Free chapter · Read without an account
Chapter 1
FREE PAGE1️⃣
Jiyo kukan Umar na ke
Na ratsawa har tsakiyar kaina, ina kan abin Sallah bayan idar da sallar walaha da na yi, Wadda yanzu bata wuce ni sam in da ada ban damu da yin ta ba.
ina dai da k'ok'arin sauke Sallar farillah akan lokacinta, amma babu ruwana da nafila
sai dai yanayin rayuwa ya sauya min hakan yasa Nafilfilin da na ke da kuma yawan Ambaton Allah yana matuk'ar farantamin, kusan yanzu inna zauna bakina baya iya zama shiru na dinga zikirori kenan da k'ara neman kusanci ga ubangiji na. ko zan samu rabauta da kuma ku'buta daga mummunan halin da na tsinci rayuwata a ciki.
Dole ina buk'atar Addu'a, ko dan kariya ga lafiyata da ta yara na,
Sai dai bani da wani wanda zai tsayawa lamarina bare har ya damu damin addu'a, duk da kuwa ina da waɗanda yakamata a ce suna min addu'ar.
Sai dai kash wani dalili ya hana na kasance tare da su bare nasani ko suna min addu,ar,
ko Kuma abinda na aikata gare su ya hana hakan,
dole dai ni ɗin ce zan tashi na rok'i Allah dan shi ɗin gafururrahimu ne zai amsamin ya kuma kawo min d'auki ya fidda'ni a cikin halin da nake ciki.
Ƙoƙarin tashi na fita nake sai ga Salim ya faɗo cikin ɗakin
da gudu yana haki tare da nuna min hanyar waje. cikin kuka yace
" Ummanmu ga Aunty can tana dukan Umar don kawai yaje k'ofar ɗakin ta yace ina Abbanmu shine take ta dukan....."
Ban tsaya na ƙarasa jin abinda zai ce ba,
na maza na ajiye abin sallar na fito dan har lokacin ina jiyo ihun kukan shi na ratsawa har tsakar kaina.
A sukwane na jefa ƙafa ta farlon,
Hakimar tana tsaye shi kuma Umar a durk'ushe ya haɗa hannayen sa biyu yana kuka.
yana magiyar tayi hak'uri dan Allah ba zai sake ba, Ita kuwa ko a jikin ta sai ma k'ara haurin shi da take da ƙafa ta ƙara ɗaga bulalar hannun ta lafta mai a baya,
Duk jikin nan yayi rud'u'rud'u abin ka da farar fata bakinsa kam sai zubda jini yake,
ba tare da ta tausaya masa ba ta hankad'ashi ya faɗi kansa ya bugu wata ƙara ya fasa wadda na tabbata ko wanda ke bakin get zai jita,
Ya zube ƙasa daga nan bai ƙara motsi ba.
Cikin zafin nama na ƙarasa ba tare da na kalle ta ba, na tsugunna na tallafo kan shi da ke zubar da jini, na kalli fuskar shi cikin zaro ido ganin ba ya numfashi, nan take na ji zuciya ta ta wani buga da ƙarfi jikina ya shiga rawa na shiga jijjiga shi ina jin zuciyata na wata iriyar tafasa.
Wannan wanne irin zalunci ne? shikenan ta kashe min yaro,
haka kawai nake faɗi a zuciyata, sai dai babu damar furta hakan a fili.
Kiran sunan shi na fara Ina daɗa jijjiga shi hankali na a tashe ina ɗan bubbuga fuskar shi nake cewa
"Umar Umar ɗi na kaga kalle ni kaga kalle ni, Umman kace fa ka tashi"
Amma ko motsi bai yi ba bai ma san ina yi ba
Cikin raunin da zuciya ta tayi ina zubar da hawaye, na ɗago kaina na kai kallo na ga wadda ta aikata masa hakan.
Tana tsaye rik'e da ƙugu tana girgiza tare da wulwula bulalar injin da ke riƙe a hannunta.
Sanye take da wasu watsatstsun riga da wando waɗanda suka matse ta sosai, wandon duka kaɗan ya rufe mazaunan ta.
Sai rigar wadda ko cibiyar ta ba ta gama rufewa ba, daga saman k'irjinta duk a waje.
Duk lokacin dana kalle ta har kunya hakan ke bani, ni da nake mace ma ba son kallon su nake ba bare namiji.
Kuma a haka tak'ama take da abaibad'an ta har tana bayyana su.
Kanta kam ta sa wani uban tulin gashin doki, wanda ta saki har gadon bayan ta idanun nan sun sha eyelashes,
Sai faman taunar cingwum take.
"Ya akai kike kallo na ko da magana ne kika wani zura min ido?
Yaro ne na daka ko zaki iya rama masa ne?"
Ta ƙare maganar tare da ɗage min girarta guda.
K'wallar data cika min ido ce ta zubo, na kafe ta da kallo Ina Jin wata iriyar k'una a zuciya ta,
Ashe dama alkhairi ya kan zama sharri? har yanzu kallon da nakewa Maryam na kasa manta baya na kasa manta irin abubuwan da suka faru.
Tsawar da ta daka min. ita ta dawo da ni daga duniyar tunanin da na fad'a.
Cikin rawar jiki na tashi ba tare dana iya cewa komai ba, na sa'bi Umar da sam baya numfashi a kafad'a ta, duk ya langwa'be jikin sa ya saki, nasan koda na yi magana ma hakan ba zai amfanar dani komai ba, sai wani tashin hankalin.
Gashi dai nice aka cuta amma bani da damar magana,dan maganar tawa ma nasan abinda zata haifar dan haka ɗana kawai na ɗauka na nufi hanyar barin farlon.
Har na kusa fita naji k'arar bude ƙofar bedroom ɗin ta,
Nasan uban gayyar ne ya tashi dan haka na ƙara ɗaga ƙafa ta dan barin farlon.
Ina Jin shi Yana magana
"Sweet heart wai hayaniyar me nake ji ne tun ɗazu? kin san ke nake jira ki tayani wankan ko? ina son fita da wuri yau"
Ban tsaya na ƙarasa jin abinda za ta ce ba cikin sauri na fice daga farlon.
Sai dai na makara har ya hango ni,
Ina jin muryar shi cikin ɓacin rai.kamar yadda ya saba magana in ya ganni, Yana tambayar Maryam ɗin
"Ita kuma wannan fa me ya kawota farlon nan? bance miki bana son ganin ta ba inba aiki zata miki ba"
Ban tsaya na ƙarasa jin abinda zata faɗa ba nayi gaba.
Kujera ya nufa ya zauna tare da ƙara jefo mata wata tambayar ganinta riƙe da bulala.
Sai da taga dama tukun tace
"Uhm kinibibin ta ne ya kawo ta mana yaro ne yayi laifi dan na hukunta shi, shi ne tazo ta nuna min iyakata dan bani na haife shi ba"
Sai kuma ta maida muryar ta kalar Kuka tace
"Wai ni Salmah za ta wa gorin haihuwa?
wai in fitsari banza ne kaza ma tayi"
Sai da ta kalli yanayin fuskar shi taga gaba ɗaya ita yake kallo
tukun ta cigaba da magana, cikin kissa
"Kaga kenan ta na nufin ni bana haihuwa in haihuwar banza ce Nima nayi"
Ta ƙarasa maganar cikin raurau da murya kamar zata yi kuka, rin abin tausayin nan.
Cikin ɓacin rai yace
"Salmar ce tace miki haka? saboda rashin Mutumci?"
Ganin yadda ya hasala yasa ta ƙara narkewa ta shiga rattabo bayanan ƙarya.
Akan dama Salmah ta saba mata haka amma sai taga baya nan,
Da dai duk wani Abu da ta san zai tunzura shi.
Sosai Haidar ya hasala ya miƙe da nufin zuwa wajen Salmar.
Cikin sauri Maryam ta tare shi, cikin sassauta murya tace
"Kaga ka bari ni zan je na same ta karka ce
mata komai ka ji,
bari na kira ta tazo ta wanke mana toilet ɗin kayi wankan kaga sauri ka ke"
Ɗaga mata kai yayi kamar ƙaramin yaro,
ya koma ya zauna yasa hannu ya dafe kanshi daya keji yana sara masa.
Ya rasa me yasa a duk lokacin da wani abu ya faru da ya danganci Salmah sai yaji kansa na masa wani irin ciwo, ya yi ta kokawa da tunanin sa kenan, amma sai ya kasa aikata komai sai dai yaji yana son bin abinda Maryam tace.
********
Ina shiga ɗaki na kwantar da Umar zuciyata na min wani irin zafi, babu zato naga an ɗago ɗan yololon labulen ɗakin,
Ɗago kaina nayi na kalli Ƙofar, Maryam ce tsaye ta rik'e ƙugu ta na girgiza jiki tare da gallamin harara cike da wulaƙanci tace
"Kinga malama ki taso muje ki wanke min toilet. Sweetheart zai yi wanka"
Kallo ɗaya na mata na ɗauke kai na, wani irin Abu ya taso min ya tokare mak'oshina.
Ganin naƙi kula ta yasa ta tafi cikin masifa har ta isa wajen Haidar.
Cikin faɗa kamar ɗan ta tace
"Ka je ka ɗauki mataki akan Salmah na mata magana amma tayi banza da ni"
Cikin tsananin ciwon da kanshi ya ke masa, yasa hannu ya dafe kan ya mik'e tsaye cikin son kwantar mata da hankali yace
"Bari naje na same ta. zata zo yanzu ai dole ma ta wanke"
Ya nufi ƙofar yana tangad'i kamar wanda ya Sha kayan maye.
Cikin sauri ta maza ta sha gaban shi ta tare hanya. don dakatar dashi kar ya fita.
tare da jifan shi da wani irin kallo me ɗauke da alamar tambaya, cikin zafin kishi tace
"Me kake nufi da zaka bi ta kai kaɗai munafuki?" ta na jin wani irin kishin Salmar na cinta.
In akwai abinda ta tsana a rayuwar ta, bai wuce taga koda ganin Salma Haidar yayi ba,
dan tsabar kishin da ta ke da ita, duk da kuwa ita da kanta ta tabbatarwa kanta babu wani sauran 'bur'bushin alamar wani abu najan hankalin ko sha,awar Salmar da ta bari wanda har Haidar zai gani a jikin salmar bare yayi Sha,awar ta.
Ta bi duk hanyoyin da za ta rusa duk wani tasirin Salmar a rayuwar Haidar, ta riga da ta kassara komai duk da Boka Gamji ya bata tabbacin babu ta yadda za'ai Haidar ya ga kyan Salmah,
Ya riga da ya mata mugun aiki akan ta,
wanda zai sa Haidar ɗin ya dinga kallon Salmar ta koma mai kamar namiji a idon shi, sai dai ya ja mata kunne ta guji yawan bari suna ganin juna.
Dan akwai k'auna mai ƙarfi a tsakanin su, hakan kuma zai iya ɓata musu aiki.
Ganin yadda tayi kicin kicin yasa Haidar ya ɗaga hannayen shi sama cikin sanyi murya yace
"Kinga in baki yarda ba mu je tare, kema kinsan bata isa komai ba bare na kalle ta, haba gimbiya ta babu wata macen data isa na kalle ta a wannan duniyar, bare harta ta wulak'anta min ke, haba shalelen mijinta wacece wata Salmah me akai aka yi ta"
Harara ta banka mai
zuciyar ta cike da ɗacin wutar kishi na ƙara ruruwa a ranta tace
"Zaka ce haka mana munafuki, ni wallahi har yanzu inna tuna wani abu ya taɓa haɗa ka da ita har zuri'a ta haɗu tsakaninku karka tona zuciyata kaji"
Ganin ta fara maganganun nan, yasan hali yanzu zata ƙara birkita mishi tunani,
ya rasa me yasa ya ke jin baya son yaga ɓacin ranta ko kaɗan.
Cikin sauri ya ƙarasa ya rungumo ta yana mai faɗa mata wasu kalmomi, tun tana ture shi har sai da ta dawo tana dariya, tukun ya kama hannun ta suka nufi hanyar ɗakin Salmar.
Maryam na barin ɗakin, na shinfid'e Umar akan tabarmar mu dake yashe a tsakar ɗakin,gefen Na'im da ke sharar barcin sa hankali kwance,
Na ruga wajen bayan k'yaure inda botikin ruwanmu da muke sha yake na sa kofi na kamfato ruwan, da sauri nazo na sheka masa shiru bai motsa ba, ji nayi komai na duniyar na juyamin.
Salim dake gefe na sai kuka yake ina lallashin sa, duk da nima kukan nake amma na zuci.
ƙara shek'a masa ruwan nayi ina jan addu'a a zuciyata,wani irin numfashi ya fusgo da ƙarfi tare da zabura, yana ƙoƙarin tashi ya gudu, cikin muryar yarinta ya ke cewa
"Umma na ki zo ki taimakeni zata kashe ni, wayyo Allah na bazan ƙara ba aunty kiyi haƙuri"
Wata ajiyar zuciya mai nauyi na sauke, ganin yana numfashi wani tausayin shi ya kamani, ƙaramin yaro da bai san komai ba aka aikatawa haka.har yana magiya ayi haƙuri, amma da yake zuciyar Maryam babu imani shine ta mai wannan dukan.
Cikin sauri na janyo shi jikina haɗi da rungume sa, ina mai fashewa da kukan dana ke riƙewa tun ɗazu, sai dai nayi ƙoƙarin hana sautin kukan fitowa.
Shafa kan shi na shiga yi Ina cewa
"Ya isa yaron Umman sa ka ganni nan ka daina kukan ka ji.
babu wanda zai ƙara dukar min kai"
Jin danshi da nayi a hannuna yasa da sauri na duba hannun.
Zaro ido nayi cikin tsoro ganin yana ɗigar jini alamar kanshi daya bugu ya samu rauni kenan.
Cikin kuka Salim yace
"Ummanmu kalli yadda nan yake jini"
yana mai nuna kan Umar ɗin.
Kama shi nayi na haɗa su na rungume, tare da shafa kansu cikin raunin murya nace
"Nagani Salim ka tayamu da addu'a Allah ya yaye mana wannan damuwar da mu ke ciki ka ji. na rintse idanuna wasu hawaye masu zafi suka zubo,
tabbas na yarda na kuma tabbatar da karin maganar nan. ta Malam bahaushe da yace" *(KOWA YAK'I JI BAZAI K'I GANI BA)*" ni kam nawa kaina na cuci kaina
"Astagfurullah Allah ka yafemin kura'kuraina" na furta hakan a hankali.
Shigowar da akayi yasa na ɗago manyan idanuna dara'dara da suka rine suka koma jawur saboda Kuka,
Na bi su da kallo Haidar ne a gaba sanye da jallabiya ruwan hanta. Kallo ɗaya na masa na ɗauke kaina.
Saboda kwarjini da ya min ga haske da na ga ya ƙara da ƙiba,
sai shek'i ya ke kamar wani sabon ango, alamar bashi da wata matsala a rayuwar shi.
Jifa na ya ke da wani irin kallo mai cike da tsana, haɗi da k'yama, kallo ne da ya ke nuna zallar k'iyayya da wasu tarin abubuwa da na kasa fassarasu.
Sai nake ganin kamar ba Haidar ɗi na ba, kamar ba mijina wanda nakasance ko yaushe Ina alfahari da shi ba, kamar ba ni ce mafi soyuwa a gare shi ba, kamar ba wanda yamin alkawarin daga ni babu wata ba babu kishiya babu saki ba.
A hankali maganganun sa suke dawo min kamar yanzu ya ke faɗar su.
_"Mutu ka raba ni da ke Uwar gidana kuma Amaryata"_ ɗaya daga cikin kalmomin da ya ke yawan fad'amin kenan, a kullum in har muna tare cikin farin ciki, hakan yasa na saki jiki na gama miƙa masa ragamar rayuwata,
sai gashi tun ba'aje ko'ina ba ya juyamin baya ya mai dani k'ask'antacciya.
Ya sa'ba alƙawarin daya ɗaukar min, ya gujemin ya manta shi kaɗai ne ya ragemin gata a yanzu. Ya manta saboda shi na rabu da kowa nawa na manta halacci na rusa Amintaka da yarda,duk saboda son shi.
Wai yau Haidar ne tare da wata mace, wadda bata kamo ni a komai ba, asali ma ba za a jerani layi ɗaya da ita ba, ta bangaren komai kyau diri ilimi nasaba,
Amma dalilin ta yau ya maida ni bola, lallai na yarda duniya budurwar wawa ce,
Tsawar da Haidar ya daka min ce ta dawo dani daga duniyar tunanin dana faɗa, bai ko kalli inda nake ba ya fara magana
"Bake Sweetheart tasa wanki toilet ba, wato shi ne dan kin raina mutane kina ji kika wuce har kin Isa ki fara tsallake umarnina ko?
harda mata gorin haihuwa"
Cikin mamakin sabon sharrin da ta ƙulla min.l na ke kallon su baki na buɗe, na kasa magana.
Faɗa ya ke baji ba gani ya k'arashe da faɗanbda cewa
"Wannan ya zama kashedi na ƙarshe da zan miki, kar ki sake ko da bana nan nazo naji labarin ko musu ya shiga tsakanin ki da ita,
bare har ta baki umarni ki ƙi bi dan in tayi magana kamar ni ne nayi kin ji ko?"
Ya ƙara buga min tsawar da ta sa na zabura na shiga gyad'a kai alamar naji.
Jin zuciyata nake kamar zata fashe saboda tsabar takaici da wani irin k'unci da ke nuk'urk'usar ta, zuciya ta na tafasa kamar zata fasa k'irjina ta fito.
ya kamata ace dukan su su biyun na tsane su, amma zuciyata ta kasa tsanar Abban Salim kwata-kwata, duk da irin abubuwan da ya ke min koda yaushe. laifin kaina na ke gani bana kowa ba.
Ƙara sunkuyar da kaina nayi dan na riga da nasan hukuncin da zai biyo baya muddin na cigaba da haɗa ido na da nasa, sai aikin shafa kan yarana na ke suma sun k'ank'ameni cikin tsoron maihaifin nasu.
"Ba dake na ke magana ba? ki ka sunkuyar da kai kamar tsohuwar munafuka, za ki tashi ki wuce ki wanke toilet ɗin ko kuma yaya?"
ya faɗi hakan kamar zai yo kaina ya dake ni cikin hargagi.
Sanadiyyar tsawar Na'im da ke barci ya farka a firgice, cikin kuka, da sauri na tashi jikina na rawa ko kallon gaba na ba na yi sosai na rarumi yaron,da tsohon zanin goyonmu da ya yayyage da dubara dai nake goyon dashi na saɓa shi a baya, ko gama ɗauruwa zanin bai yi ba na nufi hanyar waje.
Ganin na nufo ƙofar yasa Haidar ya matsamin, na wuce ita kuma dama tun lokacin da ya gama faɗan tayi waje, dan haka tana gaba ina biye da ita a baya sai wata iriyar tafiya take ta fitsara tare da girgiza jikinta ta na kaɗa mazaunai.
'Dauke kaina nayi daga kallon ta da sauri, har muka ƙarasa sashen nata.
Bayan tafiyar Salmah.
Kallon yaran Haidar yayi da su ka yi tsuru tsuru su na kallon shi.
Ji ya yi wata k'yamar su ta k'ara kama shi,
Ya tsartar da yawu tare da toshe hancin sa, dan har wani wari-wari ya ke ji tsabar sharri, duk da kuwa babu warin sai dai yace ɗakin babu wasu abubuwa sai buhun tsummokaranmu da kuma tsohuwar tabarmar da ke yashe, inbacin su ko'ina fes ya ke simintin ɗakin a share tas komai a tsare a ma'ajiyar sa.
Ko yaran duk da kasancewar suturar jikinsu tasha jiki, sannan ta musu kaɗan, fes kayan suke a wanke saboda Salmah ba dai tsafta ba.
Tsaki yaja ya daka musu tsawa yace"Dan uwarku meye kuke jallona kamar tsofaffin mayu"
Duk sai su ka sa kansu k'asa.jikinsu na rawar tsoron sa, tsaki yaja tare da sakin labulen ya fice.
Bayan fitar shi Salim da ya ke yafi Umar wayo, dan shi shekara ta goma ya ke ciki, shi kuma umar biyar.
Ya kama Umar ya miƙar ya ɗebi ruwa a buta ya ƙarasa inda Umman su ke ajiye tsohon flaks ɗin ruwan zafin ta wanda ta ke ji dashi tana lalla'bashi kamar tsoka ɗaya a miya, saboda ta san amfani shi.
Ya janyoshi a hankali cikin nutsuwar shi, ya tsiyayi ruwan d'umin ya surka da na butar ya mai da shi inda ya jawo,
ya kama hannun Umar ɗin suka fito waje, yasa Umar ya tsugunna a hankali cikin dubara ya shiga wanke mai kansa, har jinin ya d'an ragu tukun yaja hannun sa ya kai shi ɗaki ya zaunar kan tabarmar,
Ya ɗauki kujerar Umman su y'ar tsugunno.ya fito ta bayan tankunan ruwan bayan ɗakin su,
ya ajiye kujerar ya taka yasa wani ɗan icce ya kwaso yanar da ke lik'e jikin bangon wajen, ya sauko da sauri ya ƙarasa ɗakin ya tarda Umar ya jingina da bango ya tallafo kanshi yana hawaye, ya cire yanar daya kwaso ya lik'a masa dai'dai inda yake zubda jinin,cikin ikon Allah jinin ya d'auke.
Cikin tausayawa ƙanin na shi yace
"Sannu ka ji Umarin Umma, ka daina zuwa wajen su kai ma baka ji,
ba Umma tace ka dinga bari in Abban ya fito ka gaishe shi ba?"
Cike da yarinta Umar yace
"Ba Malam Bashir bane a Makarantar islamiyyar mu yace, kullum da safe muna gaisar da Iyayan mu ba zamu samu lada, shi ne fa naje gaida Abba dana k'wankwasa musu k'ofa. Aunty na buɗewa ta jawo ni ta fara dukana, kuma Abba na gani bai hana ta ba"
Cikin tausayin ƙanin nasa yace
"Ka dai na zuwa har farlon daga yau, gaida iyaye akwai lada. amma ka jira Abban ya fito sai ka gaida shi ka ji"
Gyada kai Umar yayi ya shiga ƙoƙarin kwantawa, ganin hakan yasa Salim yace
"Karka kwanta bari na ɗauko maka riga kasa tunda waccan ta lalace"
*************************
Muna shiga farlon ta nufi kujera ta zauna ta ɗora ƙafar ta ɗaya kan ɗaya.
Cikin Isa ta nuna min hanyar bedroom ɗin ta da hannu, alamar na shiga nayi abinda da ta sani.
Har na nufi hanyar da nufin shiga, naji muryar ta cikin tsawa tace
"Kinga dawo ki sauke wannan shegen yaron kar yaje yamin 'barna, ba za ki kai min shi ɗakina ba dan nasan sauke shi za ki yi"
Juyowa nayi kamar yadda tace na sauke Na'im ɗin, duk da kuwa nasan kukan zai yi, tare da wucewa dan gyaran banɗakin, aikwa ina wucewa ya fashe da kuka dan Na'im yaro ne mai k'ulafuci baya son kowa ya ɗauke shi sai ni.
Ina jin kukan shi na ratsawa har tsakiyar kaina nayi gaba, ga tunanin halin da na bar Umar a ciki na damuna, gwara nayi sauri na kammala na je naga halin da suke ciki,
Dan innayi wasa ban isa na fita a part ɗin nasu yanzu ba, ta dinga tsiromin ayyuka kenan. haka na barshi na wuce.
Na tarda Ɗakin nata kamar bola komai kaca'kaca, gasu gajerun wandunan Abban Salim nan a yashe a tsakar ɗakin, gadon ma duk a yamutse da kayayyaki ko ina dai babu kyan gani, karfet ɗin ɗakin ma duk ya haɗa wata iriyar daud'a. kwata kwata ya fita daga kalar shi ta pink ya koma kamar brown brown.
Toilet ɗin kawai na nufa, shi ma dai gashi nan gashi nan ne, ko'ina babu kyan gani, kwana biyu kawai da na yi ban gyara ba, shine ya canja haka sai iyayen tarin pant ɗin ta da ta tara sun cika wani botiki ta jik'asu. harda waɗanda ke da d'igo'digon jini.
.
Cikin gaggawa nake aikin ina addu'ar neman tsari daga sani aikin wankin wannan annakiyar ƙazantar, dan ni kaina ma da yaya nake wanke nawa in ina cikin halin al'da cikin k'yank'yami nake aiwatar da komai, da audugar mata nake aiki a lokacin ba zan manta ba muna zaman lafiya da abbansu, kafin ma audugar ta ƙare shi da kanshi ya siyo min wata.
Sai dai ma nabawa maryam ɗin in tazo, sai daga baya da rayuwa ta juyamin dole tasa nake amfani da tsumma ina wankewa, duk da irin k'yank'yamin da nake ji nawa ma kenan bare na wani.
*_😍MAMAN 'DAN ALBARKA CE_*😍✍