Free chapter · Read without an account

6

by Amina Abubakar Yandoma · KAFAR HAGU

*'KAFAR HAGU*

©️ Meenat A. 'Yandoma

Wattpad: Meenat_A_Yamdoma
Arewapen: @meenatyandoma

MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION

🅿️age 6
...Da taimakon Allah aka fito da su Farida. Bushura ta bude ido amma bata gane komai, Farida kuwa sunyi tunanin ba ta na raye. Kai tsaye wata motar aka saka su aka nufi asibiti. Medical center aka nufa da su. Bayan an ba su taimakon gaggawa Wayar Farida ce ta fara ruri. Cikin mutanen da suka kawo su ne ya kara wayar a kunne ganin an rubuta Daddy. Bai ɓata lokaci ba wurin sanar da shi halin da ake ciki. Jim kadan sai ga su mahaifiyarta duk ta fi shiga tashin hankali. Duk yadda ta so ta shiga ta ga 'ya'yan nata abin ya ci tura, saboda an masu allurar bacci dole ta kara hakura zuwa wani lokaci. Hawayen da ke fuskarta ta share. "Alhaji! Kada mu rasa 'yar mu. Jikina bani ya ke anya ba ɓoye mana suka yi ba..." Jin zata faɗin abin da ya jima da tsanar a fada wato mutuwa. Da sauri ya rufe mata baki. "Aa Hajiya. Kada ki ce za ki yi mata wannan mummunar fatan. " 
"Alhaji ba mummunar fata ba ce. Jikina ya bani likitocin nan ɓoye mana suke yi." Rufe bakinta ke da wuya wata nurse ta sanar masu likita na bukatar ganinsu. Ba su ɓata lokaci ba suka iske shi, sai dai har yanzu gabanta bai daina faɗuwa ba. 
"Ku ne mahaifan yaran da suka yi hadari?" "Eh mune. Ɗayar ɗiyar Yayana ce da ya rasu. Ɗayar kuma Ni na haifeta ɗiyata ce" Alhaji ya amsa da sauri. Doguwar ajiyar zuciya likitan ya sauke tare da gyara zama. "Abin da nake so in fada maku, ita ƙaddara da kuke gani Allah na jarabtar bawansa ne domin ya gwada ƙarfin imaninsa. Abin da zan sanar daku ku ɗauke shi a matsayin jarabawa ce daga ubangiji." 
"Alhaji! Ka gani ko? Da ma na fada yaran nan sun mutu mutumin nan ɓoye mana ya ke.." ta karasa maganar tare da rushewa da kuka. Da sauri likitan ya kalle ta. "Hajiya kiyi hakuri. Yaranku suna nan cikin koshin lafiya babu wadda ta mutu. Sai dai abin da nake so in fada miki ɗaya daga cikinsu karfe ya mata mummunar illa ya shiga ta saman mararta. Yanzu haka abu ne me matukar wahala ta haihu, in fact cikin ma ba zata iya dauka ba" Hajiya da Alhaji a tare suka mike cikin tashin hankali. "Wace daga ciki farar ko me duhun." Hajiya ta fada. Jim likitan yayi. "Farar" 
"Alhaji Faridar mu Inna lillahi WA Inna ilahi raji'un! Luuu ta zube. A rikice likitan da Alhaji suka yi kanta, babu bata lokaci ita ma aka bata gado. Alhaji ne zaune a gefen gadon ya haɗa hannuwa biyu ya rafka uban tagumi. Wadannan abubuwa sun masa yawa, ina zai saka kanshi. "Shin ina ma su Farida suka je ba tare da jami'an tsaro ba.?" Lokaci ɗaya zuciyarsa ta tuna masa da wani abu. "Gaga" Alhaji ya furta tare da miƙewa cike da ɓacin rai. "Tabbas wannan yaro ya zame mini matsala a rayuwata. Da na san gayyato sa cikin sabgoginmu zai saka ɗiyata ta ganshi har ta kamu da mahaukaciyar soyayyarsa. Har abada da bazan gayyato shi ba." Safa da Marwan Alhaji ya hau yi cike da takaici da bakin cikin wannan lamari. Hajiya bata farka ba sai  da dare yayi. A rikice ta mike ta na kiran sunan Farida. "Ku Kai ni in ga 'yata. Ita daya muka haifa, da ita muke saka ran mu samu jikoki masu yawa. Ashe ba zata taɓa haihuwa ba innalillahi wa'inna ilaihirajiun!" Kusa da ita Alhaji ya zauna tare da kiran sunanta cikin sanyi murya. Kukan ta tsayar tana me fuskantarsa.
"Kiyi hakuri ki share hawayenki. Ko alama bana so in GA Farida cikin damuwa, kukan da zaki rika yi shi zai saka har Farida ta gane halin da ake ciki" hawaye da ke fuskarta ta share.
"Ban fahimci abin da kake nufi ba" 
"Ma sha Allah! Ina so ki buɗe kunnuwansu da kyau ki ji abin da zan fada. Ƙaddara dai ta riga fata, aikin gama ya gama, don haka dole musan yadda za mu ɓullo wa lamarin nan. Ina so har cikin zuciyarki ki boye wannan Sirrin bayan ni da ke kada wani ya san da maganar nan. Kafin ki farka munyi magana da likita a kan zan fita da Farida kasar waje, sai dai ya tabbatar mini da ko munje abu ne me wahala ta haihu. Saboda haka nake so ki ja bakinki kiyi shuru kada Farida ta San da wannan maganar" Ajiyar zuciya Hajiya ta sauke tare da kallon mijin nata. "Na fahimce ka zan kuma yi abin da ka bukata. Amma ba zan iya ci gaba da zama a wannan wurin ba tare da na ga halin da suke ciki ba." Karin ruwan da ke hannunta ta fizge suka nufi dakin da su Farida ke kwance. Wasu sabbin hawaye Hajiya Mabarukata ji sun wanke mata fuska, ganin Farida da ta yi duk ta fi jin jiki. Da sauri Alhaji ya girgiza mata kai. Share hawaye fuskarta ta yi. A hankali Farida ta fara kokarin bude ido, da sauri ta mayar da su ta kulle sakamakon hasken da ke dakin. "Gaga! Baka ji ciwo ba" ta karasa maganar tare da yunkurin zata mike. Da sauri Hajiya ta rirriketa. Zafin da ta ji a mararta ne ya sakata saurin komawa ta kwanta. "Umma! Me ya same ni zafi nake ji sosai" kallon juna suka yi, domin Sufi kowa sanin abin da ya same ta. Sai dai ko alama ba su so ita ta san ainahin abinda ke damunta.
"sannu kinji. Haɗari kuka yi" Hajiya ta fada tare da gyara mata kwanciya. Gefenta ta kalla ita ma Bushura ta farka, sannu suka ci gaba da jero masu a tare. "Umma na godewa Allah da babu Gaga a cikin motar nan. In wani abu ya sake shi bazan taɓa yafewa kaina ba." A karo na ba adadi mahaifan nata suka sake kallon juna. A wannan karon Hajiya Mabaruka ta kawo wuya.
"Farida! Kada ki CE mini kauyensu yaron nan kika je. Mu kam mun shiga uku, anya ba asirce mana yarinya ya yi ba?" 
"Umma! Wallahi can muka je. Farida mutuwa za ta yi a kan yaron nan. Da muna da ƙarar kwana da yanzu wani zancen ake yi" Bushura ta karasa maganar cikin ɓacin rai. Wani ƙululun baƙin ciki ne ya tokarewa Alhaji wuya. "Duk ta ƙare sai na yi abin da zuciyata ke fada mini a kan yaron nan. Mummunan mataki zan ɗauka a kansa hukuma ce kadai zata shiga tsakani" 
"Daddy kada ka yi mini haka! Ai ƙara ni ka hukunta ni a kan ka taba lafiyar Ghali!"
Sake da baki kowa ke kallon Farida jin irin maganganun da ke fitowa da cikin bakinta.

Oga Gaga kuwa tun bayan fitar su Farida ya ke bawa Rauda hakuri tamkar zai yi mata sujjada. Wani tsohon gado na Magaji ya dauko ya kafa mata a cikin dakinsa. 
Baccin da ya fara ɗaukarta ne ta farka, Gaga da bacci ya dauka ya kishingida kansa a gefen gadon ta kalla. Wasu hawaye da bata san dalilinsu ba ta ji sun shiga tsere a saman kumatun ta. Yau ita ce kwance a wani wuri inda ba gidansu ba. Alhali iyayenta na raye a duniya karewa ma a kauye daya suke. Tun bayan tashinta ta rasa gane wace irin rayuwa ake yi a gidansu, kowa ta kansa ya ke yi hatta iyayensu mata ba abin da ya dami mahaifinsu da su fita su nemo kudi koma ta wace hanya ce, in sun dawo tsaf zai amshi wani abu. Ita kam tamkar Mujiya take a cikin al'umma an riga da an camfata da ke farar ƙafa. Hatta mahaifiyarta ta jima da tsananta. Ina akwai mutum ɗaya da zata nuna ta ce yau shi ne Wanda ke kaunarka ya share mata hawaye to Ghali ne. "Ya Allah kai ne mafi sani akan abin da ka tsaramin game da rayuwata. Allah kai sheda ne a kan irin soyayyar da nake yiwa Gaga ya Allah ina kaunarsa a duk yadda ya ke, Ubangiji ya shirya mini shi ka bani ikon cinye dukkan jarabawa ta" hawayen da ke zuba a fuskarta ne suka ɗiga a fuskar Gaga. Da sauri ya mike cikin magagin bacci. "Rauda! Me ya faru ko wani abu na yi miki, ki yafe mini kinji Rauda in ma laifin da Farida ta yi ya sakaki kuka. Fadi irin hukuncin da kike so ayi mata." Girgiza kai ta hayi. For the first time da hannunsa ya kai jikin Rauda ya rika share mata hawaye. "In kina kuka sai In ga kamar na cuta miki ne, ko dai akwai abin da na yi miki da ya bata miki rai? Saboda ke naƙi yin shaye-shaye Rauda" Murmushi da kuka ne suka hade mata a lokaci ɗaya. Girgiza mata kai ya ke tare da janyo mata bargo. "Kiyi bacci, ni bari in fita waje in kwanta" duk yadda take kokarin dakatar da shi abin ya ci tura ficewa yayi ya ja mata kofa. Shi ya kwanta a bakin ƙofa.
Safiya na yi sauran kudin da ke jikinsa ya fidda ya siyo mata kalaci ya kaiwa Magajiya nata.

Malam Iliya kuwa tun bayan da ya fita ya dira a majalisar su, domin yau suna da caca me zafi. Abokin karawarsa ya saka dubu ɗari biyu tare da akuyarsa ɗaya. Malam Iliya kuwa ya ma rasa me zai saka, domin kaf kuɗaɗen sa a wurin caca da bin mata suke ƙarewa. "Ka ga Iliya idan baka da abin da zaka saka a fitar da kai a saka wani." Jatau ya karasa maganar ya na dariyar mugunta.
"Jatau mu da Allah ya bawa arzikin da ya fi kudi. Na saka Zinatu" dariya Jatau ya kwashe da ita. "Hauka nake zaka saka mini wannan tsohuwar kilakin, duk ta gama yawon bariki. Ka dai saka mini Rauda."
Dariyar tsoffin Yan duniya suka kwashe da ita tare da tafawa. "Na saka Rauda har ma da sauran canjin da ke cikin aljihuna"
Adadin mutanen da ke zagaye da su sunyi su takwas lokaci daya wuri ya hau shewa.
Nan fa aka fara fafatawa sai dai ga dukkan alamu yau sa a babu ita a wurin Iliya.  Irin ihun murnar da aka kwashe da shi zai tabbatar maka da an cinye wasa. Wani gumi ne ya shiga wanke ilahin Jikin Iliya. "Ashe baka shirya ba ka saka 'yarka" Jatau ya karasa maganar tare da tuntsurewa da dariya.
"Baƙin ciki nake da ban cinye kudin ka ba. Dubu ɗari biyu ina ji ina gani na rasa ta. A tunaninka ko Matana na saka a cikin cacar nan zan wani damu ne"
A take aka daura auren Jatau da Rauda. Daya daga cikin abokan Iliya ne ya fada da karfi. "Aure ya ɗauru! Rauda ta zama matar Jatau...

***



Meenat A. 'Yandoma

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.