Free chapter · Read without an account

Chapter Five (Bincike)

by The Healer's Pen · NI DA KANNENA


WAYE DADDY?


Asalin sunan sa shine 'Alhaji Ahmad Abubakar Maihula' asalin sa mutumin Kano ne a ƙaramar hukumar Rano, mahaifinsa Malam Habu ya kasance bafulatani mahaifiyar sa kuma Halimatu cikakkiyar bahaushiya ce.


Su biyar iyayen su suka haifa uku maza biyu mata, Daddy shine ɗa na biyu, sai babbar yayar su Hajiya Asiya wanda Allah yai mata rasuwa bata taɓa haihuwa ba, sai wanda yake bin Daddy malam Abdullahi, sai na huɗun malam Mahmuda sai ƙaramar su A'ishah da sukewa laƙabi da A'i.


Gaba ɗaya mahaifiyar su ce ta haifesu, mahaifiyar su ta rasu tun suna ƙanana, wanda hakan wasu suna faɗin yana da alaƙa da mutuwar mahaifin su, saboda tun da ta rasu shima ya kamu da rashin lafiyar da aka kasa gane kanta, bayan shekara uku da rasuwar ta shima Allah yai masa rasuwa, haka kulawar su kacokam ta koma hannun yayan mahaifinsu tilo wanda shi ya riƙe su tare da matarsa riƙo na tsakani da Allah.


Kasancewar Daddy shi yafi faran faran da mutane hakan ya saka jinin su ya hadu da wani abokin mahaifin sa malam Muhammadu wanda shi kuma sana'ar sa fatauci ce, yana sarar huluna kala kala musamman a garin Maiduguri ya kai su garuruwan kudu, hakan ya saka ya fara jan Daddy a jikin sa ya koya masa harkar kasuwanci sannan ya saka shi a makarantar boko yana tafiya dashi fataucin idan anyi hutun makaranta.


Hakan ya saka daddy ya ƙara ƙwarewa sosai a harkar kasuwanci ya goge matuƙa, bayan ya kammala secoundry school ne suka tsunduma harkar kasuwanci ka'in da na'in har takai ga Malam Muhammadu bai cika fita ba duk inda ya kamata Daddy ne yake zuwa kasancewar sa yana da nasibin kasuwanci sosai.


Kwanci tashi kasuwancin su Daddy ya haɓaka har ta kai ga suna fitar da kayan su zuwa maƙotan ƙasashen Nigeria kamar su Nijar Cameroon da Chadi. Ganin yadda kasuwancin ya karɓi Daddy sosai ya saka Alhaji Muhammadu ya shawarci yayan mahaifinsu akan a raba musu gado domin a sallami Daddy ya zuba kuɗin sa a kasuwa a wannan lokacin ma duk ƴan uwansa sunyi aure.


Haka kuwa akayi aka raba gado kowa aka bashi kason sa shi kuma Daddy ya zuba masa a harkar kasuwancin huluna, daga baya ya faɗa harkar fata, a hankali Ubangiji ya saka masa albarka ya fara tara dukiya.


Bayan Daddy yaga ya fara samun dukiya sai hankalinsa kuma ya koma kan karatu, kasancewar yana da sha'awar sa sosai kuma yafi zuwa garin Maiduguri sai kawai ya yanke shawarar ya samu admission awannan makarantar hakan zai fi masa sauƙi a ɓangaren kasuwancin sa. 


Haka kuwa akayi bayan ya shawarci yayan mahaifinsa da Alhaji Muhammadu suka yarje masa ya shiga jami'ar Maiduguri ya fara degree sa na farko a fannin kasuwanci. 


Sai da yayi nisa sosai yana shekarar ƙarshe Allah ya hada shi da Mummy wato asalin sunan ta 'Suwaiba' wadda ita kuma ƴar asalin Maiduguri ce itama tazo karatu lokacin tana ajin farko a bangaren Shari'ah,.


Soyayya mai ƙarfi ta ƙullu a tsakanin su, bayan Daddy ya kammala karatun sa ya aure ta ya kawo ta nan Kano tare da nema mata transfer taci gaba da karatun ta a jami'ar BUK.


Bayan shekara guda da yin auren su ta haifo dan ta namiji wanda Daddy ya saka masa sunan Malam Muhammadu ake masa laƙabi da 'Ashraf' tun daga haihuwar Ashraf dukiyar Alhaji take ƙaruwa yake ta zuba kuɗi a kasuwanci kala kala wanda hakan ya daɗa bunƙasa dukiyar sa, daɗin daɗawa ga alkhairai da yake wa ƴan uwa da abokan arziƙi musamman yadda yayi dacen mata, Mummy mace ce mai kirki da son mutane bata bambantawa tsakanin dangin ta da nasa. 


Har Ashraf ya kai shekaru goma a duniya ko ɓatan wata Mummy bata ƙara yi ba, gashi ya gamu da larurar ciwon zuciya yasha wahala sosai yana ƙarami, saboda likitoci sun tabbatar da cewar zuciyar sa na da rauni saboda wani rami da yake a tsakiyar ta, shikuma idan aka samu irin wannan sai dai ayi haƙuri a lallaɓa mutum, kasancewar da gata ya saka aka dinga kula da Ashraf har ya samu sauki amma ko da yaushe yana ƙarƙashin kulawar likitoci.


Hakanne ya saka hankalin su ya tashi, ga rashin haihuwa, sai suka shiga neman shawarwarin likitoci bayan gwaje gwajen da akayi musu aka tabbatar musu da cewar Daddy ba zai ƙara haihuwa ba saboda gaba ɗaya kwayoyin haihuwar sa sunyi rauni.


Wannan matsalar ba ƙaramin daga masa hankali tayi ba hakan ya jefa shi cikin damuwa matuƙa musamman da suka je kasashen waje har uku aka ƙara tabbatar musu da hakan.


Ita kuwa Mummy rarrashin sa ta shiga yi tare da yi masa alƙawarin zata zauna dashi a hakan har tsawon rayuwar ta. Hakan da take masa akodayaushe ya saka yake ƙara masa ƙwarin gwiwa wanda ya koma kan kasuwancin sa ka'in da na'in ya fara buɗe kamfanoni guda biyu wanda daga baya ya fara buɗe wasu a ciki da wajen Kano sannan ya ɗebo ƴaƴan ƴan uwan sa da na ƴan uwan Mummy ya zuba su a kai kasancewar duk ya ɗau nauyin karatun su.


Haka rayuwa ta ci gaba da tafi masa a yadda yakeso kasuwancin sa yana haɓaka har zuwa lokacin da NURATU ta shigo rayuwar sa suka ƙulla wata yarjejeniya ta sirri wanda hakan ya kawo sauye sauye masu yawa a rayuwar sa.


                          ********************

           BAYAN SATI ƊAYA DA YIN WALEEMA


Acikin sati guda zuwa yanzu banda matsin lamba babu abinda Nuratu take fuskanta a wajen Ashraf. Duk lokacin da yake buƙata haka zai kirata a waya ko ya tako yazo, duk kokarin da take yi na kai zuciyar ta nesa abun ya fara isar ta, musamman Anuwar da Ameerah duk da ta ja musu kunne sosai akan ko da wasa kar su nuna masa wani abu. 


Ita Ameera bata da matsala amma shi Anuwar kwanannan ya rage zama ma a gida yawanci a asibitin su yake wuni ko da bashi da aiki ya gwammace ya tsaya ya taya abokin aikin sa nasa aikin. 


Duk da matakin da Anuwar ya ɗauka baiwa Nuratu daɗi ba amma da ta tabbatar ga a inda yake wuni sai ta kwantar da hankalin ta kasancewar bata so wata rana wani abun ya haɗo su da Ashraf tun da ta lura kallon kallo suke yiwa juna.


Yau ma kamar kullum Nuratu tana zaune a palour ƙasa tana aikace-aikacen ta a computer, misalin ƙarfe 4:00 na yamma Ashraf ya shigo tare da yin sallama, ɗagowa tayi a sanyaye ta amsa masa, bai nemi izini ba ya zauna kujerar da take kallon inda take, sai da ya ƙare mata kallo sannan yace:


"Ina kiran ki baki ɗaga ba."


 Sai sannan ta ɗakko wayar ta taga missedcall ɗin sa har biyar sannan tace:


 "A silent take ina aiki saboda an kusa komawa aiki."


Kau da kansa yayi sannan ya miƙe ya nufi fridge ya ɗauko coke ya buɗe ya dawo ya zauna, ganin abinda yayi ne yasa tayi saurin cewa:


 "I'm sorry na sha'afa, gidan ne ba kowa, bari na kawo maka abinci." 


Miƙewa tayi bai ce komai ba ya bi bayan ta da kallo. Bayan ta shiga kitchen ɗin ne ta tuna tuwon shinkafa suka yi da rana miyar egusi, to ba ta da tabbacin ko Ashraf na cin tuwo hakan ya saka ta dawo domin tambayar sa.


Da mamakinta ta ga wayar ta a hannun sa, tsayawa tayi tana kallon sa da mamakin ya'akai ya iya buɗe wayar, duk da yasan Ashraf software engineer ne amma abun ya matuƙar bata mamaki.


Kallon sa tayi da kanar bata lura da abinda yake ba sannan tace:


 "Tuwon shinkafa ne miyar egusi zakaci?" 


Gyaɗa mata kai yayi alamar"eh" yana danna wayar ba tare da ya ɗago ba.


Tayi mamakin yadda Ashraf yaci tuwo sosai, ƙura masa ido tayi tana kallon sa da mamakin ta taga ya rame a wannan yʼan kwanakin bata san dalili ba. 


Har yanzu wayar ta tana hannun sa ta rasa me yake yi da ita, can da ya gama abinda zai yi kawai ya miƙa mata, hannu tasa ta karɓa ba tace komai ba sai daga baya tace:


 "Yakamata mu fara training tun da kaga yanzu an ware maka special part da zaka kula dashi a office, is better kasan wasu abubuwan." 


Sai sannan ya ɗago kai ya kalleta a dai dai lokacin da ya miƙe yana wanke hannunsa a sink ɗin kusa da dinning ɗin sannan yace:


 "Ba wannan bane a gaba na tukunna, kece a gaba na idan munyi aure sai ki koya min a hankali." 


Murmushin yaƙe tayi, tare da jinjina wannan kalar yaudara ta Ashraf sannan tace:


 "Amma dai kasan Daddy yace sai ka maida hankali ka fara aiki sosai a office ya yaba da ƙwazon ka sannan zamuyi aure ko?"


Kallon ta kawai yayi tare da ƙura mata ido yace:


"Wannan nasani ke kika sauya masa ra'ayi, da ai ba haka yace ba, saboda ba kya so na shiyasa."

Ya numfasa yaci gaba da cewa:


 "Nuratu ko me zakuyi ke dashi wallahi sai na aure ki."


Sunkuyar da kanta kawai tayi tana faɗaɗa tunanin ta, tabbas har ga Allah tasan ko da wasa bata son Ashraf tana biye masa ne kawai saboda a zauna lafiya kuma su samu nasara akan sa don ya mai da hankalinsa a office.


Ɗago kam ta tayi sannan tace:


 "Ni ai bance bazan aure ka ba, amma kawai ka fara maida hankalin ka akan office tukunna, sannan me kayi min acikin wayata? banaso ka dinga monitoring komai nawa, wasu abubuwan sirri ne kuma babu kyau."


 Murumshin rainin hankali yayi sannan ya kalleta yace:


  "idan zan yi monitoring calls ɗinki sai na taɓa wayar ki? Ni bana yin haka, kawai hotunan ki na tura a wayata." 


Kallon sa kawai tayi da dukkan alamu bata yarda ba. Miƙewa tayi ta bar dinning ɗin shima daga bisani ya biyo bayanta a dai dai lokacin da Ameerah suka shigo tare da junior. 


Hannun sa ya budewa junior alamar ya taho, shikuwa bai je ba sai daya kalli Nuratu tayi masa alama da ido sannan ya tafi ya rungume Ashraf.


Nuratu tsayawa tayi tana kallon su tana murmushi saboda ta lura tun da Ashraf ya fara zuwa gidan yake jan junior a jikin sa. Haka suka ci gaba da wasannin su sai da akayi sallar magrib sannan Ashraf ya tafi.


A bangaren Mummy kuwa, nunawa daddy take batason auren Ashraf da Nuratu duk da har cikin zuciyar ta bata so amma tayi imani ita kaɗaice hanyar da zasu bi don su rabasu don idan idan ta nuna tana so ayi dole zasuyi zargin suna shirya wani abu.


Yadda ta ɗauki lamarin da zafi, har mamakin ta Daddy yake yi, tun yana yi mata faɗa har ya dawo yi mata nasiha, yana yawan nusashheta akan bata saba yiwa Ashraf abu ta ƙarfin tsiya ba saboda haka ta dai na hakan bazai taɓa sawa ta tanƙwara shi ba, amma ko a jikin ta sai ƙara ɗaukar zafi takeyi.


Shikuwa Ashraf bayan ya dawo direct ɓangaren Daddy ya nufa cikin wani yanayi na tashin hankali da firgici, ashe Mummy ta ganshi ta biyo bayan sa. 


Hargitsa komai na ɗakin ya fara yi hankalin sa a tashe, sai sannan ya hango wani safe da Daddy yake ajiyar mahimman takardu ya fara ƙoƙarin buɗewa. Ga mamakin sa yaji safe ɗin a buɗe alamar an manta ba'a danna lambobin sirrin ba, bai jira ba ya hau bincike a ciki. 


Cike da mamaki Mummy ta ƙaraso inda yake tana faɗin:


 "Meye haka?" 


Saboda iya sanin ta tasan duk fitinar Ashraf bai taɓa yi musu sata ba saboda duk abinsa yake bukata tana bashi ko da Daddy ya hana. 


Ɗagowa yayi idon sa jajir ya kalleta tare da nuna mata wani text message da akayi masa a wayar sa a hanyar dawowarsa daga wajen Nuratu.


Cikin sauri ta saka hannu ta karɓa ta fara karantawa kamar haka:


 "ASHRAF KA BINCIKI MAHAIFIN KA AKAN YA FAƊA MAKA WAYE KAI, SANNAN KA BINCIKI MEDICAL REPORT DIN KA A WAJEN SA ZAKA GA ABINDA YAKE ƁOYE MUKU KAI DA MAHAIFIYAR KA NA TSAWON LOKACI." 


Da ƙyar Mummy ta iya sarrafa kanta sannan ta nemi waje ta zauna, ta kalli Ashraf a dai dai lokacin da ya zaro wani file ɗin asibiti wanda sunan sa ne ajiki. Ya juya cikin tashin hankali yace:


 "Mummy na ga wannan file a hannun Daddy yana rungume shi yana kuka lokacin ina asibiti a London, nayi nayi ya fadamin na meye ya ƙi, Mummy dole akwai abinda yake ɓoye mana!"


Girgiza kan ta tayi cike da tashin hankali sannan tace :


"Waye yai maka wannan text ɗin?" 


Cikin sauri yace: 


"Ban sani ba Mummy, ban san ko waye ba!" 


Ya faɗa yana ƙoƙarin karanta abinda yake ƙunshe a file ɗin. 


Wata irin muguwar ƙara Ashraf yayi tare da watsar da takardun da suke ciki yayi gefe ya durƙushe ya kifa kansa da bango. 


Lokacin da Mummy tayi arba da abinda yake ciki, itama salati ta fara yi jikinta na rawa tayo kan Ashraf wanda ta ga sam baya motsi ga kuma jini yana biyowa ta hancinsa. 


Wata muguwar ƙara itama ta saki tare da jijjiga shi iya ƙarfin ta. A dai dai wannan lokacin Daddy ya shigo bedroom ɗin nasa inda yayi arba da Ashraf a wannan halin sannan idon sa ya kai kan wannan file ɗin take Daddy ya fara kiran:


 "Innalillahi wa'inna ilahi raji'un!" 


Ba shiri ya sunkuci Ashraf a kafaɗar sa yayi waje dashi.


Daddy bai jira ambulance ba, ya dai yi musu waya cewar gashi nan jikin Ashraf ya tashi, da kansa ya tuƙa motar zuwa asibiti. 


Ita kuwa Mummy ko takalmi babu haka suka tafi. Shigar su asibitin ke da wuya suka tarar da ma'aikatan suna jiran zuwan su cikin gaggawa aka shiga da Ashraf wani daki na musamman aka fara bashi taimakon gaggawa. 


Mummy banda kuka ba abinda take yi tare da yiwa Allah kirari akan kar ya karbi ran Ashraf a wannan lokacin. Shikuwa Daddy banda "innalillahi wa'inna ilahi raji'un" ba abinda yake yi, ya kasa zaune ya kasa tsaye sai kaiwa da komowa yakeyi yana da na sanin yadda akayi ya dawo da takardun nan gida.


Juyowa yayi a fusace yace da Mummy:


 "Wai ya akayi yasan da wannan file ɗin?" 


Nan fa ta labarta masa yadda akayi, Daddy ya cika da mamakin waye wannan zai yiwa ASHRAF text?


Wayar sa ya zaro daga aljihun sa ya fita ya kirawo Nuratu ya sanar mata da halin da ake ciki, aikuwa a rude itama ta fito ta nufo asibitin. Shigowar ta ke da wuya Mummy ta kamata tana jijjigata tana faɗin:


 "Zaki kashe min ɗa, in ba ke ba waye yasan sirrin Alhaji na tabbatar kece ki kai masa wannan text ɗin muguwa azzaluma ki fita ki bani waje."


Ta faɗa tana hankaɗata, ita kuwa ban da haƙuri ba abinda take bata tare da yi mata rantsuwa akan bata san ma me yake faruwa ba. 


Yanayin birkicewar da Mummy tayi tana kaiwa Nuratu duka tare da hankaɗa ta yayi yawa, duk da Daddy ya shiga tsakani amma ya rasa yadda zai yi, dole Nuratu ta haƙura ta koma gida tana kuka shaɓe shaɓe.


Kusan awa uku kenan da kawo Ashraf babu likitan da ya fito daga ICU ɗin duk hankalin Daddy ya tashi ita kuwa Mummy ta sandare a waje ɗaya ko motsi bata yi. Muryarta ta dashe ba abinda take ambato kamar "Allah ka duba Ni, ya Allah ka dubani..." kamar awa hudu da shigar da Ashraf likitan ya fito fuskar sa da alamar nasara, zumbur suka miƙe suka bi bayan sa.


Suna zaune a kujerun da suke office ɗin nasa fuskar su cike da damuwa da son sanin halin da ɗan su yake ciki. Dr Abdul ya kallesu cike da jimami yace:


 "Alhaji munyi nasara mun ceto shi da ƙyar da taimakon Ubangiji..." 


Wata ajiyar zuciya dukan su sukayi sannan Mummy ta kama kanta saboda wani sara mata da taji yayi. 


Sannan Dr Abdul ya ci gaba da maganar sa:


 "Amma Alhaji ya akayi akai sake haka har Ashraf ya sake shiga wannan yanayin? Kasan fa zuciyar ɗan adam sau daya kawai take bugawa, idan mutum ya rayu to ana biyu dole mutuwa zai yi."


"Ashraf ya hadu da first attack shekarun baya bai kamata ace yanzu kun ƙara saka shi a damuwa ba, sannan jinin sa akwai kayan maye aciki wanda hakan ne ya saka shi fita daga hayyacin sa dandanan, gaskiya ya kamata ku kiyaye nan gaba in ba haka ba zaku iya rasa shi."


"Zamu kiyaye inshaAllahu!" 


Iya abinda Daddy ya iya faɗa kenan sannan ya juyo ya kalli Mummy wadda take riƙe da kanta ga jiri yana ɗaukar ta saura ƙiris ta faɗi daga kan kujerar da take kai, da sauri Daddy ya tallafota aka saka ta a wheelchair itama aka bata gado. 


Ƙarin ruwa aka shiga yi mata da allurai kasancewar jinin ta ne ya hau sosai sannan akai mata allurar bacci daga baya. 

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.