Free chapter · Read without an account

Page 2

by AISHA YUSUF HANWA · Gaba Kura

GABA KURA



AISHA HANWA
 


PAGE 2






Sai ɗakin Inna da ta ke da Huɗu dukan su maza Salisu, Sani, Jamilu Jabiru. Amarya Saratu kuma uku Sadiƙu Ibrahim sai Jamila.  Munari da Jamila sa'anni ne suna shekara sha huɗu Mahaifinsu ya fara maganar aurar da su, lokacin tana ƙaramar sakandire babu yadda Mama ba ta yi ba akan ya taimaka ya bari ta ƙarisa sakandiren tukuna tunda ko saurayin ma ba ta da shi saboda ba ta kula su. Aikuwa ta ga tijara ganin idanunta yana faɗin ya musu adalci ma da ya ƙyale yaran har suka kai haka a gida. 

Idan ba su ga ƙoƙarin shi ba ai ba sa zage shi ba, nan da nan Jamila ta fiddo na ta mijin ganin haka ya sako Munari a gaba kullum cikin faɗa a gefe kuma matan gida na ta sakin habaici makaranta ba ta yi amfani ba tunda mangwafak shugaban ƴan boko bai fito neman auren ba
        
 Ana haka sai ga Munzali  ya aiko ya na son a yi mishi izinin fara zuwa zance wurina.


 Hankalin Maman ya tashi sanin Munzali fa ba shi da cikakkiyar natsuwar da za'a ba shi aure daɗin gushi ma babu sana'a takamammiya, amma ga mamakinta ba tare da tunani ba ko dogon bincike ya ce ya amince ya fara zuwa bai tuntuɓe ta ba balle yarinyar a ji ko tana san shi ko a'a.


Ranar da ya fara zuwa taɗi ƴan gidan nan murna kamar ranar sallah juyi ba juyi ba a yaɗa habaici ana faɗin wai sun ga alamar ba'a son munzali ko da me suka fi su oho ɗayar sai ta caɓe ai kin san dama bokon da aka fara da manufa ake zuwa wai ko  wani malamin zai ƙyasa sai ga shi an ɓuge da mafarauci ko banza idan dawa ta yi nama za  ta goge baki ita da uwarta sai ki ji shewa na tashi.

Ita ba za tace ga abunda suka tattauna ba daga gaisuwa ta ja bakinta ta tsuke shi ya yi ta zuba da sunan yana faɗa mata irin yadda yake tsananin santa. Shi da kan shi ya fahimci ba ta yi maraba da shi ba ya sallame ta amma ya ƙudurce a ran shi ba zai rabu da ita ba domin yana santa.


Manemin Jamila na turowa ya ce shima Munzali ya turo Mama ta  yi kuka har ta godewa Allah ta fawwalawa Allah lamarinta ba da yawa aka saka bikin ba saboda haka aka hau shirye shirye ta kowane ɓangare duk yadda Maman ke ƙin abun hakanan ta dage tana siyan abubuwan da kamata na biki. A haka har satin biki ya zo aka kawo lefe na Jamila acan acan abun sha'awa  amma na ta sai ya zama ɓalɓal su ce yau za su kawo gobe suce jibi a haka har sai da aka kai jajiberin biki sannan aka kawo da daddare kaya kamar na bazawara hakan dai aka amsa ba karsashi.

Washegari da wuri aka ɗaura aure biki ya kankama.


Zuwa almuru biki ya fara tashi abokan arziƙi duk an watse sai yan uwa na kusa kusa bayan an gama biko aka tattaramu zuwa ɗakin Baba dan mana nasiha, bai wani tsaya doguwar magana ba sai ma cewa da ya yi "Shi ba faɗan da zai mana sai gargaɗi duk yarinyar da ta sake ta zo mishi gida da sunan yaji sai ya ƙarya ƙafanta ya riga ya sallame su zai ji da ƙannen su.


Haka aka ja su aka miƙa kowa gidan mijinta, al'adar ɗan adam ne bin abu mai maiƙo wannan karan ma hakan ce ta kasance tsakanin su domin rabi da kwatan mutane gidan Jamila suka nufa aka bar wanda ya zama musu dole bin ayarin Munari.
    
 Babban gida ne ko in kira shi gidan gandu sasan su Munari mata takwas ne kuma dukansu surukai ne idan aka cire uwar mijinsu yara ne ratata a gidan, babu laifi Munzali ya gyara ɗakin ya sha fentin farar kasa sai ƙamshi ɗakin ya ke yi.
           
      Bayan  kammala duk wani al'adar suka tattara aka watse, ita kaɗai tsuru a ɗaki a haka abokan ango suka rako shi bayan zantukan su cikin nishaɗi da annashuwa suka tafi suka bar su, ba tare da ɓata lokaci ba Munzali da duk ya ƙosa ya tafi garin maji daɗi ya isheta da tayin naman da suka shigo da shi ganin ta ƙi kula shi ya tasa abun shi ya lamushe ya bar ƴan kasusuwa da fiffike, ko sallah da ake yi na neman albarka bai samu damar yi ba ya bi takan ƴar mutane ba tausayi babu tausasawa, da taimakon Ladiyo matar wan shi da ya kirawo ta taimake shi ganin aika aika da ya yi, da ƴan dabarun su na karkara ta samu jikinta ya dawo daidai tun daga nan ya samu abin yi babu dare ba rana ita dai idan za'a sa mata wuƙa a wuya ba ta san mene ne daɗin abun ba amma hakanan take miƙa wuya domin bata da yadda za ta yi. 
      
 Tafiya ta fara miƙawa komawa na ta sauyawa amma banda ta wurin Munari ita ta na nan jiya iya ga wani baƙi da ta yi


Matsalar da ta fara cin karo da shi shine cin abincin haɗaka haka ma girki duk a tukunya ɗaya ake yi sai dai duk rana mutum biyu za su haɗu su yi tare, miyar nan haka za ki ji ta kamar an wanke kan Mahaukaciya ba ki isa  azo kiranki cin abinci ki ce 'Kin ƙoshi ba'  to  sai a maida babbar magana ana faɗin "Me ki ka ci da zai ƙosar da ke?",  Haka nan ta ke fitowa ta yi ta yafita har a ƙare cin abinci kafin kace me ta zauna ta zuge sai tayani muni fal fuska shi kuma gogan nata bai taɓa tambaryarta ko akwai abunda ke damun ta ne 


Shi dai idan hakan ba zai  kawo mishi cikas ana shi buƙatun ba to Falillahil Hamdu. Ranar da fara zuwa gida ta sha cece kuce a gurin mutanen gidan da masu yi har zuci da masu yi da ba'a.  Duk kawaicin Mama sai da ta tambaye ta dalilin uwar ramar da ta yi. Amsar dai ɗaya ce babu komai sai Mama ta yi shiru a ranta ta fara tunanin wataƙila ciki ke gare ta.


 Da zata tafi ta tambaye ta ko ta yi mata soyayyiyar miya ne idan tana so? da sauri tace "E"  domin har ga Allah tana cutuwa anan ɓangaren. Hakan kuwa aka yi shagargari ta aiko mata da miyar cikin kwanon 26 tace ta riƙa ɗumama shi, har da guzurin katon biredin ta, ta hau biredi da gafza sai da ta yi rabin shi sannan ta haƙura.

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.