Free chapter · Read without an account

Chapter One: (Ashraf)

by The Healer's Pen · NI DA KANNENA


BIRNIN KANO (December-2023)


A zaune take a cikin mota ta alfarma tana danna wayarta mai tsadar gaske cike da nishadi da wani yanayi mai ƙayatarwa.


Ta ɗago a nutse ta kalli tagar motar, ta lura da yadda suke tafiya akan titın cike da nutsuwa acikin gudun mota matsakaici, a hankali ta maida hankalınta kan fuskar wayarta misalin karfe 12:58pm na rana ya nuna mata.


Ta mai da hankalin ta kan driver motar tace:


"Amir kadan kara sauri, kasan Daddy baya son jira."


Cike da nutsuwa da ladabi yace: 


"To anty."


Ba'a fı mintuna uku zuwa hudu da yin wannan maganar ba taji Amir yayi saurin taka birki, cakın sauri ta dago kanta ta kalli Amir dake zaune a mazaunın driver cike da tashin hankali tana ambaton "Innalillahi wa'inna ilahi raji'un"


Cikin hanzari Amir ya mai da hankalin sa kan titin tare da leƙawa ta window motar yana faɗin:


"Kaga irin ta nan, gashi nan sun kaɗe mutum, haba gudun da sukeyi yayi yawa."


bata jira wata wata be tace:


"Amir mu muka kadeshi?"


Cikin sauri ya janye hannun sa daga stirring motar yace:


"a'a bani bane wadan can ne."


Ya furta tare da yi mata nuni da wasu motoci guda biyu kirar Toyota Land Cruiser Prado da sukayi parking a tsakiyar titin.


A hankali ta mai da hankalinta kan motocin tana nazarin su, ta lura da wani abu guda daya, ga moticın dai sun tsaya mutane sun fara taruwa domin duba bawan Allah da aka kade ma'abocin tura kurar ruwa, amma babu wanda ya fito daga motar domin duba halin da yake ciki.


Hakan ya matuƙar ɓata mata rai, wanda hakan ya saka cikin Kufula ta fara ƙoƙarin buɗe murfin motar domin ta fita.


Cikin sauri Amir ya juyo ya kalle ta yace:


"Please aunty i beg karki fita, let me handle the issue."


Ya faɗa yana ƙoƙarin fita shima.


Bata ko Kalli inda yake ba ta fice daga motar.


Amir ya saka hannun sa ya dafe goshin sa, sannan ya ja wani numfashi tare da bin bayan ta cike da tsoron abinda zata iya aikatawa, saboda ya san halin ta bata tsoro.


Cikın sauri da sasssarfa ta nufi inda mutanen suka taru ta kutsa taga wanda aka bige ya kama kafarsa yana ta girgiza kai alamar shi kadai yasan me yake ji.


A fusace ta sake kallon motocin da suka bige shi, abin da ya bata mamaki da haushi wai horn ma sukeyi suna so a basu hanya su wuce, nan taji ta sake kuluwa cike da takaici ta mai da hankalin ta kan Number motocin, cike da mamaki ta tsaya tana nazarın su. 


Hayanıyar matasan da tayı yawa ne tasa ta mai da hankalinta kan matasan da suke zage-zage, ta kalli ɗaya daga cikin su tace:


"Kuyi hakuri don Allah ku samo abun hawan da za'a kaishi asibiti tunda abun ya tsaya iya haka Allah ya tsare gaba."


Ta juya ta nufi inda motar su take ta dakko jakarta tadebo kudi da bata san adadın suba ta mikawa Amir tare da faɗin:


"Ku nemi abun hawa ka raka su asıbti."


Cike da hanzari da mamaki ya dago yana kallonta zaiyi magana ta dakatar dashi da faɗin:


"Bani key din motar." 


Tare da mika masa hannu.


Ya dan dage kamar bazai bayar ba sannan yace:


"amma aunty..."


Cikin tsawa ta sake miƙa masa hannun ta a karo na biyu tace: 


"Bani nace maka"


Cikin sauri ya mika mata ta karɓa da sauri tare da shigewa cikin motar ta fara bin bayan waɗan nan motocin.


Amir ya shiga rudani saboda har ga Allah yasan ta idan ta cimma masu bazasu ƙare ta daɗi ba, sannan bai san mai zaice da Daddy ba saboda shi yace ya ɗakko ta, babu shiri ya zaro wayar sa ya fara ƙoƙarin kira.


A hankali wadannan motocin suka samu hanyar sulalewa, duk da kasancewar akwai taron jama'a a wajen bai hana su neman hanyar ficewa daga wajen ba a hankali.


Ita kuwa cıkın sauri da kwarewa ta dinga bin bayan motor har Allah ya bata sa'a tasha gabansu, babu Shiri suka tsaya a gefen titin.


Cikin hanzari ta bude motar ta fito tana huci, da gani babu alamar tsoro a tare da ita, haka ta nufi ɗaya daga cikin motocin ta kwankwasa glass din motar da ke baya, shiru ba'a buɗe ba haka ta koma gefe ta tsaya tasha alwashin babu inda zataje har sai wani ya fito daga motar. 


Tun da ba makawa ta tabbata babu wata hanya da zasu iya ƙetarewa kasancewar ƙaramin titi ne inda suke kuma akwai ƙarancin ababen hawa, shiyasa ta tabbata babu hanyar da zasu wuce dole ko ita ko su wani sai yayi hakuri ya janyewa dan uwan sa, kuma ta tabbata bazata matsa ba har sai sun fito anyi duk rikicin da za'a yi saboda abinda sukayi bai dace ba, gashi sam ita bata tsoron rikici.


Tana tsaye kamar wata soja fuskarta a ɗaure ga tsananin zafin rana duk da lokacin sanyi ne amma yau rana ta buɗe, hakan duk bai dameta ba, ga dukkan alamu irin mutanen nanne masu kafiya da taurin kai akan abinda suka sa gaba.


Tana tsaye wajen mintuna 9-10 wayar ta ta fara ringing, tayi ajiyar zuciya lokacin da hankalin ta ya kai kan sunan da ya bayyana a screen din wayar, (DADDY).


Ta fara ƙoƙarin daidaita nutsuwar ta sannan ta kara a kunnen ta tare da yin sallama.


Daga daya bangaren aka amsa tare da faɗin:


"Nuratu ya na jiku shiru ba ke babu junior, har yanzu baki ɗakko shi bane?"


Hannu ta ɗora a gashin ta alamar tayi mantuwa, ta kalli fuskar wayar ta taga lokaci har ya ƙure, ita sam ta manta da dakko shi daga school, amma saboda karya ba halinta bane cıkın ladabi tace:


"i'm sorry Daddy wani uzurine ya tareni a hanya amma yanzu zan je na ɗakko shi inshaAllahu." 


"Toshikkenan ba matsala Allah ya kawo ku lafiya, amma ku hanzarta muna da abin yi kin sani."


"Toshikkenan inshaAllahu gamu nan."


Ta amsa cike da ladabi tare da jefa wayar kan kujerar kusa da driver zuciyar ta fal da zargin dole wani ya kira Daddy ya fada masa me yake faruwa.


Bata da zaɓi haka ta juya bata ƙara bin takan motocin nan ba saboda bata yiwa Daddy gardama ta shiga motar ta jata ta ƙarfi.


Ƙasaitaccen yana zaune cikin ɗaya daga cikin motocin yana kallon duk abinda yake faruwa, yayi murmushi sannan yayi wa direbobin nasa umarni da su bi bayan ta.


A nutse take tukin ranta a ɓace zuciyar ta fal da takaicin ba'a barta ta amayar da abinda yake ranta ba, wayar ta ta sake yin ringing a karo na biyu ta dauka tare da amsa sallama cikin ladabi ta wancan ɓangaren akace:


"Madam mun kammala, everything is ready signing contract din kawai zakiyi."


Ta saisaita muryarta tace:


"Ba matsala I'm in my way nan da 5mn zan ƙaraso amma sauri nake ba zama zanyi ba kuyi arranging komai kafin na ƙaraso." 


"To ba Matsala inshaAllahu."


Cikin ƙwarewa ta karkata kan motar ta zuwa wata ƙatuwar Plaza da ake sai da foreign furnitures ta nemi waje tayi parking ta nufi hanyar shiga.


Cikin hanzari wani matashin da bai wuce Shekara talatin ba ya nufo inda take da kujara da pen ya miƙa mata zai fara bayani ta dakatar dashi da faɗin:


"Naga review na contract din ai"


Cikin sauri tayi signing ta nufi hanyar fita ko zama batai ba.


Tsaye tayi a waje cike da mamakin yadda taga wata mota tayi wrong parking tare da blocking ɗin motar ta, ran ta ya kuma ɓaci da ta gane motocin sai tayi murmushin nasara, acikin ranta tace "haka nake so."


Ba tayi niyyar kula su ba wannan karon, cikin hanzari ta nufi inda motar ta take ta buɗe ta fara haɗo kayan cikin motar da niyyar ta hakura ta hau wani abun shi kuma ko waye a ciki bai isa ya bar wajen ta daɗi ba idan ta gama uzurin ta zata dawo kan sa.


Cike da ƙasaita ya buɗe motar ya fito ya nufo inda take, da mamakinta taji murya ta bayan ta ana ce mata:


"Iya dabarar taki kenan? Na ɗauka zaki tsaya mu kara."


Ba ta kalli inda yake ba sai da ta gama haɗa komai na ta sannan ta ɗago kanta sukayi ido biyu.


Da mamakinta ta ƙare masa kallo, duk da bata taɓa ganin sa a zahiri ba amma tabbas wannan "ASHRAF" ne.


Amma kasancewar ta kwararriya a ɓoye abubuwa a ranta ta kau da kanta ta basar tare da faɗin:


"A'a ai ban fara don na sare ba, a yanzu inada abubuwan da suka fi ka mahimmanci ne, saboda haka ka jira ni, mara tausayi kawai"


Ta faɗa tare da wucewa ta barshi a wajen.


Sai da ta ɗanyi nisa sannan yayi murmushi yace:


"I'm waiting!"


Ya hau daya daga cikin motocin suka tafi tare da barin wadda tayi blocking ɗin ta a wajen.


Bin bayan su tayi da wani irin kallo mai cike da ma'anoni kala kala sannan ta fara yunƙurin fita daga harabar wajen.


Da hanzarin Yazid Manager wajen ya ƙaraso in da take ya dakatar da ita, kasancewar labari ya iske shi tuni, sannan ya kalleta yace:


"Madam bari na kai ki a mota ta."


Ko kallon sa bata yi ba ta kira ɗaya daga cikin securities na wajen tace:


"Nemo min Napep"


Turus! sukayi gaba dayan su suna kallon ta.


Yazid ya sake kallon ta yace:


"Please Madam ko Saboda oga kiyi hakuri na kai ki zai mana faɗa, don Allah Madam." 


Ya faɗa yana kallon ta tare da marairaicewa.


Ko kallon sa bata yi ba ta ƙara kallon security a karo na biyu tace:


"Ko na fita na nema da kai na?" 


"A'a"


Sannan ya nufi waje cikin sauri.


*********************


Misalin karfe 2:30 tanufo jerin manya gidajen da suke unguwar Nassarawa G.R.A acıkın birnin Kano Dabo.


Hannunta rungume da wani kyakkyawan yaro da bai wuce shekara 4 ba fuskar yaron cike da tsoro ya kalleta yace:


"Ukhty daddy fa ya hana mu hawa Napep yace min fa za'a sace mu idan muka kuma hawa don Allah mu sauka."


Ya faɗi maganar yana shirin fashewa da kuka.


Murmushi tayi sannan tace a ran ta (Allah sarki ɗan gata, da ana sace mutane da ban haife ka ba, da tuni an dade da sace ni).


A hankali ta maida hankalin ta kan sa in da taga ya fara zubar da hawaye, a fusace ta daka masa tsawa tare da fadın:


"Yi mın Shiru! ba nace ka dinga zama jarumi ba a koda yaushe, kai namiji ne, bana son shirme."


Saboda yasan halin mahaifiyar tasa ba shiri ya rufe bakinsa amma ya kara kankameta.


A hankali suka nufo wani katafaren gida wanda bamu da lokacin tsayawa mu fasalta kyawun sa, ƙayatuwarsa, da kuma girman sa, ta umarci mai napep din da yayi horn sai da yayı horn har ya gaji sannan securities guda biyu suka fito a fusace suka yo kan su, tunanin su wasu ne daban, sai da ta sauke facemask ɗin fuskarta sannan cikin sauri suke ce:


"We're sorry madam"


Suka faɗa tare da wangale musu get ɗin wannan katafaren gida mai kama da masarauta suka shige ba tare da ɓata lokaci ba. 


Saukar Su ke da wuya ta hango daddy tare da Amir a tsaye a harabar gidan kamar daman ita suke jira, ta juya ta sallami me Napep da kudi masu yawa ya tafi yana murna da godiya.


Sannan ta ƙaraso in da su Daddy suke a tsaye, ta kalli Amir tai masa wani kallo da sai daya sunkuyar da kan sa saboda ta tabbata ya sanar da Daddy komai.


Ta juya ta kalli Daddy, kafin tayi magana ya rufe ta da faɗa akan hawa Napep da sukayi kamar zai dake ta, cikin mamaki da wani yanayi mai kama da mafarki taji Daddy yana faɗin:


"....indai wannan shashancin naki zaki ci gaba dayi to zan karɓe junior daga hannun ki..."


Ya faɗa tare da fincike shi daga hannun ta.

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.