Free chapter · Read without an account
WANI SON MAI WUTA ❤️🔥 epi:1
by Aisha G Umar · TATSUNIYOYI
TATSUNIYA.
By: _*🌹𝑍𝑎ℎ𝑟𝑎-𝑡𝑢𝑙-𝑄𝑎𝑙𝑎𝑚🖋️*_
WANI SON MAI WUTA❤️🔥
Episode one: wutar da ta fara da soyayya.
بسم الله الرحمن الرحيم
*Dare ne mai nauyi*
Iska tana busawa a hankali. Sai dai surutan mutane na sa, ka ji shima iskan da ƙarfi ya ke tafiya.
A can, Al'AMEEN an ɗaure shi jikin wata babbar bishiya, gefensa kuma wutan da aka rura ne ke ci sosai.
Jikinsa ya gaji ga ciwuka na jini, yana sauke numfashi a hankali, idanuwansa na rufe, fiska a galabaice, zuciyarsa na bugawa sosai.
A gabansa mutane tsaye, wasu makamai a hannunsu, wasu kuma icche da ke ci da wuta.
Wani a cikinsu ya fito riƙe da galon na fetur, yana shirin zazzagewa a jikin Al'ameen. Al'ameen ya yi ƙara a hankali, yana tsoron hukuncin da aka ɗaura masa.
"A kashe shi! Baƙo mai mugun nufi!".
"A ƙona shi maye ne! Kada Abarshi ya daɗe!".
"Matsafi ne! A hukunta shi!"
Mutane su ke ta faɗa, fiskarsu, cike da hukuncin da za su yiwa Azzalumi.
Al'ameen ya ɗago kai, idonsa ya cika da hawaye, amma baya yin kuka, abun da ya fi yi masa zafi rashin ganinta, ba ta zo ba, tana ina?.
"AISHA..."
Ya furta a zuciya.
__________
*A wani wurin dabam*
AISHA tana gudu. Zuciyarta na bugawa da tsananin tsoro, numfashinta na yankewa, hawaye na bin kumatunta.
A bayanta mutane guda biyu suna binta, hannunta ɗaya riƙe da rigarta tana gudu, ɗayan kuma, tana riƙe da wayarta ƙarami a ciki, tana faɗin.
"Ya Allah ka kare bayinka, ka cecemu! Ka tseratar da ni, kasa kar su kamani!".
Mutanen da su ke binta ba su daina ba.
__________
*Kafin wannan rana*
AISHA ba yarinya ba ce irin na kowa, kyawunta ya sha bamban. Fuska mai tsabta, idanu masu nutsuwa, murmushi da ke sa zuciya ta lafa.
Amma duk da haka, Aisha ba ta kula samari, wato ba ta soyayya. Da yawa sun nemeta cewa suna sonta, amma AISHA sai ta ce.
"Ka yi haƙuri ba na iya so".
Amma ba ta san WANI SON zai sa ta ta canza ba, kuma zai zame mata MAI WUTA!.
Wani baƙo ya zo ƙauyensu da saƙo, saƙon da aka aikesa ya kaiwa wani dattijo daga birni. Ba kowa ba ne wannan baƙon sai AL'AMEEN.
Al'ameen bai samu dattijo ba ya yi tafiya, duk da ba don zama yazo ba, amma dole ya jira ranar da dattijo zai dawo.
Wata ranar da ake taron ƙauyen Al'ameen ya je.
Wani yaro a wurin yana gudu ya faɗi, kafin ya je ya ɗaga yaro, Aisha ta je da kulawa. Anan ne idanuwansa su ka kalleta karon farko.
Daga baya, Aisha ta shiga cikin taron. Al'ameen ya sake ganinta, ta tsaya a gefen mata, ta yi murmushi akan wasan da ake a taron.
Ya yi ta kallonta, har idonta ya shige na sa. Amma ita kallon mamaki ne, sai kuma zuciyarta ya fara harbawa.
Ta lura tun ɗazu ya ke binta da ido, kuma ba ta san shi ba, da alama baƙo ne.
"Me ke damuna?"
Ta tambayi zuciyarta, ba ta taɓa jin ƙirjinta na motsawa don ta ga saurayi ba, amma yau ta ji. Har daga baya taro ya tashi.
Washe gari kuma.
Aisha na tafiya, tulun ruwa a saman kanta, ta gaji tana son hutu kaɗan. Ta fara sauke tulun ruwanta, ya kusa faɗi, sai Al'ameen ya zo a daidai, ya riƙe, yana kallonta da murmushi.
"Na gode. Da ba ka tare min ba, da tuluna ya faɗi kuma ya fashe".
Aisha ta faɗi, ba tare da sanin WANI SOn ya shiga ba. Al'ameen ya ji daɗi a ransa na murna ya ce.
"Bakomai, amma don Allah, ya sunanki?".
"Aisha"
Ta amsa.
Al'ameen ya ce.
"Na yi farin cikin haɗuwa da ke Aisha, sunana Al'ameen, ni baƙo ne, zan iya zama anan?".
Aisha ta ɗaga masa kai da murmushi.
Tun daga ranar su ka fara magana, su ka yi sabo. Har so ya shiga tsakani.
Aisha ta gane, WANI SON ya yi tasiri akanta.
SABIR ɗan uwan Aisha ne, ya gane tana son Al'ameen, kuma ya yi farin ciki, ya goya mata baya, sannan ya zama kamar abokin Al'ameen.
Soyayya ta girma a kwanaki kaɗan, dattijo mai saƙo bai dawo ba har yanzu.
Al'ameen ya cigaba da taimakawa Aisha a duk wani abu. Ya je ya gaishe da iyayenta, sun ji daɗi ganin mutum ne me hankali.
*Wata rana* wani al'amari mai ban mamaki da tsoro ya fara faruwa a cikin ƙauyen.
Wani mutum mai suna Malam Madu, yana cikin tafiya da dare a hanyar komawa gidansa, ya ji kamar ana binsa a baya. Kuma ba taku na mutum ba, Malam Madu ya ƙara sauri hankali a tashe.
_menene yasa aka kama Al'ameen?_
_me yasa Aisha ke gudu?_
_wani lamari ne ya faru a ƙauyen?_
Na san za ku ce an haɗa da tsoron fa😱 to mu je dai mu gani👀
Ya ku ka ji mafarin tatsuniyar? Ya burgeku? Kuna son mu cigaba?
Like, comment and share fisabilillahi🙏🏻
_*🌹𝑍𝑎ℎ𝑟𝑎-𝑡𝑢𝑙-𝑄𝑎𝑙𝑎𝑚🖋️*_