Free chapter · Read without an account

12

by Hafsat mustapha · KISHIN MATA

KISHIN MATA

Hafnancy...

Kishin ilimi, Kishin Jahilci, canfe-canfe, da kuma cin amana.

•Masu tambayar WhatsApp group ɗina ga link nan ku bi*

***

  No.12

Kallonta suke cike da mamaki don zasu iya buga kʼirji suce koda ace wata acikinsu zata iyayin kʼarfin halin aikata abunda tayi yanzu,tofa acikinsu dʼin ita dince bazata tabʼa iyawa ba idan akayi duba da irin shegen tsoronta ammh sai gashi tashi daya ta shayar dasu madarar mamaki.

Jameelah ce ta kawar da silent moment dʼin ta hanyar sharara mata zazzafar mari,ta soma magana cikin muryar dake bayyana zallar bʼacin rai''Kid sis how dare you..?wani kalar shit kenan kika aikata..?dana ce miki ki rage tsoron danʼuwanki cewa nayi ki mishi rashin kunya..?ko kuwa mantuwa kikai da cewa shine gaba dake ayayin da kike kʼanwarsa..?kid sister for dat matter wanda ya isa haifen irinki,heʼs 37 and youʼre juz 17,so now compare the difference,ya baki good 20years....ʼʼ

Su Hanifa sukace''woww...! ashe Hamma yana da yawan shekʼaru haka ammh sam baya tsufa? agaskia yana da jiki meh kʼyau...!ʼʼ

Jameelah bata tankasu ba ta cigaba da magana''kinsan maʼanar constipation kuwa...?it is a medical condition which causes people to have difficulty getting rid of solid waste from their body,ma'ana shan wahala wajen kashi ko fitsari,Mubeenah wat an insult..?na tabbata baʼa tabʼa yi mishi irin wannan zagin ba kuma wallahi nasan daga ni harku dukah mun shiga uku....ʼʼ

Kʼarar wayarta ne ya katseta,jiki na rawa ta duba taga shine ke sake kʼiran,atsorace tace dasu''Gashi nan wallahi yana sake kʼira...!ʼʼ duk suka kura mata idanu suma dʼin atsorace ammah banda Baddo wanda tuni zuciyarta ya riga da ya bushe da tsoronsa ayanzu,ah handsfree ta saka bayan ta daga,bata kai ga sallama ba taji saukar maganarsa cikin dodon kunnuwanta,cikin tsananin bʼacin rai yake fadin''who was dat village idiot dat gave me the worst insult of mylife..?wacece wannan dʼin wacce ta samu guts da kuma courage na jifana da bakʼakʼen maganganu...?answer me who is the ass hole.......?

Yayi tambaya tare da sake buga tebirin gabansa idanunsa sun canza launi zuwa ja tsabar bʼacin rai,su Hanifa tuni suka fashe da kukan tausayin kansu,Baddo kuwa ko ajikinta,amaimakon Jameelah ta bashi amsar tambayarsa,sai kawai itama ta fashe da kuka tana fadin''Sahibu pls ka saurareni,wai meyasa ka cika zuciya ne haka...!?

Cike da zafi yace''Ai bazaki masan na cika zuciyar ba sai kinji kalmar saki ya fito daga bakina tukun idan har baki gayamun ko wacce jackass dʼin bace....ʼʼ

Cike da tsantsar mamaki duk suka waro eyes waje,murya na rawa tace''yan..zuu..su..sulei..man..saika..iya..sakina..akan..wannan...karamin..abun...?''

''Yo kece kike masa kallon karamin abu ammh yadda na dauki lamarin ya shallake gaban tunaninki,Jameelah u ar burning my airtime nace ki gayamun ko wacece..!ʼʼ ya ida magana ah tsawace,

Ah tsorace take kallon Baddo wacce ayanzu hawaye ya wanke mata fuska na tsananin tsoro ganin abun ashe zai zama serious,kai ta shiga girgiza mata alamun don Allah karta gaya mashi,dasauri Jameelah ta runtse idanu tace''Na gwammace ka sakeni dʼin da in gaya maka ko wacece...ʼʼ tayi saurin kashe wayar gabaki daya gabanta na dukan tara tara,sabon kuka su Ramlah suka sake rushewa dashi hatta da ita Baddon kukan take don bata zaci abun zeyi serious haka ba,

''Wayyo Allah Baddo kin kara mana wani laifin akan nada,anti Jameelah yanzu ya zamuyi ne...?sannan ni kuma banison ace ta sanadinmu ki rasa aurenki don wallahi babu tantama Hamma zai iya aikata abunda ya fada,ni kawai ki kirashi ki fadʼa mishi gaskia karki damu da batunmu ai dukah bata kisa sai inhar abun yazo ne da karan kwana....ʼʼ Ramlah ta fadʼa tana hawaye,girgiza mata kai anti Jameelah tayi tace''Ramlah karku damu da batuna yanzu dai kuyi ta kanku don wallahi yadda wan nan naku yadau mugun zafi da lamarin nan toh am very sure he can do and undo,yanxu dai kuyi maza ku kama hanya ku tafi don wallahi nasan karamin aikinshi ne ku ganshi ya fadʼo gidan babu shiri kuma abun bazai mana kʼyau duka ba,Baddo kema dʼin ki bisu kawai don kema kinsan bazan iya cetonki daga hannunsa ba....ʼʼ

Baddo ta waro idanu waje hawaye na ziraro mata tace cike da dacin rai''Antina wallahi babu inda zani in barki,bazan tabʼa tafiya na barki cikin tashin hankali da kunci ba,ina nan wallahi ruwan daya tafasa ya dadʼe be kone ba,Anti Ramlah ku wuce abunku agaidasu Yumma...ʼʼ ta fadʼa tana maida kallonta akansu,matsawa kusa da ita tayi tana fahimtar da ita abunda zaije yazo muddun ya dawo,dkyar ta samu ta yadda zata bisun,haka tana kuka Jameelah ta tayata hadʼo kayanta suka fito waje,azuciyarta tace ''Kid sis dawowa gidan nan da zakiyi next insha Allahu da auren Suleiman zaki dawo dashi akanki...!ʼʼ

Su Ramlah suka mata sallama suka wuce dakyar aka bʼanbʼare Baddo ajikin Jameelah,tana kuka itama Jameelar na kuka,Baddo sai fadi take''Antina i donʼt want to leave you...ʼʼ

Murmushi Jameelah tayi kan tace''Ni kaina my kid sis,,shiyasa nakeson nazo na nemi alfarma wajen Tsoho kan abani rukonki sai ki komo hannuna da zama ko kuwa bakʼyaso...?

Cike da farin ciki tace''Inaso mana antina ammh makaranta na fa sannan kuma banison in tsaya waje daya da hamma....!ʼʼ

Kura mata idanu tayi sannan tace''zancen school naki karki damu zamu canza miki da wani anan,ammh meyasa bakison ki zauna inuwa guda da Hamman naki..?sabida kina tsoronsa right...?toh maza ki dena kamar yadda na fadʼa,yanzu gayamun kin amince dai zaki zauna da anti Jameelarki sannan kuma kin shirya kʼarbanta amatsayin yarʼuwa..?

''Yes antina na amince dari bisa dari idan har su yabbana da Tsoho sun bada goyon bayan hakan...ʼʼ ta fadʼa with full confidence,Jameelah ta sake cewa''Mubeenah kefa da bakinki kika amince don haka banison jin stories ko wani grammers nan gaba...!ʼʼ

murmushi mai ban shaʼawa ta sakar mata sannan tace''Antina babu wani stories da zan miki wallahi,,nina amince zan zauna da Antina kuma yarʼuwata don haka ki rubuta ki ajje..!ʼʼ

Wani sanyin dadi ne ya ratsa zuciyarta ammh aranta tace''Daʼace kinsan abunda nake kokarin kullawa ne da baki amince ba,fatana ayanzu Allah yasa su Tsoho suyi naʼam da zancen....!ʼʼ

Su Ramlah dai ikon Allah suke ta kallo da mamakin irin wannan soyayyar dake tsakanin bayin Allahn nan,ashe Hafsa tana tsaye awaje ah part dʼinta tana kallonsu ammh su basu lura da ita ba,tabʼe baki tayi tana meh daga murya tace''Asauka lafiya dangin tsiya,,ke kuwa kishiyar waje wacce ta shigo ta hana na gida sukuni lafiya zaki wuce tun yau kuwa...?!ʼʼ

Ramlah na kokarin tanka mata sai Jameelah ta hanata,Emmanuel tasa ya maidasu gida,sai data ga wucewarsu sannan ta koma ciki,

Abʼangaren DCP Gidado kuwa bayan ya kʼare waya da uwargidan nashi,rai bʼace ya nemi tahowar gaggawa don luckily sun kʼare abunda ya kawosu acikin kwana hudun nan don haka ba zasu cika kwana bakwan kuma ba tunda sun gama,washegari ne yakamata su taso ammh sai yace musu wani uzuri na jiransa da gaggawa agida,haka aka kaishi airport ya hau jirgi.

****

Tun jiya da Kasim yakashe mata waya hankalinta ke tashe har zuwa wannan lokacin don ayanzu dʼin akunnen yake ammh yaki dagawa hakan yasa ta yanke shaʼawar zuwa har gida ta sameshi saidai kuma adduʼarta dʼaya Allah yasa ta sameshi,ita kadai taje tabar Zuby agida,koda ta isa saida ta soma shiga parts dʼin kowa ta gaishesu har wajen tsoho taje suka dan tabʼa fira sama sama,akʼarshe ta fakaici idon mutane ta nufi boysquarterʼs wanda yake tacan wani bʼangare na gidan,duka samarin gidan waʼenda suka kawo girma kowanne nada dakinshi anan,adaidai kʼofar dakin Kasim ta dakata sannan tasa hannu ta shiga kwankwasawa,tana yi tana waige waige gudun kar wani ya ganta,acikin baccinsa yaji kamar ana knocking,hakan yasa ya mikʼe yana jero tsaki cike da haushin an takura baccinsa,ya duba agogo 2:30pm ne yanzu kuma ko cikakken 30mins bekai ba aka tasar dashi,ya sake jan wani dogon tsaki jin ana cigaba da knocking continuosly yace ausace''Don Allah ina zuwa kafin aballamun kʼofa..ʼʼ

Idanunsa ne suka sauka akanta bayan ya budʼe kofar,dasauri ya lekʼa yaga ba kowa awaje hakan yasa cikin azama ya jawo hannunta ta fadʼo dakin,sai gata zubʼe asaman cool tiles dʼin dake malale akasa,cike da tashin hankali yace''Ke ubanwa yace kizo dakina ko so kike mutanen gidan susan da abunda muke ciki ne..!?ʼʼ mikʼewa tayi tace cikin rashin jindadin abunda yayi mata''Shiyasa ka jawoni na fadi haka don baka da kirki ko..?ai daʼace ka dauki wayata ne toh da baka ganni anan dʼin ba,,ammh rashin respond dʼinka yasa hankalina kasa kwanciya don tsoro nake karka fallasa sirrin namu shiyasa na wanko kafa nazo...!ʼʼ

Dariya mai dʼan sauti ya saki gami da lashe lips yace''Anti Azeema kenan! Idan wannan ne damuwarki toki kwantar da hankalinki babu wanda zaiji ammh ki sani bazan sake hadʼa shimfida gudʼa dake ba....ʼʼ saurin taran numfashinsa tayi ayayin da hawaye ya shiga bulbulo mata tace''NO no kanina donʼt do diz to me,letʼs finish wat we started,wallahi ko jiya ma saida babban yayanmu ya kirani yake kara jaddada mun cewa insha Allahu Mustapha na dawowa zaʼa raba auranmu,don Allah kanina karka bari arabamu don ina tsananin son danʼuwanka,plssss na rokeka koda na minti biyar ne kadan kwanta dani watakila asamu rabo ayau,,idan har baʼa samu jiya bane toh tabbas yau zaʼa samun kaji plssss Kasim....!ʼʼ ta fadʼa tare da cafko bananarsa dake cikin wando,da rawar murya yace bayan ya buge hannunta''Anti Azeema ah ina zan kwanta dake..?kina nufin agidan ubana..?shin ke bakya ma tsoron wani yazo ya kamamu ne...?ar you sure you are in ur senses kuwa...?

Dasauri tace''karka manta ka rufe dakin fa sannan kuma ai ba dadewa zamuyi ba minti biyar kawai nace plsssssss my kʼani...!ʼʼ ta fadʼa tana kokarin kwance zaninta,runtse idanu yayi yace cikin dʼan daga murya''Stop it...karma ki soma don bazan tabʼa biya miki bukatar taki bane acikin gidan mahaifina ba,infact i will nvr do that again, wanda ma nayi kuskuren yi ina rokon Allah ya yafemun ?don haka tun muna shaida juna ki fitar mun adaki salum alum kafin na canza miki kamanni yanzu...!ʼʼ

Cike da gigita yace yana jin ɗaci aransa" Matar dan'uwana ? ina Kasim kaci amanar Mustapha" ya rushe da uban kuka.

da mamakinsa tace''Dagaske sai ka iya sa hannu ka daki matar aure for speaking out loud..?Kasim ka saurari kanka kuwa..? Ni zaka sawa hannu ajiki da Sunan duka..?"

''Toh Meh zaʼa fasa..?mutuwa ko hisabi..?aini tun aranar da kikai kuskuren ɗanɗana mun zumarki, toh tun awannan ranar girmanki da darajarki duk suka zubʼe agaban idona,ayanzu baki da maraba da high class prostitute awajena...ʼʼWani irin dirty look ta watsa mishi tare da daga hannu ta sharara masa mari tace cike da zafi''how dare you look into my eyes and call me a prostitute..? In banda kaddara mai zai sa har in nemi ƙanina kuma ƙanin Mijina? koka tabʼa ganin wani akaina ne bayan kai..?

''To waya sani abu ah duhu...?ki sani Azeema sai kinyi danasanin daga hannu kika mareni,,now out of my room kafin nasa kiyi nadamar sanina acikin kaddarar rayuwarki...ʼʼ ya fadʼa yana kokarin budʼe dakin.

Ganin ransa yayi mugun bʼaci yasa hankalinta dagawa,dasauri ta durkushe tare da kamo kafafunsa ta rungume tana kuka tace''No plssss kasim donʼt do diz to me don girman Allah kayi hakʼuri ka yafemun karkace zaka juyamun baya...!ʼʼ

Sai kuma yaji jikinsa yayi sanyi don arayuwarshi kukan mace na rikitar dashi,tanan ne ake samun cin galaba akansa,hawaye fal idanunsa ya dagota yake fadin''Ya ilahi...! Anti Azeema toya kikeson inyi ne donni gaskia banason mu sake yi...ʼʼ

Rungumeshi tayi tana rera kuka ahankali,cike da tashin hankali ya dago fuskarta yana share mata hawaye yace''Yi shiru Anti Azeema wallahi ni banason kukan nan naki toh naji zanyi ammh one last more saidai kuma kiyi hakʼuri baʼa nan gidan ba ki bari zanyi mana arrangement ko zuwa gobe ne saimu hadu tunda jibi oga zai dawo,kinga ni bazan iya zuwa gidanku ba ina tsoro ammh zamuyi waya muyi arranging inda zamu hadʼe okay...?ʼʼ

Murmushi mai tafiyar da imani ta sakar mishi gami da gyadʼa kai alamun ta gamsu sannan ta gyara daurin zaninta,saida ya duba yaga babu kowa sannan ta fice zuwa cikin gida kuma babu wanda ya zargeta da wani abun,tana gidan harsu Ramlah suka iso,ganin Baddo da kaya aka shiga tambayar ko lafiya..?sukace Baddon ne da kanta tace zata biyosu don dama haka suka tsara cewa zasu fada,

***

''Amma wallahi anyi asarar mace anan,meh akeyi da matar da bata iya barwa cikinta abu harsai takai kʼara wajen miji..?Hafsa anji kunya wallahi da gani bakisan komi ba akan zamantakewar aure ba kawai kin daiyi ne ammh akan qualified on trial...ʼʼ

Cike da haushi Hafsa tace''Dallah can rufemun baki munafuka ki gayamun uban wanda zai iya barwa cikinsa irin abunda kukamun..?zakizo mun da wani tsamin baki wai am not qualified for marriage toh sannu ke meh qualification dʼin ai naga kin kyankyashe kwai...!ʼʼ

Tuni wuta ya daukewa Jameelah don ta gano cewa gorin haihuwa ce ta mata,wani irin kukan kura tayi ta shako Hafsan tana kukan bakin ciki....

Adaidai wannan lokacin kuma aka iso da Gidado…….

Wannan paid book ne, amma zan ɗan bada garabasar free pages. Maza ki hanzarta biyan 500naira kacal domin ki mori karatunki ta wannan asusun bankin 7065481260,Palmpay, Hafsat Mustapha. Sannan a turo da shaidar biya ta *** ko kuma a garzaya kan arewapan.

*Just few free pages to go…..*

To be continued…

#’Yar Mutan Naija#

***.

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.