Free chapter · Read without an account

PAGE _______39

by SultyWrites · BLOOD CROWN (THE HEIRS APPARENT)



Misalin ƙarfe 2 na dare fitsari ya tashe ta, leqawa bayin tayi taga ba ruwa hakan ya sata ɗaukan buta ta dauki wayarta ta kunna Flash light ta fita, tsakar gidan duhu ƙirin dan ba wuta, mutum ta hango tsaye ya ɗage Kansa sama, ƙurawa dan bakinsa ido tayi hakan ya sata fahimtar Magana yake, yana sanye da sweet pant black sai white vest, dukkan hannuwan sa riqe da waist ɗinsa, haske shi tayi da fitilar wayarta ta amma bai juyo ba, ba tare da wani ɗar ba ta nufeshi tana zuwa ta sake haske fuskar sa, ajiyar zuciya ta sauke ganin Jey ne. "Ashe ma Kai ne, har nace ko wani barawon ne ya shigo mana"............ Ido kawai ya zuba mata ba tare da yace komai ba sai dan bakinsa dake tauna chew gum kaɗan kaɗan cike da salo, juyawa tayi da nufin zuwa ta ɗaibo ruwan taji an figo ta, wani irin juyi yayi da ita tare da shigewa bayan wata ballalliyar kofar da aka jingine jikin bango, kallon sa take cikin ido dan gabaɗayanta rungume take a jikinsa, da hannu ɗaya yake riqe da ita dayan kuma ya saka ya rufe bakinta da hancinta, idonsa cikin nata yake mata alama da kar tayi wani yunquri.

 Kawu Adamu ne ya fito da ƙatuwar sanda yana faɗin, "kaii su waye Anan? Yanzu kuma an fara biyo dare za'a mana ɗan hali saboda anji na saya machine, to whl ba ɓarowa ba ko aljani bai isa in ajje ya ɗauka ba in kuma da Wanda ya isa ya fito muyi gaba da gaba"............. Ya faɗa Yana daga sandar sa, Umma delu ce ta biyo bayansa tana faɗin, " Haba Malam wai miye haka? ta ya zaka fito tsakar dare Ka tara mana mutane, waye zai wani bi dare ya hana kansa bacci akan wata roba robar Ka".............. Nan fa ya juyo kanta, "To to yar hassada, ke Delu ki fita ido na, to ita dai roba robar da kike rainawa ita da yawa suke nema basu samu ba dan haka ki barni na yi takiya ".

"Wani karamin ɗan iska ko yar iskar ce ta hana mu bacci tsakar dare, ɗan baccin da bawa zaiyi ma ya kwantar da haƙarƙarin sa sai azo a dinga firgita shi, ni whl bana son irin haka".......... Faɗar Shamsy yana fitowa daga ɗakinsa kansa sanye da under skirt. Kallon banza kawu adamu ya masa tare da faɗin, "Harda su kaza a cin danƙo, Kai Ka Bari sai ƙashin Ka yayi kwari Ka zama namiji sai kazo kayi magana "..........."Ahayye cas, yo ni me zai haɗani da kwarin ƙashi ina mace me rauni, amma fa in ka kawo min ba gishiri whl sai in iya kwaɓewa mu daku a fidda raini, kai yanzu na tsaya ka tsaya ai sai a zaɓeni ba'a zaɓe ka ba, ahhh yoo saboda ALLAH fa"............ Ya ƙarashe yana wani lankwashe Kai, takaici ne ya kawo kawu Adamu wuya, tsaki ya buga tare da jan sandar sa ya koma ɗaki umma Delu ta rufa masa baya.

 "Wuuu yaji tsoro".......... Shamsy ya faɗa yana ɗaura hannunsa a baki kamar me guɗa, sannan ya juya ya koma ɗakinsa.

Sai a lokacin suka saki numfashi a tare dan zakuyi mamaki in nace muku tsawon lokacin nan Jey da Hushaima basu shaqi ko fitar da numfashi ba, Wanda hakan ya sake sawa Jey shakkun Hushaima saboda ba kowa bane zai iya ɗauke numfashi na tsawon wanna mintunan ba Ka ganshi daram. Fitowa sukayi yana riqe da tsintsiyar hannun ta gam, ganin yana ƙoƙarin nufar ɗakinsa da ita yasa ta faɗin, "Malam ina zamu ne ni Ka sakeni".............." Shut up". Ya faɗa a ɗan zafafe yana ɗaura yatsansa akan ɗan bakinsa alamar ta rufe masa baki. "Anki ayi shattaf ɗin whl Ka sake ni ko na tara ma jama'a".......... bai saurare ta ba bai kuma tsaya ba har saida suka shige ɗakin nasa, wurgata ciki yayi tare da rufe ƙofar ya kunna solar touchlight ɗin dake ɗakin take ɗakin ya dau haske rauuuu. Dukda a zafafe ya wurgata cikin ɗakin bata yarda ta faɗi ba, tsaye take tana kallon sa don ganin iya gudun ruwan sa. Wata karamar kujerar roba dake gaban wani table ya nuna Mata tare da faɗin, "zauna"........... ba musu ta zauna, laptop din sa dake buɗe ya rufe tare da tattare duk wasu tarkace sannan ya zauna bakin table ɗin kana ya ce, "Ina so in tambaye ki a karo na biyu, wacece ke?" 

Dariya tayi cike da gaɓunta ta ce. "Ikon ALLAH yau ni ake tambaya wacece ni, gsky daɗi na da gobe saurin zuwa, ban taɓa tunanin wanna ranar zatazo kwana kusa ba ai"........... Shi dai Jey kallon ta yake ko kiftawa babu, gyara zama tayi tare da gyara murya ta fara magana, "Da farko suna naaa Hushaima Sahnish Shazeen, sannan ni mutum ce kamar Ka ina aiki a Starlight beauty Co. kuma nayi aiki a wurare daban daban, nayi cleaner a wata ma'aikata, nayi aikin gyaran su zobo a wani kamfani, nayi aikin raino a wani gida, nayi aikin girka abinci a otel(hotel), haka a wata moll (Mall) ma ina ɗan zagaya musu wurin ko da wasu zasu zo su nemi a zaɓa musu irin su man gashi ko na jiki masu kyau, daga ƙarshe kuma yanzu ina aiki a wajen gyaran jiki da sauransu"......... Kallon yadda take magana cike da confidence da kuma bakin gskyr ta da ya hango cikin idonta yayi, Amma duk da haka sai ya ce, " In kin gama shirya tatsuniyar taki saiki faɗamin ta asalin".

"Me sa to zan ma karya, tukunna ma in kasan bazan faɗa gsky bane me sa Ka tambaye ni, to kaje Ka tambaya kowa wacece Hushaima tunda ni ba Ka yarda da abinda na faɗa ma ba, Ni bana ƙarya kuma bana munafurci".

"Ai nasan hanyar tambayar kuma zan iya sanin waccece ke ba tare da naji daga gareki ba, kawai na zaɓi na tambaye kin ne. Ki fadamin wace ke, daga ina kuke? Su waye mahaifanku?"............  Cikin wata irin fusatar data bashi tsoro ta miqe tana faɗin, "Shin baza a iya sanin mutum dan kansa ba sai an jingina shi da wani, dole dole sai kana da iyaye ko kuma sai ansan matsayin iyayen Ka tukunna za'a ce Kai wani ne, tukunna ma miye haɗi na da kai "........... Cikin wanna munafukar muryar tasa ya ce, "lower your voice madam, karki tarawa kanki jama'a".

"Whl karka ƙaramin magana, kuma bazan rage muryar ba Kai kana tunanin akwai Wanda nakejin kunya ne, wai ko dan an same ni a ɗakin ka zanji wani abu ne, ban ajje uban kowa da zaice na jawo masa abun kunya ko abun magana ba dan haka ban damu da duk wasu maganganu ba, mu kaɗai muke rayuwar mu kuma mu kaɗai zamu rayu bamu buqatar kowa da komai ko kuma sauya tunanin kowa a kan mu, duk ma yadda kuka ɗauka hakan ne"........... tana kai wa nan ta nufi kofa a fusace, saurin shan gabanta yayi.  Cikin wani irin fushi ta ce, "Whl in baka kauce Ka ban hanya ba sai na sharara ma Mari"........... Zaro ido yayi cike da ɗinbin mamaki kafin ya haɗiye wani yawu daƙyar ya ce , "Okay naji but zauna na yarda da abinda kikace kawai tsokanar ki nake, ke ɗin wata ce kuma jajirtacciya da bakya buqatar bango domin jingina bakya buqatar dakalin dafawa, haka kuma bakya buqatar taki domin tsirowa, irin Ku abun so ne da alfahri a ko ina, ke din wata ce Hushaima plz have a seat". Ya ƙarashe da wani irin sauti yana nuna mata wurin data tashi, ɗagowa tayi ta zuba masa idanunta da suka rikiɗe zuwa ja a lokaci guda, ɗan ja baya yayi tare da harɗe hannuwansa a ƙirji yana mata jifanta da wani irin kallo, "Bazan iya zama ba ina son kaɗaicewa a yanzun, ka bani hanya"........... Ba musu ya matsa Mata ta wuce, neman wuri yayi ya zauna zuciyar sa fal da tunani iri iri.

Ko da ta dibi ruwan daga rijiya direct a kanta ta shiga watsawa saida tayi wurin sau uku ko sanyin ruwan bataji sannan ta sake ɗaibo wani ta zuba a butar dake wurge anan ta wuce ɗaki, fitsarin ta shiga tayi sannan ta dawo ta sauya kayanta dake ɗigar ruwa ta kwanta tana sauke numfashi.

 Ranar kusan makara tayi sallah dan har saida Sahnish ya shigo, sosai ya sha mamaki ganin Ƙofar ɗakin su a buɗe. Dan ta saba in dai lokacin sallah yayi saita shiga ta tabbatar ya tashi saisa da bai ganta ba ya biyo sawu, tana kwance ita ba bacci ba ita ba ido biyu ba amma ta kasa tashi. Hannunta Sahnish ya shiga bubbugawa yana Kiran sunan ta saidai har Shazeen ta buɗe ido ta tashi ita bata motsa ba, a firgice ya Kira sunan ta da ɗan ƙarfi, wata doguwar ajiyar zuciya ta sauke tare da buɗe idanun ta da har yanzu basu washe ba . "Hushaima lpy? Ko baki da lpy ne?"

"Sahnish har kun tashi mie?"......... Ta faɗa tana tashi zaune. "Har ma anyi Sallah ai, nayi mamaki da banji yau kin shigo wuri na ba kamar yadda kika saba saisa ma na shigo na duba".......... da sauri ta miqe tana faɗin, "Miyesa baka tasheni da wuri ba, ni ai kafin ayi Sallah nake shiga na dubaka". 

A gurguje taje tayi alwala ta dawo Shazeen ma data buɗe ido ta shiga tayi, shi dai da kallo ya bisu har sukazo suka tada sallar suka idar, sai lokacin ya ce, "Hushaima meya faru dake ?" .

"Meka gani?".......... Ta tambaya ba tare data kalleshi ba. "Fuskarki ta nuna kamar akwai damuwa".

"Na danyi ciwon Kai ne amma na sha paracitamol (paracetamol)".

"Dama na sani za'ayi haka, ko in ɗauko miki ragowar maganin maleria nan ki Sha?"........... Tashi tayi ta cire hijab ɗin ta wuce toilet ta ɗauko bucket a toilet tana faɗin, "Ni fa naji sauki ba abinda zan sha kaji". Daga haka tayi waje samu tayi already mutanan gidan sun hau layi dan yau ta makara, Bonbon dake sawun farko cikin makirci ta ce, "Aunty Hushaima zo ki ɗiba mana ni bari na dawo kan layin naki"..........." Kar na takura Miki bonbon ban sani ba ko uzurinki yafi nawa, karki damu zan jira ".

"Ah ah gsky". Ta faɗa tana barin in da take tazo ta ɗauki bokitin Hushaima ta sa akan layin ta sannan ta ɗauke nata ta dawo dashi layin Hushaiman, godia ta mata sannan ta koma kan layin nata. Tsaki Jamcy taja tare da faɗin, "Shiga sharaf ba shanu, a dai rage shishigi".

"In ba tsoro ba mutum ya ambaci suna mana tarihi ya maimaita kansa yanzu sai na sake rage yawan hakoran mutum"........... Dariya duk suka kwashe da ita wadda ta Ƙara tunzira Jamcy amma batace komai ba sai kwafa da taja dan har yanzu tana jinyar bakinta ne. Haka Hushaima ta ɗiba ruwan ta wuce ba tare da tace da su ci kanka ba, bata samu Sahnish a ɗakin ba sai Shazeen dake ƙarasa assignment ɗinta dan haka ta shigewarta wanka Saboda yau zata aiki.




-----------------√




Cikin kuka take faɗin, "Dad Dan ALLAH ka ban wayata, mumu ki sa baki mana" .

Zaburowa mumu tayi da faɗin, "Ni sai dai in sa miki duka wawiyar banza wawiyar wofi ".

"Mumu Amma naga ai mijina ne Kuma ........" Dad ne ya tare da faɗin, " To tattabara sarkin aure, tun wuri ina shaida Miki ki cire zancen auran nan a ranki dan sunan sa warwararrre, tukunna ma a prison zakuyi zaman auren ne? mutumin dake hannun hukuma a yanzu"............ Wani sabon kukan Nayrah ta fashe dashi, a lokacin ne Kuma doctor ya shigo ɗan kallon su yayi tare da yin sallama ya ƙarasa shigowa, amsawa sukayi dad ya masa ya aiki, sake dudduba jikin Nayrah ɗin yayi kafin ya ce, "Ranka ya daɗe in baza ka damu ba ku ɗan bamu waje ina so nayi magana da ita". 

"Ba dai wata matsala ko Dr?"........... Mumu ta tambaya. Girgiza mata Kai yayi kana ya ce, "Nop babu, kawai Ina so na mata wasu yan tambayoyi ne". Ba musu suka juya suka fita Saida suka rufe ƙofar doctor ya ce, "Sorry to interfere but wanna biological parents dinki ne?".......... Nayrah da har lokacin kuka take me cin rai na jin cewa an kama Amjad ɗin ta, ɗaga masa Kai kawai tayi alamar eh.

 Ɗan shuru yayi kafin ya ce, " Ya kamata ki rage Kukan nan ko ki daina shi gabaɗaya for your health, a yanzu hutu kike buqata ba wai ki dinga tafasa jinin ki ba ".........." Dr ka aramin wayar ka Dan ALLAH ". Ta faɗa da dasasshiyar muryarta.

"Me zakiyi da ita?" ............ "An kwace tawa ne Kuma inaso na kira mijina"........." So you are married?". Dr ya tambaya da mamaki. Sake gyada masa Kai tayi alamar eh, dan shuru yayi can Kuma ya zaro wayar ya cire password sannan ya bata. Hannun ta har rawa yake wurin karɓa da sauri ta loda number Amjad a wayar sannan ta kira saidai baya shiga haka taita gwadawa amma amsar ɗaya ce wayar a kashe, dan dole ta haƙura ta bawa Dr wayar tare da komawa ta kwanta. Bai ce mata komai ba ya ɗauki kayan aikin sa yayi waje anan ya samu Dad Mumu ta sashi gaba tana ta masa zazzage zazzage, "Emm inaga ba damuwa zaku iya tafiya, ya kamata a barta ta huta dan tana buqatar sa Kuma bama san ana hayaniya sosai"........... Ya faɗa saboda ganin zaman nasu ba abinda yake haifar wa sai ƙarin tashin hankali wa marar lpyn.

 Mumu ce ta ce, "Dr ai ni nake kwana a wajen ta"........... Girgiza mata Kai yayi, "Hajiya ko bakya nan mu nan hospital ɗin muna da kwararrun ma'aikata dake kula da majinyata, ba laifi idan kunje kun dawo da safe "........... Dad ya ce, "Shikenan ba damuwa duk abinda ake ciki in da wani abu ka kirani ka faɗamin"..........."karka damu Alhaji, ba wata matsala in sha ALLAH ". 

Daga haka suka shiga yiwa Nayrah ɗin sallama hankalin su kwance cewa an kama Amjad basu da wata sauran fargaba. Ko da suka shiga samun ta sukayi kwance ta bawa ƙofar baya, Mumu ta ce, " Inajin ma tayi bacci ai muje kawai". Juyawa sukayi Dad a gaba Mumu a bayansa kamar wata uwar sa suka fice tare da jawo mata ƙofa, duk tana jinsu amma taƙi motsawa.

Juraysh kuwa daƙyar ya lallaba Anah sannan ya baro gidan Misalin 12:30am.

Shi kuwa Amjad suna dawowa gidan nasa, ɗakin sirrin sa ya shige ya Kira su Ash conference call, tattaunawa suke Kan aikin da suke na shadow Amjad ya ce, "Widad a wurin Ka ne fa har yanzu ba wani labari, har yanzu baka samo mutumin da suka bada detail a Kansa ba ne?". Shuru yayi har saida Amjad ya ɗan buga hannun sa a goshi dan ya sallama widad shiririta kawai yakeyi dan yasan halinsa wani sa'in, ya tsinto yar muryar nan tasa kamar ɓarawon da aka ritsa, " Na samo komai, kawai Ku gama naku aikin sai Ku min magana"......... Cikin rashin yarda Amjad ya sake faɗin, "In da akwai wani taimako da kake buqata Ka faɗa tun wuri?" .

"Babu"........... Ya faɗa daga nan suka cigaba da tattaunawa shi dai widad sai in ta kama yake sanya baki amma yana sauraran su, Ace ya ce, "But widad what's special game da mutumin?". Shuru sukaji suna dubawa suka ga ya sauka daga Kan layi, Amjad ya ce, "Don't worry dukda akwai abubuwa a gabana zan bibiyi abun".......... Daga haka sukayi sallama kowa ya kashe.

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.