Free chapter · Read without an account
11
KISHIN MATA
Hafnancy...
Kishin ilimi, Kishin Jahilci, canfe-canfe, da kuma cin amana.
•Masu tambayar WhatsApp group ɗina ga link nan ku bi*
***
No.11
Tunda Kasim ya koma gida sai duk ya kasa samun sukuni da kwanciyar hankali,idan ya runtse ido sai yaga kazamin picture dʼinsu shida matar danʼuwansa Azeema sanda suke aikata alfasha,sai yake ganin tamkʼar yanzu abun ke faruwa ga wani irin jarababben feelings da yake neman sake taso mishi akanta,zubʼewa yayi saman gado yana mai rushewa da kuka yake fadin''innalillahi waʼinna ilaihi rajiʼun..! *KASIM MUNNIR* What have you done..?
sake barkewa yayi da wani sabon kukan yana fadin''Ya Allah plssss forgive me ka nesantani daga wannan balaʼi,Ya Allah na tuba bazan sake aikata alfasha da kowacce yʼa mace ba,Ya Ubangiji, ina rokon ka shiriya, da tsoronka,da tsarkaka,ka gafarta min dukkan zunubaina,kadan ko da yawa,na farko dana karshe, na sirri dana bayyane,Ya wanda ke sarrafa zukata, Ka sarrafa zuciyata akan yi maka da'a ba sabonka ba,Ubangijina na tuba ka yafeni kar kace zaka hanamun Mubeenah kasancewarta kamilalliyar mace,ada naso bʼata mata rayuwa ne ammh dake kai dʼin baka zalunci haka kuma baka bari azalunci wani saika tseratar da ita ga fadawa cikin tarkona sannan ni kuma ka jarabceni da mugun sonta,Ya Allah don darajar soyayyar da kakewa fiyayyen halitta karka hanamun Mubeenah.....ʼʼ
Kuka yaci mugun kʼarfinsa,kallo dʼaya zaka mishi ka tabbatar da cewa lallai yayi nadama sosai abun dai gwanin ban tausayi,ana haka nefa sai yaji kʼarar sakʼo ya shigo wayarsa kʼirar Infinix hot,bebi takan wayar ba saida ya sauke bashin sallolin da ake binshi,zuciyan nan tasa tayi bakikirin cike da takaicin salloli sun wuceshi ne alokacin yana can yana sabawa mahaliccin nashi,sai doubting yake ko Allah zai karbi wannan sallolin nashi?besan shi Allah Al-gafur Ar-rahimun bane,muddin ka tuba ka kuma rokʼeshi gafara toh tabbas zai gafarta maka tare da saukar da rahamarsa agareka,
Bayan ya idar kota kan abincin da kʼanwarsa Hanifa ta kawo mishi beyi ba ya jawo wayar yana dubawa,
*'MATAR TWINY'* shine sunan daya soma arba dashi as the sender,tuni yaji gabansa ya hau dukan ganga,da sauri ya budʼe sakʼon idanunsa suka sauka akan short message dʼin data aiko,
''Hi! Second hubby da fatar ka isa gida lafiya?thanks so much for giving a helping hands,ka huta lafiya and dnt forget to delete diz message after reading..ʼʼ
Wani dogon tsaki yajah cike da haushinta,har zaiyi deleting message dʼin sai ganin call dʼinta yayi yana shigowa,dasauri ya kashe wayar gabaki dʼaya yana jero mata zagi,ita kuwa acan bata zaci hakan daga gareshi ba,haba sai nan da nan hankalinta ya nemi tashiwa ta kasa zama haka kuma ta kasa tsayuwa,can wani tunani ya fadʼo ranta ta saki wani irin kasaitaccen murmushin da ita kadai tasan manufarsa tace ahankali''Kasim nasan bazaka tabʼa gangancin fallasa wannan sirri namu ba or would you...?
Tayi tambaya tamkʼar yana gabanta,girgiza kai tayi tana mai bawa kanta amsa''No nasan you wonʼt try dat shit ammh duk da hakan ya zama dole na tauna tsakuwa don aya taji tsoro,Kasim insha Allahu we must finish what we started,saina samu rabo dakai sabida tabbatar da cewa lafiyata kalau dama matsalar daga danʼuwanka yake,Ya Allah kasa matsalar badaga wajena yake ba kar nayi kukan danasani mara amfani,ai kuwa da Kasim ya mori gangar jiki abanza alhalin ni kuma banci riba ba...ʼʼ ta ida maganarta gami da rushewa da kuka,tana cikin wannan tashin hankalin ne Zuby ta fadʼo gidan don dama ta kʼirata tace mata ta dawo,tuni ta wartsake gudun karta dago wani abun don yadda kasan psychologist haka Zuby take.
****
A bʼangaren Gidado kuwa tunda ya tafi basu wani cika waya sosai da Jameelah ba don bata son ta matsa mishi bayan ga aiki agabanshi ammh itakam Hafsa waya akan waya babu ko dʼan tunanin cewa kai wannan fa aiki yaje yi yakamata nadan daga mishi kafa,a'ah sam batayi wannan tunanin ba har abun yakaishi wuya har tasa yayi mata magana yace sudan rage wayan,toh tun asannan tadanyi sanyi da takurar,akalla kwanakinsa kusan uku kenan acan sauran mishi kwanaki hudu ya dawo don dama sati dʼaya ne zasuyi,kuma idan ya dawo Jameelah ce zata kʼarbi girki.
Sosai Baddo ke jindadin zama da anti Jameelah har takeji ma kamar kar malaʼikanta ya dawo,acikin yʼan kwanakin nan da sukayi Jameela ta koyawa Baddo girki kala kala na zamani da ababen marmari,ga dressing dʼin daukar ido da take koya mata,iya sarrafa kalamai infact har zaunar da ita tayi tace''ke kʼanwata inaso kibar tsoron yayanki don shi dʼin ba dodo bane ko malaʼikan mutuwa ba,mutum ne shi kamarki dai,dadin abun kuma danʼuwanki wanda kuka hadʼa jini dashi,yanʼuwan kwarai da kʼyautatawa da kuma kʼaunar juna aka sansu dashi bawai nuna tsangwama da tsana ga junansu ba,ayau inason kibar jin tsoronsa,bawai nace ki dena bane kwata kwata ba aʼah kidan rage don kece ke cutuwa,ki maidashi tamkʼar yadda kike kallon kowa kike kuma sakewa da kowa,danʼuwanki ne ba dodo ba kinji yʼar kʼanwata...?
Hawaye masu zafi taji sun zubo mata tana jin wani irin mugun kʼaunar antin tata na kʼara shigarta dakʼyau,gaskia Anti Jameelah daban take acikin mata,acikin matan ma sarauniyarsu yʼar aljannah,duk yadda take kamantawa mutane kirkin Jameelah ashe ma ta dara hakan,wani abu dama saika samu kusanci da mutum kake sanin true colours dʼinsa,wani zaka ga ashe hawainiya ne mai canzawa,wani kuma yadda yake azahiri toh zaka sameshi ah badininsa ma hakan yake idan ka matso kusa dashi, rungumota tayi tana mai sake barkewa da kuka,Jameelah ta shiga bubbuga bayanta take fadin''haba kid sis meye na kukan kuma...?bazaki mun abunda nakeso ba kenan ko..?shikenan ya isa idan kina ganin kinfi jindadin tsoron nashi toh ai babu damuwa hakan nada kʼyau...!ʼʼ
Da sauri ta tari numfashinta cikin shesshekʼar kuka tace''Haba antina harni na isa naki kʼarban shawararki balle fa shawarace meh kʼyau kika bayar wacce zata amfaneni sabida kina kʼaunata harga Allah ni kuma na dau miki alkʼawari daga yau bazan sake jin tsoron danʼwana *SULEIMAN* ba,hakʼikʼa kalamanki sun sanyani jin wani irin bakʼon jarumtaka atare dani,Hamma Gidado kai danʼuwana ne wanda jini ya hadʼamu ba dodo ko malaʼika ba kamar yadda antina ta fadʼa don haka bazan sake bari zuciyata ta nemi yin bindiga akan tsoronka ba,Antina i love you so much Allah ya gaggauta azurtaku da yaʼya masu albarka...ʼʼ ta ida magana tana mai rushewa da sabon kuka,Jameelah ta kʼarba mata itama cikin raunin''Ameen ameen *MUBEENAH....!* Allahu ya kʼarbi adduʼarki my kid sis wallahi inason haihuwa.....ʼʼ ta fadʼa ayayin da hawaye zafafa suka wanke fuskarta,kukan tausayinta Baddo ta cigaba dayi tasa hannu tana share mata hawaye take fadin''Ya ilahi..! Antina pls dnt cry be strong for me,insha Allahu zamu cigaba dakai kukanmu ga mahaliccin sammai da kassai don shine mai bayarwa sannan kuma mai hanawa,nasan yana sane be manta dake ba antina,daga yau zamu fara tsayuwar dare my lovly anti har zuwa ranar da Allah zai share mana hawaye,Anti Surayya da Anti Azeema suma dʼin duk zamu sanyasu cikin duʼaʼinmu....!!ʼʼ
Kuka yaci mugun kʼarfinta,zuciyarta tamkʼar zatayi bindiga ta fito waje don tsananin tausayin waʼennan bayin Allahn,Anti Jameelah kuwa wani irin zazzafar kʼaunar yarinyar ne ya kʼara lullubʼe zuciyarta,badon kar ace tayi kʼarya ba da zatace ko danginta wato jininta basu kai Baddo shiga cikin wani hali da kuma damuwa akan rashin haihuwar tata ba,tuni taji zuciyarta na raya mata wani babban alʼamari wanda take ganin zaiyi matukʼar wuya abada goyon baya ammh ta yanke shawarar tuntubʼar Tsoho da zancen.
********
A yau ‘yan matan gidan,su Ramlah su Hanifa gayya dai sukayi gabaki daya yara yanmatan gidan suka kai ziyara gidan Gidado,toh ba laifi dai Hafsa tadan musu tarban arziki tunda har ta riga Jameelah shiga kitchen ta hadʼa musu kwamacalar da suka kasa cinta,akʼarshe na Baddo suka ci sai santi suke ta zubawa,Hanifa har kasa hakʼuri tayi tace tana kai loma''Baddo wai da gaske kece kika dafa abincin nan don nidai wallahi ban yadda zaki iya dafa abinci mai taste haka ba..?ʼʼ
Fatima dʼiyar Baba haruna har kusan kwarewa tayi sabida saurin magana''Gaskia Hanifa nima dai ban yadda ba itada common indomie dʼinnan yaushe Baddo ta gama iyawa da har zata iya dafa fried rice yayi dadin wannan..!? Anti Jameelah sai kʼyakʼyatar dariya take tayi ita ko Baddo kunyace ta kamata jin yadda yanʼuwan nata ke mata sharri ammh abʼangare guda kuma tana mai cike da kʼauna da kuma alfahari da antinta wacce itace ta koyar da ita abubuwa da dama kuma take kan koyar da itan,
''Antina ce ke koyamun...!ʼʼ ta fadʼa tana kallon Jameelah cike da kʼaunarta,waro eyes waje sukayi har suna rige rigen cewa''kai haba Antinmu da gaske..?ashe lallai muma zamu tare agidan kina koya mana...ʼʼ
Ramlah da tun dazu batace komi ba tace''Ai kuwa dako kunci ubanku ahannun Hamma Gidado idan yaga zaku takura mishi mata....ʼʼ aka kwashe da dariya adaidai lokacin Hafsa ta fito ta tarar sun ajje mata kular abincinta agefe suna cin na Jameelah,kala bata ce dasu ba taje ta budʼe kularta,yadda ta kawoshi haka ta sameshi ammh saidai an dʼan jagwalgwala wajen dandane dandane,tuni taji wani bakin ciki ya turnuke zuciyarta ta juyo afusace take fadi cike da dacin rai''Ammh wallahi Jameelah kinyi kadan ki gwadan salon makircinki,ki sani kowani bakʼin wuta da nashi hayakʼin haka kuma komi fitinar dʼan bunsuru,ya kiyayi matar kura,don iskanci ni zaki wulakanta ki ture abincina gefe wanda nasha bakʼar wahala na musu ina cikin amarcina ammh ban damu ba na tashi na girka musu nan wai naga dangin miji shine zaki ture nawa gefe ki basu naki...?
Har ga Allah Jameelah batasan basu tabʼa abincin ba donko dubawa batayi ba ta ajje nata,ammh data tambayesu sai ce mata sukayi sun tabʼa shiyasa bata damu ba,duban Ramlah tayi wacce ayanzu take mamakin yadda akai tayi sanyi wanda ada can ta tsaneta tace da ita''Haba Ramlah nifa banson hadʼa husuma meyasa zakumun kʼarya ashe ko tabʼawa ma bakuyi ba..?why?ʼʼ
Kai tsaye Ramlah tace''Abincin ne babu taste kamar an wanke kan mahaukaciya shiyasa muka kasa ci...!ʼʼta fadʼa ba tare da jin tsoro ko dar aranta ba,su Hanifa suka kwashe da dariya sai fasa mata kai suke''ohhh yarʼuwata kina aljannah tawar...ʼʼ
Cike da zafin rai Hafsa ke nuna Ramlah da yʼar yasa take fadin''Ramlah you..?kece ke fadʼamun bakʼar magana ayau tamkʼar saʼarki ko kuwa kin manta cewa ni dʼin yayar kʼawarki Nabeelah ce dadin dadawa kuma matar yayanki...?ʼʼ cikin rashin damuwa Ramlah tace''Madam ba mantuwa nayi ba kawai i juz dnt lyk matar auren da bata iya girki bane,I am a wife material 100yards,na iya kaza na iya kaza ashe duk cika baki aketa mana baʼa iya komi ba,am sorry to say someone here is not qualified don haka ni Ramlah na canza sheka anti Jameelah ina yinki,ki dadʼe kiyi lasting matar police kama barawo....!ʼʼ
Kai Ramlah akwai daru da kuma iyasa mutum hawan ruwa,fashewa da kukan bakin ciki Hafsa tayi tace with virbating voice''Lallai Ramlah zaki gane cewa shayi ruwa ne,tabbas kin debowa kanki dala babu gamo,kuma Nabeelah zata dawo zan fada mata irin wulakancin da kikamun don tasan matsayin kawancenku....ʼʼ tana gama jawabinta ta kwashi kulolinta tana cizgar kuka tayi part dʼinta sai kuma duk jikin kowa yayi sanyi hatta dani kaina marubuciyar don tabbas anan zamu iya cewa baʼa kʼyautawa Hafsa ba,Jameelah ta rufesu da fada sosai don abun yafi yi mata ciwo ammh Ramlah ko ah jelar kallabinta,Hafsa na isa daki ta dauki waya ta sanya kʼiran Gidado yana dagawa ta kora mishi bayani tana kuka,shi kanshi ransa yayi matukʼar bʼacewa da zancen ammh sai ya shiga lallashinta har ta sakko,bayan sun kʼare wayar ya latso Jameelah,tana ganin call dinsa saida gabanta ya fadi don tasan ta faru ta kare wai anyiwa mai dami daya sata,da rawar jiki ta danna receive bayan ta tashi daga cikinsu takoma gefe ''Assalamu alaykum sahibu.....!ʼʼ
''Hey...! hang it over there,hearthrob kin matukʼar bani mamaki wai dake ne zaʼa hadu aci mutuncin matata,toki sani wannan dʼin ya zamo nafarko kuma na kʼarshe da zaʼa kuma maimaita hakan in ba haka ba kuwa zan dauki tsassauran mataki,ki sani yadda na aureki don ina kʼaunarki toh itama haka na aurota don ina kʼaunarta,babu wacce tafi wata awajena....ʼʼ
Hawayen mamakinsa ne ya wanke mata fuska tace murya na rawa''Suleiman nice kake fadawa waʼennan maganganun don ranka ya bʼace...?atleast keep calm and listen mana..!ʼʼ cikin hargowa kamar zai daketa ta waya yace''Banason jin komi bawa Ramlah waya don an fadʼamun cewa itace gang leader dʼin,bani ita in fara cin kutumar ubanta kafin na gangaro kansu Hanifa,maza nace.......!ʼʼ ya ida magana tare da buga tebirin gabansa wanda har cikin dodon kunnuwanta ta jishi,one thing about DCP Gidado shine he is hot tempered lyk mad ooo,dasauri ta zare wayar daga kunnenta tana sake duban ko dagaske shi dinne ya kirata don be tabʼa gwada mata tsantsar bʼacin ransa kamar yau ba,dgaske shi dinne,katse mata tunani yayi yace''ko bakiji abunda nace bane...?ki bani ita kafin ranki ya bʼace...ʼʼ
Kala bata iya ce masa ba ta matsa inda suke duk sun kura mata ido ne sanda ta fara wayar kuma sun dago da wanda take wayar dashi wato malaʼikan duniya mikʼawa Ramlah wayar tayi tace''ungo yayanki keson magana dake...!ʼʼ
Wani irin back tumble Ramlah tayi ta hantsilo daga saman kujera tace ah tsorace''wayyo Allahna na shiga uku shegiyar matar nan tayi karata wajen mugun nan,Hanifa ku taso mu tafi...!ʼʼ ta fada tana kwasar mayafinta da fashion bag dʼinta kuma duk yaji abunda ta fadʼa,tuni zuciyar Baddo takai kololuwar baci ganin antinta na tsiyayar hawaye abunda ta tsani gani kenan,basu zata ba haka kuma basu tsammaci hakan ba ni kaina ban tabʼa mafarkin hakan ba,sai gani mukai Baddo ta wufce wayar daga hannun Anti Jameelah ta kange akunnenta tana huci tare da ciccin magani,cike da zafi ta soma magana''wai wayekai..?wai shin kana jin kanka wani sarkin ne ko kuwa what do you take urself as..?can you die of constipation..?I asked bcz Iʼam worried about how full of shit you are,ka sani ina iya shanye komi ammh banda zubar ruwan hawayen Antina Jameelah,zan iya yakar duka mutanen duniyan nan in har akan ganin bʼacin ranta ne balle kai karamin alhaki,kasani duk abunda kake ji dashi toh kuwa na fika jinshi shiru shiru ba wasa bane kawai gudun magana ce........ʼʼ
Cike da tsananin mamaki ya tari numfashinta ta hanyar doka mata tsawa''Who the heck ar you young woman...?gayamun wacece ke don ban dago muryarki ba...!ʼʼ
Tace''Aiko zamu shekaru dubu ahakan ne bazaka tabʼa dagowan ba don dʼan hakin daka raina yana neman shayar dakai madarar mamaki...ʼʼ har yana kokarin magana tace''Dakata yallabai zanso ka addana kalamanka har sai zuwa nan gaba,have a nice day.....!ʼʼ tayi saurin datse call dʼin tsoro fal ranta kʼarfin hali ne kawai tayi.....................
Wannan paid book ne, amma zan ɗan bada garabasar free pages. Maza ki hanzarta biyan 500naira kacal domin ki mori karatunki ta wannan asusun bankin 7065481260,Palmpay, Hafsat Mustapha. Sannan a turo da shaidar biya ta *** ko kuma a garzaya kan arewapan.
To be continued…
#’Yar Mutan Naija#
***.