Free chapter · Read without an account

A House Divided

by NorthernAngel · His Rose

Bayan ya fito daga wanka sanye da towel kawai a jikinsa, Zafar ya nufi master bedroom din. Yadda ya barta haka ya same ta a kwance, sai dai wannan karon ta dukunkune waje daya kamar mai jin sanyi. Ya wuce closet ya shafa Augustinus Bader cream dinsa—a luxury essential that kept his skin perfectly hydrated and glowing with a healthy sheen. Ya fito sanye da black Loro Piana sweatpants da white fitted t-shirt da ta nuna kowace murda ta jikinsa. Ya fesa Clive Christian No. 1 Passant Guardant; the scent was the definition of pure opulence, a complex blend of rare ingredients that announced his presence with an intimidating yet seductive aura.
Yayi combing curly hair dinsa that is not much sam, daga haka ya fito ya nufi kan gadon inda take kwance curled up, ta danne hannunta akan cikinta kamar tana jin zafi. Zafar ya kira sunanta, “Zara,” amma bata amsa ba, hakan ya sa ya karasa kan gadon ya zauna yana kallonta. Gumi ya gani a fuskarta duk da sanyin AC dake dakin, idonta a rufe ga dry tears a kwance kan fuskarta, which made his heart ache with a surge of protectiveness. Cike da tausayinta ya sake cewa “Zara.”
Bude idonta daya gama ja tayi suka yi ido hudu na wasu seconds, amma da sauri ta sake rufe idon tana juya masa baya. Wani irin kunya da takaicin kanta ne ya kamata, she felt so profoundly ashamed and embarrassed. Da tana da yadda zata yi, da ta cire wannan yanayin nata gaba daya; shi ne dalilin da yasa ta daina karance-karancen erotic novels, and it’s been her deepest, most guarded secret since she was 21, sai yanzu da Zafar ya sani, wanda hakan ya sa take jin kanta very small and exposed. Ga wani azaba da maranta ke mata, yau kam sosai taji kasan cikinta ya kulle. She felt physically sick—a mix of nausea from the adrenaline crash and the heavy, dragging weight in her pelvis. Zafar ya sauke ajiyar zuciya, a hankali ya sa hannu ya dago ta amma ta yi saurin tirjewa tana rufe fuskarta cikin pillow. Sake dagota yayi with force this time ya rungumota jikinsa, ta yi saurin boye fuskarta a kirjinsa, her shoulders shaking with unspoken turmoil. Gently Zafar yace “babygirl,” shiru tayi bata dago ba. Zafar da duk wani motsi nata ya sani, a hankali yace “Come on Zara, Zafar nefa, it’s Zafar.” Still bata dago ba yace, "Stop trying to hide from me, Princess. I'm still the same man who just put a ring on your finger." Ya sake kokarin dagota amma ta ki yarda. Zafar ya rada mata a kunne, "Listen to me, Princess. There is nothing 'wrong' with you. Having a high drive isn't a sin or a sickness, Zara. It's part of who you are—a woman with a heart full of passion. It's part of the woman I've loved for years.” Fashewa da kuka kawai Zara tayi tana jin kaman kasa ta tsage ta shiga saboda yadda ya fito mata da zancen fili. Zafar ya girgiza kai yana cewa “No Zara, don’t do this to me, please. I know your heart hurts right now, but there is nothing to be ashamed of. There is nothing 'wrong' with you. Having that kind of desire for the person you're about to marry... that's a gift, baby." Ya dan tsaya don ya tabbatar kalaman sa sun ratsa ta. "I'm not judging you, Princess—I'm actually honored by it. It's a testament to how much you want me, and how much you trust me. So I don't look at you and see 'too much.' I see a woman who loves me with everything she has. But Zara, I want our first time to be perfect, without a single doubt in our minds before Allah. We're almost there, Princess, I promise. I'm not rejecting you—I'm just protecting us.” Daga haka ya miko mata hannu yana cewa “Give me your hand. Let's just sit here until the pain passes, okay? I'm not going anywhere, I’ve got you.” Zara ta sauke wani nannauyan ajiyar zuciya, bata dago ba dai amma ta mika masa hannunta. Ya kama yana kaiwa lips dinsa giving it a lingering, soulful kiss kafin ya sake shigar da ita jikinsa yana sa kansa cikin wuyanta, inhaling her soft scent which was his ultimate sanctuary. A hankali da shakakkiyar murya Zara tace “Zafar.” Ya dago yana kallonta har lokacin idonta a rufe, yace “Yeah baby?” With a low raspy voice Zara tace “I’m still sensitive tho.” Zafar’s eyes immediately softened with a mix of guilt and overwhelming affection. Ya cireta daga jikinsa slowly ya kwantar da ita yana cewa “I’m sorry, I’m sorry. I didn't mean to overwhelm you.” Daga haka ya kama hannunta kawai ya rike firmly, ya dauki remote din AC din dakin yana adding temperature din don ta sami saukin ciwon marar...  They stayed like that for 30 minutes, a hankali Zafar ya lura shiru, koda ya duba ya ga ashe har tayi bacci. Ahankali yace “Zara,” ta bude ido da sauri ta kallesa. He gave her a soft, melting smile kafin yace “Are you feeling better?” Ahankali ta gyada masa kai da dan murmushi kafin ta sake rufe idonta. Zafar ya dan ja hancinta affectionately kafin yace “Toh get up, you need to clean yourself. Do you want to have a walk? It’ll make you feel better. There is a restaurant nearby and it’s open 24 hours, sai muje kici abinci, kinji ba?” Gyada masa kai tayi, sai kuma tayi saurin girgiza kai cikin shagwaba tace “You said you’ll cook for me.” Zafar yace “Yes, I thought you’d like to go out but it’s cool. Go and clean yourself sai ki sameni a kitchen.” Daga haka ya mike yana mika mata hannu, ta kama ta tashi itama. Har lokacin daga ita sai towel dake jikinta. Ya rakata har bathroom sannan ya juya ya fita daga dakin ya nufi kitchen. Wanka Zara ta sake yi, sannan ta gudanar da nighttime skincare dinta a bathroom. Ta fito sanye da wani towel din ta nufi gadon ta dauki satin negligee set din—a beautiful camisole and shorts—sannan tasa robe din da yakai knees dinta. Ta nufi closet inda taga duffle bag dinta ta bude, she spritzed her Valentino perfumes, letting the floral and fruity notes settle on her skin like a second layer of luxury. Ta shafa Rare Beauty lip balm, sannan ta dauki kneading comb ta nufi mirror tana kallon kanta. Sosai peach sleepwear din yayi mata kyau, adding a soft glow to her skin. Idonta sunyi haske yanzu, sai dai dan kumbura da sukayi saboda kukan da tayi. Ta fito daga closet din ta fita daga dakin gaba daya da comb din a hannu tana massaging scalp dinta. Tana fitowa parlour ta ga Zafar shima ya fito daga kitchen yana gyara apron dinsa. Zara tayi dariya da bata yi niyya ba tace “I just hope you mean it when you said you can cook.” Zafar baice komai ba, ya tsaya yana kallonta with an intense, admiring gaze kafin ya karaso kusa da ita. He leaned in and kissed her cheek softly yace “Kinyi kyau.” Zara tayi murmushi tana gyada kanta in agreement tace “Yeah, you have good taste. I never thought peach would look this good on me.” Zafar ya girgiza kai with a classic smirk yace, "It’s not just the taste, Zara. It’s the canvas. Peach only looks that good because it’s you wearing it." Cike da iyayi Zara tace "Fair point. I make everything look like a masterpiece, don't I?" Zafar let out a deep, resonant chuckle yana cewa "Damn right! Hard to argue with the truth." Zara ta boye fuskarta a kirjinsa tana dariya, kaman ba ita bace data kasa kallonsa dazu. That was the one thing he loved most about her—how she could transition from being vulnerable to being his confident, playful queen in a matter of moments. Hannunta ya ja suka nufi kitchen area. The kitchen was a masterpiece of modern coastal design—sleek white marble countertops that felt cool to the touch, custom-made oak cabinetry, and top-of-the-line appliances that blended seamlessly into the walls. Panoramic glass windows offered a breathtaking view of the dark ocean, making the space feel like a sanctuary of luxury. Suna shiga ya janyo mata counter stool din yace ta zauna. Zara ta nuna mai kneading comb din hannunta tana cewa “Let me drop this,” daga haka ta fito ta koma parlour. Zama tayi kan sofa ta karasa massaging kanta kafin tayi amfani da band din da ta sa a hannu tayi packing gashinta into a simple ponytail. which accentuated her delicate features and her cute chubby cheeks. Daga haka ta bar comb din kan sofa ta nufi dayan sofar inda wannan 6ft plush teddy bear din yake tana cewa, “Ohhh, I miss you Bubba bear.” Ta rungume teddy din a hankali tace, “I think I should name you Roman, what do you think? Should I call you Rome baby?” Deep voice din Zafar taji daga bayanta, cold and sharp. “What did you just say, Zara?” Da sauri ta dago ta kalle shi kafin tace, “Nothing, I was just talking to myself.” Zafar ya hade fuska kamar bai taba dariya ba, his eyes turning into dark pools of ice. “I thought I heard you call it a stupid country name.” Zara tayi blinking eyes dinta slowly kafin ta kalli inda yake tsaye, taga har ya koma kitchen. Teddy din ta dauka ta nufi kitchen din tana cewa, “Roman is not a stupid country, it’s the original city of love! Even the name ROMA is just 'Amor' backwards. It’s written in the stars—and in the spelling—Zafar. He's literally named after love because you gave him to me.” Zafar ya daki counter din kitchen din da wani irin karfi, the sound echoing like a gunshot through the villa. Zara tayi flinching tana matsawa baya da sauri a mugun tsorace. With a sudden, booming roar, Zafar yace, “I don't care if it’s the city of love, or whatever, Zara!” His voice dropped to a dangerous, low vibration that made the air feel heavy. “If you have an issue with me, or if I did something to annoy you, then look me in the eye and deal with me. But I am warning you—never let that name cross your lips in this house again. Not even for a toy.” Ya matso dab da ita, his massive shadow looming over her and the giant bear. “Don't test my patience by bringing your past into our present. Is that clear?” Zara ta hadiye wani daci, tana jin yadda jikinta yake daukar rawa saboda kwarjinin da yake mata a lokacin, amma girman kanta ya hana ta nuna masa tsoronta. Ta daure fuska cike da bori tace, “Gaskiya, you need to step back. What's with the 'tough guy' act? If you think looming over me like a shadow is going to make me shake, you’re wrong. I’m not one of your business rivals you can just bully into silence.” Zafar da ya fahimci cewa ta gama tsorata, sai kawai ya juya ya koma kan carrots din da yake yankawa yana cewa, “Nidai na gaya miki.” Cike da rainin hankali Zara tace, “Look at you, back to your carrots. You think you can just intimidate me and then walk away? Ashe ba dadi? Or you think just because I agreed to come on this date and said yes to your proposal means na manta da abinda ka gaya mun akan sex life dinka? Nidai ba haka nake ba, amma dai na kasa yafe maka. I'm just telling you the truth so you know where we stand.” Daga haka ta juya ta fita daga kitchen din da teddy a hannu, ta nufi backdoor din ta koma beachfront din. Ta zauna kan silk lining din da har lokacin yana nan under the moonlight. Tana cikin farin ciki, yes—he made her so happy today, zata iya cewa this was one of the best days of her life, amma maganganun da ya fada mata kwanakin baya sun ki fita daga ranta. Anytime the memory resurfaced, she felt a wave of resentment wash over her. She just hoped that with time, wannan radadin zai dena damunta.. Kusan 10 mins tana kwance a gurin jikin human-size teddy bear dinta, tana kallon yadda farin watan yake haske saman ruwan beachfront din. Zafar ya karaso kusa da ita rike da wani tray mai dauke da bowl din noodle da another bowl of mixed fruits, sai glass din chilled tart cranberry juice da kuma bottle water. Ya ajiye tray din gabanta ba tare da ya kalleta ba, ya saka mata fork a cikin abincin. His movements were stiff, his jaw clenched, showing he was still holding onto that lingering irritation. Zara ta matso kusa dashi tana kissing cheeks dinsa, a hankali tace, “Stop being grumpy, I still love you.” Ya kara hade rai ciki-ciki yace, “You’d better not stop.” Daga haka ya janyo ta jikinsa still babu fara’a a fuskarsa; har yanzu yana jin zafin sunan Roman da ta ambata. Tun haduwarsu a Toronto yaji baya son yaron, har background check yayi akansa but he couldn’t find anything harmful about him. He just couldn't stand the idea of anyone else occupying even a tiny corner of her mind. Abuncin ya hau bata a baki, Zara tana murmushi tana jin wani sanyi a ranta. It’s hard to stay mad at him, especially how he notices the little things and doing them. Noodle din yayi dadi sosai, exactly the way she likes it, tamkar wanda Muazzam yayi mata ranar. Ta tambaye sa ko zaici yace mata he’s full. Tass ta cinye noodle din, looking so happy and satisfied with his cooking skills. Tace, “This is so good, so you can truly cook.” Zafar just gave her a smirk without saying anything, but his eyes softened for a brief second as he watched her enjoy the meal he made for her. Zara ta janyo chilled drink dinta tana sake cewa, "You cook, I eat. It’s the perfect marriage dynamic, don't you think?" Zafar yayi dan chuckling yana cewa, "Anything for my princess." Daga haka ta janyo bowl din fruits ta fara bashi a baki shima har suka shanye tare. Ya mike yana bata hannu yace, “Let’s take a walk.” Ta kama hannunsa suka fara tafiya a beachfront din, sunata hirar su da wasa musamman Zara. The tension from earlier seemed to melt away under the rhythmic sound of the waves. Gurin 1am suka dawo, ya kwashe kayan suka nufi cikin gida suka shiga kitchen. Haka ya tsabtace kitchen din tsaf, yayin da Zara ke bashi labarin encounter dinta da yaran Noor. He just listened to her, smiling as he picked up on the affection she had for the kids in her voice. Bayan ya gama suka fito yafara switching lights din ko ina tana biye dashi yayi locking front door, suka nufi back door zai rufe Zara ta tuna da teddy dinta tace mai zata dauko. Zafar yace “Stay here, I’ll get it for you.” Da sauri Zara tace “No! I’ll get him myself.” Daga haka ta fita zuwa inda tabar bear din tana tunanin haka kawai yaje ya jefa mata shi cikin ruwa yace mistake ne. Ta dauko abunta ta dawo ciki tana kallonsa yayi dan murmushi yana gyada kai, amused by her sudden distrust. Bata ce komai ba dai yayi locking door din ya hau rage wutan hallway din har suka hau sama. Suka shiga master bedroom, Zafar ya nufi gado ya dauke towel din da Zara tabari a gurin yana dan buga mata a kai yace “Dirty girl.” Tabe baki tayi tana ajiye teddy dinta a tsakiyar gado ta kwanta gefe tana shigewa jikin teddy din. Zafar na shanya towel din yafito ya ganta har ta kwanta yace “Zara get up, tashi, I need to make the bed.” Zara just pout refusing to budge tace “What’s there to make? Nidai na riga na kwanta.” Zafar shook his head at her stubbornness yace “Ae fa sai kin tashi, You walked barefoot in the sand and climbed straight into bed without washing your feet. Plus, you just finished eating, princess. Go brush your teeth.” Cike da takaici Zara tace “And you think I don’t know all that? Toh ni haka naga daman bacci yau so mind your business and leave me alone.” Daga haka ta juya mai baya while huffing. Sosai taba Zafar dariya dan yasan yayi bruising ego dinta ba kadan ba. Suppressing his amusement, he leaned in yana ce mata “I'm just advising you, yanzu haka zaki nayi in munyi aure? Nifa sam bana son kazanta, I have zero tolerance for messiness...” Kafin kace me Zara ta mike tana fashewa da kuka cikin masifa tace “Toh waye kazamin?” Her voice was loud and dramatic, her ego truly stung by his playful jab. Shrugging kawai Zafar yayi ya juya ya nufi babban sofa dake dakin. It was a custom-made Italian velvet chaise lounge, looking every bit like a piece of art in the corner of the room. He walked with a lazy, confident stride, knowing exactly how to get under her skin. Ya cire rigar sa yayi kwanciyar sa yana ciro phone dinsa daga aljihu, completely ignoring her outburst. Zara tafi five minutes a tsaye tana kallonsa, her mind racing with a mix of annoyance and the urge to prove him wrong. Ta shige bathroom with a huff, ta buga kofar for extra emphasis. Brushing teeth dinta tayi ta wanke da mouth wash, ta nufi gurin shower ta kunna foot wash spray ta sa kafanta a ruwan. Nan da nan kafan ya dawo fess kaman bata taba taka kasa ba. Ta fito daga bathroom taganshi kwance inda ta barshi kan sofa sai dai tass ya gyara gadon amma teddy bear dinta a kasa ya wullar tsakiyar dakin. Kwafa Zara ta sakeyi, her eyes narrowing as she glared at the back of his head. Ta dauki teddy dinta daga kasan ta nufi gado tayi kwanciyar ta, hugging the bear tightly as if to spite him. Tana jinsa ya tashi ya kashe lights ɗin dakin sannan ya koma ya kwanta kan sofa din, leaving the room in a heavy, charged silence… Washe gari da asuba, Omar ya dawo daga aiki cikin gajiya amma tare da natsuwar kammala nauyin dake kansa. Bayan an idar da sallah a masallaci da misalin karfe 6:30am, ya shigo gida kai tsaye ya nufi gym. He spent an hour of intense workout, pushing his body to the limit to clear his mind after a long shift at the hospital. Daga nan ya sauko ya shiga bedroom dinsa, ya fada wanka domin ya wanke gajiyar dake jikinsa. By 8:15am sharp, Omar ya fito daga wing dinsa, looking sharp in his jallabiya. Tafiyar minti bakwai ta kai shi babban part din Mom. Yana shiga, kamshin Infinity Flow daga Aromatic •89 Perfumed Floor Cleaner ya gaishe shi, a crisp and sophisticated scent that made the entire space feel fresh and expensive. Maids din dake gyaran gurin suna ta faman aiki cikin sauri. Omar ya hau sama kai tsaye, inda ya samu wata maid tana mopping katon parlourn dake hawa na biyu. "Call all the girls for me, be fast about it," ya fada mata a takaice ba tare da ya kalle ta ba. Ya zauna a daya daga cikin luxury sofas din, his eyes glued to his phone as he scrolled through medical journals. Bayan kamar minti hudu, Mom ta shigo parlourn, her presence announced by the sophisticated trail of her perfume. Fitowarta kenan daga part din Baffa, sanye da wata tsadaddiyar shadda dake nuna cewa ita ce da girki a yau. Omar ya sauko daga sofa din cikin hanzari ya dan sunkuyar da kai, "Ina kwana Mom." Wani genuine murmushi ne ya bayyana a fuskarta, "Ah, Doctor ka tashi lafiya?" Ta kalli maid din dake kusa tace, "Martha, ya kuka bar Omar haka? Go and bring him coffee mana." Har Martha ta juya taji yace, "Hey, don't bother, I’m fine Mom, thank you," Omar ya fada cikin muryarsa mai natsuwa. Mom tace, "Toh shikenan, Martha wuce kici gaba da aikinki." Ana cikin haka, sai ga Aisha da Ameera sun fara fitowa, sanye da hijabs dindinsu har kasa, suka karaso cikin ladabi, "Yaya ina kwana." Omar ya gyada kai, "Ina sauran?" Aisha ta mike da sauri, "Let me check them," ta nufi bedroom din Jiddah. Kafin ma ta taba kofar, Jiddah ta fito fuska a daure, ta shigo parlourn ta nemi wuri ta zauna tare da gaishe shi. Omar ko kallonta bai yi ba, idonsa yana kan Ameera, "Ina Yusrah?" Ameera ta sake komawa ta duba, jim kadan sai gata ta dawo, "Yaya taki zuwa." Mom ta kalleta da sauri tace, "Kamar ya taki zuwa? Kince mata yayanku ke kiranta?" Ameera ta turo baki, "I told her fa Mom, tace wai ita bata san kayan da zata saka ba. Ta fito da kayanta duka waje, Mom her room looks so messy, she's literally in the middle of a wardrobe crisis." Aisha ta girgiza kai tana cewa, "Toh ai ita dama kullum dakinta haka yake, always messy. Ki koma kice mata Yaya Omar ne yake kiranta, not anyone else." Ameera ta juya tana kunkuni ta sake nufin bedroom din Yusrah. Tana shiga, ta samu Yusrah sanye da bra da pant kawai, tana ta faman watsar da kaya. Yusrah ta juyo cike da fushi, "Wai bance miki ki dinga knocking ba? Ni sa'arki ce?" Ameera ta tabe baki, "Yaya Omar yace in fada miki, if you don't show up in two minutes, he's coming in here to get you himself. Kuma kinsan halinsa." Jin sunan Omar ya sa Yusrah ja da baya, ta dauki wani brown hijab dinta har kasa ta janyo shi ta saka da sauri, ta fito tana tura baki tana cewa, "Doluwa kawai." Tana isa parlourn, gabanta ya fadi ganin Omar ɗinne dai a zaune. Ita a tunaninta Ahmad ne, domin Ameera ta fada mata "Yaya" ne ke kiranta batayi specifying ba. Ta karaso jikinta na dan rawa, "Yaya good morning." Wani kallo Omar ya jefa mata wanda ya sa ta ji kamar ta nemi  wurin boyewa, "Yaushe na zama sa'anki?" Da sauri ta fara girgiza kai, "Wallahi ni haka tace min, tacemun wai Ya Ahmad ne ke kirana." Ameera ta mike, "Kaii, Ya Yusrah kiji tsoron Allah! Ban ce ya Ahmad ba." Jiddah ta katsesu cikin kosawa, "A'a, both of you should not even start this morning. Kar ku cika mana kunne." Yusrah ta rakube a gefe tana kunkuni, "Nidai Allah sai ya saka min tunda aka min sharri." Sai kuma ta kalli Omar cikin darda, "Yaya gani." Omar yace, "Kinsan makaho ne ni ashe, ban ganki ba." Shiru ta yi tana wasa da yatsun hannunta, ta nemi guri ta zauna tana addu'ar Allah ya sa lafiya ya tara su duka a wannan safiyar. Parlour ɗin ya yi tsit, kowa ya yi shiru yana jin yadda atmosphere ɗin ya yi heavy da tension. Omar ya gyara zamansa, his eyes fixed keenly on Yusrah, kafin ya kira sunanta a hankali, “Yusrah.” Da sauri tace “Na’am.” Omar yana kallonta strictly yace, “What happened yesterday? I mean, tsakanin Zara da Noor.” Yusrah naji haka ta mike, ta dawo kusa da Mom ta zauna tana facing ɗin Omar tace, “Yaya, ni dai ina zaune a parlour ɗinnan jiya da rana nida Ya Aisha. Then sai Ya Jiddah ta fito daga bedroom ɗinta all dressed up, ta gaya wa Ya Aisha su tashi suje wai Salma called her on the phone. Wai Yemma na kiransu a part ɗinku saboda Rose ta yanka Ya Noor a hannu. Aisha ta tashi suka tafi, so I followed them to see what they were up to. Ina shiga najisu, they were saying wai sai sunyi mata duka yau. Yemma ta fito ta barsu a part ɗin, Mom was not home at the time. So I called you baka ɗaga ba, shine na kira Ya Zafar na faɗa mishi. Shi kuma ya kira Ya Ahmad yace yazo gida maza. So Ya Ahmad came in time, suna ta plan ɗin yanda zasu hau sama suyi mata.” Omar ya yi shiru na ɗan lokaci, ransa ya gama ɓaci, yace “Baki san me ya haɗasu ba?” Yusrah tace, “Naji su Ya Jiddah nacewa akan Zara ta ɗauki su Zwar ne, kuma Salma taje tacewa Yemma she saw Zara in Ya Zafar’s room.” Cike da mamaki Mom tace, “tabɗi jam, Lallai Jiddah da Aisha. Are you serious right now? Har ku zaku shigar wa Noor faɗa? Noor fa? Har kun manta abubuwan da suka faru a gidan nan kafin Noor tayi aure? In banda mahaukata ne ku, Hajiya Aziza har wani ƙaunar ku take da zaku shigar mata faɗa ɗan ubanku? Har zaku ce zaku je ku taba yarinya akan yar iska marar kunya da mutunci irin Noor? In kun daketa me kuke tunanin zai faru? I won’t defend anyone, duk hukuncin da yayyinku suka muku, babu ruwa na. You guys are just hypocrites who don’t even know who truly loves you.” Mom ta mike tsaye tana nuna su, “Me kuka taba tsinta a gurin Noor da uwarta? Wani sharri ne ba ayi muku a gurin ubanku ba? Who always fights for your rights if not Muazzam and Omar? Kun taba jin ko Zafar yasa baki akan abunda uwarsa da ƙanwarsa keyi a gidan? He is not blind, yana gani amma he can’t tell his mother the truth. Shine yanzu zaku ce baku da masoya sai su? Just because your brothers brought their sister home? What has she ever done to you? This is nothing but pure jealousy and hatred!” Yusrah tayi saurin cewa, “Shine ma Mom. Ya Jiddah is always jealous of every pretty girl, shiyasa ma suke faɗa da Ya Noor kullum. Ai wata ran itace bata da gask...” Yusrah bata ƙarasa maganar ba taji saukar mari a fuskarta. Jiddah ce ta shaƙe mata wuya tana cewa, “Ni sa’arki ce? Today, I will finish you in this house!” Mom ta mike tana kokarin kwace Yusrah amma Jiddah ta ki sakewa. Aisha da Ameera basu ko motsa ba, because they were both annoyed with Yusrah’s big mouth. Mom cikin ɓacin rai ta fara ihu tana cewa, “Jiddah kashe mun ʼya zakiyi? Kashe mun ʼya zakiyi akan Aziza da shegiyar yarta? Cika mun yata ko in saɓa miki Jiddah! Omar me kake jira ne bazaka zo ka karyamun itaba saita kashe mun yarinya?” Omar wanda ransa ya dade da baci ya mike. Ya isa gurin ya finciko Jiddah da karfi ya watsa mata mari guda biyu a fuska. Jiddah ta ja baya tana jin kanta yana juyawa. Da sauri Yusrah ta koma bayan Omar tana kuka, jikinta sai rawa yake. Jiddah ta ɗago ta kalli Omar da jajayen idanunta tace, “Allah ya isa walla—” Bata ƙarasa ba Mom ta sauke mata wani marin, which cut her lip. Mom cikin ihu da bala’i, “Ni za ayiwa kutumar uba? Ke Yusrah, wuce ki kira babanku! Je ki gaya masa ga Jiddah nan tana mana rashin kunya nida Omar. Ki faɗa masa akan Hajiya Aziza ta turamun yaya su zane Zara tana so ta haɗasu da yan uwansu. Tell him everything! Break the news! Tell him the truth about what is happening in this house.” Yusrah bata tsaya wata-wata ba ta juya ta sauka ƙasa, ta bi ta garden ta nufi wing ɗin Baffa da sauri. Omar bai sake cewa komai ba yasa kai ya fice, cikin sauri da ɓacin rai yake tafiya. Zuciyarsa sai tafasa take yana tunanin da ba don Ahmad ya shigo gidan ba, da yanzu sun ci mutuncin Zara. Wannan tunanin ya ƙara tabbatar masa da dalilin da ya sa Zara ta bar gidan; tausayin ƙanwarsa da son ta ne yake azabtar da shi. Ya ji haushin kansa da ya kushe shawarar Muazzam na tafiya da ita Algeria tun farko. Saboda tsananin ɓacin rai, har gani ba ya yi sosai har ya isa wing ɗin Yemma. Yana zuwa, kai tsaye ya shiga cikin babban falon. A second parlour ya gansu duka sun ci kwalliya, da alama dining hall suke shirin tafiya. Zwar na ganin sa ya zo da gudu ya rungume shi yana cewa, “Uncle Omarrr!” Omar ya ɗan ɗaga yaron kaɗan, trying to maintain his cool, sannan ya sauke shi ya ƙarasa inda Yemma, Noor, da Imaan suke zaune. Yana tsaye, ya kalli Yemma dake riƙe da Mezyan a hannunta yace, “Ina kwana.” Yemma ta lura da yanayin sa da yadda ya gaishe ta a tsaitsaye ba tare da ya ƙara da "Yemma" ba. Ciki-ciki ta amsa, “Lafiya lau.” Noor da take kallonsa tace, “Ina kwana Ya Omar.” Bai ko kalleta ba, haka ma Imaan da ta gaishe shi. Idonsa na kan Yemma yace, “I came here to personally ask you what your problem with Zara is.” Cikin mamaki Yemma ta kalle shi, kafin ta yi leaning back jikin kujera ta ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya tace cikin muryar isa, “And what does that mean, boy?” Kai tsaye Omar yace, “An ce kin tara matan gidan nan jiya kince su daki Zara. I want to know the reason for this hatred, because it obviously didn’t start yesterday.” Hankali kwance Yemma tace, “You’re right! It didn’t start yesterday. It started twelve years ago when my only son told me he found a girl he wanted to marry. I was happy for him, until he told me she was your sister. I have no problem with you or your mother, Maryam was a good woman. My problem is that your sister is an Igbo girl from a Christian family. So, I strictly told my son No! Five years ago, you guys set him up in Toronto. Dana ya dawo ya sake kawo maganar ta, na ƙara ƙi, because even when she was with her mother I didn't approve, let alone now that she's been raised by non-believers. That’s why I matched him with your cousin, whose upbringing and faith I trust. But your sister’s return ruined everything. Kafiran iyayen rikonta sun riga sun shiryo ta, ta shigo da asiri. Tunda ta dawo ban sake gane kaina ɗana ba; an maida min shi wawa akan mace. I know what you’re doing—you want the Galado wealth all to yourselves, shiyasa kuke so ya aure ta saboda...” Cikin tsawa Omar yace, “Enough Yemma, enough! Duk maganar da kike yi ba ta dame ni ba. I think that’s a problem between you and Ya Zafar. Idan ɗanki ya ƙi jin maganarki, then who are we to stop him? Zafar is our brother and we trust him. Ko yanzu yace ya shirya auren Zara, zamu ba shi ita ne because we care about her happiness. What brought me here is to tell you... duk wanda kika sa ya daki Zara kuma ya biye miki, whatever I do to them, you will be held responsible. Kuma zan gaya wa Baffa duk wani mugun halinki towards my sister saboda ya ja miki kunne. Babu ruwanki da Zara, please. Your son is the one you should have a problem with, not her.” Noor ta miƙe cikin ɓacin rai tace, “Haba Ya Omar, this is Yemma you’re talking to this way fa!” Omar ya watsa mata wani mugun kallo, “The only reason my handprint is not on your face right now is because of my nephews here. And the only reason ban tattaka ki ba is because you’re a married woman now. But that doesn’t mean I can control my anger if you provoke me, Noor.” Ya juya kan Yemma, “Don Allah Yemma, babu ruwanki da Zara. Ki kama girmanki tunda ba a kanki take zaune ba.” Yana kaiwa nan ya fice daga part ɗin. Cikin ɓacin rai Yemma ta janyo wayarta, jikinta har rawa yake ta fara kiran Zafar. Bai ɗaga ba har ya tsinke. Ta sake kira, a karo na uku Zafar ya ɗaga cikin tsawa muryar Yemma na rawa tace “Zafar, where are you? Kana ina nace?” cikin muryar bacci, “Yemma, I told you zan tafi Abuja jiya ai.” Yemma ta daka masa tsawa tana kuka, “I want you in this house in less than two hours, Zafar! Har ni Omar zai zo ya yi wa rashin kunya? saboda kaja mun. Toh maza kazo gidan nan ayi ta ta ƙare yau!” Ta kashe wayar. Kafin su ce uffan, sai ga sallamar Yusrah. Ta gaishe su cikin dan fargaban su tace,“Yemma, Baffa ya ce kizo...”

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol