Free chapter · Read without an account

8

by Amina Abubakar Yandoma · KAFAR HAGU

*'KAFAR HAGU*

©️ Meenat A. 'Yandoma

Wattpad: Meenat_A_Yamdoma
Arewapen: @meenatyandoma


***


MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION

🅿️age 7
..."Amma Jatau! Baka tunanin kayi gangancin auren Rauda?" Daya daga cikin abokansa ya fada. "Wane irin ganganci. Yarinya ɗanya sharaf! Ni kuma dubeni tsufa duk ya cim mini. A tarihin rayuwata kaf ba a taɓa cacar da na ji dadinta ta zame mini riba kamar ta yau ɗin nan"
"Baka fahimci me nake nufi ba. Ina nufin ya za ku yi da Ghali?" Caraf Malam Iliya ya karɓe zancen. "Kaga Dan Asibi! Aure dai an ɗauka. Kada ka kawo mana wata tsurfa da iyayi. Duk soyayyar da ya ke yi mata ai dole ne ya hakura tunda ta yi aure" dariya Dan Asibi yayi domin ya fi su sanin waye Gaga. Yaron da yayi sanadiyyar mutuwar ɗan cikinsa ta ya zai manta da tarihin Ghali a cikin rayuwarsa. Ai shi yanzu sai dai ya ba wasu labarin Ghali. Bakin cikin da Iliya ke ciki haka ya baro Majalisar su cike da damuwa. Jatau na tambayar yaushe za a kawo masa matarsa, amma Iliya bai tanka ba. Kai tsaye gidansa ya nufa.
Tun daga zauren ya ke jiyo Muryar Gwoggo. Ganin ya shigo gidan ya nemi wurin zama ya saka ta gane akwai damuwa. "Iliyasu! Lafiya kuwa ko anyi mutuwa ne, ko kuma Rauda ce ta mutu?"
Ajiyar ya sauke tare da kwalawa Baraka kira. "Gwoggo yau dai na saka Rauda kuma an cinye ta" Rass! Gabanta ya yanke ya fadi. "Ban fahimci me kake nufi ba. An cinye ta kamar ya?"
"Ina nufin na sakata a cikin Caca, da nufi in ciyo kudi kimanin dubu ɗari biyu da kuma akuya. Sai dai yau sa a ta juya mini baya, an cinyeni. In taƙaice mini zance ya koma karami Jatau ya cinye Rauda" Ruwan da Baraka ta ɗebo ba shiri ya ɓare a cikin ƙasa. Gwoggo kuwa numfashinta tsayawa yayi na wucin gadi. "Shi kenan Iliya ka kashe mu. Ka kashe mana rayuwarmu mala'ikun azaba ba su gama ziyartar gidan nan ba" ta karasa maganar tamkar zata rushe da kuka. "Gaskiya ban yarda kana cikin hankalinka ba. Aa baka cikin nutsuwarka babu shakka ka tuna baya, akwai abin da ka sha" Baraka ta fada tare da riƙe haɓa cikin zallar tashin hankali. A yanzu kam Iliya ya kawo iya wuya. "Akwai abin da na sha da ya wuce ruwan ransa? Ke ba fa ni son rashin mutumci. Ai dama na san babu wanda zai damu da wannan ƙatotuwar asara har ta dubu ɗari biyu da akuya da nayi." Ya karasa maganar tamkar ya kawo ma Baraka bugu. "Ayiriririiiii! Nanaye. Daɗina da gobe saurin zuwa. Alhamdulillah! Shaho ya karɓi rabonsa yanzu kuma Malam da kai da waccan tsohuwar da Baraka, in ma Gaga ya barku kun rayu to a cikin mugun yanayi za ku kasance." Atine da ke uwar ɗaka jin an ambaci Shaho da sauri ta fito. "Lafiya kuma yau na ji an ambaci sunan ɗana? Ko tabarmar cin naman mutanen da ku ka saba kafawa yau da na gida za a fara?"
"Kwantas Atine! Rauda dai ta zama Matar Jatau" wata irin zabura Atine ta yi tare da dafe kirji. "Anya kuwa Zuwaira kin san me bakin ki ke furtawa? Rauda fa budurwar Gaga ko in ce rabin jikinsa" 
"Ita ɗin dai kamar yadda kika ji na fada. " Sabuwar guɗa Atine ta yi tare da kallonsu.
"Ai tunda yasha jinin ɗana nake rokon Allah ya sa kowa a gidan nan ya karbi rabonsa. Gwoggo ina tunanin lokacin komawa ga Ubangijinki ne yayi"
A kaf duniya babu abin da Gwoggo ta tsana fiye da ta ji an kira mata mutuwa. Don haka a fusace ta kalli Atine. "Ki ga mutuwa a kan ɗanki ni bazan mutu ba duk sai na ga taku mutuwar" "Gwoggo rabu da su. Kinsan hassada da baƙin ciki ba abin da ba su kawo wa. Yanzu kamata yayi musan nawa zamu tatsa a wurin Jatau kafin Rauda ta tare." Jin an ambaci kudi, ji tayi tashin hankalin da take ciki ta nemeshi ta rasa.
"Yawwa iliyasu. Da kasan za a sami kudi duk baka sanar da ni ba sai yanzu? Kai kuwa ai ba a yin haka. To yanzu nawa kake ganin zamu tatsa kafin a kaita gidan miji. Ai kayi farar dabara da ka aurar da ita. Na san za a yi alfahari da kai, sunnar Annabi sukutukum ka rayata kai kam ka samu dala."
Washe baki Iliya ya yi jin Gwoggo ta sauko. "Ai Gwoggo kin haifi ɗan arziki ita ma  Zinatun a cikin makon nan zan sakata cikin Caca. Ta je can wanda duk ya ci ya samu." 
"Allah ya kiyaye ya tsare tsautsayi da asara. Duk ranar da ka sakamin ɗiya cikin Caca zamu tuna baya ne Ni da kai. Domin dambatuwa za muyi da kai a cikin gidan nan" "Ni duk ku tsaya." Baraka ta fada a fusace.
"Me ake nufi da ni da na ji ana maganar amsar kudi wurin Jatau amma ni ba a fada kasona ba" Dariya Gwoggo ta yi.
"Ai mun dauka adawa kike yi da auren. Amma tunda kin ɗauki haske sai ki zo a yi lissafi da ke, amma ki sani gado da katifa kai harma da kayan kicin suna kanki. Duk tallar da kike ɗora mata da kudin da Ghali ke baki, yanzu sai ki fito da su" Ashar Baraka ta ɗura jin abin da Gwoggo ta fada.
"Idan Ubanta Iliya bazai yi mata kaya ba sai dai a kaita daga ita sai kayan jikinta gidan Jatau ɗin. " Atine da Zuwaira me za su yi ba dariya ba. Dariyarsu ce ta tsaya ganin jami'an 'yan sanda sun afko cikin gidan ba tare da sallama ba. "Waye Iliya a gidan nan" kallon kallo aka fara cike da mamaki. "Ni ne wani abu ya faru?" Ka zo in muka je caji ofis za ka ji koma me ye.
"Ban gane ya biku ba. Ina za ku kai mini ɗa me yayi muku?" Gwoggo ta faɗa a rikice. "Hajiya ba wata matsala ba ce babba. Idan muka je can da ya gama abin da ya kai shi za mu dawo miki da ɗanki" matan gidan kuwa kowa ta yi cirko-cirko. To me ya aikata da har 'yan sanda ke nemansa haka? 
Haka aka rasa ƙeyar Iliya Gwoggo na ihu ko saurarenta ba su yi ba. Babu inda suka zame sai caji ofis. Idanuwansa ne suka sauka a kan Zinatu da ke ta faman rarraba ido. Gefenta wata ce zaune tasha uban bandeji a goshi. "Yawwa ofisa ga Ubanta nan" figigiyar yarinyar ta fada tana zazzage ido. "Malam Iliya ka san wannan" jami'in ya karasa maganar tare da nuna masa Zinatu. "Eh na santa ɗiya ta ce."
"Ma sha Allah! Ina fatan ka ga wanna me daure da bandejin?" "Eh ofisa na ganta."
"To fada ne ya haɗata da ɗiyarka Zinatu ko kuma in ce Zinatu ce ta iske ta har inda take, tare da yi mata ɓarin makauniya."
A maimakon su ga Iliya ya shiga tashin hankali ko damuwa, sai ji suka yi ya tuntsure da dariya. "Ja'ira! Ai ke kam nasan ni na haifeki. Lalacewarki da kome duk ni kika biyo 'yar nema" kallon kallo jami'an tsaron suka fara. "Ofisa dama na fada muku da baku kira wannan tsohon ba, ni kawai a bi muni haƙƙina"
"Kul Abida! Wannan mahaifina ne faɗanmu ya tsaya iya mu biyu. In ba haka ba sai na karasa sauya miki kamanni a wurin nan" tsawar da Ofisa ya daka musu ce ta saka su yin shuru.
"Mun kira mahaifinki ne don ya yi belinki tare da biyan wadda kika fasawa kai tarar kudin da muka saka miki. " 
Ya mutsa fuska Abida ta yi. "Sai da na ce maku kada ku kira mahaifina ku barni in yi belin ɗin kaina da kai na. Amma tunda ya zo sai yayi Belin ɗina. Sannan Ofisa ayi min tsakani da wannan in ba haka ba, duk ranar da na kara ganinta da saurayi zanyi abin da ya fi haka" 
"Ofisa kana ji ko? A gabanku ma ta maimaita" sallamar da aka yi ce ta saka su juyawa. Saurayin Zinatu ne wanda aka yi faɗa a kansa. "Girar sama da ƙasa Zinatu ta hade. Hutar da Malam Iliya yayi, shi ya yi belin Zinatu. Abinda kuwa bakin ciki duk ya turnuƙeta, da gaske dai Zinatu ta kwace Ɗan Bala. Bayan sun fito Iliya sai ƙara watse haƙora ya ke yi ganin yadda ya fiddo kudi. "Baba mu tafi na ce" ta fada a fusace.
"Ke kuwa ki tsaya a yiwa Baba alheri mana" "baya bukata ka rike kudinka"
"Ka ga munafukar yarinya! Ni na ce miki bani bukata, yaushe muka yi haka da ke. In ya bada 'yar Uwarki da na aurawa Jatau ko katifa ce ba sai a cika a sai mata ba?"
Fiddo idanuwa Zinatu ta yi cikin tashin hankali. "Baba! wane Jatau ɗin?"
"Wanda kika sani"
"Shi kenan Baba! Ka kashe mu lokacin wafatin kaf zuri'armu ya yi...


Meenat A. 'Yandoma

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.