mutuwa? Wayar sa ya janyo ya kunna haske sannan ya tashi ya fita ta balcony ɗin sa, idan ba wanki ba, be fitowa nan wurin. Balle kuma da daddare, time ya kalla yaga sha biyu ashe de ya ɗan yi baccin da yawa sai ya ji kamar yanzu ya kwanta.
"Ko ki min shiru".
Ta ji muryarsa a kausashe ya faɗa. Tsit ta yi gabanta yana bugawa sosai. Sai de hawayen be dena zuba mata ba. Shi kuwa ya jima a kan ta yana jin kukanta, kana ji kasan kuka ne da take cikin ƙunci da neman mafita.
"Ko kuma ki tashi".
Ya sake faɗa yana kaurara Muryarsa.
"Ki bar wurin".
Ya faɗa zai juya idan sa ya sauka a akan ƙafarta dake kumbure suntum ta ɗaurata akan cinyarta tana rera kuka. Har wani green green cikin ƙafar ya yi. Sosai ya zuba ƙafar ido kafin ya kalla fuskarta yaga ta yi shaɓe shaɓe da hawaye, idan sa ya kumbura suntum ta yi lufu lufu, kallo ɗaya zaka yi mata indai kana da imani ta baka tausayi, bakin nan ya bushe sosai har ya fara tsagewa. Da sauri ya kauda kan sa, ganin ta fara ƙoƙarin tashi tana share hawayenta amma wasu hawayen suna sake zuba mata, kafin ta je zata tashi ta saki ihu tana komawa ta zauna, ta yi saurin toshe bakin ta da dukkan hannunta, jikinta har rawa yake yi tsabar warning ɗin da ya yi mata. Ga hawaye shaɓe-shaɓe a fuskarta sosai wani yana bin wani da gudu.
Rintse idan sa ya yi sosai, yana jin wani irin abu mai girman gaske yana danne duk wata masifa dake cin sa a zuciya, dan kuwa wallahi muddin ka ga kalleta sai ka ga ta baka tsantsan tausayi, idan kana da saurin kuka ma, sai ka zubar da ƙwalla.
"Wait".
Ya faɗa yana ganin zata sake tashi tana riƙe ƙafar a hannu kamar zata yi langa.
"Ki tsaya na ce".
Ya faɗa a ɗan raunane da sauri ta tsaya tana neman faɗuwa saboda ƙafa ɗaya take kai, ɗayar ta riƙe ta. A hakan ta tsaya har ya je shi ya dawo, ganin tana tsaye yasa shi jin wani irin a ran sa. Meye hakan yake damun ta? Sai ka ce marar kan gado?
"Mtsww".
Ya ja tsaki, yana zuwa ya zaunar da ita, be ce da ita komai ba, ya kama ƙafar na ta sake kumbure ya ɗaura a cinyar sa bayan ya tsugunna a gabanta. Ƙurawa ƙafar ido ya yi sosai, gaba ɗaya ta zane ta da baƙin lallen yin flower, ta yi hauka a ƙafar, babu wani datti a tattare da ita fes da ita. Amma kumburin da ƙafar ya yi ne yasa shi tabbacin sanin wannan ciwon ba na yau bane. Kuma ga dukkan alamu targaɗe ne.
"Dan Allah kar ka taɓa min".
Ya faɗa a hankali tana kai hannunta kan ƙafar. Be ce da ita komai ba, kawai sake jan ƙafar ya yi yana yi mata wani mumman kallan da yasa ta ɗauke hannunta ba shiri ta gimtse bakin ta, tana cigaba da hawayenta.
Jan ƙafar da ya yi ne yasa ta sakin azabbbane ƙara tana kai hannunta kan nasa, kallan da ya aikata mata da shi ne yasa ta saurin janye hannunta tana ƙwalala id da toshe bakinta.
"Shiru zaki min".
Ya faɗa mata sosai yana haɗe fuskarsa, wanda tana ji tana kallo, ta toshe bakinta da hannunta, tana rintse ido. Sai hawaye kawai take yi. Sai da ya tabbatar ya gama aikinsa sannan ya shafa mata ointment masu zafi sosai ya naɗe ƙafar da bandage. Kafin ta shiga suke ajiyar zuciya, ta haɗa uban gumi sharkfa zuciyarta sai bugawa take da sauri tana sauke ajiyar zuciya. Ya dauko mata ruwa ya ɓalla wasu magani ya bata. A hankali ta sa hannu ta karba tana share hawayenta da bayan hannun, ya miƙa mata ruwan, ta sha sai kuma ta shanye tas ledar pure watern da ya bata. Kafin a hankali ta tashi zata tashi tana sake ɗauke ƙafarta.
"Gidan uban wa zaki ?
Ya ji bakin sa ya faɗa yana daka mata tsawa dan de shi kam ba shine ya faɗa ba. Sai da ya faɗa kuma ya ji to meye nasa a ciki? Kawai ya ja wani mumman tsaki. Hawaye ta share tana zauna a takure duk jikin karkarwa yake yi mata. Bata taɓa tunanin haka yake da faɗa ba. Dan gaisuwa ce ke haɗa su da ita.
Gama haɗa kayan sa ya yi kawai ya miƙe ya tashi ya bata waje. A hankali ta yi kwance tana rufe idan ta akan kujerar, tana cigaba da ɗan share hawayenta akai-akai.....